Showing 108001 words to 111000 words out of 148334 words

Chapter 37 - SO KO ABOTA BOOK COMPLETE BY Maman Nurool-Huda.doc

27 Sep 2025

2904

Kin Zama baba yayi saboda inda zuciyarshi ke tafasa,Abba yace"bukar ka zauna inshaallah komai zai Zo da sauki"

Inna ta karbe zancen da cewa Ina ya gan ta Zama ko ni tashi zanyi bazan zauna ba sai an warware Mana komai"

Abba ya girgiza Kai yayi gyran murya sallama yayi duk aka amsa

Yace"kowa dai yasan rudani da muke ciki har aka Sami rashin fahimta da farko dai Zan Fara tambayar balkisu su wanene iyayen zeenat,ko Kuma in ce ya akayi aka sameta ?"

Mama ta d'ango kanta duk sai taji bata da karfin jiki labarin inda komai ya faru ta basu ta Kare da zubewa kasa tace"duk Wanda na b'atawa Rai ya yafe min,alhaji Dan Allah ka yafe min umurni tsoho na bi ka yafe min "

Kowa a wurin is in shocked har shaheed da ba first din Jin maganar ba kenan yace"kenan zeenat da Sameer Yan uwane?"

Appa yace"kuyi hakuri har yanzu zeenat na matsayin Yar mu babu abinda ya canza ko ba Haka ba zeenat

Zeenat ta mike ta rungume baba tace"baba ni yarka ce"

Appa yace"mashaallah kayi hakuri bukar mun b'oye maka umurni baba (Mai kanti) ne Kuma kaima kasan amanarshi "

Zeenat tace"toh Ina anty hafsat din?"

Appa yace"kiyi hakuri tana mental asylum Bata da cikaken hankali tun Randa ta haifi ki ta kamu da ciwon hauka mun dawo da ita munyi iya kokarin mu na sawon shekara goma Sha biyu Amma ba a dace ba yanzu shekara goma kenan da Muka maidata asibiti itace Wanda mama ke zuwa dubawa in kin ji tace zata asibiti "

Zeenatu tace"zanje in duba ta Nima Ina son in ganta please,itace Daman Wanda ke wancan d'anki muna Mata Waka da mu ke Yara "ta Kare da fashewa da kuka

Appa yace"eh "

Shaheed yace"ni nasan Sameer will be happy to know that he has a beautiful sister Bari in Kira shi "ya Kare da fito da waya zai Kai kunni mama tace"kul karka kuskura zeenatu Bata da alaka da Sameer ko d'anya

Mami tace"Kuma aka ce yar Kabir ce?"

Mama tace"ko shakka babu amma ai shi ba d'an Kabir din bane"

Mami ta b'ata rai tace"wace irin magana ce haka"

Murmushin takaici Mama tayi ta kwashe labarin komai ta basu,Mami tace"ah lallai tsintaciyar mage Bata mage yanzu wanan yaron dama Yana da hanun a Cikin kissa nan da ake Mana dan ya Raina mana wayyo ya dinga nuna shi bincike zaiyi Kuma a fili yake nuna ba ruwansa,aiko Ina komawa gida sai ya bar gidan Nan matsiyaci Mai halin fir'auna sai kuwa na wulakanta shi

Shi Shaheed ma kuka yake he can't believe Sameer fuska biyu gare shi hanya zai iya yafe Masa kuwa??dole ayi wani abu

Zeenatu tace"Mami Sameer ya wuce duk inda kike tunanin tantiri ne number d'anya korar shi inda kike tunanin bazaiyi aiki ba yanzu haka he has threatning to rape Hanan Kuma zaisa a sace Rabi'a Kuma babban burin shi ya kashe Shaheed

Ai tunda aka Kira sunan hanan ta zabura tace"na fahimta yanzu,ko shiyasa sai yayi ta rungumeni wani lokaci abubuwan shi har mamaki yake bani amma in nayi tunanin shi Yaya na sai in gan ai babu komai a ciki Ashe burin shi kenan"

Baba da duk jikinshi yayi Sanyi yace"toh miye abinyi??"

Zeenatu tace"nidai kawai baba a basu diamond dinsu a sallamesu Kuma Shaheed shima ya sallameni su je su ji da matsalansu bana son su,bana son alakar da zai had'ani da Kabir"

Tunda ta fara magana Shaheed ke Mata wani kallon yace" Inna wani kunu kuka bawa zeenatu ta Sha take hauka ko kunun dawa ne yayi tsami"

Inna ta fashe da kuka ta mike ta bar d'ankin tana cewa ba akyauta Mata ba gaskiya

Mikewa zeenat tayi tace"zaka gan hauka in na Kaika kotu"

Cikin matsifa da kunan rai yace"kafi kotu Zaki kaini,in baki kaini kotu ba kin raina uncle Kabir din dan bazan ce baba tunda Yana kusa,Kuma wallahi ki fito mu koma gida in ba haka ba zaki gan tijara kin ji na rantse miki da Allah,ka ji min birgagiyar yariya yau tayi hankali gobe ta botsera,today she is in love tomorrow she is out love Zan ko yi maganin ki,Ina ruwana da abinda uncle Kabir yayi ko a labarin kin ji ance Shaheed ko balarabe, da kike niman lika min laifin shi "

Matsifa kawai yakeyi dan zeenat ta b'ata me rai Mami tace"balarabe meyasa baka da kunya ne"

Yace"Mami in tsaya Jin kunya a cuceni kina fa jin rainin wayau da take son min wallahi Zan bata mamaki kin ji na rantse"barin d'ankin mama tayi

Shaheed ya tashi ya koma inda appa ke tsaye ya dafa shi appa ya kalli hanunshu dake kafadarshi shaheed yace"kana ji ko"

Wani tsawa Mami ta daka me tace"meyasa baka da hankali ne?"

Dawowa yayi ya zauna yace"appa na gan Mai kanti a inda suka kaini"

Su Appa suka zaro Ido suka ce Yana Raye?"

Yace"eh Yana Raye "
Wani farin ciki Suka ji Shaheed ya Fara Basu labarin inda sukayi da Mai kanti ya Kare da Yi musu godiya domin duk wanan matsifar da suka Shiga saboda family dinsu ne

Suna cikin planing inda za a ci uban Sameer called dinshi ya shigo wayar Shaheed

Shaheed ya d'anga yace"

Maman Nur
[6/23, 1:11 PM] +234 703 129 7709: =?D?=?D?=?D?=?D?=?D?=?D?
*SO KO ABOTA*
=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?
By maman nurul
Hudah

Wanan littafin na kudine d'ari uku ga Mai bukata za a tura naira d'ari uku ta wanan account number 0092544083
Aisha Mohammed
Acess bank,ko katin mtn domin niman Karin bayani ayi min magana ta wanan number=?I?09090112846

Book>??


Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"gashi Yana kira"d'aukawa yayi yasa a speaker

Sameer yace"ya naji ku shiru har yanzu,meke damunta?"

Shaheed yace"rabu da shirmemiyar yariyar nan nifa Ina ganin sallamarta zanyi in huta ka ji yariyar na niman raba zumunci karfi da yaji ashe gidan Mai taje wajen appanta tana cewa Kai ba d'an uncle Kabir bane so ma kake ka sace Rabi'a ka Kuma yi raping din Hanan maganganun dai ba Kan gado Wanda ko kad'an hankali bazai d'auka ba,shine iyayen suka kwabe ta harda Mata gargadin in ta Kuma fadin wanan magana sai sun tsine Mata toh kasan ta da shirme sai ta sume,Koda muka je asibiti sai ta tada hauka Wai in ban yarda da ita ba in bata takkadarta ka ju mahaukaciya harda cewa jiya a asibiti Kai ka d'auke key Kuma ka fad'a Mata da bakin ka Kai ka kashe iyayen m......"

Be karasa ba Sameer ya goge zufa yace"karya take wallahi ni ban san meyasa yariyar nan ta tsane ni ba yanzu"

Shaheed yace"aiko ta d'aura d'anmara yaki dakai tunda harda recording Tay....."

Da sauri yace"recording din me??"

Shaheed yayi wani murmushi gefen Baki yace"ai Mami ta fasa wayar tace"baza ji nonsense dinta ba,yariyar Nan tunda Muka shirya take hauka "

Ya wani sauke ajiyar zuciya ba tare da yasan yayi haka ba harda furzar da iska yace"nagode da kuka yarda dani"

Shaheed yace"Babu wani yarda ai gaskiya ne ya za ayi tace"Kai ba d'an alhaji bane sai ma ka gan inda iyayen nata suka ci kaniyarta maman tayi mugun fushi da ita Kuma tace"zasu Zo har gida su baka hakuri,amma dai nasan Kai ka d'auke key din ko?dan nasan zaka iya wanan "

Sameer a ranshi yace"kenan iyayenta Basu San komai ba toh Ina taji?"

A fili yace"ah'ah Basai sun zo ba,ku Basu hakuri please"

Shaheed yace"sauran bayanin sai mun dawo domin nace su barta a nan a koya Mata hankali tukkuna,Amma baka bani amsa ba Kai ka d'auke key din ko dan nasan zaka iya wanan tunda ka tab'a b'ata elevator "

Ya d'an Yi shiru sai Kuma yace"ai gani nayi zamuyi bacci shiyasa"

Shaheed yace"ok Daman na fad'an musu kana da dalili"

Suna Gama waya yayi ta Kiran sunan zeenat!zeenat!!zeenat!!!da badan Ina son ki ba da babu abinda zai hana in kashe ki karki kaini bango please"murmushi yayi Jin sun yarda dashi yace"fools sai na kashe ku"

Appa ya kalli shaheed yace"kayi kokari in kun je gida ku danne karku nuna me wani abu please mugu ne

Mami ta fashe da kuka domin abin yayi Mata zafi mutuwar Yan uwanta ya dawo Mata sabo tace"hajiya gobe Zan zo muje asibitin mu duba hafsat dan Allah ku yafewa Kabir ba laifinshi bane Khadija ce ta cuce mu saboda son duniya shiyasa ake son Yara suyi wa iyayensu biyyaya baba be tab'a son aurensu ba Amma ya nace yanzu wa gari ya waya"

Umma tace"Allah yasa mu dace sai kin zo"

Suna tafiya appa da Abba da baba suka tafi part din Inna tana zaune da zeenat sunyi jigum sallama sukayi suka samu wuri suka zauna

Abba yayi gyran murya yace"Inna ashe baba na Raye?"zabura tayi tace"Ina yike toh "

Labarin komai suka bata suka ce inshaallah za a dawo dashi "

Inna tayi ta kuka tana ta tsinewa Sameer da alhaji buba

______________

Tasleem ne cikin Shiga irin na Yan Mata marasa ji Wanda suka San harkar iskanci da abinda ke cikinta ta tsuke cikin bornshot kallo d'anya zakayi Mata kasan ta kware a harka

Pakawa tayi a harabar Sam club dake b?yan gari ta kalli sunan dake walkiya sanan ta fito kamshi take sosai tana cin cingum rigar ta iya cibiya ce

Tana fitowa kallo ya koma kanta amma ta basar tana sa glass ga wata arniyar sanchors me hill dake kafarta ya Kai har guiwarta

Tafiya take Kamar Bata son yi taje zata shiga hall din security suka Hana ta

Canza muryar tayi cikin turanci turawa tace"sorry ni bakuwa ce jiya na shigo kasar Kuma an sanar min wanan shine hotest club a garin nan duk da nasan shima maneji ne"

Had'iye miyau security yayi sanan ya Mika Mata wani mask yace"mu sai an sa mask ake Shiga

Karb'a tayi tasa mask din ta shiga tunda ta Shiga duk wata mace dake zaune a wajen ta Raina kanta

Harda Mary dake kula da wurin tana zaune a bar tana dudduba inda komai ke tafiya

Sake Baki tayi tana kallonta shima alhaji buba Dake zaune zagaye da Yan Mata biyu ya saki Baki

Wani rawa tasleem keyi na manyar Mata

Mary ta cire mask din fuskarta ta karasa inda take cike da kishi dan tasan in har Sameer ya ganta sai ya foller tunda bunsuru ne karta kwace Mata shi godiyarta d'anya yau ya ce bazai Zo ba"

Tana zuwa ta jawo ta tace"who the hell are you and me ya kawo ki nan?"

Tasleem ta kalleta tace"you must be Mary right?"

Mary tace"yes me kike a nan?"

Tace"na Zo ne in raba ki da sauranyinki domin na samu labarin Yana son hot babes kin me tsufa"

Janta Mary tayi tace" get out"

Tasleem ta fisge hanunta tace" ke har kin Isa ki Kore ni"

Alhaji buba ya taso yace"me ke faruwa"

Tasleem ta karasa ta manne me tana shafa me kirji har tayi nasaran cire me mask ta Kai fuskarta dai'dai nashi tana manne hanjinta da nashi wani nishi yayi tace"kishi take Wai"

Dariya yayi kamar wani dolo yace"ai Mary wanan janta gefe zakiyi kuyi yarjejeniya in ba Haka ba in Sam ya ganta ta gama maye gurbinku Daman kin San ya Fara cewa zai Karo wata ku Zama ku biyu"

Mary tace"name your price "
Tasleem tace"muje mota muyi magana ni dama turo ni akayi wata makiyarki in Zaki biya ni abinda yafi nata Zan bar Nan bazan Kara dawowa ba"

Mary tace"ai nasan Debby ce haushi take ji Dan nayi snatching Sameer a gunta?"

Tasleem a ranta tace"kenan tsohuwar budurwar Sameer ce dabby din


Ba tare da tunanin komai ba ta bi tasleem mota

Driver seat tasleem ta Shiga ita Kuma Mary ta Shiga baya

Tasleem tace"kulle kofar Mana kin San komai na bukatar sirri

Tasleem ta d'au hanky ta rufe hancinta tawa motar central luck sanan ta fesa wani spray kafin Mary tace"tayi wani Abu ta ja motar ba ayi minti biyu ba wani bacci ya d'auketa

Gida tasleem ta kaita wani d'anki ta b'oyeta ta daure tare da Mata allura ta fita ta shige main house din tayi wanka da brush ta saka bakar wando da wata tshirt fara ta Kama sumanta a sama ta kalli agogo 8:59pm Daman tana fashin sallah tea tasha da bread ta fito ta kulle gidan ta tafi office dinsu tun a gate ake tsara Mata tana fitowa a mota ta Kira wani tace" a Kai min Wanan suspect din interrogation room James"

yace"wallahi mun yi me duka mun manna me iron but he is not ready to confess"

Tasleem Bata kulashi ba ta Shiga ciki tace"Kai Paul ka Kai min shi dark room Paul yace"ok"

Tace"duk wani abinda ake amfani wajen horo a Kai min shi Nan

Yace yes ma"

Yana kamewa

Cire jacket din jikinta tayi ya rage t-shirt


Ta zauna tana latse latse a laptop bayan 20minit ta wuce ta tarar har an kaishi ciki

Zama tayi ta ajiye bindiga a tebu dake sakaninsu tace"wanene *camelion* Kuma ina kuka Kai me kanti meya aikata Kuma me yake Shirin aikatawa next,duk ina son ji"

Wani murmushi babcy yayi yace"wallahi ko Zaki kashe ni bazan fad'a Miki komai ba ki tambayesu ai Suma sun wahalal Dani Amma ban fad'an balle ke da kike mace

Tasleem tace"hmmm Zan baka 3minit ka Fara jawabi"

Har 3minit yayi be Fara jawabi ba aiko mikewa tayi ta kaime naushi a baki sanda hakorinshi ya cire shima ya tabbatar nata ba irin nasu bane"

Tace"now Ina jinka I don't have time to waiste cikin azaba yace"bazan fad'......"be karasa ba ta d'auki plyer tasa a bude me Baki cike da mugunta da kuma kwarewa ta cireme hakora uku,su officer din suka rintse Ido Amma ko a jikinta

Ta koma ta zauna tace"Ina jinka,ihu yake Amma yaki magana

Tasa handglove ta d'auki wani abu kamar almakashi ta kama hanunshi ta cire me yatsa d'anya ai babcy Suma yayi

Tayi wani murmushi shiko paul alokacin data yanke sanda ya saki Kara domin ya ji shi

Tana ganin ya sume tace"ku jona shocking machine"

Paul na kokarin jonawa yace" da izinin waye ake me wanan horon "

Juyawa tayi ta gan


Maman Nur


Maman Nur
[6/23, 1:12 PM] +234 703 129 7709: =?D?=?D?=?D?=?D?=?D?=?D?
*SO KO ABOTA*
=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?
By maman nurul
Hudah

Wanan littafin na kudine d'ari uku ga Mai bukata za a tura naira d'ari uku ta wanan account number 0092544083
Aisha Mohammed
Acess bank,ko katin mtn domin niman Karin bayani ayi min magana ta wanan number=?I?09090112846

Book>??

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login