Showing 138001 words to 141000 words out of 146065 words

Chapter 47 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

inalilahi a ransa, kallan Turab yai sannan yace " jeka zauna."
Turab ya mike ya koma gun xamansa.
Gaba d'aya d'akin yayi tsit kowa ya koma gun zamansa, Sarki ya mike tsaye tare da zare rawanin kansa ya ajiye akan teburin dake gabansa, sannan ya tako a hankali har zuwa inda Magajiya take gaba d'aya kana kallanta kasan a tsorace take, kallan ta Sarki yai ya dade idanunsa na kanta sannan ya kalli Hisham, sannan ya maida dubansa kan Abdulmajid, haka yabi kowa da kallo d'aya bayan d'aya.
Akan Barde ya tsaya yace " Barde jeka taho da gawar Hajiya."
Nan barde ya mike.
Sarki ya kalli Magajiya sannan yace " kafin in sallaci gawar Hajiya inkaita makwancinta inaso in sanar da abu d'aya kafin in yankema Matarnan hukunci, daga wannan lokacin na ajiye mukamin mulkin Masarautar Zazzau, sannan na d'aura d'ana Abu Turab a wannan matsayi, wannan matar a d'aureta da kaca itada d'an uwanta Waziri a rufaffen d'aki, sannan bazan yanke mata hukunci ba d'an da take neman ganin baya, wanda ta makantar dashi bayan neman ajalinsa, wanda ta ke neman halaka masa rayuwa a koda yaushe shine zai yanke mata hukunci da kansa, sannan na umarceshi da yanke mata hukunci mai tsaurin gaske."


Ya juya ya fara takawa kallo d'aya zakamai kasan lalai yana cikin tashin hankali.
Matan sarki ne suka mike suka bi bayansa.


Sunje zasu fita daga kofar Magajiya cikin karaji tace " KAI ABDUSSALAMAD!"


Gaba d'aya d'akin kowa juyowa yai ya kalleta tace " mene? Kaba Abu Turab mulki? Inji uban wa? Inji uban wa? Kana tunanin ni Magajiya zan yarda wannan dan tsinaniyar yahau mulki? Mafarki kukeyi daga kai har yan d'akin nan, indai har ni inada.........."


Kasa karasawa tai jin muryarta ta sarke, duk yanda tai gun yin magana ta kasa, tsugunnawa tai da sauri tare da rike wuyanta, a hankali kowa na d'akin ya fita wannan abu yafi komau yi mata ciwo, balle tana kallan Abdulmajid Khadija ta turashi a kekensa sunyi gaba, ga magana ta tsaya cak.
Masu tsaro ne sukazo inda take rike da kaca, Hisham aka fara sawa kaca, kallan Magajiya yai yace " Allah ya isa tsakanina dake, shawararki itace tasa zuciyata ta rikid'e gaba d'aya, sannan maganarki bazata taba d'aowa ba wannan rana itace rana ta karshe da kikai magana da bakinki, domin kuwa inbaki mantaba da gubar da kikasha danyima Basira sharri, a lokacin dana amshi wannan gubar dama ansanar da sharad'inta, bata fita duka a jiki sannan kar babba wanda ya wuce shekara 45 yasha wannan gubar sannan duk sanda ran wanda yasha gubar nan ya baci sosai to xata cigaba da mai illa ta cikin jikinsa, sannan idan tai nisa xata jawo kurmancewa, sannan zata nakasa gab'obin jiki."


Kakari ta shiga yi idanunta kamar zasu fito, kirjinta ta shiga bugawa da karfin gaske, Hisham yace " kina tunanin duk abinda kikemin a banza?"
Ya juya yai gaba.


Durkushewa tai cikin tashin hankali tana rike da wuya, tana wani irin gurnanin gaske.


Bayan sun fita ne daga d'akin Turab ya kalli Bilkisu yace " bari muje mu d'auko Hajiya."
Kallansa tai cikin tsananin tausayawa sannan ta daure ta kakaro murmushi tace " to, bari inje gun Umma."


Gun Abdulmajid taga ya nufa, ya kalli Khadija yace " kawoshi zamu gun jana'iza tunda anan za'ai."
Khadija ta saki hannun kujerar data rike tana kallan Turab, bai ko kara kallanta ba ya tura Abdulmajid.
Suna d'an matsawa kadan Abdulmajid dake hawaye yace " Turab ta yaya xan iya zuwa gun jana'izar Hajiya?"
Turab yace " me kake nufi? Kai ba d'an Abba bane ko me?"


Abdulmajid ya juyo ya kalli Turab idanunsa na kara zubar da hawaye, Turab ya kalleshi yace " meye hakan kuma?"


Abdulmajid ya maida kansa kasa.


Bilkisu ta kara kallan Khadija wacce ke tsaye kusa da Mahaifiyarta.
Karasowa tai kusa dasu tace " ciki zaku shiga gun zaman makoki?"
Umma ta kalleta da idanunta da suka kod'e tace " ta yaya zamu iya shiga ciki? Da wani idon zamu kallesu?"
Khadija tace " mun gode da kulawa amma....."
Bilkisu ta katseta tace " in kuna ganin hakan ne yadace ba matsala."
Ta juya ta fara tafiya.


Sai datai nisa sannan ta juyo ta kara kallen inda suke, can ta hangosu sunyi nisa.


Juyawa tai ta nufi bangaren Umma.


An d'auko Hajiya an mata wanka an mata sallah sannan an kaita gidanta.
(Allah ya mana kyakyawan karshe Ameen suma Ameen)




Ana gama jana'iza Abdulmajid ya kallu bawansa yace " mu fita."
Turashi yai sukai waje.
Motarsa ya sakashi sukai waje.
Sai a sukai nisa akan titi sannan Ya juyo yace "ina zamu?"
Idanunsa a rufe yace " ina zani? Ni kaina bansan inda zani ba, banida gun zuwa......"
Hawayene suka kara zubomai.
Yace kaini can bayan gari iska nake san sha, nan ya kara jan motar sukai gaba.


Sunyi tafiya mai nisa kafin su fita can wajen gari.
Sai daya gangara gefen titi wajen wata bishiyar darbejiya katuwa yace " nan yayi?"
Abdulmajid ya kalli gun yace yayi.
Nan ya fito dashi ya d'aurashi kan kekensa.


Abdulmajid ya kalleshi yace " barni anan kai tafiyarka."
Yace " Yarima....."
Abdulmajid yace " ina san kasancewa ni kadai, sannan karka kara kirana da Yarima."


Jiki a sanyaye ya kalli Abdulmajid sannan ya hau mota ya koma.
Yana komawa gidan sarki gun Abu Turab ya nufa ya sanar dashi abinda ya faru.
Turab wanda dama nemab Abdulmajid yake yace " kasan gidan Barde?"
Yace "eh"
Turab yace " kaje gidan kace Umma na naiman Mairo in ta fito ka kaita gun Abdulmajid a hanya ka ce mata injini nace Abdulmajid na cikin wani yanayi tai kokari ta taimaka ta dawo dashi nan."


Yace to, Turab yace " ni ban isa fita ba cikin wannan yanayin." nan ya amsa da to yai waje.


Gidan Barde ya nufa yai yanda Turab yace mai, a mota tana shiga ya sanar da ita sakon Turab.
Gaba d'aya ta kagu su isa inda yake dan jitai gaba d'aya jikinta yayi sanyi, dan ta tabbata tunda taji Turab ya ce a sanar da ita haka to tabbas babban abu ya faru.


Suna isa ta fito da sauri ko motar bata rufe ba ta taho inda yake da sauri.


Daga dan nesa kadan ta tsaya tare da kuramai ido, kallanta shima yakeyi idanunsa na zubar da hawaye.
Jitai idanunta sun ciciko, a hankali take takawa zuwa inda yake idanunsu nakan juna.


Kusa dashi ta tsaya sannan a hankali tace " me kakeyi a nan?"
Idanunsa ya rufe tare da kokarin shanye kukansa, tace " me kakeyi anan?"
Kallanta yai sannan yace " Maryam ni ba d'an Abba na bane."
Tace " mene?"
Hawaye na zubomai yana dariyar takaici yace " iyayen da kike tunanin iyaye nane ba sune suka haifeni ba."


Yanzu kam ta fahimceshi sai dai ta tabbatar inta nuna karayar ta to lalai batasan wani hali zai shiga ba, ta daure tace " to sai ka canza daga Abdulmajid dan ba sune iyayenka ba?"


Ya kara cewa " yariman da nake tunanin ni yarima ne mai jiran gado ashe ni ba kowan kowa bane."


Tace " dan kai ba yarima bane sai aka canza ka daga Abdulmajid?"


Hawaye suka sake zubomai yace " wacce ta d'auki ciki na ta haifen ko sau d'aya ban taba girmamata ba da sunan uwar data haifeni."


Yanzu kam sai da hawaye suka gangaro mata tace " Yanzu lokaci bai kure ba ai..."


Yace " Maryam duk wata rayuwa da kika sani nawa ta karyace."
Tace " hakan na nufin a karyar harda san da kake min?"


Hannu yasa ya share hawayen yana girgiza kai, kara takowa tai wanda takun ya zama ta karasa daf dashi ta tsuguna inda yake sannan tace " then it's okay."


Kallanta yai sam ya kasa magana, murmushi ta mai sannan tace " me yasa bakazo guna ba?"
Yace " ta yaya zanzo bayan ina tsoron kiji abinda ke faruwa, da wani ido kike tunanin zan kalleki? Ga takurar da namiki a da, wanda nije sanadin hanaki auran wanda kike......"
Hararsa tai tace " ka taba ganin wanda ya auri mijin wani? Duk aurab da kaga anyi a duniya to dama wannan auran Allah yayi sai anyishi, duk kuwa kiyayar dake tsakanin masoyan biyu, duk kuma inda kaga aure bai yiwu ba to lalai dama Allah baiyi za'ai wannan auran ba, duk kuwa da irin san da suke ma junansu."


Yace " amma ai nasan kinasan Turab, inaji kamar nine sanadi..."
Tace " ina sanshi kam, sai dai yanzu a wannan lokacin na tabbatar san da nakemai yana neman zama past tense."
Kallanta yai, murmushi tai tace " Turab yace ka koma ai jana'iza dakai."


Ta mike dan taji kunyar kalamanta ta rike keken zata tura.
Kansa ya juyo saitinta yace " Maryam me kike nufi????"
Harararsa tai tace " abinda nake nufi bansan ragon namiji."


Kara kallanta yai yace " Maryam kina nufin......"
Tace " tambayarka nai? Inka fahimci me nace sai ka had'iye a ranka."


Bai san sanda wani lalausan murmushi ya bayyana a fuskarsa ba.....






Magajiya kam an rufeta ruf a wani d'aki wanda yake dulum duhu gareshi sosai, an d'aureta cikin kaca, abinci sai dai a turo mata ta karasa ta d'auka taci.


Gashi bata saba cin irin wannan abincin ba, ga ta da gardamar tsiya, gani take tafi karfin haka, kin cin abincin tai har dare.
Wani irin ciwon ciki ne ya shiga murd'a mata, ga bata isa yin magana ba.........




*TURAB*
*KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*Nayi mistake wancan page din zan saka 87 na kara sa 86*


*88*


Gidan ya cika taf ana ta fama zuwa gaisuwa, Turab jefi jefi yake kallan Mahaifinsa wanda yake ta amsar gaisuwa daga manya manyan mutane, bayan anyi sallar la'asar ne Sarki Ya shiga d'akinsa tare da bada umarnin a kira masa Turab.


Ya dade sosai baiyi magana ba kafin yace " wanene mahaifin Abdulmajid?"
Turab ya kalleshi a sanyaye yace " Abba!"
Sarki yai saurin cewa " su waye iyayensa?"
Turab yace " d'an gidan Waziri ne."
Kallansa Sarki yai yace " waziri?"
Turab yai kasa da kansa.
Idanu ya dan runtse kafin yace " Tun yaushe kasan maganar nan?"
Turab ya d'ago yace " sanda na fahimci abinda sukama Hajiya, daga nan ne abubuwa dayawa suka fara bayyana."


Shiru ne ya ratsa kafin Sarki yace " Allah kana ganin abinda ya sameni, kaine ka bani mulkin nan ba ni na ba kaina ba, saboda mulki an bani d'an da ba nawa ba a Matsayin nawa, sannan an halakamin matan da zasu haifar min, an kuma halakamun nawa jikin dan kar na haifa, sai dai duk da haka bazanyi fishi ba saboda ka bani wannan d'an da ke gabana, Allah ina rokanka daka karemin wannan yaran daga sharrin duk mai sharri ka kuma bashi ikon rike mulki da taimakon talakawa, ka bashi ikon yin hukunci na gaskiya ba san rai ba, ka karemin shi daga had'uwa da wanda zai nufeshi da sharri, Allah ina rokonka wannan yaran............."


Kasa karasawa yai saboda muryarsa da yaji ta fara rawa.
Duk dauriyar zuciya irin ta Turab sai da hawaye suka zubo masa,kallan Mahaifinsa yake cikin tsananin tausayawa, lalai yau Allah ne kadai yasan yanda bawan Allahn nan yake ji a ransa.
Sarki ya kalleshi yace " Abu Turab."
Nutsuwa Turab yai tare da tattara hankalinsa kan mahaifinsa dan ya fahimci magana mai mahimmanci yake san yi.
Sarki ya cigaba " zan d'auki ragowar mata na uku zamu koma can wajen gari inda nai katan gidana, inaso daga anyi sadakar uku inyi murabus in baka mulkina sannan in tattara inbar gidan nan."
Turab yace " Abba akan me zakayi murabus?"
Sarki ya girgiza kai yace " kana tunanin bayan faruwar wannan al'amarin zan iya cigaba da zama akan mulkin nan?"
" to me kayi? Duk ai laifin ba naka bane na Umma Magajiya ne."
Sarki ya girgiza kai yace " Me kakeso ince? A matsayin na sarkin garin zazzau wanda ya kasa kula da matarsa? Ko a matsayina na sarkin garin wanda matarsa tafi karfinsa?"


Turab ya motsa baki yana sanyin magana, sarki yace " na gama yanke hukuncina sannan umarnine daga Sarki bawai mahaifinka ba."
Turab yai kasa dakai.
Sarki yace " sannan Magajiya, Hisham da Matarsa, inaso kowa kamai hukunci dai dai da laifinsa, sannan kada ka kuskura ka sassautama d'aya daga cikinsu, wannan ma umarni ne."
Turab ya kalleshi yace " Matar Waziri?"
Sarki yace " kwarai, a matsayinta na uwa, akan me zata amince da abinda mijinta da kanwarsa suka tsara?banda itama tana san jininta yahau mulki?"
Turab ya had'iyi wani abu tunowa dayai mahaifiyar Khadija ce.
Sarki ya cigaba " sannan duk wanda suke da hannu akan al'amarin nan, da al'amarin Hajiya inaso ka hukunta kowa, shima umarni ne."
Turab yace " to Ranka ya dade."
Sarki yace " Abdulmajid......."
Sai kuma yai shiru dan baisan me zai ce ba, Turab ya kalleshi yace " Abba, me zai hana mu bar maganar matsayin Abdulmajid a junan mu?"
Kallansa Sarki yai yace " mene?"


Turab yace " Abba wace rayuwa Abdulmajid zaiyi in har akasan asalin abinda ya faru dashi?"
Sarki yai shiru.
Turab yace " Abba idan muka duba wannan lamari wanda akafi cuta ba kowa bane sai Abdulmajid, gaba d'aya shine aka ruguzawa rayuwa, sannan shine wanda za'afi tausayama."
Sarki yace " Abdulmajid ni kaina bazanso akan laifin da banasa ba ya shiga garari na rayuwa ba, amma kana tunanin hakan zai yiwu?"
Turab yace " a lokacin da akai maganar nan akwai mutane dayawa, sannan shi sirri duk yanda akaso da b'oyeshi in har akwai mutanen da suka sani to fa ba wani abu da za'a iya yi, ina tunanin mai zai hana tunda yanada ilimi sannan yanada babbayar hanya na matsayinsa na d'an Sarki a nemar masa aiki babba na gomnati yabar garin nan, yanda baya kusa ma balle gulma a dameshi, sannan yanada matsayin da ko asiri ya tuno ba abinda zai sameshi."


Sarki kallansa kawai yake cikin jin dadi, yace " lalai Kai Kainuwa ne, dashe ne wanda Allah yai, ba shakka kasata xataji dadin mulkin ka."
Turab ya sunkuyar da kai cikin jin kunya.
Sarki yace " ni kuma zan kwabi duk wanda ke d'akin sannan ni zan sa a bashi aikin ba sai ka wahala ba."
Turab yace " Godiya nake, amma Abba mai zai hana ka cigaba da zama anan ko dan shawara da nunamin hanya?"
Sarki ya girgiza kai yace " Turab kasan me yasa ake kishi, gaba, tsana, sharri da mugunta akan mulki?"
Turab ya gurgiza kai cikin rashin fahimta, Sarki yace " saboda duk wanda ya d'and'ani mulki sai yayi da gaske zai iya yageshi daga ransa. Mulki abu ne mai dadi wanda a hankali yake halaka zuciya, idan na zauna anan to lalai zuciyoyinmu sasu dinga samun sab'ani, wannan dalilin ne yasa kaga ba'a fiya yin murabus a mulki ba, har sai rai yayi halinsa."


Turab yai shiru baice komai ba, Sarki yace " ka sa a sanar da matan nawa hukunci na."


Turab yace " To Abba."


Sarki ya mike ya shiga band'aki.
Nan Turab ya taso.


********


A can wajen gari kuwa bayan sun shiga mota ita da Abdulmajid, habu na waje a tsaye ta kalleshi tace " Turab yace amaidakai gun zaman makoki."
Yace " Maryam wai ta ina zan iya zama agun?"
Tace " Dama shakuwa ta d'a da mahaifi bata shiga sai jini ya ratsa?"
Kallanta yai baice komai ba, tace " ka taba ji ance d'a da uba ko d'a da uwa sun hadu amma basu san juna ba?"
Yace " eh in rabuwa ta hada iyayensu ko aka tsinci yaran."
Tace " Shi shakuwa da kauna tana shiga zuciyoyi ne basai jini ya ratsa ba, na tabbata Sarki a zuciyarsa kana nan a matsayin d'ansa, sannan kaima na san yanda kake kaunar Sarki a matsyin mahaifi bazai canza ba."
Murmushi ya mata yace " lalai zuciyata tana cikin kunci sai dai wani bangaren yana cikin tsananin farinciki, dan inaji inhar kina tare dani ba bakin cikin da bazan iya shanyewa ba, sannan duk wani tashin hankali inaji indake to lalai komai zaizomin da sauki."


Harararsa tai tace " a hakan? Kana kukan?"
Yace " ai samun nutsuwa danai ne ya sani kukan."
Ta kara harararsa tace " Gaskiya Abdulmajid kai dan yaudara ne."
Yace " ban gane ba."
Ta hade rai tace " inba haka ba ya akai kasan kalaman da zasu sa mace tai sanyi?"
Dariya yai yace " inhar kalamai nane suka saki yin sanyi lalai ban yarda ba, dan kuwa na tabbatar da tuni kin amince dani."
Hade rai tai tace " amma ai kasan nasan tarihinka da ko?"
Yace " Maryam wallahi ai na rantse miki ban taba sanin wata 'ya mace ba, na dai yarda da nayi lalata na taba mace wanda nake dana sani sosai, sai dai Allah bai taba bani damar lalata da wata ba."
Kallansa tai tace " me yasa to in aka ce kanayi baka musawa?"
Yace " Ince me to?"
Tace " yanzu fa kana tunanin bazaka sake ba?"
Da sauri yace " Maryam baki yarda da irin san da nake miki bane?"
Had'e rai ta sake yi tare da gard'e hannayenta tace " inafa nake da tabbas, abu na d'a namiji?"
Yace " Maryam wallahi........"
Sai kuma ya kalleta yace "Wait...Maryam kina nufin kin amince dani a matsayin abokin rayuwarki kenan?"
Baki ta tabe tace " hmmm waya sani?"


Wani lallausan murmushi ne ya bayyana a fuskarsa yana mata kallan tsantsar so wanda ba algus a ciki.
Mairo ta kalleshi tace " yanzu zan maidakai gida kai zaman makoki."
Kai ya d'aga kawai yana murmushi, tace " tambaya biyu zan maka, Waziri shine mahaifinka?"


Abdulmajid ya d'aga kai tare da kallan window, tai murmushi yake, tace " Mai zakayi idan Babana ya hanani kai?"
Yace " Zanyi iya kokarina wajen ganin ya aminta dani."
Tace " shikenan."


Murmushi sukama juna, sai da aka fara ajiyeshi ta tabbatar Habu ya kaishi gun zaman makoki sannan ta shiga gun Umma.


Tana shiga Gimbiya na kokarin fita, Mairo ta bita da kallo, kafin ma acemata jikinta ya bata itace, saboda yanayin shigarta.
Tace " Gimbiya Barka da warhaka."


Bilkisu ta juyo ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login