Showing 18001 words to 21000 words out of 148334 words

Chapter 7 - SO KO ABOTA BOOK COMPLETE BY Maman Nurool-Huda.doc

27 Sep 2025

2881

tace"iam sorry sir"

Da k'yar ya samu ya tura ta ta Fadi saman kujera tafiyarshi ma canzawa yayi Yana wani layi yaje wajen fridge ya Ciro wani kwalba na tutolin ya bude ya kurba"

Zeenat dai na zaune tana kallonshi da mamaki

B?yan ya Gama Sha ya Zo gab da ita Kamar zai fado a jikinta tayi saurin tashi

Nunata yayi Yana buga kanshi Yana murmushi yace"keee Zan shiga ciki in kwanta Kan in fito duk wani file dake table former assistant dina kiyi treating and karki tafi ban sani ba,banma amince ki fita a office din Nan ba"

Da wuri tace"ok sir"har ta Kai kofa yace"tsaya dan gidan ku"

Tsayawa tayi cak zuciyarta na mugun bugu

Yace"biyo ni"

Ganin ya Kama hanyar d'ankin tsoro ya kamata tace"sir "

A tsawace cike da maye yace"you heard me right,don't let me repeat myself "

Tsayawa tayi tana kallonshi har ya shige,tunani take ta bishi ko ta bari karfa yayi raping dinta"

Wata zuciyar tace but you don't have a choice

Binshi tayi ta tarar dashi kwance har zata fita taji yace"cire min wando"

Tace"what?"

Yace"you are trying my petience girl,do as I said in na tashi abinda kike gudu shi Zan Miki"

Zeenat ta fashe da kuka tana dukawa tace"Allah fa na ganin ka,Kato da Kai ni Zan cire maka wando haba ka ji tsoron Allah "

Tsawa ya daka Mata yace"Zaki cire ko kuwa?"

Cikin kuka ta cire me takalmi da socks sanan ta cire me Riga ya rage shi da vest

Jin munshari yasa ta mikewa ta bar d'ankin domin tana da tabbacin yayi bacci

Tana fita ta Fara duba files din da ya ce,babu laifi tana brain sai dai abinda ya Bata mamaki cewa Kan ya tashi abinda ko file d'anya bazata iya gamawa yau ba,dubawa ta kumayi daga wani company they want a sample na extate da zasu sa ma'aikatansu wanan ma will last her for a week because after making a plan dole sai ta samu material tayi making dinshi physical not on paper,beside sai ta je ta gan filin"

Ajiyewa tayi domin ba abinda zai yiwu bane"

D'aukan wani tayi sai ta gan is just 2 bedroom flat guda hud'u ake so,computer ta Fara dubawa ta gan information din shi an dubo filin da size da komai hamdala tayi

Ta duba handover note da Abdul ya ajiye Mata
Tana tunanin wa zata Kira sai ta gan wani paper number din ko wani department ne sai ta Kira ta fad'an musu su kawo board da materials

Ana kawowa babu b'ata lokaci ta Fara zana plan dinta had'aden plan ne

Awa uku besa ta Gama ba domin bayan tayi a board ta Fara yin na paper da za a tura asa hanun,zufa sosai zeenat tayi ga yunwa

Agogo ta duba ta gan is after 4:pm ta tuna batayi sallah ba ta rasa ya zatayi domin yace ko Nan da can Kar taje

Da sallama ta tura d'ankinshi ta gan bacci yake Kamar gawa toilet ta Shiga ta d'auro alwala ta fito daman ita tana da hijabi a bag in zata fita

Babu dadduma Dan Haka ta nimi inda ba a fiya takawa ba ta tadda sallah b?yan ta idar tayi addu'a sanan ta Koma bakin aikinta yunwa kamar ya kashe ta

4:duk aka watse building yayi tsit Kuma be tashi ba

Itako wani aiki take tana duba agogo time to time ga uban yunwa Kuma shiru har yanzu

Ganin har pass 6pm yasata mikewa dan leka ciki

A office din ma be fito ba tana leka d'ankin ta ganshi zaune ya rike Kai idanunshi yayi ja shifa ya ma manta da ita

D'agowa yayi suka had'a Ido sai yace"Zaki iya tafiya gobe karki Bari in Riga ki"

Bata ce komai ba Kamar Wanda kwai ya fashewa a ciki ta bar building din

Takaici yasa ta tayi ta kuka a Keke napep har me Keke ya shiga anguwansu kukan take sanda ta gan ya Sha kwanar gidansu ta Fara goge hawayenta tana fitowa ta wanke fuska da pure water hanunta ta biyashi ta Shiga gida

As usual har anyi shimfid'an mazan sun je sallah domin magrib tayi,matan Kuma wasu sun tayar wasu na gindin famfo suna alwala

Ummi da fitowar ta kenan tana ganin zeenat ta d'auke Kai

Zeenat a ranta tace"I didn't expect ki tambaye ni damuwata dama

Zata shige anty maryam tace"keee zeenat Zo Nan

Zeenat ta juya,fuska d'aure anty Maryam dake sa hijab domin tayi alwala tace"bafa Dan kin samu aiki zakiyi ta dawo lokacin da Kika gan dama ba babu kuku ki da zai Miki girki ki dawo ki zauna kici,tunda Kika Sami aiki kike Mana iskanci Kuma dan iskanci da kayan da Kika fita ba dashi kike dawowa ba ki d'ai bi a hankali karki jawo mana abin kuny.... "

Bata karasa ba Inna da fitowarta kenan daga part dinta tace"in ma ta jawo ba ita ce farau ba wasu sunyi kafin ita,kin San fa kanwar ki har Yan biyu ta Haifa a gida ko kin d'au bamu da labari ne,toh ki fita harkar takwarata in ba Haka ba Zaki Sha mamaki kin takura yariya da ita da gidan ubanta na gadoma"

Ummi na Jin su tayi shiru,sai dai ta ji dadin amsa da Inna ta Bata, ta takura zeenat babu dalili

Itako zeenat shigewa tayi ta kwanta a gado Sameer ya fad'o Mata yau ya wulakanta abinda yayi Mata yafi na shaheed Muni

Hawaye ta farayi tuna abinda ya faru da k'yar ta mike ta shiga toilet ta dade a ciki tana kuka Kan ta d'oro alwala ta fito tayi sallah magrib tana zaune ta jira Isha tayi sanan ta fita domin cin abinci

Duk Yan gidan na zaune tunda ta fito ya jafar ya Kura Mata Ido duk anty Maryam na lura Amma ba bakin magana gudun Inna ta wanke ta

Zuwa zeenat tayi ta gaidasu appa suka Mata ya aiki,Abba yace Wai wani time kuke tashi ne?"

Tace"officially 4:pm ne but in muna da outside work zamu iya dadewa kamar yau min fita aiki ne shiyasa kuyi hakuri"

Appa yace"akwai matsala ne na gan kamar kinyi kuka"

Turo Baki tayi tace"ba ogan mu bane sai yayi ta sani aiki dayawa ba shiyasa Dana gaji nayi kuka"

Su Yaya aminu Suka saki dariya Yaya jafar yace"wai ke a tunanin ki kyauta za a biya ki ba tare da kinyi aiki ba?"

Zeenat ta mike taje tasa hanun a abincin su Rabi suna tsokanar ta

Wayar ta yayi Kara tana dubawa ta gan Sameer

B'angaren Sameer ko

Maman Nur
[6/23, 1:09 PM] +234 703 129 7709: =?D?=?D?=?D?=?D?=?D?=?D?
*SO KO ABOTA*
=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?
By maman nurul
Hudah

Wanan littafin na kudine d'ari uku ga Mai bukata za a tura naira d'ari uku ta wanan account number 0092544083
Aisha Mohammed
Acess bank,ko katin mtn domin niman Karin bayani ayi min magana ta wanan number=?I?09090112846


Bismillahir Rahmanir Rahim

B'angaren Sameer ko,daman cike da b'acin rai ya bar office din,gaskiya yau zeenat ta b'ata me rai,gida yayi direct ya shiga part dinshi ya kulle ko Ina har window yasa wayoyinsa a silient zama a kasa yayi ,time to time Yana kwantar da kanshi saman table din saboda b'acin rai ya dade Yana haka kafin bacci ya fisge shi

Shiyasa be gan kiranta ba,be tashi ba sai kusan magrib yayi alwala yaje masallaci ba tare da ya duba wayar ba amma yana da niyyar daman in ya dawo ya kirata shiyasa Yana dawowa ya Fara kiranta Kuma Taki d'angawa

Hankalinshi ya mugun tashi ganin 40missed calls yace"dole akwai abinda ya faru,Yana cikin trying kenan sai ga Hanan ta shigo tace"Yaya ka zo mu ci abinci in ji Mami"

Da Kai ya amsa Mata Sanan ya bi bayanta Yana trying number still bata d'anga ba

Yana zuwa ya tarar da shaheed zaune Yana cin abinci hankali kwance,be ko kalli inda yake ba ya ja kujera ya zauna

Mami tace"ya dai Sameer na gan kamar baka da walwala"

Yace"Mami kin San daga bacci na tashi shiyasa duk jikina yayi weak'ya Kare da Kai waya kunni besan lokacin da yace"common zeenat pick up ba"

A lokaci d'anya Mami da Hanan Suka ce wacece zeenat?"

D'angowa yayi dan besan a bayyane yayi maganar ba yace"wata friend Dina ce"

Zaro Ido Hanan tayi tace"Kai Yaya Fadi gaskiya Kai da baka kula Mata shine har zakayi friendship da wata Kai dai ka fad'a Mana *SO NE KO ABOTA?* "

Mami tace"yaushe zata zo ta gaida ni please bani ita mu gaisa"

Da mamakin inda suka d'auki al'amarin yake kallonsu yace"relax Mami is not what you think we are just friends,bafa budurwata bace jiya fa Muka had'u "

Budan bakin shaheed sai cewa yayi"Mami relax wata birgi birgi ce fa amalala marata beda control in ta ma Zo jika Mana wuri zatayi da fitsar...."

Be karasa ba ya ji an Kai me pounch dayasa cokali dake hanunshi fadiwa

A zafafe Sameer yace"so nawa Zan fad'a maka ka fita daga lamurana,meyasa zaka saka baki a abinda be shafe ka ba"

Shaheed ya jawo jug din juice din tangara zai fasawa Sameer akai Sameer ya Kama me hanun yace"yau Zan nuna maka iyakar ka"

Dambe ne ya b'arke tsakaninsu ,su Mami Suka mike Hanan ta fashe da kuka,domin sai dukan shaheed ake

Mami tayi tacewa su bari sunki jinta,Sameer yace"yau sai na kashe ka kowa ya huta,karyar iskanci kake wallahi, zeenat kake zagi?"

Mami tayi ta Jan Sameer Amma yaki ya d'anga daga jikin shaheed

Kawai sai ta fashe da kuka abinda Sameer baya so,ji yayi jikinshi yayi mugun sanyi ya tashi Yana bawa Mami hakuri,da k'yar shaheed ya mike yaje da gudu zai kaiwa Sameer duka Sameer ya tare shi da wani punch dayasa bakin shi fashewa

Zai Kara me Mami ta rike hanun ta wankawa Sameer mari,shima shaheed dake kokarin kaime ta wanka me Mari tana kuka
. Cikin kuka da gajiya da halin yaran tace"Wai ya kuke so inyi da ku ne?ya kuke so inyi ne,Ina iya kokari na na ganin na faranta muku amma babu abinda zaku saka min dashi sai tashin hankali Kuna tunanin da Yaya Mohammed da Kabir na Raye zasuyi alfari da ku ne?ko kuwa da a ce kkhadija da Fatima na Raye zasu Baku award ne akan halin Nan naku,wallahi Mohammed da Kabir ba a tab'a Jin kansu ba har suka bar duniya domin sun had'an kansu basa fad'a Amma madadin kuyi koyi dasu Amma ku baku gan makiyan ku ba sai junan ku,Kai Sameer Ina Kaine babba meyasa kake biyewa balarabe har kuke tashin hankali,ba a kwana biyu bakuyi dambe ba Kuna tunanin iyayen ku zasuyi farin cikin haka ne,mutuwarsu ya ishe ku ishara kuyi hankurj ku so juna a ce a Rana d'anya iyayen ku suka mutu amma ku ki rungumar juna,kowa ya guje ku ni dana ce Zan zauna daku Kuna niman kasheni a tsaye,Kai balarabe saboda bakin halinka mijina ya Koroni ko shekara bamuyi da aure ba na hakura da auren Kuma bazaku bari in huta ba"

Sameer yace"Mami kiyi hakuri Amma Ina son a raba Mana dukiyar mu kowa ya bude kasuwancinsa na gaji da iskancin yaron nan "

Mami tace"ai an raba wanda zai rabu kamfani Kuma ai wasi'a kabiru ya bari kan kar a raba ku had'an hanun ku jagorance shi"

Shaheed yayi tsaki yace"Zan baka mamaki badai akan wanan wawiyar zeenat ka dakeni ba har ka fidda min jini a gefen baki?ni din nan da kake gani zan baka mamaki Kuma ni da Kai ne wallahi, katon banz....."

Be karasa ba Mami tace"balarabe in baka kashe shi ba, baka birgeni ba dan ubanka d'auko wuka ka caka me ka bani karshen mamaki,balarabe Ina gargadin ka,ka fita idona in rufe,Ina fad'a maka kullum shaye-shaye hauka ne baka gan Wanda zaka Raina ba sai Yayar ka ko? toh in baka bashi mamaki ba ni saratu Zan baka mamaki,mu zuba Dani da kai shege ka fasa"

Tsaki yayi ya bar wurin,Mami ta Kama hanun Sameer ta jashi ta zaunar dashi a falo tace"babana bana hana ka kula shi ba meyasa Kai bazaka ci girma ba"

Yace"Mami yaron Nan ya rainani' ko a office abinda ya ga dama yakeyi yayi?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ta min Kamar shine gaba dani ko kad'an ba respect tsakanin mu haba Mami in an d'auke ni a matsayin babba arad'a ni c e o Mana"

Mami tace"haba banana mu daina maida hanun agogo baya mana,Kai fa kasan irin yakin da akayi dana so yin haka ya tara Mana lawyers har kotu yaron nan ya so ya kaimu Wai shine keda highest share karka manta ya so ya dawo maka da shares din ka,kasan fa beda mutunci"

. Yace"toh ya dawo dashi Mana me yake jira"

Mami tace"ah'ah haka bazata faru ba ni da nike son ku had'an kanku "

Tashi Sameer yayi ya shige ciki ya cigaba da trying zeenat amma still Bata d'anga ba

Shafa kanshi yayi yace"what wrong with her?she is not picking my call"safa da marwa ya dingayi a falonshi Amma zeenat Taki d'angawa

A lokacin ko zeenat na kwance a part din Inna a 3seater tana gani taki d'angawa

Yaya jafar sai mikar da wuya yake Yana son ganin ko waye,ya gan friend a ranshi yace"zai iya zama na macece "

Ji yayi hankalinshi be kwanta ba yace"ke zee bazaki d'auki waya ba"

Turo Baki tayi tace"kyaleshi ai Nima da nayi ta kiranshi kin d'angawa yayi Nima nayi fushi"

Ji yayi gabanshi ya Fadi yace"ke ubanwa ke Kiran ki?"

Tace"Yaya ni Dan Allah ka kyaleni"

Rabi ce ta shigo da Fahad a hanun tace"zeenat anty Jamila tace"Dan Allah ki rike shi muje chemist tayi allura mu dawo"

Zeenat tace"nifa ban son takura ita data haifesa taje da d'anta Mana ko ta nimi wani ni za ayi ta takurawa kamar Yar raino"

Inna da fitowarta kenan daga bedroom tace"Kuma ki Gama a zage ki,ai matan gidan sam Basu da Hali Amma Yi hakuri ki rike Mata na yau kawai takwara"

Rabi ta ajiye shi jikinta har zata fita taji ya tsala ihu

Zeenat tace"maza dawo ki d'auke shi yaro sai shegen kiwuyar tsiya,daukeshi"

Rabi tace"kiji tsoron Allah zeenat wallahi Zan in na rantse ko kafara bazanyi ba mintsininshi kikayi dan mugunta"

Zeenat tace"nidai tafi dashi indai kin gan na mintsileshi ne"

Inna tace"allahu Akbar jikar isah Ali pantami Wanda in Suka rantse Basu kafara,Zaki daukeshi ne ko sai na ci Miki muntunci"

Rabi ta daukeshi tace"ai dole ki goyi bayanta daman halin ku d'anya a wajen ki ta gado mugun Hali ai"

Inna ta fashe da kuka daya jawo mutan gidan aka tambayeta sai cewa tayi Rabi ta zagi uwarta da ubanta ai sai baba ya d'auke Rabi da Mari ya Kuma ce ta Bata hakuri tana kuka ta Bata hakuri sanan Suka bar part din

Duk wanan abin zeenat bata tanka ba shima jafar be ce komai ba sai ma d'auke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login