Showing 1 words to 3000 words out of 146065 words

Chapter 1 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

🕊 *KAINUWA* 🕊
_........Dashen Allah_




*Haske Writer's Association*




*Na Ayusher Muhd🤸🏻‍♂*




*Bismillahi Rahmani Rahim*


_All character and event in these novel are Fiction_
May Allah guide us through the right path (Ameen).


_Godiya ta musaman ga masoyana, ina godiya da alfahari daku nagode kwarai da gaske._


Aunty Nah Hafsa Khabeer (Aunty Goggo) Allah ya kara kareki ya biyamiki bukatunki (Ameen)


*1*




*The year 1970*




Gida ya cika taf da mutane duk inda ka duba wasa ake yi, wasu na wasan dokuna wasu na wasan shad'i wasu busa suke yi, wasu waka suke yi, haka wasu wasan kidan kalangu sukeyi.


Hidima dai kala kala irin ta wasan ninmu na hausa na da, kowa ka gani fuskar nan tasa a washe take alamar farin ciki.


Bayi sai murna sukeyi dan irin wannan sha'ani shi ke sa su su fito haka, maroka sai tasu hidimar suke yi.


Gidan sarauta na kasar zazzau kenan wato Zariya.


Zazzau na daya daga cikin manyan masarautu a Najeriya. Masarautar taci kasashe da dama da yaki, Girman kasar Zazzau ada ta kai har Suleja a Jahar Niger.


Masarautar Zazzau ita ce tafi kowace masarauta a yankin Afrika ta yamma yawan makarantun zamani da na addini, shiya sa ma ake mata taken Zazzau, birnin Ilimi.


Zazzau yana d'aya daga cikin Hausa bakwai wanda Bayajidda ya kafa, gari ne na sarauta.




A wannan shekara ta Alif dubu d'aya da d'ari tara da saba'in karni ne na sarautar Abdulsamad wanda ya kasance d'a ne ka AbdulJalal wanda ya mulki kasar shima ta gadon mahaifinsa.


Abdulsamad yana shekara 20 kacal aka daura shi akan mulki sakamakon rasuwar mahaifinsa, suna da yawa a gun mahaifinsu sai dai shine ya kasance d'an sarauniya Kubra sannan yaro ne mai hankali hakan yasa mahaifinsa ya bada wasiyyar shi yakeso a nad'a.


An aura ma Abdulsamad mata a wannan lokacin wace ta kasance 'ya ce ga waziri wato " Safina" wacce ta kasance tun tana yar shekara uku mahaifinta ya bada umarni a koyar da ita tarbiya ta matan sarki, hakan yasa ta taso mace mai tsauri da tsananin jan aji, abinda zai baka mamaki ko Abdulsamad sai ya sara mata a gun ji da kai da mulki.


Safina ta auri Abdulsamad tana yar shekara 15, wacce aka nad'a a matsayin sarauniya, ta kuma bada umarnin a dinga kiranta da *Magajiya*.


Yayanta Hisham shine ya gaji mahaifinsu, wanda aka nad'a sarautar waziri.




Auran Abdulsamad da Safina babu soyayya a ciki sam aurene na umarni, sai dai ita dama Magajiya sam babu soyayya a tsarin rayuwarta abu d'aya aka nuna mata ta auri sarki ta haifar masa d'a wanda zai gajeshi.
Wannan shine abinda iyayenta suka daura ta akai.


A wannan lokacin shekarar Sarki Abdulsamad da Magajiya 20 da aure sai dai har yanzu Allah bai azurtasu da haihuwa ba.


Sarki ya cike mata 4 sannan yana da kwarkwara 9 amma har yanzu ba labarin ko da batan wata.


Wannan abu na matukar damun Sarki da Magajiya, tayi magani harta gaji har yanzu babu labari.


Sai dai alwashi ne tasha babu mai haifar ma Abdulsamad magaji sai ita in har ba ita ba kuwa to lalai bataga wacce ta isa ba.


_Wannan kenan_


Kwatsam Magajiya ta fara abin laulayi haka kuma tace ai likita ya bata umarnin zama a d'aki ba tare da fita ba har sai ta sauka, sannan ya hana mijinta kusantarta saboda mahaifarta batada karfi.


Sam wannan bai damu Sarki Abdulsamad ba shidai farin cikinsa shine zai samu magaji.


Magajiya sam ta daina fitowa haka ma bayinta sai wadanda ta yarda suzo gunta a haka har watan haihuwa tai, nan tace itakam gidansu takesan komawa.


Kasancewar Sarki Abdulsamad bai isa da itaba yasa ta shirya ta tafi.


Har ta sauka sannan aka aikomai da cewa ta haifi namiji.


Fadar farincikin da Hisham yake ciki ma b'ata lokaci ne, wanda ya kasance yau ne ake hidimar sunan d'an nasa wanda aka samai suna Abdulmajid.


Anata hidimar suna a waje sai dai daga kuryar d'akin Magajiya itace zaune akan kasan carpet gewaye da tintin sannan d'akin anyi jere sosai na kayan karfi masu kyau da tsada, tana zaune cikin shigarta ta matar Sarki, gefenta kuma Hisham ne a zaune, su biyu ne kacal a d'akin sakamakon sallamar bayinta datai.


Kallan Hisham tai cikin isa da mulki tace " Yaya baka manta da abinda na fad'a ma bako?"


Dariya yai yace "in banda abinki Magajiya ai ba wanda zai ji wannan sirri dan kuwa ita kanta Sauda(matarsa) na ja mata kunne akan ma karta kuskura ko da wasa tazo gidan nan inkuwa tazo to lallai karta bari su Hadu da Abdulmajid.


Murmusawa tai kadan sannan tace " daga Abdulmajid na rufe haifar wani d'a a gidan nan, babu macen da zata haihu bare ma har a fara tunanin wanda za'a daura akan mulki."


Hisham yai murmushin mugunta yace " Magajiya gaskiya kwakwalwarki tana aiki ya akai kika zo da tunanin karyar ciki? Sanda na sanar dake Sauda na da juna biyu?"


Wani murmushin kasaita tai sannan ta sa hannu akan lab'anta alamar shiru sannan a hankali tace " Yaya kenan ai na fad'a maka tabbas d'ana shine zai gaji sarautarnan, inhar bazan haihu ba dole ne nai amfani da kai jinina."


Wani kallo sukama juna na jin dadin abinda suka kulla, Hisham yace " Nace Sauda ta bari sai nan da wata uku sannan ta dawo."


Magajiya ta jinjina kai alamar gamsuwa tace " gwara ta kara zama saboda kar aganta aga kalar haihuwa aga kuma ba ciki, dan ma matar nada hakuri kaga bata mana musu ba sanda muka bata umarni."


Hisham ya sosa keya yace " inta kawo wargi ai sai ta amshi takardarta."


Murmushin jin dadi Magajiya tai sannan tace " ka sa a kara aikomin da maganin nan dan wanda nake badawa a sa ma matansa a girki ya kare."


Ya dan sa dariya yace " gaskiya Magajiya ke karshe ce, shi yasa nake baki girma da darajaki, amma bakya gani ko an daina basu maganin yanzu ba abinda zai faru? Gani nake mahaifar tasu ma ai ta gama aiki."


Wani murmushi tai wanda ya fahimci cewa tana nufin ta sani amma a kawo.


_Nikam nace Hmmm_




Sarki Abdulsamad kam kana kallansa zakasan yana cikin tsananin farin ciki.


Bayan ya dawo daga hawan doki ne ya shigo fada sai ga wani bawansa ya sanar dashi yayi bako.


Nan ya bada izini akan bakon ya shigo.


Wa zai gani? Amininsa ne wanda suka shaku sai dai dayake shi dan Katsina ne wanda aiki ne ya kawo mahaifinsa garin Zariya, har suka shaku haka kafin daga baya su koma garinsu.


Da sauri ya karasa gun sarki saboda tsananin murna, nan Sarki ya kallesu da ido wanda ya nunama dogaran akan yanaso su fita, ba musu kuwa sukai waje.


Rungume juna sukai cikin tsananin farin ciki Sarki ya kalli abokinsa yace " Amadu ashe zan ganka?"


Wani irin farin ciki sukeji na ganin juna, bayan sun nustu ne suka shiga hirar yaushe gamo.


Can Sarki yace " ko ziyara Amadu? Da alama yanzuma ba saboda ni kazo ba."




Sarki gani yai Amadu yayi kasa da kansa alamar damuwa, cikin kulawa yace "menene?"




Hawaye ne ya ciciko a idan Amadu cikin wata muryar abin tausayi yace " Mai martaba ina cikin wani mugun hali."


Mamaki ne ya kama Sarki yace "Name kenan?"


Ido Amadu ya runtse yace " kanwata aka ma fyade a kasarmu, wanda hakan yasa dangina da na matata duk hankalin mu ya tashi sakamakon habaici da kyamatar mu da akeyi."


Cikin tsananin tashin hankali Sarki yace "kanwar ka badai Basira ba?"


Amadu ya jinjina kai cikin takaici sannan yace " ita kuwa shiyasa naga zamanta acan bazai yiwuba dan ko fita bata iyayi shine nace bari inzo in rokeka ko zaka tambayarmin yayarka Aunty Babba ko zata zauna agunta ko da kuwa na wata d'aya ne, bani da wanda na sani bayan kai a kasar nan, gashi duk samarinta sun gujeta."


Cikin tausayawa Sarki yace " amma garin yaya?"


Amadu yace " da daddare matata ta aiketa siyo maganin zazzabi dan bawa d'ana da bashida lafiya, nikuma bana gari, a hanyarta ta dawowa aka tareta aka mata fyade, duhu yasa batasan waye ba bare ta nunashi."




Sarki yai shiru yana nazari, Amadu yacigaba " Mai martaba in kuwa kanada wani dogari ko bawa da kake tunani ka hadata dashi a musu aure dan kuwa babban abin kunya ne a ma mace fyade ka san bazata taba samun miji ba sai dai wani iko na Allah gashi ta girma shi yasa nake tunani ko wanene ma kawai ka bata a daura auren kafin nan sai ta zauna gun Aunty Babba."




_da yake a wancan lokacin babban abin tashin hankali da kunya ne a ma mace fyade ko ta je gidan mijinta ba tare da budurcin ta ba_


Sarki yai shiru, tausayin rayuwar Basira yakeyi, yarinya ce wacce ba ruwanta ga hakuri.


Bayan dogon nazari ya kalli Amadu yace " kaunar da mahaifinka yakema nawa, da wanda kaima kake min yasa na yanke shawara ni zan aureta sqi dai inaso karka bari zancen fyade a fito a ko ina, mu birne ta a nan inba haka ba kyamatarta za'a dingayi a gidan nan."




Tsananin mamaki yasa Amadu ya kasa magana sai dai wani zazzafan kwalla daya gangaro masa, kai ya girgiza yace " nagode dajin haka sai dai bazan yarda ka auri macen da aka taba a waje ba."


Sarki yai dan murmushi yace" Amadu kenan menene amfanin abotar? Kana tunanin akwai mai rike ma sirrinka bayan nidin? Yanzu in muka mata aure da wani bawan ko dogarin daga yaje ya ga ba cikakiya bace shikenan sai wulakanci, haka ma in sanar dashi mukai bazai fasa wahalar da ita ba."




Amadu yai shiru, Sarki ya dafa shi yace "karka damu a goben nan ma zan aureta sai dai bazan bari a sani ba tukunna har sai 'yan taro sun watse saboda hidimar suna da akeyi."






Amadu ya zube yana godiya, Sarki yace " ka koma kasarka gobe da safe zanyi shigar burtu na zo ba tare da sanin kowa ba sai wanda na yarda dashi."


Amadu wani dadi ya kamashi ya hau godiya sannan yace " nidai zan jiraka mu tafi tare sabida tsaronka."


Sarki yai murmushi yace " idan ka tsaya kuma waye zai sanar dasu maganar auran? Sannan nima banaso asan zanje har can din, sannan ka bari in sa akaika a mota dan nasan a irin a kori kurar nan ka zo."




_A waccan lokacin in har kaga mutum da motarsa to fa lalai d'an wani ne sannan motar ma mu a wannan lokacin tsohon yayi muke daukanta irin mai shafaffen booth din nan ce.._




Sun dade suna tattaunawa kafin Amadu ya mike yamai sallama, godiya da jindadi kam yayi ba adadi.




Nikam nace hmm wata sabuwa....








*ABUTURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA* 🕊
_........Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)






*Haske Writer's Association*




*Na Ayusher Muhd*


*2*


Shiru Sarki yai yana nazari bayan fitar abokinsa, baiyi zata ba sai jin muryar Aminin nasa yai a kusa dashi alhalin ya dauka ya tafi.


Amadu yace " Amma Mai Martaba ba matanka hud'u ba?"


Idanunsa ya bud'e ya saukesu akan Amadu sannan yace " Amadu kaje ka sanar da Barde ya kaika gida, ni kuma gobe zanzo."


Jin haka yasa Amadu ya fita jiki a sanyaye, Mai martaba yai shiru tare da maida idanunsa ya rufe, ya dade a haka kafin ya bud'e idanunsa sannan ya kira wani bawansa ya sanar dashi akan ya kira masa kaninsa wanda suke uwa da uba daya.


Bai dade da fita ba sai gashi ya dawo shi kuma kanin nasa Kamal na biye dashi a baya.


Yana shiga ya saki fuska tare da cewa " Mai Martaba ina can ina hawan doki ka aika a kirani, Allah yasa ba matsala bane."


Abdulsamad ya tattara hankalinsa kan kaninsa yace " Kamal yanzu ace na baka mata zaka aura?"


Kai ya d'aga mai alamar eh sannan yace "ko ma wace iri ce in har ba mara da'a bace ko wacce ta lalata tarbiyarta da darajarta a waje ba."


Sarki yai shiru kafin yace " in kuma d'aya daga cikin wacce ka lissafo baka so ne fa?"


Kamal yai murmushi kafin yace " maganar gaskiya zan aureta in har umarnine daga bakin Sarki sai dai in har umarnine daga bakin yayana bazayi ba gaskiya."




Ya dade yana kallan Kamal kafin ya daure da murmushi yace " ya kaje gun d'an naka?"


Kamal ya washe baki yace " Abdulmalik yana can yana bacci amma yau kam zai yi kwanciyar gajiya, ai yau kowa na cikin farincikin magajin sarki."


Sarki ya kara fad'ada murmushinsa yana jin dadin kasancewarsa uba kafin ya sallami Kamal.


Bayan fitar kamal ne ya shiru yana tunani ( _a yanda tarihi yake mata guda hudu ne kamar yanda musulunci ya umarta mana sai dai akwai kwarkwara wanda suke zama matan sarki in anci garinsu da yaki ko kuma makamancin haka sannan su wad'an nan basu da gadon sarki in ya mutu_)


Lalai yau ya yanke hukunci ba tare da yasan mafita ba sai dai yayi hakan ne saboda tunanin kare mutuncin aminin nasa.
Matarsa ta karshe ko ince Amaryarsa wacce ya aura a waccan shekarar ita yake tunanin rabuwa da ita badan komai ba sai dan rashin san auransa da takeyi shi kansa yasan tauye mata hakki mahaifanta sukai gun bashi ita, yarinyace 'yar shekara 12 mahaifinta yayane ga sarkin Daura wanda sunyi hadin auren ne a san ransu, ace shi yana shekara 40 amma an bashi yar shekara 12 ai kowa yasan hakkinta aka tauye shi yasa ko tunanin nemanta bai taba yi ba.


Da wannan shawara ya mike tare da ba bayinsa izini akan yanasan a kira Magajiya zuwa turakarsa




**********


Magajiya kam tana zaune sai shigowa ake yan suna ana mata barka, ba amsa wa take ba sai kai kawai da take kadawa cikin isa da takama.


A ranta wani irin nishad'i takeji tabbas tana cikin tsantsan farin ciki dan saura kiris burinta ya cika, wannan burin nata kuwa bai wuce ace d'anta Abdulmalik ya hau mulkin garin na Zazzau ba.




Wata baiwar ta ce ta iso kusa da ita ta rada mata a kunne sakon Sarki, idanu ta juya tare da d'an yin karamin tsaki a ranta, itafa batasan takura akan mai shi baxai zo inda take ba sai dai ace wai taje?


Tafi minti talatin kafin ta mike ta fito.


Turakarsa ta nufa yana xaune akan kilisar dake shimfid'e a gun, nan ta shiga kanta tsaye.


D'agowa yai ya kalleta ta iso ta zauna d'an nesa dashi kadan cikin isa tace " gani ranka ya dade."


Kallanta yai yace " Magajiya na tasoki kina cikin taro ko?"


Kallansa tai ta danyi murmushi tace " da alama kanada magana mahimmiya ne."


Ajiyar zuciya yai sannan yace " ana cikin farin ciki sai dai zan sanar dake wata magana ne."


Kallansa tai tare da tattara hankalinta kansa.
Yacigaba " so nake in ba Rabi'atu takardarta ina tunanin zallintar da mukema yarinyar nan ya isa haka."


Kallansa tai cikin mamaki tace " ban gane ba? Ka taba gani inda sarki ya saki mace?"


Yace " yau xa'a fara a kaina."


Tace " in ka saketa kana tunanin akwai mai auranta?"


Abdulsamad yace " zan saketa ne amma bazan bari tabar gidan nan ba, ni zan rike ta har sai ta samu wanda takeso in aurar da ita."


Kallansa tai har zatai magana ta fasa dan itakam yanzu babu wani abu da zai dameta d'a ne ta samu yanzu dan haka komai ma zai faru sai dai ya faru.


Ganin tayi shiru yasa ya fahimci ta amince nan ya rubuta takardar saki d'aya ya mika mata yace " ki sanar da ita sai ta koma bangarenki da xama ko bangaren Hajiya Umma (mahaifiyarsa)


Jiyai tace " sai dai bangaren Umman dan nikam banasan tarikice."


Sarai maganar tad'an kona ransa sai dai bai nuna mata ba, takardar ta amsa sannan ta mike ta fita.




Itakam Rabi'a bayan Magajiya ta aika tazo ta sanar da ita halin da ake ciki sam bata damu ba sai ma dadi da taji ta kuma ji dadi kwarai da akace zata zauna anan, dan dama tsoronta mahaifinta.




Suna yayi dadi an kashe kud'i, 'yan gari sun sha kalo, anyi hawan doki sosai, jaruman maza sun sha wasa da takubba, masu wasa da kura sun sa mutane nishad'i da sauransu.


Da haka kowa ya koma gida, Magajiya ta dauko unguwar zoma mai kula da ita.




*********


Washegari Sarki Abdulsamad bayan yayi sallar asuba yakira bawansa wanda ya aminta dashi haka kuma shine dama yake jansa a mota ya sanar dashi zasuyi tafiya, suna sallar asuba ya fadama fadawansa akan zai dan yi zagaye cikin gari dan ganin halin da mutanensa ke ciki.


Kasancewar kowa yasan dama al'adarsa ce yasa ba wanda ya kawo komai a ransa, suna fita suka dau hanyar katsina.


*******


A can katsina kuwa Amadu ya sanar dasu akan gobe za'a daura ma Basira aure da zarar anyu sallar azahar a masallaci.


Basira kam batada bakin magana dan ita tun bayan faruwar wannan lamari sam ko magana ta daina yi, ko tambayar mijin batai ba ta mike ta koma ciki.


Matar Amadu ta shigo ta ganta a zaune a bakin irin gadon nan na karfe, ta kalleta tace " Basira bakyaso ne?"


Kai basira ta jijiga mata alamar A'a.
Numfashi ta ja sannan tace " Basira ya kamata ki cire abin nan aranki yau wata d'aya da sati biyu kenan da faruwar wannan al'amari, daga ni har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login