Showing 24001 words to 27000 words out of 148334 words

Chapter 9 - SO KO ABOTA BOOK COMPLETE BY Maman Nurool-Huda.doc

27 Sep 2025

2911

shi"kuka sosai Mami keyi tace"Yaya Kabir Baku kyauta min ba miyesa nima mutuwa be d'aukeni ba in huta kamar ku ai da ban gan wanan ranan ba"

Maganganun Mami ya daki zuciyar Sameer Dan haka ya bar wurin Yana regretting meyasa ya biyewa shaheed gashi zuciya ta d'ibeshi ya sumar dashi,abinda yake gudu kenan tuntuni Amma yaki ganewa

Hanan tace"Mami asibiti ya kamata mu kaishi baya fa numfashi

A fusace Mami tace"toh ya kike son inyi ni ban aikeshi ba,yaron nan baya Jin maganata abinda ya gan dama shi yakeyi daman Wanda be ji Bari ba ya ji oho"

Kiran ambulance akayi aka d'auki shaheed Kamar gawa suna zuwa likitoci suka Fara bashi taimakon gaggawa,drip aka same da wasu allurai akayi treating ciwonshi

Zeenat dai tsoro ya hanata fitowa,tama kasa tashi sai kuka

Sameer ko rike Kai yayi a hankali abinda ya faru ya Fara dawo mishi na inda sukayi ta janta da sauri ya fito ya zo inda abin ya faru babu zeenat

Ya Shiga office din shaheed ba zeenat ya duba ko Ina har zai fita ya dawo ya d'anyi danne danne a laptop dinshi Wanda ko 2minit beyi ba ya fita yaje department dinsu tasleem ya tarar dasu tsaye suna gulma suna ganinshi kowa ya koma desk dinshi

Fuska d'aure yace"ke Ina zeenat?"

Tace"tana can ta kulle kanta a toilet din 4th floor da alamu jikinta ciwo yakeyi na buga taki budew...."

Be jira ta karasa ya bar wurin

Yana kaiwa yayi ta bugawa yace"zeenat bude please Sameer ne iam sorry nasan kina jina

Ganin bata da niyyar budewa Kuma Yana Jin sheshshekar kukanta yasa shi cewa in baki bude ba zeenat Kika Bari na bude da kaina in na shigo sai nayi kasa kasa dake"yasan ta da tsoro yanzu zata Bude

Aiko budewan tayi tace"Yi hakuri"

Kallonta yayi sai ya ji tausayinta ga rigarta a yage ya hade hannayensa ya zube akan kneels dinshi yace"iam sorry zeenat please forgive me ,please karki min kallon d'an tasah wallahi bazan juri a ci Miki mutunci bane,wallahi da Kika daina kulani Baki ji tashin hankalin dana shiga bane,ki yafe min"

Zeenat cikin kuka tace"Ashe kasheni zakayi kun b'alla min hanun kun barni da asara"

Be jira ta karasa ba ya mike ya rungumeta tana kaime bugu a kirji Amma be kyaleta ba harta gaji ta lafe jikinsa,d'aukarta yayi sai office dinshi ya ajiyeta a kujera yace"kin San kuwa inda naji da Kika daina kulani friend karki Kara in ba Haka ba wallahi mutuwa zanyi"

Kura me Ido tayi yace"tunanin me kike"

Tace"be dai mutu bako?"

Yace"miye damuwarki ko ya mutu?"

Tace"tabbas bazanji ba dadi ba in har ya mutu,amma ba Zan so a ce Kai ka kashe shi ba domin bazan so ka je gidan yari ba"

Wani dadi sameer yaji da besan ko na miye ba yace"toh meyasa?"

Tace"saboda Kai abokina ne?"

Yace"kina nufin Kin yafe min?"

Tace"eh ya wuce Allah ya kiyaye gaba"

Yace"karki damu in ya dawo bazai Kara shiga harkakin that I assured you"

Zeenat ta shafa gefen fuskarshi tace"thanks"

Ya Kama hanunta ya Kai Baki yayi kissing sai tace"ashhhh"

Yace"Sannu Bari in ja miki"

Ja yayi yasa aka nimo musu aboniki tana kuka ya shafa Mata, ya Kira aka kawo Mata wani Kaya ta shiga ta canza

A lokacin lunch wani babban resturant ya kaita Suka ci abinci sanan suka dawo dukda idanunta ya kumbura Amma ta sake dashi suna Hira sosai beyi aiki ba yau sun manta wani shaheed

Lokacin tashi ya kaita gida da kanshi

Tana shiga gida mama tayi ta kallonta Amma Bata ce komai ba bari tayi ta shiga ciki sanan ta bita,lokacin aiki ake a gidan na abinci

mama ta gan tana cire Kaya tace"zeenat magana Nike so muyi

Zeenat ta juyo ta kalleta tasa hijabi ta zauna a kasa mama na bakin gado

Mama tace"zeenat meke faruwa ne?na gan kullum kayan da Kika fita dashi ba dashi kike dawowa ba,kina aikata wani Abu ne da bamu sani ba?'

Hawaye ya cika idon zeenat tace"wallahi mama ban tab'a aikata abinda Zan cuce kaina ba ko in ci amanar ku,wallahi wacan ranan ogana ne yayi min ihu na tsorata na saki fitsari jiya ma Haka shine sai ya siyo min wani Wai babu kyau zama da najasa,yau Kuma dambe akayi naje rabawa shine aka yaga min Riga ya siya min,kin gan ma hanun na har Ciro na ji'ta Kare da nuna Mata hanunta"

Mama tayi murmushi tace"oh har can Kika Kai sakarcin naki kina musu fitsari a jiki?'

Zeenat tace"nifa Ina ganin lalura ce"

Mama tace"iskancin dai toh miye tsakanin ki da ogan naki da yake siya Miki Kaya masu tsada Haka?"

Zeenat tace"mama abokina ne fa,we are just friends"

Mama tace" *SO NE KO ABOTA*? "

Zeenat tace"Abota ne mama"

Mama ta mike tace"kiyi ta yaudarar kanki nidai shawarar da Zan baki shine ki Kama mutunci kanki karki bari ko wani namiji ya yaudare ki da abin duniya,in sonki yake ya Zo gida a ajiye magana bawai kuyi ta b'atawa juna lokaci ba"

Zeenat tace"inshaallah mama nagode da kulawar ki"

Mama tace"ni na tafi "tana fita zeenat ta cigaba da cire kayanta tana tunanin tambayar Mama"

Zaune suke suna cin abinci Inna in ta Kai shinkafa sai ta Kora da fanta ga tulin balangu gabanta,zeenat na taya ta ci sun Hana kowa

B?yan an Gama ci Yaya jafar da ya Aminu suka fita

Yaya aminu yace"Da ka tsaya kana Sanya bayan kasan da balangu zaka Gama da Inna,ballagu dubu ya biya maka bukata yanzu ka fad'a mata ko kuwa"

Yaya jafar yace"na Fara bin b?yan gida Ina Mata shi a dunkule Amma ban bayyana Mata ba so Nike ta jiku da balangu da fanta tukkuna in sanar da ita"

Yaya Aminu yace"ai in Inna ne akan balangu zata iyayin komai

Haka fa jafar yayi ta kaiwa Inna balangu da fanta aiko yanzu tana mugun yinshi

Yau dai ya fad'a Mata zuciyarshi shifa zeenat yake so aiko ta amince tasa aka Kira su Abba tace"in ba aurawa jafar zeenat ba zata shiga duniya"

Da appa ya nuna Kin amincewa sai ta fashe da kuka tace"basa girmamata

Abba yace"ni abinda ban gane ba ita zeenat din tana son jafar din ne?"

A fusace Inna tace"Kai dana auri ubanka Sona yake?be ma kamata a ce Kuna wanan surutan ba zumunci za a had'a fa yanzu duk duniya zeenat zata Sami miji daya fi jafar ne?"

Baba ya nuna amincewarsa Amma appa yace"ba zai yiwu ba domin ba ayiwa Maryam adalci ba in auren zai Kara ya Nima a waje Mana Amma fa duk ana gida daya

A lokacin da Maryam ta samu labari hauka ta tada tana zagin ummi Wai asiri tayi ummi Bata tanka ba,hakan yasa umma fushi tace"aure kamar anyi an Gama ba fashi

Shiko jafar Shurun su appa ke d'anga me hankali,domin har yanzu Basu ce komai ba

Duk wanan abin, zeenat bata San ma anayi ba domin yanzu in ta fita aiki sai yamma wani farin ciki take ji in suna tare da Sameer gashi ba shaheed Yana asibiti

Sosai suke cin karansu ba babbaka Sameer bayayin wani aiki sai hira da yawon zuwa rasturant

Tunda abin ya faru beje gida ba baya son had'an Ido da Mami sai yau

Hanan ce kawai a gida a falo tana kallo

Yace"Ina Mami?"

Tace"tana asibiti kasan ba a sallamo ya balarabe ba"

Ya shafa Kai yace"Hanan iam sorry wallahi I lost my temper ne but it won't happen again"

Tace"nasan ya balarabe ke farawa but beating him to that extend I didn't expect it from you,I mean d'an uwanka ne your blood meyasa zaka biye mishi"

Yace"but I said iam sorry"

Tace"it ok yanzu Ina sis in law Dina zeenat "

Yace"yaushe ta Zama sis in law d'inki"

Tace"like seriously,kana son fad'an min har yanzu baka San kana sonta ba?stop deceiving your self wanan *SO NE BA ABOTA BA* tunda akanta zaka iya dukan Dan uwanka besides na gan soyyayarta a idonta so is better ka sanar da ita kafin wani yayi wuf da ita

Ta Kare da mikewa ta shige kicin

Sameer ya kasa motsawa Yana juya zancenta ya dade a Haka kafin ya saki murmushi yace


Maman Nur
Maman Nur[6/23, 1:09 PM] +234 703 129 7709: =?D?=?D?=?D?=?D?=?D?=?D?
*SO KO ABOTA*
=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?
By maman nurul
Hudah

Wanan littafin na kudine d'ari uku ga Mai bukata za a tura naira d'ari uku ta wanan account number 0092544083
Aisha Mohammed
Acess bank,ko katin mtn domin niman Karin bayani ayi min magana ta wanan number=?I?09090112846


Bismillahir Rahmanir Rahim


Murmushi yayi yace"yes iam in love with zeenat,it love not friendship"rufe bakin shi yayi da tafukan hanunshi yace"can't believe this"

D'ankin shi ya nufa ya gan wuri da dan kura domin shi baya bari a shigar me d'anki unlike shaheed dake da almost 3savant masu gyra me d'anki


Da kanshi ya Fara gyran wurin ya d'au more than 40minit Yana aiki Yana Waka nimenj baby Ina kwana, baby Ina gajiya Rabin raina.......da alamu Yana Jin dadin aikin,bayan ya gama ya shiga wanka ya fito cike da farin ciki wando bakin jeans yasa da blue Riga polo

Ya fashe jikinshi da tularai sanan ya fito ya zauna a dining Hanan ta me serving abinci ta zauna tace"Yaya Amma asibiti zaka ko?"

D'an jimm yayi na d'an lokaci sai Kuma ya cigaba da cin abincinta

Hanan tace"look Yaya ka tafi asibiti in ba Haka ba Mami bazata ji dadi ba tun randa abin ya faru Mami ke kuka tana kiran sunan su Abba akan meyasa zasu mutu su barta da ku,shin Wai Kuna da wasu ne Banda Mami in kuka kasheta fa mune da asara,Kai ne babba ya kamata ka Fara Jan Yaya balarabe a jiki shi bazai tab'a saukowa dan ku shirya ba number one matsalanshi girman Kai,2,ga shegen taurin kai,3 a lokacin da ka bashi 5 shi tunanin shi ya baka ashirin Kai ka sani but as Yaya Kaine ya kamata kayi ta Kau da Kai akanshi please,bawai Ina Goyan bayanshi dan ya'lyana bane no dukkan ku biyu Ina sonku "

Sameer yace"but Hanan ya dace balarabe ya raina ni inda yakeyi,tun muna Yara yaron Nan ba gan abin raini ba in ba ni ba,ki duba fa tun iyayenmu na Raye abbana yayi ta cewa Kar in biye mishi a ce har yanzu bazan huta ba,yaro ya maidani abin wasanshi"

Hanan tace"in zaka Fadi gaskiya babu Wanda ya balarabe be Raina ba,kasan irin gata da ya balarabe ya samu,mummy ta me gatan da baya ganin kowa da gashi akai mummy ce ta nuna me kowa Kashi ne Kai ka sani ai,ita ta b'ata shi gashi ta mutu ta bar mu da wahala"

Yayi murmushi yace"Hanan Ina son shaheed Amma halinshi ne bana so,bani da Wanda ya fishi ,shi ya gode Yana dake Amma nifa nikadai ne ba kani ba yaya"

Hanan tace"ni Kuma fa?"
. Karan hancinta ya ja yace"hakane Ina dake Yar balarabiyar kanwata"

Duk sukayi dariya yace"Dana tashi zanje asibitin na dubashi Zan Kuma bashi hakuri inshaallah hakan bazata Kara faruwa ba"

B?yan yayi nak ya mike ya d'auki makullin mota ya fita,asibitin da aka Saba kaisu in Basu da lafiya yayi yasan Yana can

Cikin fadiwar gaba ya karasa word din da nurse ta nuna me

Da sallama ya tura Kofa Mami ce zaune tana bawa shaheed abinci sai shagwab'a yake zubawa

Fad'an take me sosai tace"balarabe kashe kanka zakayi kenan ko,ka ce ni ban Isa in hana ka ko in saka ka ba toh Ina tabbatar maka wata rana mutuwa zakayi a banza,yanzu ba ciwukan sun warke ba saura gobe ka Kara niman fad'an shi wallahi kashe ka zaiyi a banza ai Yana ma kokari in ba dan yana Kau da idanunshi ba saboda ni ai da tuni ya hallaka ka,Kai ka ce taurin kai ba toh ka cigaba mutuwa zakayi a banza"

Zaiyi magana sai ya hango Sameer tsaye,ganinshi kawai yasa shi fashewa da kukan takaici haushi yake ji Wai a ce Sameer ya mare shi,gaskiya bazai yarda ba amma this time ta kasa zai soki zuciyarsa wallahi sai yayi nadamar d'auke me kwanaki goma na rayuwarsa kwana goma Yana asibiti

Kallo d'anya mama tayiwa Sameer ta d'auke Kai rabonta dashi tun a kamfani

Karasawa yayi ya duka yace"Mami kin tashi lafiya??"

Banza dashi tayi ta mike ta rungume shaheed dake kuka tace"wani wurin ke maka ciwo?"

Ya girgiza Kai yace"gida zani"

Jikin Sameer yayi sanyi yace"ya jikin naka?'

Shaheed yayi banza dashi

Sameer yace"shaheed iam sorry ban so Haka ta faru ba please forgive your big brother "

Shaheed ya kwanta ya rufe fuskarshi da wani bargo

Mami ta Jin dadin hakurin da Sameer ya bawa shaheed dan Haka sai ta saki fuska
. Ya Kama hanunta yace"Mami kiyi hakuri I failed you wallahi ya b'ata min rai ne,Amma henceforth bazan kara bari fushi ya Jani har in me Haka ba"
. Mami tace"Wai miye ma ya had'a ku ne?"
Sameer zaiyi magana shaheed yayi saurin bude fuskarshi yace"Mami zanje toilet"

Fuska d'aure tace"in Goya ka ne?"ta Kare da hararanshi

Mikewa yayi zaune yasa bakar takalmansa da ya haska farar kafarsa

Sameer yace"in taimaka maka ne"

D'angawa Sameer hanun yayi ya shige Yana jiyo Mami na cewa saura kayi abinda ka Saba ka zauna kayi ta zuge zuge ka a ciki wallahi tafiya zanyi in barka ka ji na rantse maka da Allah"

Murmushi yayi ya zauna a wc Yana jiyo hirar su da Sameer

Yace"zaka San ka tab'ani wallahi"

Kiran Aliyu yayi yace"please ya kawo Masa weed da sigari nashi ya Kare

Barrister yace"Wai ba a sallame ku bane har yanzu?"
. Yace"eh Ina ganin sai gobe ka fa San ba karamin duka d'an iskan yayi min ba"

Barrister yace"kaima kasan baka da karfi meye na tsokanar shi har kuyi dambe"

Yace"barni dashi kawai muna nan wallahi zaka gan martanin da Zan maida me,hmmm ai yanzu za a fara yakin badai Dan love din da suke da wanan sakarya ke tsole me Ido ba,Zan b'atashi ai"

Suna Gama waya ya fito Yana tabe Baki ya koma ya kwanta

Mami ta mike tace"Sameer jira ni Ina zuwa in shiga wan can d'ankin kanin shaheeda Jamil ba lafiya Bari in duba shi kaima in Zaka tafi ka duba shi,Dan Ina ganin gobe Monday za a salamme mu"

Yace"inshaallah Mami Zan leka su"

Tana fita Sameer yace"shaheed ko kayi bacci ne?let talk please"

Shaheed yayi me banza Sameer zai Kuma magana sai wayarshi tayi Kara

Dubawa yayi ya gan zeenat ce yana murmushi ya d'anga yace"ya dai my zeenat"ai kamar an daki kirjin shaheed ya bude Ido Yana leken Sameer da ya juya me baya

Sameer yace"lafiya Lau sweetheart ya aiki ya gida yau bamu had'u ba sai nike Jin Kamar bani da lafiya har d'an Rama nayi

Sosai zeenat tayi dariya tace"Allah ko Nima fa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login