Showing 12001 words to 15000 words out of 148334 words

Chapter 5 - SO KO ABOTA BOOK COMPLETE BY Maman Nurool-Huda.doc

27 Sep 2025

2915

yake da mugunta?wanan ai mugunta ce ba komai ba da cin zali karki damu sai allah ya saka Miki"

Kuka zeenat keyi ga yatsun hanunshi ya kwanta a fuskarta har ya tashi abinka da farar mace

Kuka take sosai me shago na lallashi yace"Yi hakuri Yar nan ai dole kiyi kuka wanan mugunta haka"

Gajiya yayi ya koma shago domin taki yin shiru tafi 1hr tana rera kuka,duk wani d'oki da farin cikin zuwan aikin babu shi

Wayarta tayi Kara ta d'anga sir Sameer ne sheshshekar kukanta da yaji ne yasa shi cewa subhannallah friend kina Ina??"

Cikin kuka tace"kayi hakuri sir bazan iya aiki a kamfanin ku b....."

Bata karasa ba yace"what are you saying zee,after all the effort I put in place just kawai in baki aiki you want to turn down the offer meya faru suddenly???'

Cikin kuka ta zayyane me komai,ran Sameer ya mugun b"aci me yaron nan yake takama dashi ne da yake take kowa Yana zaluntar mutane

Cewa kawai yayi ganinan fitowa"

Ba ayi minti goma ba sai gashi ya fito da kafa ya tsallako,ranshi ya b'ace ganin inda fuskar nata ya tashi gashi tayi jazur d'anga skirt dinta tayi tace"har wuta sigarin shi yasa ya Kona ni me nayi me ya tsane ni haka,wallahi tsanata ce karara a kwayar idonshi "

Rintse Ido Sameer yayi jikinshi na rawa ya Kama hanunta tare da d'aukar d'an kwalinta da jakar ta ya Fara janta

Tana cewa Ina zaka kaini be kulata ba ya fara janta

Cikin tashin hankali tace"Ina zaka kaini?"

Be kulata ba sai cikin office a reception ya tsaya Yana cewa Ina kake looser?Ina kake shaheed ka fito dan ubanka yau zanyi placing dinka a inda kayi belong to "

Ihun da yakeyi ne ya jawo hankalin jama'a duk suka fito wasu ma leke daga office dinsu domin wanan ba sabon abu bane a gunsu sun saba fad'a ko kad'an Basu jutuwa kamar ba Yan uwa ba"

Zeenat da ta gan abin yayi zafi ta Kama hanun Sameer tace"dan girman Allah kayi hakuri ka bar maganan nan bawai na fad'an maka dan in had'an ku bane ka bar maganar please"

Duk abinda Sameer keyi shaheed na kallonshi a tvn office dinshi domin Yana iya kallon wajen office din akwai camera

Murmushi gefen baki yayi yace"mahaukaci kawai ai bansan akwai abinda zanyi amfani dashi dan ya fusata ka haka ba sai yau,toh miye tsakanin shi da yariyar kodai?hmmm Ashe Zan jefi tsunsu biyu ne da dutse d'anya, Sai Kuma ya kyalkyale da dariya harda tafi yace"kin zama weapon da zanyi amfani dashi dan cin uban shi bari dai mu gan iya gudun ruwansa"

Kallo yayi Yana jin nishad'i duk wani haukan da Sameer keyi Yana kallon da inda zeenat ke Bashi hakuri ya bar magana

Yace"shegiya me Ido Kamar kwarurun lahira"
Gani yayi Sameer ya
Jata Yana haurawa da alamun office dinshi zaizo

Mikewa yayi ya cire suit dinshi ya rage shi da rigar ciki ya cire necktie din ya fita

Karo sukayi yayi murmushi rainin hankali yace"


Maman Nur
[6/23, 1:08 PM] +234 703 129 7709: =?D?=?D?=?D?=?D?=?D?=?D?
*SO KO ABOTA*
=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?
By maman noorul
Hudah

Wanan littafi na kudi ne d'ari uku ga Mai bukata zai tura naira d'ari uku ta wanan asusun banki Aisha Mohammed
0092544083
Acess bank
Ko katin mtn,domin niman Karin bayanin a min magana ta wanan number via watsaap 09090112846


Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"Wai meke faruwa ne nike Jin haushin Karnuka haka?"

Ba karamin Shaka Sameer yayi ba,watoh shi yake Kira Kare indirectly"

Wani kallo Sameer ya jefa shi dashi zuciyarshi na suya rainin yaron Nan ya Fara wuce Gona da iri,yace"me Kake nufi da kana ta Jin haushin Karnuka?"

Sir Shahid ya saki wani kasataccen murmushi ya jingina da kofar office dinshi yayi crossing legs dinshi yace"Kai meyasa kai dakiki ne?baka da tunani ne ko ka manta nan office ne ba market square ba kana damun mutan......"

Be karasa ba sir Sameer ya jinjina kai yace"shahid are you high ko ka Sha kwayar da ka Saba Sha ne kafin ka zo office karka manta ni yayanka ne Kuma Ina da shares a kamfani I can do as I plea......"

Shima sir Shahid katseshi yayi da cewa"and iam the c o e which means ni ke da highest share my friend ka fad'a min meya kawo ka buiding dina, I have better things to do"ya Kare da yiwa Sameer kallon banza

Satar kallon zeenat yayi sai ta b'oye bayan sir Sameer jikinta na rawa

Iya Shaka Sameer ya Shaka yace"na zo ne in ji dalilin dayasa ka daki Yar mutane harda konata"

Fuska d'aure Shahid yace"make your self clear sauri nike,ni ban fahimce ka ba"

Jawo zeenat Sameer yayi gaba yace"me tayi maka ka Mata mugunta ko kwayar da kake Sha ne ya Fara tab'a ka?"

Wani kallo ya watsawa zeenat dayasa tayi baya yi yayi kamar yanzu ya ganta yace"keee me kike a wanan office din ashe ba na miki warning bana son in Kara ganin ki a building din nan ba?"

Zeenat ta tsorata iya tsorata jikinta na b'ari ta koma bayan Sameer ta Kama me Riga tace" mu wuce wallahi mugu ne beda. ....."

Bata karasa ba Sameer ya Kuma jawo ta gaba yace"Kai nike saurare me tayi maka ka dake ta"

Shaheed ya shafa suman kanshi daya Sha gyra cikin ko in kula yace"ko zaka Rama Mata ne?"

Sir Sameer da Rai ya Riga da ya b'ace ya kalli staff duk an taru ana kallonsu hakan ya Kara ingiza shi yace"baxan rama Mata ba, ita zata Rama da kanta Kuma in ka cika d'an halak,dan gidan ku ka Mata wani Abu"

Wani murmushi rainin hankali Shaheed yayi yace"Ina jira ta ramar, yau ko Zan baka mamaki "

Zeenat ko kallon Sameer tayi tana girgiza Kai fuska d'aure yace"zeenat je ki wanka mishi Mari"

Zeenat ta girgiza kai tace"a barshi na yafe me,na hakura"

Shaheed yace"ubanwa ya baki hakuri da Zaki ce kin hakura Zo Mana ki rama"

Zeenat ta girgiza kai tace"ni ko ba a bani hakuri ba na hakura please friend a barni da Wanda ya min d'anzu wallahi wanan Karon zaifi na d'anzu Muni mu tafi kawai"

Sameer da idanunshi sun canza kala yace"zeenat ni nace ki je ki Rama marukar da yayi Miki Ina tsaye ba abinda zai Miki kije in kin d'aukeni da muhimmanci"

Shaheed dai rungume hanun yayi Yana kallonsu

Zeenat ta kalli Sameer ta gan fuskarshi d'aure tace"a dai barshi kawa......"

Katseta yayi cikin tsawa yace "wallahi ba za a bar shi in har kin d'auke ni da mutunci zeenat kije ki rama in ko Kika ki, bani bake daga yau karki nuna kin sanni"

Zeenat ta kalleshi jiki a sanyaye ta fara karasawa aiko Bata karasa ba Suka had'a Ido da Shaheed wani kwarjini ya Mata ga kallon da yake Mata na Allah ya baki sa'a ai da sauri tayi baya ta b'oye bayan Sameer fitsari ya kubce Mata

Tasleem tac???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?e"kin gan ta kanki"

Wanan abinda zeenat tayi ya b'atawa Sameer Rai ya so ne ta Rama yau ya nunawa Shaheed iyakar shi,yaro sai rashin kunyar tsiya"

Jawo ta yayi yace"for the last time ki je ki Rama ko Kuma ki hakur......"

Be karasa ba ya gan jikinta a jike sai ya ji ya karaya,tsaki yayi cike da haushi ya bar wurin

Shaheed ya bishi da kallo yana murmushi


Zeenat ta fashe da kuka takaici Wai sai yaushe zata daina fitsari a jiki in ta tsorata

Wani staff yace"Kamar fa fitsari tayi a jiki"

A fusace Shaheed yace"daga yau duk randa ya Kara zuwa kallon abinda ke faruwa zanyi sacking nashi bana son gulma"ai one by one sukayi ta barin wurin domin sun San halinshi ya tsani gulma har tasleem ma tafiya tayi ta bashi wajen ya rage su biyu

Zeenat na ganin haka ta Fara Jan kafarta har tayi nisa taji yace"ai nine ajalinki shashasha"

Bata juya ba ta karasa office din Sameer Aiko ya cika yayi Pam a gindin window ta ganshi tsaye Yana kallon waje sai numfashi yake saki yana goge hanci time to time,Yana sniffing

Rasa ya zatayi yayi gashi jikinta da fitsari

Gyran murya tayi,ya juyo Yana ganinta fuska d'aure idanunshi yayi ja yace"get out"

Zatayi magana ya katseta da cewa"I said out"

Kin fita tayi sai ma zuwa da tayi ta rungumeshi ta baya ya Fara kokarin b'anb'areta ya kasa domin gam ta rike shi

Da karfin tsiya ya turata ta Fadi cikin matsifa yace"na saki abu zeenat kin kiyi Dan ni kin raina ni,Amma shi ai kallo d'aya yayi Miki kikayi baya"

Cikin kuka tace"bar had'a Kanka dashi,wallahi ni ko Jin sunanshi nayi tsorota nike,mugu ne"

Wani kallo takaici yayi Mata yace"oh ni ne baki tsoro ko? maza tashi ki fita Kan ranki ya b'ace"zatayi magana yace"I said get out kina sa min najasa a office maza fita kin sa kanin bayana ya raina ni shashasha kawai"

Kuka sosai zeenat keyi tace" now you are sounding like him beyi suiting dinka ba,wallahi bazakayi kyau da vilain (mugu)ba"

Wani haushi ya Kara ji yace"get out before I called the security"

Cikin kuka cike da rashin kunya tace"ba inda zani wallahi if you like call the army bazan fita ba Kai ka ce mu Zama friend ai ba tilasta ka nayi ba Kuma a siyo min Kaya in canza tunda nayi fitsari a wancan ai lalura ce bani na d'aurawa kaina ba eheee"

Yace"Daman kin iya rashin kunya watoh ni Kika raina ko zanyi maganin ki ai,daga yau you are sack"

Tace"wallahi ban Koru ba sanda ka bari na ce na Sami aiki a gida watoh su min dariya ko?"

Komawa yayi ya zauna Yana tunanin me zai Mata,be Gama yanke hukunci ba ya gan ta shige toilet ta barshi da takaici,haushi Kamar ya kashe shi kansa sai ya gyara jikinsa tunda ta rungume shi

Ta dade Bata fito ba sai ji yayi tace"bakayi ordering Kaya ba?"dan lekowa tayi

Yace"banyi ba?"

Yatmusa fuska tayi tace"me kake jira toh"ganin kallon da yayi Mata ne yasa ta komawa ciki tana kunkuni

Da Kamar bazai Kira ba sai ya d'au waya ya Kira a kawo kayan

Tafi awa a ciki Taki fitowa har aka kawo kayan gani tayi an wurgo leda ciki ta zabura domin a zaune take babu Kaya jikinta

Tasowa tayi ta d'auki ledar yauma da inners wear

Sawa tayi ta fito tana kunkuni kasa kasa sai cewa take tun d'anzu an bar mutum zaune fin awa sai ka ce duniya za a siya me common dogon Riga

Be kulata ba shima ya shiga ya canza Kaya ko wanka yayi oho

Yana fitowa ya ganta zaune a kujera tace"toh a Kira cleaners su gyra wurin in ba Haka ba zarni zai dame ka,kasan na girma"

Kara d'aure fuska yayi sai ya bata dariya ita kanta ta rasa dalilin dayasa Bata tsoron shi

Be Kuma kulata ba ya Kira aka saftace wurin

Babu Wanda yayiwa wani magana tana zaune a kujera har lokacin lunch yayi ya tashi ya fita ya barta tana me magana ko kulata beyi ba yayi tafiyarsa

Tabe baki tayi ta mike da leke ta bar floor din a kasa ta tarar da tasleem

Tasleem tace"Sannu hajiya b'arnata ke da aka bawa chance ki mareshi maimaikon ki mareshi Kika tsaya Sanya da inda kike da b'arnan Kika me Mari ai sai an me surgery,ki b'arnata me fuska"

Zeenat tace"bar zance nan ai matsoroci akeyiwa barka jarumi sai jaje ni Ina nake da wanan jarumta ni kadai nasan me Nike gani a kwayar idonshi zeenat na magana tana dafa wani desk dake reception din ai ji sukeyi laptop ya Fado kasa na desk din kunle ne

Tasleem tace"kin fa tura laptop din

Jiki na rawa ta juya ta kalla tasa hanun akai kafin tasleem tayi magana kunle ya dawo rike da takeway din abinci ya d'auka laptop din yana dubawa yace"screen din ya fashe fa?ink din ya fito,ai sai ki biyo ni,muje office din sir shaheed ki me bayani domin bazan d'au asara ba sawa zaiyi a cire a salary na

Tunda ya ambaci sir shaheed jikin zeenat ke rawa sai rabka salati take tana kuka tace"inallillahi wa inailahi raji'un ya Allah ka taimakeni rabbi ka rufa min asiri duniya da lahira wayyo ni zeenat Inna baki kyauta min ba da nayi mugun gado"

Kallon kunle tayi tace"please ka bari ya cire ni Zan bada kudin gyra ka rufa min asiri Kamar inda allah ya rufa maka na shiga uku na lalace ni zeenatu ni nasan yankan rag...."

Bata karasa ba taji muryar dake razanan da ita yace"waye ke damun mu"

Ai wani uban tsalle tayi ta Haye saman desk tuni computers biyar suka Fado kass,wani irin ihu tayi jiki na b'ari tace

Afuwan my fans suna naje yanzu na dawo,da Wanda suka kirani text duk Ina godiya

Wasa farin girki we are still on free pages but an Fara biya vip is 500 me niman Karin bayani ga number ta=?I?09090112846

Maman Nur

Maman Nur
[6/23, 1:09 PM] +234 703 129 7709: =?D?=?D?=?D?=?D?=?D?=?D?
*SO KO ABOTA*
=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?
By maman nurul
Hudah

Wanan littafin na kudine d'ari uku ga Mai bukata za a tura naira d'ari uku ta wanan account number 0092543083
Aisha Mohammed
Acess bank,ko katin mtn domin niman Karin bayani ayi min magana ta wanan number=?I?09090112846


Bismillah Rahmanir Rahim

Hankalin zeenat ya mugun tashi tace"kayi min rai Yaya shaheed wallahi nayi nadama kome ma ka ce inyi zanyi ka ji na rantse maka wallahi lalura ce gado ta nayi daga gun Inna itama fa sanda tayiwa kakan mu b'arna sosai wallahi jininta ne da wanan aiki a tarihi ma ance agogo shi sunfi d'ari tana b'atawa wallahi kaji na rantse maka har yau in ta d'auki agogon hanun mutum daina aiki yake,ka rufan asiri ai ka gan ba laifina bane"

Kunle ya saki Baki Yana kallonta

Tasleem tace"assha kin ko yi mugun gado "

Shidai crossing legs yayi Yana kallon ikon Allah Yama rasa me zaice,
zeenat tayi ta yarfa hanun tana ruzgar kuka

Yafi minti 10 Yana tunani kafin ya daka Mata tsawa yace" keee Zaki sauko ne ko kuwa?"

B'are baki zeenat tayi ta saki ihu tace"Rai fa nace ka min,na roke ka dan girman Allah ka rufan asiri Ina tsoron gamuwata da kai ni nasan bazaiyi kyau ba, ka min rai ka bari in shiga toilet wallahi zawo zata kufce min"

Wani murmushin takaici yayi yace"Zaki saukone ko in sa security su sauko min dake"

Zeenat ta girgiza kai tace"tasleem ki bashi hakuri please ni nasan za a iya samun matsala wanan karon in ya damke ni,wallahi Ina wani hali"

A tsawace yace"Zaki sauko ne ko kuwa"

Kuka ya kubce Mata tace"Zan sauko da kaina kayi hakuri please"

Saukowa tayi ta ji Mararta ya wani rike nishi kad'an zatayi fitsari ya fito

Tace"na yarda Zan bika office amma please ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login