Showing 51001 words to 54000 words out of 148334 words

Chapter 18 - SO KO ABOTA BOOK COMPLETE BY Maman Nurool-Huda.doc

27 Sep 2025

2892

su ba

Shiko Yana shiga ya tarar da zeenat kwance ta rufe har Kai da bargo idanunta sun canza kala sun koma ja Kamar garwashi abinka da farar mace

Kallonta yayi da mamaki yace"ya na gan kamar baki tashi ba?"

Kuka ta fashe dashi tace"wallahi zazzab'i nike ji jijiyoyina kamar zasu sinke ciwon Kai nikeji ka taimaka ka kaini gidan mu"

Ya karasa ya Kai hanun wuyanta yaji jikinta da zafi ya duba bedside ya gan breakfast Bata ci ba"

Tabe Baki yayi yace"toh sannu ki ci sai ki Sha magani ko Kya samu karfin jiki akwai karamin yaki yau a gidannan kin San shima fa karamin mahaukaci ne Amma nidai abinda Zan fad'an Miki shine da kin gan zai Fara dukana ki Shiga tsakiyar mu ki ce Kai meyasa zaka dakan min miji"

Cikin wani irin murya me nuna me ita na Jin zazzab'i tace"waye ne zai dake ka"

Beyi magana ba ya mike ya laka window"

Mamaki take domin kallo d'anya zaka me ka gane a tsorace yake a ranta tace"me ke faruwa ne?yau the almighty sir shaheed ya tsorata

Had'an Mata tea yayi yace"Sannu ki Sha tea din ga magani,mtsss sai kiyi tasa mutum aiki kamar jaki"

Karb'a tayi domin tana bukata,shanyewa tayi ta's

Yace"sannu kin ji yunwa gashi Kin shanye shi tas kamar Wanda ya sauko daga roka"

Ajiye Mata Irish din yayi a cinya yace"maza cinye"

Tace"bani da appetite ne"

Ya harareta ya d'auke Irish din yace"kashe kanki yariya ni ba ruwana"

Itadai Bata ce komai ba sai hawaye da takeyi

Yace"toh tashi kiyi wanka"

Mikewa tayi tana dafa bango toilet ta shiga ta Tara ruwa sanan ta shiga bath din ta kwanta domin dadin ruwan takeji

Shiko sai jira yake Amma shiru Bata fito ba

Jin shirun yayi yawa ne yasashi binta daman babu key ta dai tura kofar ne ganinta yayi cikin ruwa ta lumshe Ido

Tsaki yayi ya karasa kawai ji tayi an sungumeta a razane ta bude Ido sai ta ganta jikin mutu rintse Ido tayi ta saki Kara tana kokarin sauka shiko ya Kara matseta jikinshi bata da wata mafita than ta Kama shi domin zata iya Fadiwa in tayi Wasa hakan tasa ta zagaye hanunta a wuyarshi sai fuskarta yayi gab da nashi suna shakar numfashin juna,Jin numfasu gab da gab yasa ta rintse Ido shiko ya zuba Mata Ido Yana kallon fuskarta

Murmushi yayi sun dade a haka Jin har yanzu be sauke ta ba yasa ta bude Ido sai Suka had'a Ido

A hankali yayi ta Kai fuskarshi kusa da nata ya lumshe Ido ta gama sadakarwa kissing dinta zaiyi sai kawai taji ya sauketa

Wani irin kunya ne ya lullubeta domin babu Kaya jikinta

Wani irin ihu tayi ta jawo bargo ta rufe sai kawai ya shige bayi Yana murmushi

A gurguje tasa kayan da ta gani a gefen gado doguwar Rigar shadda ce anyi me aikin senagal kayan ya karb'ata ya bi jikinta sosai kamar an gwadata

Ta zauna a stool sai gashi ya fito d'aure da towel alamun yayi wanka

Juya me baya tayi Kamar Bata ganshi ba Yana wakar shi na fad'an a rijiyar kwanar sahiba urhmm uhrmmm sa mini kugiya,na yarda na amince urhmm. Urhmmm "

Itafa haushin shi take ji domin wakar bata Dadi a bakinshi kasancewar ko hausa yakeyi zaka jita wata iri yafi Jin turanci da larabci bawai baya Jin hausar ba no Yana ji but halshensa daban take da ta nan

Shiryawa yayi saf cikin shadda irin ta jikinta sai kallonshi take ya Zo dab da mirrow ya d'auki comb ya Fara taje Mata Kai ya gyra shi saf ya Kama Mata Yana tabe Baki ashe dai sumanta ne da gaske"

. Powder ya d'auka sai ji tayi ana shafa mata ta kalleshi ya d'ange mata gira

Saf yayi Mata kwaliya tana mamakin shi ji tayi yace"nifa ban iya d'aurin d'an kwali ba kiyi da kanki irin wanan da ake Kira house wife
Cikin rashin walwala tace"fita zamuyi ne??"

Yana combin g suman kanshi yace"zamuyi welcoming din wani ne nasan ya iso ai"

Bata Kuma cewa komai ba har ya gama ya Bata mayafi yace"daga Kai Zaki sa ko Kuma dai sa hijabi kawai"

______________

Mami da Hanan na kokarin cire banan da shaheed ya manna Sameer ya shigo

Juyawa sukayi a razane har abin ya bashi mamaki

Tsalle Hanan tayi tana murmushin dole tace" Yaya barka da dawowa"

Yace"barka me kuke yi haka Mami"

Mami tayi saurin karasawa ta Kama hanunshi ta juyar dashi hanyar dining tana cewa nayi kewar ka son muje ka ci abinci nayi maka girki"

Karasawa yayi ya zauna Hanan tayi Saving dinshi yace"toh ki zauna Mana Mami meke faruwa ya na gan kamar baki ji dadin gani na ba"

Zatayi magana sai ta gan ya mike Ya Kai wayarshi da tayi ringing kunnin yace"Zan Kira ka amma in har zai b'ata Mana lokaci a San inda za ayi dash..... "

Be karasa ba ya hango hoton dake manne

Gabanshi na fad'iwa yace"

Maman Nur
[6/23, 1:09 PM] +234 703 129 7709: =?D?=?D?=?D?=?D?=?D?=?D?
*SO KO ABOTA*
=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?
By maman nurul
Hudah

Wanan littafin na kudine d'ari uku ga Mai bukata za a tura naira d'ari uku ta wanan account number 0092544083
Aisha Mohammed
Acess bank,ko katin mtn domin niman Karin bayani ayi min magana ta wanan number=?I?09090112846


Yace"zeenat ???"

Mami ta rintse Ido ta bude karasawa yayi Yana murza idonshi zaiyi magana sai ga su shaheed da zeenat sun Danno Kai falon shaheed rike da hanun zeenat

Wani kallo Sameer ke binsu dashi amma sai karyata zuciyarshi yake

Zuwa dining yayi ya d'auki jug din ruwa ya Wasa wa kanshi daga Kai ya wanke fuskar

Amma su yake gani,a take idanuwarshi Suka canza kala b'acin rai ya bayyana karara

Shaheed besan sanda ya saki hanun zeenat ba domin ya tsorata

Zeenat na ganin Haka ta Ruga da gudu taje wajen Sameer ta rungumeshi ta fashe da kuka tace"please take me out of here,ka d'aukeni mu gudu I don't want to be with him my Sameer do you know he trick me he toy with my emotion,my Sameer do you know he........."labarin komai ta bashi tana wani irin kuka tace"ya had'ani da iyayena mu gudu my Sameer mu tafi wuri me nisa ni da Kai Zan rayu, ta Kare da Kama hanunshi

Da k'yar shaheed yayi gathering courage ya karasa ya Kama hanunta yace"kina matata zaki rungume wani Kato??"
. Zeenat tayi saurin komawa bayan Sameer

Tsaki shaheed yayi ya Kai hanun da niyar jawo ta Sameer ya kaime wani naushi sai kawai jini ya b'alle me a hanci wani Kara ya saki Yana cewa wayyo hancina

Mami ta rasa me zata ce domin Bata tab'a tunanin abin na shaheed ya Kai Haka ba,Daman tsagerancinshi yakai haka?"

Wani ihu Sameer yayi daya firgita duk wani abu Mai rai dake rayuwa a gidan,sameer yayi watsi da kayan dining din ji tasssss, wanan hayaniyar shi ya fitar da Inna Dake bacci da baba zulai

Rufe shaheed da duka yayi kamar zai kashe shi har ya zamto shaheed baya iya motsawa

Mami ta koma falo ta zauna tayi tagumi tana kuka,Hanan ce me bashi hakuri Amma sai ya tureta itama dai da alamu ta gurd'e

Baba zulai tace"na Shiga uku ni zulai tunda aka haifeni ban tab'a ganin irin haka ba ni zulai gida zan tafi Kar ayi kisa gaban mu muyi kwanar prison

Inna ta karasa ta kaiwa Sameer tafi a baya tace"Dan ubanka sake shi kashe shi zakayi "

Wani juyowa Sameer yayi hanun a dunkule zai kaiwa Inna naushi

Zeenat ta rike me hanun, cikin b'acin rai yace"leave me alone duk wani Wanda yake da hanun a cikin rabani dake sai na gan bayanshi Ina itace Wanda ta haddasa wanan matsifa yau zata gane Bata da wayau"

Zeenat ta bishi da wani kallo tace"Kai ka dawo hankalinka da Kakata kake fa "

Tsaki yayi ya bude troly dinshi ya d'auki key da gudu yayi d'ankinshi ai sai gashi ya dawo da bindiga Yana halbin iska

Wanan abin ya bawa kowa mamaki sa bindigan yayi Akan shaheeed yace"yau zan kashe ka in kashe banza wallahi yau zanyi maganin ka kowa ya huta"

Ganin dai da gasken kashe shaheed din zaiyi Mami ta mike tace"ni ban hana ka me komai ba Amma please Sameer sauke wanan bindigan a kanshi"

Shidai shaheed ko motsi ba yayi domin ya daku

Zeenat ko rawar jiki ta farayi toh Ina ya samu bindiga,hankalinsu be tashi ba sai lokacin daya maida bindigan Kan mami yace"dake Zan Fara saboda kece Mai daure me gindi

Hmmma tashin hankali da ba a sa Mata Rana ai Inna fitsari ta saki a jiki hakoranta na rawa sai Kara sukeyi alamun sanyi ya kamata

Ba'ba zulai dai sai kalman shahada take tace'ya rabbi karka sa in mutu kafura,ka bani dama d'anya Tak in koma gaban ya'yana Kan in mutu dudu befi kaza biyu Dana ci ba balagun ma shegiyar tsohuwar Nan zeenatu kad'an ta bani ta killace abinta Ashe dai rayuwata na ci"

Wani tsawa Sameer ya daka musu yace"ku min shiru

Hanan tace"Yaya meke damun ka? Do you realize Mami ka sawa bindiga??"

Yace"and so???"

Mami tace"kyaleshi Hanan may be mutuwa ta shi zai sa su so juna Sameer ka kasheni na ce kasheni Nima zanfi son haka"Kama bindigan tayi shi Kuma ya danna kunnama

Ji kake


Maman Nur
[6/23, 1:09 PM] +234 703 129 7709: =?D?=?D?=?D?=?D?=?D?=?D?
*SO KO ABOTA*
=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?
By maman nurul
Hudah

Wanan littafin na kudine d'ari uku ga Mai bukata za a tura naira d'ari uku ta wanan account number 0092544083
Aisha Mohammed
Acess bank,ko katin mtn domin niman Karin bayani ayi min magana ta wanan number=?I?09090112846

Please in baki biya ba karki karanta min littafi,in kika karanta na biki bashi


Bismillahir Rahmanir Rahim

Ji kake patttttt patttt an halbi iska domin Hanan ce tayi saurin d'anga me hanun da yanzu Mami ta Zama labari

Mami ko rintse Ido tayi jira kawai take ta ji ta a lahira sai ta ji babu zafin da take expecting bude Ido tayi tana kallon Sameer dake huci

Hanan ta kwace bindiga tayi wurgi dashi Bata San lokacin data wankawa Sameer Mari ba tace kasan me kake kuwa ka dawo hayyacinka

Su baba zulai dai yau an ga duniya ta b'oye b?yan kujera jikinta na karkarwa Inna dai suman tsaye tayi zaninta ya jike da fitsari ita kanta zeenat fitsarin tayi tanawa Sameer wani kallo Mai wuyar fassara bata tab'a tunanin Yana da other side Haka ba,he went too far meyasa zaisa mamin shi on gunpoint

Wani kuka Mami ta fashe dashi dayasa Sameer Jin jikinshi yayi Sanyi

Beyi magana ba ya take Shaheed dake kwance ya bar wurin

Baba zulai tace"alhamdullilah Amma wanan yaron anyi asarare mugu ne Kuma beda halin kwarai a ce yaro yasawa uwarshi bindiga a Kai toh Allah ya hane mu da haihuwar matsifa irin shi"

Zeenat ta rasa ya zatayi bin Sameer zatayi ko Kuma zata taimakawa Sameer dake kwance ?"

Baba zulai tace"ke zeenatu tashi muje nan gidan ba wurin Zama bane kunji na rantse Miki ko kwana uku bazaki Kara a duniya ba in Kika cigaba da Zama anan gidan, ni zulai tunda aka haifeni ban tab'a ganin irin haka ba wallahi"

Inna tace"muje kin fiya surutu"

Aiko kayan su Basu d'iba Suka Kama hanya "

Fuska daure Mami ta kalli zeenat tace"ke Kuma me Kika jira da bazaki tafi gidan ku ba?"

Zeenat zatayi magana mami ta daka Mata tsawa tace"get out kafin ranki ya b'ace Kuma bana son in kara ganin ki a gidan nan ki cire ran rayuwa da d'anya daga cikinsu domin bazan Bari ba,ke matsifa ce a rayuwarsu tunda Kika shigo rayuwarsu bamu da kwanciyar hankali bana son in Kara ganin ki a gidan nan"

Zeenat ta fashe da kuka toh miye laifinta shi Wanda ya haddasa rigimar ba a ganin laifinshi sai ita

Tafiya take tana kuka ko wayarta mami Taki Bari ta d'auka

Tana fita Mami ta Kira likita ya zo gida Hanan na dingishi ta fita ta Kira masu aiki su Zo su gyra wurin

Likita na zuwa suka taimakawa Shaheed aka kaishi d'anki allura akayi me tare da treating wood dinshi

Bude Ido yayi zaiyi magana sai ya Kuma lumshe shi wani naunayan bacci ya daukeshi

Sameer ko komawa d'anki yayi ya jawo tebu kamar inda ya Saba in ranshi ya b'ace yayi resting akai Yana wani irin kuka Yana Kiran zeenatu,sosai take Jin zuciyarshi na Kuna

Da Kuma ya tuna abinda ya faru d'anzu na yasawa Mami bindiga sai yaji tsanar kansa meyasa yayi irin wanan fushin daya kasa banbance what right or wrong he can't believe he point his gun at Mami,why meyasa Shaheed ya zab'i ya rabashi da farin cikin shi me yayi me a rayuwa shi yasan Shaheed ba son zeenat yake ba ya dai yi hakan ne Dan ya bakanta me gashi Yana niman yayi ruining life din 4people saboda sakarcin shi,shi din ba farin cikin zai samu ba zeenat ma Haka sanan shima sameer cikin kuncin itama shaheeda Haka tunda yake da mace d'anya yasan Shaheed itace shaheeda they are childhood friend kowa ya sani why the sudden change of mind "

Waya ya jawo ya Kira shaheeda Yana d'angawa yace"where are you???"

Shaheeda dake bacci wayarshi ne ya tashe ta ta d'anga tace"ina Saudi ne ya dai Sameer ya naji muryar ka Haka meke faruwa?"

Yace"Kiran ki nayi in Miki congrat ko Kuma in ce Jaje domin Shaheed yayi aure"

Wani murmushi tayi tace"this is an expensive joke and I didn't find it funny so ka canza topic kodai zolaya ta kake dan kawai ban taya ka murna ba na bikin ka,iam sorry Shaheed ya fad'a min but a lokacin na koma Saudi muyi magana da mummy na akan ta fad'awa Abba Shaheed zai turo and Shaheed insisted I go shiyasa"

Sameer yayi wani dariyar takaici yace"he fooled you the same way he fooled everyone yace ki tafi ne kawai Dan ya samu wurin yin inda yake so,can you believe just to get back at me Shaheed married zeenat?"

Tace"

Maman Nur
[6/23, 1:09 PM] +234 703 129 7709: =?D?=?D?=?D?=?D?=?D?=?D?
*SO KO ABOTA*
=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?=؋?
By maman nurul
Hudah

Wanan littafin na kudine d'ari uku ga Mai bukata za a tura naira d'ari uku ta wanan account number 0092544083
Aisha Mohammed
Acess bank,ko katin mtn

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login