Showing 48001 words to 51000 words out of 146065 words
Chapter 17 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
kuwa bazanso in bar tarihin karya ko dadin baki agunki ba."
Kallansa tai ta kasan ido, ba shakka kalamansa sun mata dadi.
Kanta na kasa tace " Amma ai ina gani ya kamata ka nunamin ko na maka alamar so ko aminta da hadin da akai."
Murmushi yadanyi kadan yace " Bana sanki!"
Cikin tsananin tashin hankalin jin wannan kalmar yasa ta d'ago ta kafeshi da ido, iska yadan furzar yace " kina sa ran daga ganinki sai in fara sanki?"
Idanunta tai kasa dasu batace komai ba, yace " Bilkisu!"
Kallansa ta karayi, yace " kina da kyau na tabbata kowa na fada miki haka, kinada mulki wanda ke kanki kinsan haka, sai dai inaso ki sani karkiyi tunanin hakan zai na soki, ba wai dan abinda kike dasu baimin ba sai dai dan ni ban yarda da wadannan sune abinda ya cancanta ba a so, sannan ban yarda da love at first sight ba."
Jiyai tace " sai me ka yarda dashi?"
Murmushi ya mata yace " sirri ne."
Shiru ne ya ratsa na 'yan dakiko.
Jiyai tace "Nagode."
Kallanta yai cikin mamaki yace " name fa?"
Tace " Na gaskiya daka fadamin."
Yace " Ina miki fatan alkairi a rayuwarki, ana tabbata ba lalai mu kara haduwa ba."
Mikewa yai zai tafi, jiyai tace " in kuma na bukaci hakan fa?"
Juyowa yai cikin mamaki ya kalleta bai amsa mata ba.
Wani sansanyar murmushi tamai tace " Ban taba had'uwa da mutumin daya fadamin gaskiya ba sai kai, da fari na fara jin haushi sai dai a hankali na fahimci gaskiya dama d'aci gareta."
Kallanta kawai yake baice mata komai ba.
D'agowa ta kara yi ta sakar mai murmushi tace " Da alama kai zaka gaji masarautar Zariya."
Cikin mamaki ya kalleta sannan yace " me kike nufi?"
Tace "sani ne bakai ba ko kuma bakasan ne na fahimceka? Na tabbata ka san cewa bazan auri wanda bashine zai gaji sarauta ba, sannan tunda mahaifinka ya turoka nan alamace ta kai yakeso ka mulki masarautar sa."
Gabansa ne ya fadi cikin mamaki yace " aurenki haka yake nufi?"
" Da farko ance mana baka gani sai dai daga baya aka kara aikowa akan ka samu sauki."
Idanunsa ne suka dan rage girma ya matso kusa da ita yace " waye ya sanar daku hakan?"
Murmushi tamai tace " na sani sirri ne dan nima ni kadai Mahaifina ya sanar ma hakan, da farko abin yaban haushi dan a gaskiya wannan dalilin ne yasa na tura Munnira ta ganka, sai dai yanzu na fahimci kanada dalilinka nacemin baka gani da alama da bakaso zuwa ba."
Wato da bayan sunyi bincike sunji labarin baya gani, amma mai martaba ya aiko da sakon yana gani.
Mikewa yai daga tsugunnan dayai a gabanta, baice komai ba yai waje ransa a b'ace.
Kenan saboda dalilin nan aka turoshi? Shikuma harda kokarin yi mata sauki dan bin umarni?
Ba shakka ransa ya bace na biyomai ta bayan gida da akai...
*TEAM ABU TURAB🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*31*
Yana fita Jakadiya ta matsu gunsa da sauri tace " Ranka ya dade Mai Martaba nasan ganinka."
Kallanta yai yace " Yana ina?"
Nan ta nuna mai hanya, tana gaba yana binta a baya zuciyarsa fal take da tunani kala kala.
Wani katon d'aki ne ba komai a cikinsa, capet ne a shimfid'e sai 'yan tum tum.
Sallama yai ya shiga kamar yanda Jakadiya tace ya shiga.
Zama yai nesa da Mai Martaba sannan ya tankwashe kafofinsa, sannan ya gaisheshi.
Tunda ya shigo shikuwa Mai Martaba yake kallansa, cikin yaban nutsuwa da zatinsa.
Cikin mulki ya amsa sannan yace " Abu Turab Barka da zuwa Masarautarmu, ina fatan komai ka sameshi yanda ya kamata."
Kansa na kasa yace " ina kara godiya da karamcin da muka samu."
Shiru ne ya d'an ratsa kafin Mai Martaba yace " Ammm Abu Turab"
Abu Turab ya nutsu, Mai Martaba yacigaba " Kaga Bilkisu?"
"Naganta Ranka ya dade."
Me kake tunani game da ita?
Abu Turab ya d'ago sannan yace " Ina kara jinjina ma na tarbiyantar da ita dakai da sai dai fatan Allah ya kyautata rayuwarta."
Murmushi Mai Martaba yai yace " Ba shakka kai din jinin Sarauta ne ko daga yanda kake bani amsa cikin fasaha ba tare da na zargi wani abu ba."
Abu Turab yai kasa dakai yace " ina godiya da yabon da kamin."
Shiru suka kara yi kafin Mai Martaba yace " bari na gyara tambaya ta to, mai kake gani game da auranka da Bilkisu?"
Sarai yasan abinda yakesan ji kenan sai dai shi bashida ansar wannan tambayar dan kuwa shi dai ba santa yake ba, ba kuma zai iya kallan idan mahaifinta yace baya santa ba, sannan a xahiri gaskiya bai kuma tsaneta ba.
Kansa na kasa yace " Ranka ya dade ai wannan tambayar tana hannun Bilkisu, duk abinda ta yanke shine daidai."
Kallansa yai cikin yabawa da nutsuwa da kaifin tunaninsa yace " duk da haka inasan ji xaga gareka, Bilkisu ita kadaice 'yata, duk da ina sha'awar ta auri mai mulki sai dai abin da nafiso shine inga ta auri wanda zai kularmin da ita."
Abu Turab ya nisa sannan yace " Ran ya dade ka gafarceni amma mune muka nemi had'in auran nan hakan ai yana nuna muna so ne."
Cikin jin dadi yace " nagode da jin amsoshinka, Allah yamana jagora."
Ameem ya fada.
Shiru sukai kafin Abu Turab yace " Zan koma gobe in sha Allah, in munji daga gareku xamu damu dawo da yardar Allah."
Duk da baiso tafiyarsu gobe ba saboda yana san yaga sun kara fahimtar juna, sai dai bazai iya hanashi ba.
Yace " Allah ya kaimu."
Sallama yamai sannan ya mike ya fito, a falo ya tadda Sabi'u yana zaune sallama kawai yai ya wuce shi ya shiga ciki, Sabi'u cikin mamaki ya kalleshi zaiyi magana yana fuskarsa a had'e yasan ko yamai magana ma ba lalai ya amsa mai ba.
D'aki ya shiga ya yazauna a bakin gado tare da dafa kansa.
Tunanin maganar da Bilkisu ta fadamai yakeyi, me mahaifinsa yake tunani? Anya kuwa abinda take tunani haka ne? Shiru yai yama rasa ta inda zai fara ba ma kansa amsa.
Washe gari kuwa da safe yace ma Sabi'u ya shirya zasu koma, Sabi'u bai musa ba dan yaga yanda yake tun daren jiya.
Sun sanar da tafiyarsu haka aka kawo kayan tsaraba kala kala daga bangaren Fulani wato maman Bilkisu da kuma bangaren Mai Martaba aka basu.
Sunje shiga mota Munnira ta taho da gudu, ganin zai shiga yasa tai sauri cewa " Uncle Turab!"
Abu Turab ya tsaya sannan ya waiga, ganin Munnira yai ta karaso da gudu, ya kalleta yace " Munnira ya da gudu?"
Tana haki tace " UmmaBilkisu ce ta aikoni naga kuma zaku tafi."
Kallanta yai yace " aiken me kenan?"
Wata yar karamar jaka ta mikomai tace " Gashi."
Amsar jakar yai sannan yace " ki mata godiya."
Tace to.
Mota ya shiga Sabi'u yaja.
Suna hawa kan titi Sabi'u yace " da na dauka itace ta bata maka rai, amma ganin sakonta yasa nasan ba ita bace, me ta kawo mana ne?"
Abu Turab ya bud'e jakar, wani kwalbar turarene mai kyau yana bud'e kwalbar wani kanshi ne ya bud'e motar, rufe turaren yai ya ajiye shi sannan ya jinginar da kansa kan kujera tare da rufe idanunsa.
Ganin haka yasa Sabi'u yai gum....
*********
A can kuwa Zariya yau da sassafe aka kawo musu gulmar zuwan abu Turab can.
Tashin hankalin da Magajiya ta shiga baya misaltuwa, cikin sauri ta aika a kira mata Hisham ko wanka lokacin baiyiba haka ya fito dan ancemai kiran na gaggawa ne.
Sun shiga can kuryar d'aki ta kalleshi cikin yanayinta na isa da san boye damuwarta tace " Hisham mai martaba ya biyomana ta bayan gida."
Kamar ya kenan?
"Ya tura d'ansa ganin 'yar sarkin kano."
Hisham yace " ita zai aura?"
Ranta ya b'aci tace " kai ni meyasa kwakwalwarka kamar ta kifi take?"
Kallanta yai cikin tsananin kunar rai sai dai tsoro yasa yace " Magajiya ban fahimceki bane."
Kallansa tai tace " 'yar sarkin kano fa na fada maka, wacce nafadama xamu hadata da Abdulmajid kai bakasan me auranta yake nufi ba?"
Hisham yace " Au matar da kikace za'a tura?"
Tak tsaki tace " Bakasan halin Mai Martaba ba kenan, ba kuma kasan me yake tunani ba."
Hisham ya kalleta da nufin san karin bayani.
Tace " ya fara shiri akan d'aura Abu Turab mulki."
Idanu Hisham ya zaro yace "Mulki kuma? Makahon?"
Idanu tadan kanne na bacin rai tace " shine abinda na kasa fahimta, me zai sa Sarkin Kano ya aminta da makaho a matsayin siriki? Me yake tunani akan aura ma yarsa kwaya d'aya makaho?"
Hisham yace "au ya amince ne?"
Tace " majiyata ta sanar min da alamar amincewa dan kuwa ancemin har kiransa yai daga baya sai dai ba wanda yasan me sukai a ciki."
Cikin tashin hankali Hisham yace " ai kam bazai taba yiwuwa ba, mulki na Abdulmajid ne haka kuma yarinyar dole ne mu san yanda zamuyi."
Magajiya tace " tashi zakai yanzu ka je Masarautar kano, ka samu Hajiya Karama kawata wato Amaryar sarki ka tambayeta komai, sannan ka san yanda zakai su tsani Abu Turab ni zan shiryama duk abinda zaka fada."
"Hakan yayi Ranki ya dade, yaushe ya kamata in tafi?"
Tace " a yau zakaje dan da zafi zafi akan bugi kirji."
Hisham yace " na fahimceki amma in suna can fa?"
Shiru tai sannan tace " sai yafi ma, yanda za'a katse auren a basu sallama."
Dariya yai yace " ko banza naga idan d'an jakar uba."
Murmushi tai sannan tace " ai shi mugunta wani sa'in alheri yake sama, in har shi yana tunanin mugunta yamana dole ne mu maidashi abinda zai amfanemu in yaso sai muga yanda xaiyi, kuma Wallahi zaisan niyama haka, zai kuma san Makaho da mai gani ba karfin su d'aya ba, da MAGAJIYA yake zance."
Hisham yasa dariya yace " wa ya isa dama yaja dake?"
Tai d'an tsaki tace " Abdulmajid inyaso yazo ko zuwa jibi ne."
Yace " Hakan yayi."
Sallama ya mata akan zaije ya kimtsa.
*************
Khadija tayi kwalliya ta fito da nufin zuwa gidan wata 'yar uwarsu a cikin gari, tana tafe cikin sanyinta dan dama mai sanyi ce.
Ita kuma a tsaye take a jikin wani shago tana amsar sakon da aka aikota ta amsa, juyowa tai cak idanunta suka hango Khadija wacce take nufo gunta.
Kura mata ido tai cikin waswasi dan kuwa an dade rabon data ganta, ta kusa da ita taxo wucewa, cikin rashin yarda da abinda take tunani tace " Khadija!"
Kallo gun Khadija tai tare da tsayawa, Mairo ta kalleta tace " Khadija!"
Khadija ta matso gunta fuskarta d'auke da murmushi tace " Naam."
Mairo ta matso tace " Khadija ce ta gidan Waziri?"
Khadija tai dan dariya tace " nice dai Mairo, da ban ganeki ba sai da kika matso daf."
Gaban Mairo ne yadan fadi dan itakam tasan ita Abu Turab yake so, daurewa tai tace " yaushe kika dawo?"
Khadija tai murmushi tace " Ban dade ba, Allah dai bai had'amu bane."
Mairo tace " ikon Allah! Kuma kina shiga gidan Sarki?"
Tace sosai ma, ko shekaran jiya ma naje."
Mairo ta daure tace " Ya Turab fa? Kun had'u?"
Gani tai Khadija tayi kasa dakai tana murmusawa, sannan tace "mun had'u sosai ma."
Mairo tai dariyar yake tace " bari naje aike na akai kar aga na dade."
Khadija tace " to, sai mun sake haduwa."
Juyawa yai ta amshi sakonta ta juya da sauri ta fara tafiya, jitai gaba daya jikinta yai sanyi, ba shakka Abu Turab zai mata wuyar samu yanzu a da tana tunanin kila tanada chance amma yanzu kam ta tabbatar ya mata nisa, balle ga Bilkisu, ina ita 'yar gidan wani Barde ina takara da manya?
Haka ta isa gida jikinta duk ya gama yin sanyi, tana shiga ta ajiye sakon ta shiga d'aki ta kwanta, a hankali taji wani zazzafan hawaye yana zubo mata ta kuryar idanunta....
*TEAM ABU TURAB🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*32*
Magajiya ce xaune a kilisar Mai Martaba, ta umarci kowa ya bargun, sun dade a zaune kafin cikin kasaitarta tace " Ranka ya dade ashe Abu Turab yana kano?"
"Eh." Abinda yace kenan yai mata shiru.
Kallansa tai fuskarta dauke da murmushi tace " Daren jiya na aika yazo mu gaisa sannan yaci abincin dare a guna akacemin ai yayi tafiya."
"Ha ka." Nan ma daga fadar haka taji bai ce komai ba, sosai ranta ya b'aci ammabta daure tace " Dama zuwa nai in fadama wata magana."
"Inajinki."
Ta nisa sannan tace " tunanin hada auran Abdulmajid da Gimbiya Bilkisu nakeyi."
Yace " hmm shawarace mai kyau hakan sai ki aika musu da takarda."
Kallansa tai cikin mamaki tace " ai kai ya kamata ka aika Ranka ya dade."
Kallanta yai sannan yadan murmusa yace " fadamin kikai ai ba shawara kika zo nema ba, kinga kuwa banida abin cewa."
Kallansa tai sannan tace " Ranka ya dade ka taba nuna cikakiyar kulawarka ga Abdulmajid? Kana sane lokacin auransa yayi amma sam banga kana nema masa wacce ya kamata ba."
Kallanta yai yace " kin taba bani girmana na uba a kan al'amuransa?"
"Me kake nufi da kalamanka?"
"Inkin gama inaso in runtsa kafin na fita fada."
Ya fada tare da dan lumshe idanunsa.
Ba shakka ranta yayi tsananin baci ace kamar ita Magajiya ita mai martaba zai wulakanta?
Kallansa tai rai a bace, mikewa tai ta tako a hankali har inda yake ta tsugunno inda yake ta sakar mai wani sansanyan murmushi tace " Takawa kardai ka manta da Abu Turab idanunsa basa aiki, Abdulmajid shine kadai wanda zai kula dashi, ina ganin ya kamata ka kara karfafa zumuncin dake tsakanin 'yan uwan biyu, ganin Abdulmajid shine babba kuma magajinka."
Kallanta yai kawai, itakuma ta mike cikin salan tafiyarta, babu wanda ya isa ya juyata ko kuma ya nemi wulakantata, dolene abi abinda takeso inhar ana bukatar zaman lafiya a wannan gidan.
Mai Martaba kam bayanta yabi da kallo sannan ya girgiza kai har ta fita yana kallanta, a fili yace " nine sarki ba ke ba, sannan da Abdulmajid da Turab karkashin ikona suke da ke kanki, tabbas zan nuna miki kashin namiji da mace ba d'aya bane."
*********
Abu Turab kam suna isowa ya wuce b'angaren Mahaifiyarsa, mamaki ne ya kamata da Lantana tace mata ta fito ga Abu Turab nan ya dawo.
Zama tai a saman kujera, shi kuma yana zaune a kasa ya lankwashe kafafunsa.
Bayan ya gaisheta ne ya nemi a basu guri, nan su Lantana suka fita.
Kallanta yai yace " Umma me mai Martaba yake nufi da auran Bilkisu?"
Kallansa tai sai dai babu mamaki a idanunta tace " Mahaifinka yana san ka gaje shi."
Yace "in gajeshi? Ban fahimta ba."
Basira tadan yi yake tace " Ni kaina bansan me yake nufi ba."
Mikewa yai waje.
Yana fita Lantana ta shigo da sauri, tace " Tuba nake ranki ya dade, banyi da nufin jin abinda kuke cewa ba sai dai na taho kawoma Uban gidana ruwa naji abinda yake cewa."
Basira tace " ba komai Lantana."
Lantana ta ce "Amma Bakya ganin hakan shine ya dace? Ko kin yafe musu abinda suka aika tama Yayanki?"
Abu Turab wanda ya dawo domin sanar da ita kartama Mai Martaba maganar tukunna yana tsaye jikin kofar yaji wannan kalaman na Lantana.
Ji sukai yace " Me kike nufi da kalamanki?"
Basira ta kalleshi a d'an razane,itakam Lantana jikinta rawa ya shiga yi.
Takowa yai har inda suke, Lantana ta mike da sauri ta koma ciki.
Zama yai daf da mahaifiyarsa gwiwowinsa na kasa yace " Umma meke faruwa? Dama ni nasan akwai abinda kika dade kina b'oyemin sai dai nayi alkawari bazan taba fara miki magana ba."
Jiki a sanyaye cikin sanyin murya tace " Tabbas akwai abinda nake b'oyema, a koda yaushe in nai yunkurin sanar dakai sai inji bazan iya ba saboda tsoron kar in sa ma d'aukan fansa a ranka."
Yace " Umma dan Allah ki sanar dani tun daga farkon rayuwarki."
Basira ta numfasa sannan tace " Sunana Basira........................................................................"
Haka Basira ta zayyanemai kaf abinda ya faru da ita tundaga fyaden da aka mata zuwa auranta da Mai Martaba ba da sanin matansa ba, har zamanta a can gidan da kuma zaman da tai anan gidan, da matsalolin data samu bayan ta samu ciki har zuwa haihuwar tashin hankalin da ta fuskanta na zuwan Hisham da jin maganganunsu.
Tana kuka tace " Kaji dalilin dayasa muka taso a gidan Malam"
Idanun Abu Turab sun kada sunyi wani mugun jaa, ita kanta bata taba ganinsa cikin wannan yanayin ba, fuskarta ta canza bakinsa kawai yake motsawa ta ciki, sai dai kaga alamu ta waje.
Handkerchief ya zaro daga aljihunsa ya mika mata baice komai ba ya juya ya fita.
Tabbas tasan ya shiga cikin tashin hankali, sai dai ita kanta mikin daya fara dishashewa a xuciyarta ne ya tashi.
Sam ko sandar ma bai d'auko ba, yana kokarin shiga b'angarensa yaji muryar Abdulmajid "Kai Blind man."
Wani mugun kallo ya juyo ya wurgamai sannan ya bud'e kofa ya shiga ciki.
Abdulmajid ya juya ya kalli masu kula dashi cikin tsananin mamakin abinda ya gani yace " kunga idanun Abu Turab? Ba kallona yai ba kuwa?"
Sukam basu gani ba sukace " Tuba muke ranka ya dade amma bamu gani ba."
Cikin fada yace " karya kuke munafukai, xakuce baku gani ba, anya kuwa idanun makaho ne wannan?"
Abu