Showing 42001 words to 45000 words out of 148334 words

Chapter 15 - SO KO ABOTA BOOK COMPLETE BY Maman Nurool-Huda.doc

27 Sep 2025

2895

cikin yar'su ta samu gidan hutu,domin an karrama su iya karramawa sun ji dadin inda aka tarbesu cikin mutuntawa"

Amarya tayi ta kuka tun ana lallashi har aka gaji aka barta daga Nan kuma wani naunayar bacci ya d'auketa

Zeenat

Mafalki take Wai an canza Mata ango,Wai tana zaune wani mashayi Wanda ta tsana a duniya ya shigo Mata d'anki ya danneta ya biya bukatarsa ta kaishi Kara kotu akan ya Mata fyade sai aka ce mijinta ne ai Yana da right na yin duk inda ya so Amma ita bata hakura ba ta Kuma kaiwa court of appeal

Wanan abin da tayi shiyasa ta gan appa da tunda take dashi Bata tab'a ganin b'acin ranshi ba ya tsine Mata tare da cewa baya son ya Kara ganin kafarta a gidanshi baba ma tsine Mata yayi harda mama umma ce kadai ke tausanta

Ji tayi kamar an shafa kanta ta juya domin gyra kwanciya ta gan bayan mutum na barin d'anki

Wani razanan Kara ta saki dayasa Inna da baba zulai da Suka ki wucewa tashi

Jikin zeenat yayi ta rawa tana Kiran sunan Sameer

Inna tace"meya faru?"
. Kuka sosai take ta d'auki waya ta Kira Sameer Amma tana ringing be d'anga ba"

Inna tace"wa kike Kira?_

Tace"Sameer Ina son in tambayeshi ko shine angona wallahi mafalki nayi Wai na auri wani mashayi "

Inna tace"toh in bashi ba waye shine ai angon bana Yi Miki bayani ba "

Ji tayi zuciyarta tayi sanyi ta duba agogo

2:03am

Gidan gona dake b?yan garin erena (Niger state )

Babban gidan gona ne daya amsa sunansa gidan gona akwai komai da ake bukata a gidan gona babban wuri ne da ake businesses Kuma akwai staff quarters gefe d'anya Kuma can karshe wani babban ad'aden dubplex ne Mai shege kyau ginin zamani

Zaune yake a cikin duplex din a falon daya ji kayan alatu yayi crossing legs ga Kuma yaran aikinshi tsaye abinda ya bani mamaki ciki harda Hamza(saurayin tasleem)sai gyra cocaine yake da hanun a wani table

Shaka yayi ya d'ango Yana girgiza kanshi irin ya ji abin d'in nan har kwakwalwa

Cikin maye yace" camelion kwana biyu baka leko b...."be karasa ba ya Kuma buga kanshi Kamar wani Mai kwarkwata

Murmushi Wanda aka Kira da camelion yayi yace"kasan ai takun ne sai an bi a hankali yanzu dai miye labari tsohon yayi bayani"

Kasa bashi amsa Hamza yayi domin ya rigada ya haura, na Kuma kallon Wanda aka Kira da camelion domin muryarshi sound familiar sai dai fuskarshi sanye yake da mass irin na armrobbers idonshi kawai kake gani"

D'anya daga cikin yaran dake tsaye yace"yaki yin magana babu inda bamuyi ba yaki yin magana infact yau kwanarshi 5 baya Mana magana

Mikewa yayi ya haura sama wani d'anki ya bude ya Shiga 18inches matrass ne irin me tudun Nan daga shi babu komai

Wani tsoho na hango daga Nesa a kalla zai kusan Kai shekaru 70

Zaune yake a takure abin duniya ya dameshi ga abincin da aka ajiye me na safe be tab'a ba harda na Rana

Karasawa camelion yayi su babsy Suka bi bayanshi

Sa hanun yayi ya d'ango fuskar tsohon yace"kaifa ka saka kanka a wanan damuwa ka Fadi inda diamond din suke a wuce wurin

Wani murmushi tsohon yayi yace"yaro ya kamata ka gane ni bazan ci Amana amintaka ba da a ce Zan fad'an maka wallahi da na dade da fad'an maka ka tambayi ubangidan naka Wanda shi ya Fara saceni shekaru ashirin da biyu Kenan Kuna fama da a ce Zan fad'an dana fad'an Ina son ku sani ko da zaku karar da dukkan zuri'a ta kamar inda kuka fad'an bazan fad'a ba,ai da Zan fad'an da a baya na fad'an tun Ina da sauran karfu ba yanzu da na tsufa ba"

Camelion ya Kai hannu hanci ya wani ja majina yace"tsoho karka kaini bango kasa in kashe kowa naka"

Murmushi tsohon yayi yace"me kake jira ai ni kaina Zan so haka'yana Gama magana ya gyra kwanciya abinshi ya barsu tsaye

Rike Kai camelion yayi Wai me zaiyi ne Dan tsohon Nan ya fad'an me wanan sirrin?'

Kiran alhaji buba yayi Yana d'angawa yace"tsohon Nan bashi da amfani me zai hana a Kau dashi?"

Alhaji buba yace"da kuwa ka aikata babban kuskure a rayuwar ka kawar dashi tamkar mun maida aikin mu baya ne shifa kadai yasan sirrin gidan alhaji fulani harda naka sirrin Kuma Ina da tabbacin ya fad'anwa wata sirrin a cikin matan ya'yansa uku har yanzu na kasa Gane wanne ciki matar Musa ne ko dauda ko bukar Kuma matan ba fita suke ba balle Musa musu tarko kasan a wanan ranan da na saceshi anyi haihuwa gidanshi,ana gobe Zan sace shi alhaji fulani yaje gidan Yi me barka tunda aminan juna ne a ranan ya fad'an me wanan sirrin a lokacin babu Wanda yasan naka sirrin daga baya alhaji jibo (tsohon mijin Mami)ke sanar Dani sirrinka da alhaji ya fad'an me toh in Muka ce zamu kashe Taya zamu samu diamond din??ka Bari mu lallab'ashi dan Allah"

Katse Kiran yayi ya fita ranshi na suya

Yana komawa ya bude ledar cocaine d'anya ya d'anga sama ya zazzage shi a bakinshi

Niko nace ka ji wata salo ko??

Yana gamawa yace"Kai babcy shigo min da Mary "

Kiran Mary akayi a waya sai gata ta shigo cikin burnshot da half vest sai wani hill tana wani tafiya kamar wata miss word

Hayewa tayi sanarshi tana shafa summan kanshi suna kiss ganin abin nasu yayi nisa ta kaishi d'anki sai ihun ta kawai ake ji shima haka

Minna

Washe gari da misalin karfe 5:am shaheed ne ke gudu a mota baya son Mami ta farka ta gan baya nan horn yayi me gadi ya bude me ya shiga

Yana shiga falon ya gan wuta a kashe haska wayarshi yayi sai ya gan wasu kwance

Komawa yayi ya bi kofar baya ya tafi d'ankin shi ya kwanta tuni bacci ya kwashe shi domin beyi barcin kirkin ba jiya

Da safe akayi bud'an Kai na zamani da Kuma gata amarya ta samu kyaututtuka domin anyi shi ne Kamar biki

Anci an Sha su anty Jamila suka bar gidan bayan sun danka amanar amarya

Maida amaryar akayi ciki wani d'anki ta zauna tayi tagumi ta rasa me ke Mata Dadi kawai sai aka buga kofa

Juyawa tayi ta kalli kofa a razane ta mike jiki na rawa

Matsawa baya take Yana matsowa har ta Kai jikin bango as usual me Hali baya fasawa sai kawai ta saki fitsari

Wani mugun dariya ya kece dashi Yana nuna ta yace

Maman Nur
[6/23, 1:09 PM] +234 703 129 7709: =?D?=?D?=?D?=?D?=?D?=?D?
*SO KO ABOTA*
=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?
By maman nurul
Hudah

Wanan littafin na kudine d'ari uku ga Mai bukata za a tura naira d'ari uku ta wanan account number 0092544083
Aisha Mohammed
Acess bank,ko katin mtn domin niman Karin bayani ayi min magana ta wanan number=?I?09090112846

Please karki karanta on Baki biya ba please


Bismillahir Rahmanir Rahim


Yace"girl ya kike??"

Cikin rawar jiki zeenat tace"la...f...iy....a sir,please sir ka fita nifa matar d'an uwanka ne yanzu be kamata ka shigo min Haka ba"

Jinjina kanshi yayi sai Kuma ya bushe da dariya yace"girl you are talking back at me, how dare you"

Zeenat ta yarfa hannu tace"wayyo Allah na mutu na lalace ni me nayi maka Kuma kayi hakuri ai Zan gama maka aikin ka,be kamata ka shigo min d'anki ba nifa matar yay.....*

Wani dariya ya bushe da ita yace"in ji ubanwa yace ke matar shi ne?toh in baki sani ba ki sani ni shaheed Mohammed fulani nine mijinki Wanda ya biya sadakin ki ni na aure ki zeenat ba wanan wawan ba"

Zeenat ji tayi maganganunshi suna amsa kuwa a kanta zuciyarta na bugawa wani Abu na taso mata,wani dariya tayi kamar wata mahaukaciya tace"ni nasan Wasa kakeyi,ka dai Zo nanne ka sani bakin ciki as usual ni meya had'a ni da Kai har Haka da aure sai shiga tsakanin mu"

Dariya yayi yace"kiyyaya in baki manta ba ai na fad'a Miki ni in na tsane mutum Zan iya zuwa any length just in tarwatsa me farin ciki,ban b'oye Miki ba na fad'an Miki tun first meeting dinmu cewa ni mutum ne me son ganin b?yan mikiyi na ko ta halin Yaya,na Baki warning karki Kara bari ko hanya ya had'a mu but dan ki nuna min ke Yar tasha ne sai Kika zab'i kiyi aiki a kamfani na ba tare da izinina ba

Juyawa yayi ya d'ora da cewa"da Kike son nuna min ke isassa ce sai Kika zab'i kiyi mingleling da Sameer my number1 enermy wallahi duk duniya babu Wanda dariyar shi ke bakanta min Kamar Sameer to the extend that in na gan Yana dariya sai na bi diddigi na binciko meyasa shi dariya na ruguza shi,sai gashi shigowar ki rayuwar mu kullum yake dariya,da kin San inda Nike ji in yayi dariya wallahi da Baki yarda kin kasance farin cikin shi ba "

Zeenat yace'wallahi ban yarda ba Sameer shine mijina karya kake wallahi"

Wani dariya yayi ya had'a hakoranshi sai Suka ba da kara shhhh ssshhhh nasan daman Zaki Sami kanki a rud'ani shiyasa na zo dan in Miki bayani "

Dole in gode Miki na fad'awa Sameer sirrin gidan ku a eatry ranan da ya bayyana miki soyyayarshi I was there Kuma naji komai when I said komai I mean komai harda zagina da kikayi tayi ni d'an Guguwa ne Ina Shan hayaki bani da aiki sai mugunta,Ina tunanin me Zan Miki sai kawai Kika Fara bashi labarin gidan ku kina cewa Inna ki me kwadayi ce in aka bata nama zata iyayin komai akan nama da fanta,kin San miye nayi next?"

Ta girgiza me Kai yace"Kuna rawa a lokacin da yake shafa ki Kuna iskancin ku da yike ke Yar iska ce, Kika sake me jiki yayi inda ya so ko?,Niko sai nayi muku video na tafi gidan ku domin da kuke waya Ina asibiti naji kin fad'an Masa shikuma ya maimata,Ina zuwa na Sami wani kanin ki karami da bazai wuce shekaru 10 ba domin babu kowa a lokaci nace ya kaini shashin Inna"

Ya ko kaini har falonta na tarar tanawa wani yaro fad'an akan ta aikeshi fanta ya yadda kudi

Tana ganina tayi ta kallona da mamaki tace"mashaallah balarabe a falona bawan Allah badai matsala ko?"

Murmushi nayi Mata nace babu komai Kaka Ina wuni na sameku lafiya "

Tace"lafiya Lau "

Nan ko na tattara natsuwata nace Inna Daman wata magana ne ya kawo ni Kuma nasan duk duniya ke kadai ce Zaki iya yi min shi"

Tace"toh Ina jinka bawan Allah ,Allah yasa ba gidan mu zaka kwace ba"

Nayi murmushi nace ai sai dai in Baku gidan ai inna ba komai bane illah Allah ya d'aura min soyyayar zeenatu Inna Ina son zeenatu bazan iya rayuwa babu ita b...."

Ban karasa ba tace"toh me ake jira ne,balarabe da Kai ai an baka"

Nace"toh anan matsalan take Inna domin babu inda banyi da ita ba zeenatu taki bani had'in Kai sai ma ta Fara soyyaya da yayana Kuma wallahi Inna ni nasan halinshi d'an iska ne,wallahi Inna yaudarar ta zaiyi ni Kuma da nike sonta taki kulani inn....Inna,sai Kuma na fashe da kuka"

Inna tace"laailah a illalahu Mohammed rasulullahi balarabe kuka kake?lallai kana son takwara,Nan Bata san babu kukan da Nike ba

Nace Inna in ma Baki yarda ba bari in nuna Miki zahiri"

Videon Nan na nuna Mata ta kalla ta gan har sanda yayi Miki kiss ta saki kuka tace"yanzu tarbiyar da muka bawa takwara kenan? Allah ya Isa tsakanina da wanan d'an iskan yaron na b'ata min jika da yayi wallahi bazan yafe mishi ba,Niko nayi ta karawa wutar fetur kin San me nayi"

Zeenat dake daskare tana kallonshi ta girgiza kai,yayi murmushi yace"da zan wuce sai na ajiye mata bandir din kudi Yar d'ari biyar nace Inna gashi a siyi balagu Amma karki fad'an Mata na Zo zata tsaneni Kuma naji suna Shirin barin garin nidai kawai ki amince in kawo kudin aure mu Raina musu wayau"

Tayi murmushi tace"toh balarabeAllah nagode ai Kaine mijin zeenat Allah ya so ni banyi gangancin had'an aurenta da wanan sokon ba akan balagun talatin da yake siyo min"

Washe gari sanda na tabbatar gidan ku babu kowa nasan duk an je makaranta sauran Kuma sun tafi aiki Daman nasa an yanka rago an soya Mata nayi shopping na Kai Mata Nan ma sanda na ja Mata kunnin akan karta yarda ki san Ina zuwa wajen ta,number ta na amsa bayan kwana biyu na kirata mu gaisa kawai sai naji muryar Sameer tana d'angawa na gane ranta a b'ace yake kawai sai na bukaci ta tashi ta bar wurin muyi sirri"

Aiko sai ta tashi ta bar wurin da k'yar na roke ta akan tayi hakuri karta nuna me komai ta Bari muje a haka,da yike Inna Yar duniya ce sai tace Kuma kayi gaskiya Bari muje a haka"
. Komawa tayi Bata nuna me komai ba sai ma nuna me da tayi tana tare dashi da wanan Daman muka samu mukayi amfani dashi wajen ganin mun rud'anki ,sai daifa ni su Abba Suka sani ba Sameer ba domin Inna ce ta bashi shawaran akan ya Bari sai ya dawo daga tafiya ayi zancen auren nashi,Nima Dan muyi confusing d'inki sai nayi tafiya shiyasa da su Abba Suka tambaye ki sai kika ce eh domin a tunanin ki Sameer ne ke San Baki mamaki,in Banda ke dakikiya ce taya zakiyi aure keda ango bakuyi magana ba an tab'a surprised da aure ne,still hankalina be kwanta ba domin na lura su abban naki Basu da kwadayi basuyi gadon Inna su ba,da farko kin yarda sukayi Wai sai an ji ta bakin ki kin San me nayi???

Zeenat dake ganin dishi dishi ta girgiza Kai hawaye na saukowa kumatun ta"

Yayi murmushi yana Zama bakin gado yayi crossing legs dinshi yace"a wanan ranan da kuka je club da kawar ki nayi videoring wanan rawar da kikayi shi na nuna musu kuma a daren ranan na Zo b?yan kin shige gida

Jikinsu yayi sanyi sosai baba da Abba sun d'auki zafi Amma nayi ta Basu hakuri akan shi Sameer din ne ke zuga ki da k'yar dai suka hakura sai suka amince na turo magabata na,sun Kuma amince ni d'in Mai kaunarki tunda na so ki b?yan nasan ke club girl ce"

Ni nasa akayi aiki a Sim d'inki aka Hana international number shigowa wayarki,sai dai Kuma banyi zaton zai dawo d'aurin auren' ba kwasam sai na ganshi a daren kasa bacci nayi sai na had'a baki da staff din kamfaninshi na Abuja ana dab da zuwa d'aurin aure aka Kira shi emergency infact to tell you the truth Ni nasa kofi ya Kira mami becsuse I needed some space to make my moves and God willings plan yayi aiki now you are my religions wedded wife,jama'a sun shaida ke matata ce,yau sai gaki karkashin Wanda Kika tsana mashayin da Kuma d'anguguwa can't wait to see fuskarku ku biyu in ya dawo kin San me zai bani joy?'
. Ya kalleta ya gan idanunta Kamar kafewa suke ya karasa yace"shine in gan Kuna bakin ciki dukkanin ku biyu in gan gari ya waye gaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login