Showing 57001 words to 60000 words out of 148334 words

Chapter 20 - SO KO ABOTA BOOK COMPLETE BY Maman Nurool-Huda.doc

27 Sep 2025

2926

ba na haramta Mata zama tare da dukkanin biyu bazan yarda ta Zo ta b'ata Mana zumunci ba,dan Haka tunda ka aureta ka rama abinda akayi Maka ai yanzu sai ka Kai Mata takardan shima Sameer din ba Bari zanyi ya aureta ba kowa ya rasa"

Shigewa toilet yayi ya had'an ruwan zafi ya shiga, ya ji Dadi ruwan sosai sanda ya gasa jikinshi sanan yayi wanka ya fito ya tsaya gaban mirrow Yana ganin inda fuskarshi ya kumbura ba komai ke Bashi haushi ba sai inda zeenatu ta rungume Sameer da aurenshi akanta,rike Kai yayi yace"I have to take action dole in har a gidan Nan zamu zauna inyi bacci da ido daya in ba haka ba za a gama latse min mata"

Towel ya d'aura ya fito ya gan Mami na zaune inda ya barta gaban mirrow yaje ya Fara shafa Mai

Mami tace"Wai Ina zaka balarabe tara fa tayi Ina zaka?"

Be ce komai ba ya cigaba da abinda yakeyi Yana Gama shafa Mai din yaje gaban wardrobe ya Ciro Kaya yasa
. Mami ta mike tace"baka Jin Ina maka magana ne balarabe ga abinci ka ci ka kwanta ka huta"

Ganin fita zaiyi yasata ta mikewa ta Kama me wando tace"babu inda zaka"

"Mami ki Bari Mana bana son Haka fa ko in cire Miki wandon ne?"

Sake wando tayi tace"ni nasan zaka iya fisateare kuma nasan fitar Nan taka ba ta alkhairi bane Kai meyasa baka da yafiya I agree Sameer yayi loosing temper dinshi yayi abubuwa da Basu dace ba Amma ai ko Kai shaida ne ba halin Sameer bane ni Zan iya shaida Sameer akan bashi da wani mugun hali balle yayi kissa abinda Kayi me yasa ya aikata abinda ya aikata so mu bar maganar please"

Ba tare da yayi magana ba ya Kama hanya waje Mami ta Kuma Kama me wando
Kokarin janye hanun Mami yake a kugunshi amma Taki bashi dama

Cikin Jin haushi yace"Mami Zan tura ki fa"

Tace"me kake jira"

Da k'yar ya samu ya kubce ya fita da gudu ya bar gidan

Tace"Allah ya shirye ka balarabe"

Hanan tayi dariya,fitarshi da minti Sha bakwai sai ga Sameer ya dawo ya tarar da mami da Hanan a falo

Kallon inda Mami ke zaune yayi sai ya gan Bata kalleshi ba latse wayarta takeyi

Karasawa yayi inda take ya zube kasa yace"mami nasan ba abinda zance miki da zaki yarda dani domin ni d'in me laifine Amma ina rokon ki dan darajar annabi ki yafe min mamina iam sorry for everything"

Mami ta d'ango ta kalleshi sai kuma ta sauke Kai hawaye cike da idonta shima din hawaye yakeyi tace"da a ce khadijat ne zaka iya sa Mata bindiga aka??"

Kuka ya fashe dashi Yana girgiza Kai yace"Mami don't said that kema kin San sharri zuciya ce Amma bazan tab'a gangancin yi Miki abinda nayi ba iam sorry Mami"

Tace"yanzu sai miye nan gaba domin nasan yakin be Kare ba shi ba yarda zaiyi ba Kai Kuma biye Masa zakayi,ya fita kome ya fita kullawa oho "

Sameer yace"Mami kiyi hakuri for your happiness Zan danne zuciyata kuma na yafe Masa inshaallah bazan kuma biye Masa ba domin bana son b'acin ranki Kuma ni yanzu ma bani da lokacinshi bincike mutuwar daddy ya dameni Mami I don't know Ina ji a jikina kashe shi akayi in baki manta ba a ranan ya Kira ki ne yace akwai maganar da zai fad'an Miki I feel akwai connection tsakanin mutuwar iyayenmu da Kuma daddy"

Fuska d'aure Mami tace"wani daddy?"

Yace"Abba su Amira mijinki ammi"

Ammi tace"toh in ina da muhimmanci a gunka karka Kara d'auko maganar bincike s bana son ji"

Mikewa yayi shima ranshi b'ace yace"Mami wanan karon bazan yi miki biyyaya ba that man kamar mahaifina yake and I will not rest sai na kawo duk wani Wanda yake da hanun a mutuwarshi to justice that I promise you"

Tace" kenan ban Isa da Kai ba kaima"

Yace"ba maganar Baki isa dani bane Mami in zaki fad'an min dalilin ki na rashin sonyi bincike wallahi Zan hakura Amma wanan kwanar bazai taimaka ba I mean Mami mijinki ne fa baban ya'yanki ke ya kamata ki tabbatar anyi bincike Amma kike niman Kau da zancen inda ban San halinki ba sai in ce kina da hanun a ciki kissan"Yana Gama magana ya shige ciki ta bishi da kallo yayi kwafa

Can dai da misalin karfe 10 sai Suka ji knocking Hanan taje ta bude tayi mamakin ganin Yan sanda

Tace"how may I help you?'

Yan sanda suka ce

Maman Nur
[6/23, 1:10 PM] +234 703 129 7709: =?D?=?D?=?D?=?D?=?D?=?D?
*SO KO ABOTA*
=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?
By maman nurul
Hudah

Wanan littafin na kudine d'ari uku ga Mai bukata za a tura naira d'ari uku ta wanan account number 0092544083
Aisha Mohammed
Acess bank,ko katin mtn domin niman Karin bayani ayi min magana ta wanan number=?I?09090112846


Suka ce we have the warrant to arrest one mr Sameer Mohammed Kabir"

Hanan tace"what?for what???"

Babban cikin Wanda kallo d'anya zaka musu ka gane babu alaman wasa a fuskarshi yace" please ko zakiyi Mana magana dashi in Yana ciki"

Hanan zatayi magana sai ga Sameer ya fito yace"Hanan su waye"

Matsawa gefe tayi sai ya Mika musu hanun Suka gaisa,suka ce Sameer muke Nima

Confidently yace"nine Sameer hope ba matsala?"

Officer ya Ciro wata farar takkada ya nuna me yace"it a warrant to arrest you domin wani me suna shaheed Mohammed yayi pressing charges against you for asault beating him and having an affair with his legally weded wife so I suggest ka Kira lawyer ka"

Sameer ya nuna kanshi,mamaki karara a fuskarshi sai Kuma abin ya bashi dariya yayi dariya takaici yace"kuruci dangin hauka in Banda abin shaheed ni brother shi ne,we can settle this at home,please officer ga wanan ya Ciro kudi ya Mika musu yace"it a family matter zamuyi settleling a gida he is my brother my blood my cousin,it just a misunderstanding"

B'ata fuska officer yayi yace"iam sorry Mr Sameer we are good citizen we promote fighting against curruption we don't accept bribe iam sorry zamu tafi da Kai"

Sameer yace"ok no prob muje"juyawa yayi da niyyar yiwa Hanan magana sai ya gan Bata Nan

Dawowa tayi da Mami da har ta kwanta,hanan ta Kira ta sai kawai tasa hijabi

Tace"Sameer meya faru Ina za a kaika?"

Yayi murmushi yace"shaheed yayi Kara na "

Ko chance din magana Basu bashi ba aka tasa keyarshi a mota Mami ta koma tasa takalmi sanan ta d'au key din mota ta bisu

Duk inda Mami taso a Bata bailing sameer abin gagara yayi ta Kira number shaheed yaki d'angawa,kin tafiya gida tayi ta zauna tayi tagumi hanya ba guduwa zatayi ta barsu ba yanzu ma maganar zuwa kotu ake ana Kuma binciken inda Sameer ya samu bindiga,godiyar Allah shi d'anya akwai licence

Gari na wayewa Mami ta cigaba da zirga-zirga ta Kira alhaji buba ya taho police station din shima yayi iyakar kokarin shi Amma ance baza a sake shi ba sai shaheed ya Zo

Mami tayi fushi ta turawa shaheed text akan in be sa an saki Sameer ba wallahi ba ita bashi

Da misalin karfe goma sai ga shaheed din ya shigo station din ya nad'an kanshi da bandage Wanda jiya babu shi duk cikin karawa wuta petir ne?"dashi da barrister aliyu ne

Suna had'a Ido da Mami ya tsuke fuska Suka Shiga office din d p o Nan fa shaheed yace"shi Allah baran be hakura ba kotu zai Kai Sameer ,

Mami ta wanka me Mari tace"wallahi balarabe ka fita a idona in rufe zanci ubanka in ka Kara magana"

B'ata rai yayi yace"toh ai gaskiya ne ke ba a gaban ki ya suman Dani ba so biyu Yana suman dani Kuna akan matata dan rainin wayau"

Sameer yace"shaheed da Ina son in fita tun jiya dana Kira lawyers Dina su fidda ni but na duba is not worth it we are family you are my brother drop this childishness before it too late

Tabe Baki shaheed yayi yace"in ka fasa Kiran lawyer naka ka Raina Allah,officer nidai abinda nike so shine ya fita daga harka matata eheeee".

Mami dai sai kallon shaheed takeyi shi Kuma yaki ya kalleta d p o yace"tunda d'an uwanka ne please kayi hakuri babu dadi irin haka for the sake of matan nan kayi hakuri tun jiya take nan"

Alhaji buba yace"shaheed as Wanda ya isa ya fad'an kaji Ina rokon ka please kayi hakuri please shaheed"

Shaheed yace"ok but karya Kara min irin Haka danni ba jakin shi bane da zai Kama yayi ta pounding duk lokacin da yake so Kuma a gaban matana so yake ta raina ni,Kuma ni gaskiya a fad'a me karya kuskura ya Kara kallon min Mata bana so"

Mami tace"tunda ita matar tafi mu ka tattara ka koma part dinka banso bala'i"

Yace"ba a komawa din, ai gida na ne sai dai shi Sameer din ya bar gidan"

Mami tace"officer bana fad'an maka ba? bashi da kunya hayaki da totulin sun b'ata me Kai baya ganin kowa da daraja nifa a matsayin uwa Nike a gunshi Amma Baya gani na da gashi"

Murgud'an Baki yayi kamar wata mace yace"ai tunda ba ke Kika haifan ba da sauki"

D p o yace"kaima daga yau in ya mare ka ka Rama Kai ba namiji bane?"

Yace"ni namiji mana Amma ban cin tuwo,shiyasa yake iya dukana"

Sosai sukayi dariya harda Sameer Mami ce ta tsuke fuska tana me wani kallo"

Sa hanun yayi a saki Sameer Suka fito suna kallo ya Kara gaba da barrister Aliyu gidansu zeenat yayi direct ya tarar da appa zai fita Nan ya tsaya ya tsarashi da karya da gaskiya appa yace",Bari in Kira ku tafi "

Yace"ya gode Amma Bari ya Shiga ya gaida Inna"

Zuwa yayi b'angaren Inna ya tarar da Rabi'a na shara ta ajiye tsinsiya ta gaidashi ya amsa cikin sakin fuska yace"Baki je school ba?_

Tace"ban da lectures yau"

Ya jinjina Kai yace"Ina Inna?"

Tace"tana ciki ba lafiya tun shekaran jiya"

Yace"ok Bari kawai inje Kar in tada ta"

Rabi'a tace"in ta tashi Zan fad'a mata ka Zo "

Yayi murmushi,b'angaren Inna ko tana jinshi amma ta Kuma lullbewa ita Bata son ma abinda zai Kara had'ansu"

Ko da ya koma har zeenat ta fito da appa sanye da hijabi har kasa

Appa yace'gata nan Dan Allah a kula dukda bata sanar damu abinda ya faru ba"

Godiya yayi ya Kama hanun zeenat din suka tafi mota

Zama tayi a gaba tana Wasa da yatsunta

Ya kalleta yace"waye yace"ki dawo gida??"

Zeenat ta marairaice tace"Mami ce ta koreni?"

Be Kuma magana ba ya ja motar da gudu ita tsoro ma take ji haka yake driving dama? lumshe Ido tayi ya budesu tace"ya jikin?"

Banza yayi Mata itama sai ta ja bakinta tayi shiru har suka Kai gida babu Wanda yayi magana"pakawa yayi Suka fito ya Kama hanunta suka Shiga ciki"

Su Mami ne zaune da Sameer Mami na me nasiha sai ga shaheed ya shigo rike da hanun zeenat,kallo d'anya Sameer yayi musu ya d'auke Kai"

Shaheed ya karaso yace"Mami Mami!!!!share shi tayi sai yayi murmushi yace"kin gan na je d'auko matata ko?"

Zeenat dai a takure take ta samu wuri ta rakube Hanan ta kalleshi tace"ya balarabe baka da mutunci wallahi "

Yace"yariyar Nan kin kusa dakuwa,nidai Bari in shiga ciki da Matata Kar a Kare Mata kallo sameer ya ji zuciyarshi ya buga Yana zafi kawai sai ya mike ya shige ciki Yana jiyo shaheed na Waka,wanne wanne ne,wani ko sai wani,wani sai d'an wani,kaiko d'an wanene?kwarya ta bi kwarya in ta hau akushi Bata maruwa"

Mami ta saki baki tana kallonshi tace"ah lallai balarabe ya ji hausa zaka ci gidanku wallahi Dani kake zancen"

Kama hanun zeenat din yayi suka shige

Zama tayi bakin gado tana kallonshi

Yace"Ina jinki?"

Marairaicewa tayi tace"sir me kake so in ce ai Kai ya kamata ka rama bani ba"

Cikin matsifa yace"ai tun kan mu fita nace Miki da yayi yunkurin tab'ani ki Shiga tsakanin mu Amma saboda bakin Hali Kika tsaya Kuma Dan iskanci da aurena a kanki Kika rungume d'an iska a gabana"

Zatayi magana yayi kamar zai Kai Mata naushi tayi baya

Yace"nafa kusan zubar Miki da hakora kin ji na rantse Miki da Allah duk Randa na kama ki kin kalleshi sai na kashe ki kuma hijabi zakiyi ta sawa"

Tace"toh"

Ya d'aure fuska yace"jita kamar albino "

Tace"kayi hakuri please bazan Kara ba '

Yace"kima Kara jita kawai "sosai yake matsifa Yana cewa"simple instructions you cannot follow in kin gan zai dakeni ki shiga tsakanin mu kin wani tsaya kamar ice watoh ya kasheni"ya Kare Yana shiga toilet zeenat Bata San lokacin da murmushi ya sub'uce Mata ba,da alamu rashin shiga tsakanin nasu ya b'ata me rai

Beyi minti biyu ba ya fito ya tarar tana latsa waya,tana ganinshi ta d'an firgita shi Kuma ya d'auke Kai kamar beyi noticing komai ba,ajiyar zuciya ta sauke ta mike

Yace"Ina zuwa?"

Tace"fitsari zanyi"

Ya jinjina Kai"

Zeenat na Shiga toilet ta tura Kofa tayi murmushi tana replying Sameer tace"iam happy zamuyi ta ganin juna kullum I miss u my Sameer"

Shiko tana shiga ya makale a kofa Yana leke Aiko a tsaye ya hangota rike da waya

Ya jinjina Kai ta dade a haka sai taji yace"in kawo rezor ne mu yanka mahaifan?"

Firgita tayi tace"yanzu Zan fito"

Fitowa tayi yace"kwanta kiyi bacci tunda Baki da lafiya"

Zeenat ta kwanta shima ya kwanta domin zazzab'i yake ji"

Lura tayi da yayi bacci sai ta d'au waya ta Kira Sameer Yana d'angawa tace"hau watsaap"juyawa shaheed yayi sai tayi saurin b'oye wayar sai Kuma ta gan baccinshi yake

Chatting suke tana ta smilling

Da misalin 6:pm ya tashi domin wani nauyayan baccinr ya d'aukeshi ai sai ya gan wayam Bata gado

Zubur ya mike Yana rike Kai ya duba toilet Bata ciki ya Zo zai fita ya gan wayarta sai ya d'auka zai bude ya gan key tsaki yayi ya rasa ya za ayi ya bude sai kawai yasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login