Showing 57001 words to 60000 words out of 146065 words

Chapter 20 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

ya jinjina yana murmushi yace " na d'an manta kadan."


Kula ta nuna mai tace " gashi kaci inkaje can, Goggo ce tace in kawoma, nasan in mace zan bika hanani zakai."


Kallanta yai yace " akwai maganar ma danakeso muyu dake, kizo mu tafi tare, in kuma da abinda zakiyi kizo ko zuwa gobe ne."


Kallansa tai cikin mamaki tace " yaya? Wai da gaske kake?"
"Me kika gani?"
Zatai magana ta hango Khadija a kusa dasu kad'an ta kura musu ido.
Mairo ta kalleshi tace " yaya anzo gunka."
Juyawa yai ya kalli gun, sannan ya juyo yace " zamu tafi sai na ganki."
Mota ya bud'e ya shiga.


Dama su Basira sun shiga tasu motar.
Nan aka jasu shi da Garzali, Basira kuma da Lantana.
Yana kallan Khadija ta glass har suka wuce.
Ba shakka har zuciyarsa yanajinta, balle yanda yaganta a tsaye tana kallansu ya tabbata taji ba dadi na ganinsu tare.


Motarsu na wucewa Khadija ta karaso gun Mairo ta kalleta jiki a sanyaye tace " wani asibitin zasu?"
"Me yasa baki tambayeshi ba?"
Khadija ta kalli Mairo tace " Mairo menene tsakaninki da ya Turab?"
Mairo ta kalleta cikin mamaki, ita ya kamata ta mata wannan tambayar, zatai magana taji ta kara cewa " ko da yake bake ya kamata in tambaya ba."


Juyawa tai zata tafi, Mairo ta kalleta tace " wani abu ya hadaku da Yaya ne?"
Khadija ta juyo sai dai batace komai ba.
Mairo tacigaba " Kinaso kicemin bakisan wa yaya yake so ba?"


Khadija ta kwakwalo murmushin takaici tace " na sani yanzu, nasani ni kadai nake bilayi na."
Mairo zata sake magana taga Khadija tayi gaba.
Kallan mamaki ta mata tace " Wai batasan ita yaya yake so ba?"




Juyawa tai itama ta fita....


*TEAM ABU TURAB🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*37*




Sun isa asibiti Doctor Jamil wanda ya kasance director ne a wannan asibiti, matsayi da girmansa yasa mutane suke karramashi dayawa, sannan ga kokarin yin aiki da kyautatama wanda bashi dashi.
Kafin su isa dama Sarki ya sanar dashi komai hakan yasa suna isa wani yaransa yazo ya kaisu wani d'aki, wanda yasa aka kamashi domin su.
D'aki ne babba gani matsayi da mukamin wanda zai zauna a d'akin, Dr Jamil da kansa yazo, bayan sun gaisane ya nemi keb'ewa da Abu Turab, hakan yasa Basira da Lantana suka koma gida tunda akwai masu kula dashi.
Dr Jamil ne ya kalli Abu Turab yace " Yarima ni kaina nayi mamakin jin abinda ya faru, dan mun taba had'uwa dakai lokacin bakafi shekara 13 ba, sosai na d'auka baka gani."
Abu Turab ya d'an murmusa yace " ya fad'ama komai kenan?"


Murmushi yai sannan ya matso tare da nad'o wani abu kamar kyale yace " sry fa zaka zama makaho na kwana biyu."
Ban fahimta ba?
" zamu kula da kai zuwa gobe, sai muce an maka aikin gobe, sannan mu rufe idanuwanka na zummar mun maka aiki, zamu jira zuwa awa 24 sannan mu duba muga ko an samu cigaba, kaga a kalla xamu kai zuwa kwana biyu saboda kar mutane su fahimta, in mun since sai kuma ka jira ko da kwana 3 zuwa hudu ne sannan mu sallameka."


Abu Turab ya jinjina kai sannan yace "Na fahimta na kuma gode sosai, Allah ya saka da alkairi."


Kafadarsa ya dafa sannan yace " Karka damu, d'a kake a gurina abinda zan maka banaji ma zan wa nawa 'ya'yan domin Abdussamad ya taimakeni dan shine silar zamana duk abinda na zama a yanzu."


Abu Turab ya kalleshi sai dai baice komai ba.
Dr Jamil yace " duk abinda kake bukata ka fito ka sanar dani, kaji?"
Abu Turab yai murmushi sannan ya d'aga kai alamar to.


Zarya kawai take a cikin d'akinsu, hankalinta ya gaza kwanciya sam, ganin ba haza ga yamma tayi ta jawo hijab dinta ta fito da sauri.
Tana kokarin fita Mahaifiyarta na kawo kai.
Tsayawa tai, Ummanta ta kalleta tace " Khadija ina kuma zaki?"
Bakinta ta d'an motsa kamar zatai magana sai dai bata ce komai ba.


Kallanta ta karayi tace " dama fad'amiki xanyi yanzu mahaifinki ya dawo yace in sanar dake Saifullahi yazo yana gun Magajiya, nan kuma bayan Magrib zai shigo."


Gabanta ne ya fadi dan ita sam ta manta da wani Saif da ake san bata.
Ta kalli Umma tace " Umma nifa na d'auka an bar maganar nan."
Ambar maganar kamar ya kenan? Khadija wai me kika d'auki maganar mahaifinki ne?


Kasa tai dakai sannan tace " naji Umma kiyi hakuri amma dan Allah yanxo zan d'an fita kadan ba dadewa zanyi ba."


Ina zaki?
Yanzu zan dawo nan kasan layi zani.
Umma tace " kinga dai magrib ta kawo kai karki dade.


Da sauri ta wuce ta a tafe tana amsa wa da to.


*******




A bakin asibitin ta sauka ta fito ta shiga ciki, tsayawa tai tana tunani inda zata nufa, Allah ne ya taimaketa ta hango Garzali.


Da sauri ta karasa gunsa, shikuma lokacin yana kokarin komawa ne dan yaje gida d'auko wani sako da Abu Turab ya aikeshi.


Sai data kusa isa tad'an kwalla mai kira, juyowa yai yana ganin itace ya karaso da sauri sannan ya gaisheta.


Amsawa tai sannan ta d'ora da cewa " ina akwma kwantar da Yaya? Muje ka nunamin."


Garzali yace " to ranki ya dade."


Nan yai gaba ita kuma tana binshi .


Sunyi tafiya mai d'an tsawo kafin su isa d'akin.
Nan yai sallama ya shiga tare da ajiye mai ledar aiken, Abu Turab ya kalleshi zaiyi magana ya hangota tsaye a jikin kofa.


D'auke kansa yai daga inda take yace "Garzali kai ne? Har ka dawo?"


" Nadawo Ranka ya dade, sai dai bani kadai bace."


Zai sake magana Abu Turab yace " karka damu jeka."


Garzali ya fita daga d'akin.


Tana tsaye a kofar, gani tai ya koma ya kwanta.


A hankali tasa kafarta cikin d'akin, sai dataje kusa dashi ta bayansa ta kuramai ido cikin sanyin murya tace " Yaya ina wuni?"


Shiru yai baice komai ba, zama tai a kujerar dake jikin gadon da alama wani ne ya jawota ya zauna agun, kallansa tai bayan ta zauna ta sa hannunyenta kan gadon tana wasa da hannu a hankali ta ce " Yaya ina cikin wani hali, duk duniya kai kadai ne nakejin zan iya sanar mawa, na rasa yanda zanyi, ina tsoro abubuwa guda uku."


Shiru tai kafin tai ajiyar xuciya ta cigaba " ina tsoron Abbana da Umma Magajiya dan na tabbata ba tun yanzu ba suke aikata laifi, na biyu ina tsoron kar a cutar dakai."


Shiru tad'an sakeyi tad'an furzar da iska sannan tace " yaya, bansan ya zanyi ba da alama maganar Saif tananan, ni kuma......"


Kasa karasawa tai saboda zuciyarta dataji tayi rauni.


Abu Turab yana jinta har kuma zuciyarsa yakejin kalamanta.


Hawayen dayad'an ziraro mata ta goge, tai murmushi sannan tace " Yaya sai dai akwai wani abu da yake sani farin ciki, inajin dadi sosai da wannan aikin da za'ama, na rasa meyasa inaji a jikina lokacin ganinka yayi, sannan inhar kana gani ina ganin ba yanda su Abba zasuyi."


Murmushin yake ta sake yi tace " Kayi hakuri na takurama da nakeyi, na sani yanzu bakasan kula ni."
Ta mike jiki a sanyaye tace " Yaya inaso kasa abu d'aya a ranka, wlh wlh ni bazan taba cutar dakai ba bama kaiba, bana fata in cutar da kowani mutum a duniya, ko da kuwa a rashin sani ne."


Juyawa tai xata tafi, dan dama wannan amsar itace wacce ta dade tanasan ta bashi, tayaya yaya zai dubeta yace mata wai itama tana da tabbas din bazata cuce shi ba?"


Sai datakai kofa ta juyo tace " Allah ya baka lafiya Yaya."


Nan ta juya tai gaba, juyowa yai da sauri ya kalleta, bayanta ya kalla lokacin data rufe kofar.
Idanunsa ya runtse sannan yad'an had'a lab'ansa.


Ba shakka sai ya jure sosai, dan a lokacin datake magana jiyai kamar ya juyo ya lalasheta, Saif? Saifullahi? Wa kenan?"




Tunowa yai da abinda Mahaifinta ya musu, kwafa yai sannan ya juya.


Itakam tana fita ana kiran sallar magrib.


A can gida kuwa sai nemanta akeyi dan kuwa Saif kafin ai sallah ya iso,anan sukai sallar Magriba, sai dai shiru ba Khadija.


Hankalin Waziri da Mahaifiyarta ya tashi sosai.


Nan yasa aka fito dan nemanta.


Saifullahi yaro ne ga Senate Kassim, 'yan siyasa ne sannan bayan siyasa sun gaji kudi.


******,*




Mairo kuwa da yamma itama ta shirya fes dan zuwa gun Abu Turab saboda shi yace mata tazo akwai maganar da zasuyi.


Ta fito zata fito ta gami dashi a zaune a ciki motarsa a kofar gidansu.


Yi tai kamar bata ganshi ba xata wuce, Abdulmajid ya fito daga motar xai nufota, da sauri ta koma ciki.


Komawa yai ya xauna a saman mota dan jiranta, Mairo kam tana shiga ciki ta dafa kirjinta tace " nikam wannan akwai dan masifa, na tabbata kuma tsabar rainin hankali ne ke damunsa wlh ba so ba, wannan wani irin rainin hankali ne.


Itakam tsoronta d'aya shine karta fita tana mai magana Mahaifinta ko wani ya gansu a sanar mai.


Dole ta koma ciki fitar da batai ba kenan.










*ABU TURAB TEAM🤝🏻*








🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*




_Gaisuwa Gareki Kawar Arziki *Faizah* nagode kwarai da kauna, Allah yabar zumunci Ameen suma Ameen_




*38*





A kwanar gidansu ta tsaya, tana tsaye tana kallan gidansu daga d'an nesa, ita a rayuwarta bataji zata iyama wani saurayi kara, Abu Turab take so ba taji zata iya zance da wani.


Juyawa tai, sai dai ina zata? Idanunta ta d'an runtse kadan sannan ta cije lab'anta, a hankali take takawa harta kusa isa gidan.
A waje taga mahaifinta shida masu musu hidima na gida, sunyu carko carko.

Tsoro yasa tad'an hanzarta dan ta d'auka ko wani abun ne ya faru.
Tana zuwa kusa dagun fitilar dake kofar gidan ta hasko ta.
Wani daga cikinsu yace " Yallabai gatannan."


Nan kowa ya juyo ya kalleta, Waziri ya kalleta cikin takaici sai dai alama ya mata akan ta wuce ciki.
Nan ta shiga gida, ko d'aki bata shiga ba ya shigo ransa a b'ace yace " Khadija ke ba....."
Kallan idanunta yai yaga sunyi jaa sosai da alama har kuka ma tayi.
Yana san yarinyar jiyai bazai iya mata fada ba, yace " jeki kintsa kizo ku gaisa da Saifullahi, tun dazu yake jiranki."
"To, amma banyi sallah ba."


Kiyi sauri kiyi kizo yana jiranki.
Tace to.
Juyawa tai ta shiga d'aki.
Ummanta tana kitchen tana duba kayayyakin abincin da za'a kaimai.


Sallah tai sannan ta gyara fuskarta, ta jawo hijabinta ta zura.
Mahaifiyarta ce ta shigo kallanta tai tace " Khadija ina kika je?"
Shiru tai hakan yasa tace "ki canza kaya kisa sabo."
Tana kainan tai waje.
Labanta ta ciza na takaigi sannan ta kwabe kaya tasa wani.
Fitowa tai ta nufi inda Umma ta nuna mata.

Sallama tai sannan ta shiga.


Saifullahi ya amsa sallamar tare da kurama kofar ido.


Tunda ta shigo yake zuba mata murmushinsa na yaudara har sai dataji kafafunta suna neman hard'ewa.
Zama tai daga can nesa dashi, sannan a hankali ta motsa baki tace " Ina wuni?"
Gani tai ya mike ya dawo gabanta inda take zaune, kanta na kasa sai gani tai ya sunkuyo inda kanta yake cikin salonsa na soyayya yace " Gimbiyata sai yau Allah yai."


D'agowa tai tare da d'an jan jikinta baya tace " Saif meye hakan?"
Ajiyar zuciya yai yace " tun randa na ganki a kano sai yau Allah yai na sake ganinki, nikadai nasan dadin danake ji."
Baki ta tabe ba tace komai ba.
Gani tai ya sake matsowa ta d'ago da sauri tana kallansa tana zazzare ido.
Dariya taga yayi yace " Sry mikewa zanyi so nake in kara ganinki sosai."


Mikewa yai ya koma gefenta kadan ya zauna yace " Khadija dan Allah ki saki jiki dani, sam banasan inga mace tana wannan kunyar."


Kallansa tai tace " Ai kuwa mace da kunya aka santa tayaya za'ace ta daina?"
"Oh God c'mon my Khadija."


Yanda yaga tana kallansa alamar tsananin mamaki yasa ya saki dariya yace " Khadija wannan kalan fa? Gaskiya xanji dadi in mukai aure dan inasan wannan kalan dayawa."


"In mukai aure kamar ya kenan?"
Gani tai ya canza fuska yace " bangane ba, kinaso kice bakisan wani watan iyayena zasuzo gaisuwa ba? Daga nan kuma sai me?"


Tsananin mamaki da fargabar kalamansa ne yasata yin shiru, nan fa ta tuno da abin begenta Turab.
Jitai idanunta sun ciciko.
Saif ya kalleta yace " Deejah na menene?"


Kaina ke ciwo, tun d'azu.
Ya kalleta kalar tausaya yace " sannu."
Mikewa tai tace "Saif i am sry amma dan Allah zan je na kwanta, kaina saramin yakeyi."


Kai ya jinjina yace " sannu, jeki kwanta nima gidan kawuna zani gobe da safe zan wuce kano."


Tace " Nagode Allah ya kiyaye hanya."


Tana kai nan tai waje.
Shiru yai sannan ya mike tare da murmusawa.


Tana fita tai hanyar d'akinta jitai Ummanta tace " Khadija? Ya tafi ne?"
"Eh."
Ta wuce ciki.
Kwanciya tai ta shiga yin juyi akan gado.






**********




Magajiya zaune ta a lissafi da hannunta wanda nikaina bansan me take lissafawa ba, Abdulmajid ne ya shigo rai a b'ace, yana shiga ya zauna dabas.
Harararsa tai tace " kai kuma meye hakan? Zaka shigo ba wani tafiyar takama da isa irin na magajin Sarki?"


Kallanta yai yace " Umma ki taimaken ki auramin Mairo, in ban koyama yarinyar nan hankali ba ta hanyar auranta ba, banaji hankalina zai kwanta."


Wani mugun kallo ta bugamai tace " in har koya mata hankalin kake san yi da gaske ai basai ka aureta ba, kawai ka sa a hukuntata."


Kai yad'an sosa yace " Ai Umma.."


Katseshi tai cikin fada tace " badai auren Mairo bakam, nasan sarai me kake nufi, kai maza ka cireta a ranka, na fadama
"


Mikewa yai cikin takaici yai waje....


Ita kuwa Mairo yau bakin ciki duk ya hanata sukuni gashi ta ma Abu Turab girki da kanta, haushi da takaici duk ya gama isarta tana kallo kishiyar babarta da 'ya'yanta suka cinye abincin.


***********


Washegari an rufe idan Abu Turab, mutane sai zuwa dubashi akeyi kowa na kawo abubuwa na kayan dubiya.


Bayan azahar yana zaune yad'an samu ya zare abin da aka d'aure idanun nasa dan hutawa, Garzali ya shigo yace "Ranka ya dade Mairo ce."


Bai maida ba yace "ta shigo."


Shigowa tai fuskarta d'auke da murmushi.
Ta karasa kusa dashi inda kujera take ta zauna, sannan ta kalleshi tace " Inna wuni yaya."
Bai amsa ba yace " Hajiya Maryam na d'auka jiya zan ganki?"
Baki tad'an turo tace " wani bunsuru ne ya tare mana kofar gida ya hana ni fita."
Bunsuru?
Tace eh, amma karka damu ya gaji ya tafi.


Yace " ce miki nai na damu?"
Fuska ta d'an tsuke kad'an tad'an juya kai tace "ba kara?"

Cikin rashin zato taji yace " meye tsakaninki da Abdulmajid?"


Kallansa tai cikin mamaki, zatai magana sukaji an bud'e kofar da karfi.


Abdulmajid ne, Garzali na bayansa yana kokarin mai magana akan karya bud'e.
Abu Turab ya kalleshi sannan ya kalli Garzali yamai alama daya koma.


Abdulmajid me ya karaso ransa a b'ace ya kalli Mairo sannan ya kalli Abu Turab yace " Tsakaninmu kake tambay?"
Abu Turab yamai wani kallo sannan yace " banaji dai acikin kalamaina na sako ka,sannan bakasan laifi bane shigowa mutum guri ba tare da neman izini ba?"


Abdulmajid ya matso saitin Mairo ya tsaya yace " ke harkin isa jiya inzauna jiranki amma kiki fitowa? Shine yau dan kin rainamin hankali in ganki anan?"


Abu Turab a ransa yace " Au kaine Bunsurun?"
Baisan sanda yai dariya ba.
Hakan ya kular da Abdulmajid matuka.
A zuciye ya kalleshi yace " kai kuma me kakema dariya?"
Abu Turab yace " wani bunsuru na tuna, sannan inka gama abinda kake plz kai waje dan na tabbata ba dubani kazo ba."
Kallan Mairo yai yace " wuce muje."
Harararsa tai tace " inje ina? "
Wuce muje nace ko?
Tace " yau naga ikon Allah a matsayinka na wa?"
"Mene?"
Tace " ban fahimta bane ina zaune kawai kace in tashi muje."
Ransa yakai kololuwar baci dn dama Magajiya ce tasashi wannan zuwa dubiyar anma da yasan abinda zaigani kenan ko abinda zata mai kenan a gaban yaran nan da baizo ba...
Kwafa yai sannan yai waje a zuciye.
Yana fita taja tsaki.










*TEAM ABU TURAB 🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*39*


Yana fita Abu Turab ya kalleta tare da daure fuska yace " Mairo, Abdulmajid d'in ne Bunsuru?"


Tace "laa yaushe nace haka yaya? Nifa zancen da nake daban."
Girman idanunsa ya rage yace " fad'amin tsakaninki dashi."
Tace " ni meye tsakanina dashi kuwa? Nema kawai yake ya takuramin da kuma san ya wulakantani."


Shiru yai sannan can yace " amma kamar yana sanki."
Dariya tad'anyi, sannan tace " kai ka yarda yaya? Wannan ne yake so na? Banaji yasan ma menene soyayya abu d'aya ya sani shi...."
Sai kuma tai shiru, kallanta yai yace " me ya sani?"
A ranta tace " neman mata mana, amma a fili tace bakomai."
Ganin batasan fada yasa yace " ki dai bishi a hankali kinsan halinsa sarai."
Baki ta tabe batace komai ba.
Ta dade sosai a asibitin dan sai da su Basira sukazo sannan suka tafi tare da ita, Zuciyar Basira fal da farincikin ganin yanda Mairo take kula da Abu Turab.




*************


Magajiya ce ta shirya tsaf tasa aka mata girke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login