Showing 123001 words to 126000 words out of 146065 words

Chapter 42 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

haka."
Sarki ya kalli Turab bayan ya zauna yace " me kakeyi anan kabar yar mutane ita kadai, ba kayi dubiyar ba?"
Yace " yanzu nake kokarin tafiya dama inasan zuwa gunka ne nida Umma."
Magajiya ta kalleshi sai dai kafin tai magana yace " Dama wani abu nake san......"
Katseshi magajiya tai da sauri tace "Ya kamata ka koma gida ko? Ba dadi ango daga aure ace yana waje."
Turab ya kalleta sannan ya kalli Hisham wanda yai tsuru tsuru yace " Magana ce akan Abdulmajid."
Yanda gaban Magajiya ya ke faduwa zata iya cewa wannan shine rana ta farko da takejin faduwar gaba haka ba kakkautawa dan tabbas tasan so yake ya sanar da tsakaninta da Abdulmajid......
Meye mafita?
Kafin kwakwalwarta tai aiki muryar Turab taji yace "Umma maganar da mukace zamuyi da Abba akan abinda ya samu Abdulmajid, ina ganin dolene ga Waziri anan wanda nake tunanin yafi kowa sanin abinda ke faruwa."


Wata irin ajiyar zuciya ta saki wanda sai da kowa ya kalleta.
Kallan Hisham tai sannan ta kalli Turab a ranta tace " tanan ka b'ulo?"
Hisham kam gaba d'aya ya rasa abinda ke mai dadi, ga Abdulmajid yace karya kuskura ya aminta akan shine sila.
Magajiya ta kalli Turab sannan ta kalli Sarki tace " haka ne Turab sai dai ina ganin abari yaji sauki tukunna kafin ai wannan maganar."


Turab ya kalleta yace " haka ne amma bakya tunanin kafin nan wanda ya aikata laifi ya kamata shima ya fuskanci, ba dai saboda zargin da akema yayanki bane yasa kike......"
Wani mugun murmushi tai tace " Kana tunanin in har Waziri nada hannu a ciki zan nemi birne laifinsa?"


Turab zaiyi magana sarki yace " ya isa haka, ina kuma tunanin tunda naji maganar na kuma sam mai ya faru yanzu dolene ayi bincike a fada, gunda alkalai suke."
Hisham! Kaine ka aikata?"
Hisham ya kalli Abdulmajid sannan ya kalli Magajiya tunowa yai da Khadija wacce ta fito da akwatinta a gida tana jira ta tafi aka aiko yazo shine yace ta jira ya dawo.


Ina zai sa kansa?
Magajiya tsoro take kar magana ta shiga fada dan tabbas in ta shiga daga bincike sai ance meye dalilinsa na aikata hakan, daga nan kuma tana tsoron kalaman da zasu fito daga bakin Hisham in yaji ana tsananta bincike a kansa.




***********








Turab ne ya kalli Magajiya wacce fuskarta yau ta bayyana da shakka karara, murmushi taga ya sakar mata a ransa yace " are u scared?"
"In kika tsorata tun yanzu the game will not be fun."
Idanun Turab kawai take kallo..........




*TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*79*




Mikewa tai tace " Turab me yasa kuke san bud'e abu cikin bainar jama'a? Me zai hana........"ganin irin kallan da Turab, Sarki da Abdulmajid suke mata ne yasa ta fahimci tana neman kauce hanya, daurewa tai sannan tai wani murmushi tare da komawa ta zauna tace " Yaya! Abu d'aya zan tambayeka kafin in cigaba da magana, da gaske kaine ka nemi halaka Abdulmajid?"
Hisham ya kalleta cikin mamaki dan shi gaba d'aya ya rasa ma mai zaice, Abdulmajid ya kalla wanda shima kallanaa yakeyi.
Turab ya kallesu sannan yace " Abba da alama ya kamata kaba Umma lawyer cikin gida."
Kallansa tai tace " mene?"
Turab yai dan dariya yace " menene na tada hankali Umma? Naga kamar kina neman d'aurama Waziri laifin da ba lalai shine ya aikata ba."
Bakinta ta dan motsa sannan tace " me kakeso kace a takaice?"
Sarki ya kalleshi sannan ya kalli Hisham yace " Waziri!"
Hisham ya rusuna da sauri, takawa yana kallansa yace " me zaka iya cewa game da abinda ke faruwa a d'akin nan?"
Hisham yai kasa dakai cikin tashin hankali, Sarki yace " jeka jirani a fada in har bakada abin cewa anan, to lalai zaka samu abin cewa a can, saboda dolene ka sanar damu dalilin dayasa ake zarginka."
Hisham yace "Tuba nake ranka ya dade amma ni kaina bansan dalilin dayasa akemin wannan zargin ba."
Turab yace " gaskiya ne, nima kaina ban fahimci me yasa ake ma wannan zargin ba, me ka aikata takamaima? Shi yasa nake ganin gwara aje fada yanda za'a tabbatar da zargin da akema ba gaskiya bane."
Abdulmajid yace " Haka ne, nima ina tunanin hakan yafi Umma."
Magajiya ta kalleshi gabanta na faduwa sai dai jin wata dabara ta fad'o mata yasa ta murmusa tace " hakan yayi, sai yaushe yanzu za'ai zaman?"
Turab ya kalleta, kamar wanda ya shiga ranta sai jitai yace " Abba gani nake yanzu in har ba abinda zakai gwara ai shari'ar nan yanzu, in ba haka ba shi kansa Waziri banaji zai samu kwanciyar hankali."
Takawa yai gyaran murya sannan yace " hakan yayi, ina neman Waziri da Turab a fada nan da minti talatin."
Abdulmajid yace "Abba nima ina neman alfarma dan hallarta."
Sarki ya kalleshi yace " karka damu, kai dai ka kula da kanka."
Abdulmajid kasa yai da kai dan shi kam yafisan yasan kome ke faruwa a idanunsa.
Turab ya fahimci haka sai yace " Abba zaman asibiti ba dadi mai zai hana mu nemi sallama, in yaso saboda kafarsa sai a dinga turashi a kujera?"
Sarki yace " a'a ku barshi anan dan samun lafiyarsa."
Magajiya kam kamar wanda aka nausa a ciki haka taji ta, tsananin tashin hankalin data shiga, dolene a cikin minti talatin d'in nan tai tunanin abinda zata tsarama Hisham dan fad'a a fada dan in batai da gaske ba lalai asirinta zai tuno, ita tsoronta ma wannan munafikin yaran dazai kasance a gun.


Sarki ne ya mike sannan yai waje.
Yana fita Turab ya mike shima yai waje dan ya tabbatar Magajiya tana bukatar kadaicewa da yayanta.
Abdulmajid ta kalla sannan tace " Abdulmajid bari in raka Yaya tunda fada zai wuce."
Kai kawai ya d'aga.
Suna fita ta mai alama daya biyota, sai da sukai tafiya sosai gun da ba mutane sosai, yau ko tafiyar kasaitar ma batai ba, suna shiga gun daba mutane ta juyo tace "Yaya ya zamuyi?"
Hisham yace "game da me kenan?"
Tace " ina tsoron kar muje akwai wata shaida da wannan yaran yake dashi na kana da hannu akai, dan yanda yake magana na tabbata akwai wani abu a kasa."
Hisham ya kalleta yace "ni ba wannan ne a gabana ba Khadija na gida tana jirana."
Kallansa tai tace " Waziri!"
Kallanta yai dan yanda ta kira sunan alamace ta ranta ya baci, Magajiya ta had'e rai tace " me kake san kace? Ba damuwarka bane ko me ya faru?"
Ya kalleta yace " ba haka nake nu......"
Tace " ko ma menene ba damuwa ta bace, abu d'aya na sani idan har ka kuskura ka bari sunana ko alamun sunana ya fito daga cikin wannan abu to ba shakka zan iya yada kai, kafi kowa sanin wacece ni, akan kaina ba abinda bazan iya aikatawa ba."
Ta juya ta fara tafiya, idanu ya runtse dan yama rasa ya zaiyi, da girmansa da komai amma yana cikin halin tsoro na jin kunyar duniya, juyowa tai ta kalleshi tace " ahhhh na manta ka kiyayi bakinka tun kafin 'ya'yanka susan kisan kan daka aikata."
Ta juya tai gaba.


Hannayensa yasa ya shafi fuskarsa sannan ya kalli sama, a hankali ya juya yai waje.
Gida ya nufa.
Khadija na kwance akan gado kalaman da taji tsakanin Magajiya da Hisham ne suke mata yawo a kwakwalwar, kalaman da bata taba jin mugayen kalamai irinsu ba, filo tasaka ta rufe kanta wasu zafaffan hawayene suka shiga zubo mata.
Mahaifiyarta ce ta shigo ta kalleta, jikinta ne yai mugun sanyi ta karasa gunta tare da d'aga filon, Khadija ta gani tana hawaye hannunta ta rike tare da cewa tashi khadija.
Khadija ta mike a hankali ta zauna, hannu tasa kan goshinta saboda taji zafi sosai sanda ta rike hannunta.
Jin yanda kanta ya d'au zafi yasa ta kalleta tace " Khadija meke damunki? Meke damunki da kike san tafiya ki bar mahaifanki?"


Khadija a hankali ta kwantar da kanta kan cinyar mahaifiyarta wasu zafaffan hawayene suka zubo mata a hankali tace " Umma mecece rayuwar nan? Me cece a ciki da har mutane ke jefa kansu akan san zuciya wacce ba komai bane a ciki sai tsantsar buri da halaka dake cikinta?"


Umma ta kalleta tace " Haka rayuwar ta maidamu Khadija, ni kaina ina dana sanin abinda zuciya ta sani na aikata, a koda yaushe ina takaicin abinda na aikata."
Khadija ta d'ago ta kalleta tace " Umma!"
Kallanta mahaifiyar ta tai tare da maida hankalinta kanta.
Khadija tace " me yasa kike yadda akan duk abinda Abba yace? Mai kyau ko mara kyau? Haram ko halal?"


Umma idanunta ne suka canza kala tana kallan Khadija, tace " ban taba yimai musu ba haka kuma ban taba bijerima abinda yake so ba, shine ginshikin yan uwana, da abin hannunsa suka zama abinda suka zama yanzu."
Khadija tace " saboda abin duniya? Saboda 'yan uwanki suji dadi kike yarda da duk hukuncinsa? Ba kya tunanin kema kinada kamasho na laifufukan da ya aikata?"


Umma ta mike tare da kokarin maida kwallarta tace " Khadija! Kada ki kuskura kiyi rayuwa irin tawa, kada kisa 'yan uwa da iyayenki gaba da maganar Allah, wannan shine babban kuskuren da muke tafkawa idan Mahaifanmu,mijinmu ko 'yan uwanmu suka samu abu, bama tunanin dacewarsa ko kaucewarsa a addininmu sai muyi kokarin aikatashi dan musu biyayya da faranta musu."
Ta kalli Khadija wacce ke hawaye tace " khadija me kika sani? Me kika ji wanda ya tada hankalinki haka, kin canza, kin rame tunda kikazo ko abinci baki ci ba sannan neman barin gari kike yi, menene kikaji da yasa ko kallan iyayenki bakyasan yi?"


Khadija ta runtse ido wasu hawaue suka fito tace " menene ribarku akan kai Ya Abdulmajid gun Umma Magajiya?"
Gaban Umma ne ya fadi ta kalleta a tsorace, Waziri da tun dazu yake tsaye yana jinsu duk gab'obin jikinsa sunyi sanyi, jin wannan magana ta khadija yasa ya kalli kofar d'akin da sauri, cikin tsananin tsoro.

Khadija tace " kuna tunanin wannan sirri bazai taba fitowa ba? Idan Abba yayi hakan dan samun karfin mulki da juyowar mulki daga zuri'ar jinin sarauta zuwa nashi, kefa?"
Umma kallan Khadija kawai take batasan hawaye na zubo mata ba.
Hisham juyawa yai jiki a sanyaye yai waje zuwa masarauta, dan bazai iya jin naganganunsu haka ba.

Umma ta tsugunna a inda take tare da dafa kanta, Khadija kuka take dan bazata iya fadar dayan abinda taji ba dan ta tabbata Umma batasani ba, sai yanzu ta fahimci tsantsar dalilin dayasa Turab ya canza mata, ba shakka ba yanda za'ai sanda yake mata yai tasiri in har yasan sirri nan, bayan ita din jinin Hisham ce bawai rikonta akai a gidan ba.....




************


A cikin fada kuwa Sarki na zaune akan kujerarsa ta mulki cikin nad'i na sarauta, Galadima da Barde su kadai aka kira sai alkalin cikin gida.


Sai dogarawa dake tsaye a gefe, Turab ne ya shigo ya zauna a inda ya kamata, shiru sukai suna jiran Hisham dan isowarsa.


Galadima ne ya kalli agogo yace "Ranka ya dade minti 15 ya wuce daga lokacin daka bashi."


Sarki yace " a kara mai minti biyar."
Minti biyar ce tai, Barde yace " minti biyar tayi ranka ya dade."
Sarki ya kalli Alkali yace " wannan alama ce ta ya aikata abinda ake tunanin ya aikata ko?"
Turab kam addu'a kawai yake akan Allah yasa ya zo.


Alkalin zaiyi magana aka sanar da isowar Waziri.
Wani irin dogon numfashi Turab yaja na jin dadi.
Wannam shine shafin farko na d'aukan mataki akan abinda Magajiya ta aikata musu, shi, mahaifiyarsa, Sarki, Abdulmajid da Khadija.


Bazai so wani abu ya jawo rashin zuwan Hisham ba.




**********
Mairo kam duk ta rasa me ke damunta, ba shakka tunanin halin da Abdulmajid yake ciki shine ya dameta, yaci abinci? Ya sha ruwa? Karfa tun abincin data bashi har yanzu bai sa komai a cikin sa ba?
Mikewa tai zaune daga tsintar wanken da bata san ma me takeyi ba.


Tace a fili, zanje in dubashi ne bawai dan na damu da halin da yake ciki ba, sai dan zuciyar muslunci da tausayi.
Kai ta d'aga tace " ai duba mara lafiya ma babban aikin samun lada ne, dan haka dubiya zanje bawai dubiya zani saboda Abdulmajid ba....."


😄😄😄😂Nace anya kuwa Maryama????


*Turab*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)





*HASKE WRITERS ASSOCIATION*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*Na Ayusher Muhd🤸🏼*


*80*


Kowa da ke cikin gurin ne ya zuboma Hisham ido, jiki a mace ya shigo ya zauna.
Galadima ya kalleshi sheke ke ya tuno abinda dansa ya sanar dashi, ba shakka ko waye ya ji dolene yasan da hannun Hisham a wannan lamarin inba haka ba ta yaya ya san inda aka kai Abdulmajid?
Gyaran murya da sarki yai ne yasa kowa ya nutsu, Takawa ya kalli Hisham sannan ya kalli Alkalin yace " a fara."
Nan alkalin ya ciro takardar ya fara karantawa kamar haka.
" A jiya ranar lahadi ne aka kawo karar Hisham wanda akace ya nemi da a kama Abdulmajid wanda hakan ya jawo masa karaya a kafarsa da kuna manyan ciwuka a gab'obin jikinsa."
Kallan Hisham yai yace " Hisham kana da abin cewa a game da laifin da akace ka aikata?"
Kalaman Abdulmajid ne suka fad'omai ya kalleshi yace " ta yaya zan so wani abu ya samu d'an kanwata? Ni fa na kasa fahimtar takamaimai me na aikata"


Galadima yace " ina muka san manufarka?"
Turab ne ya d'ago sannan ya kalli Hisham ya juya ya kalli Alkali yace " Gaskiya ni kaina na kasa gane takamaimai me ka aikata, zuwa gun d'aurin aurena dakai ka tambayeni a inda na taho? Ko kuwa jin Abdulmajid ya taho a motar daya kamata in taho da kaji hankalinka ya tashi? Ko kuma ganin da Sabi'u yama ka je ka d'auko Abdulmajid? Ni kaina Mai Martaba na Kasa gane mai Waziri ya aikata."


Hisham yace " dan na tambayeka in da ka taho gani nake ai ba laifi bane."
Turab ya jinjina kai yace " haka ne, sai Dai ya akai kasan inda Abdulmajid yake farat d'aya? Ba tare da bincike ba?"
Hisham ya d'ago ya kalli Sarki.
Sarki ya kalleshi yace " amsarka nake san ji."
Hisham ya daure yace " nima ba sani nai ba bincike nai har Allah ya kaini gun."
Galadima yace " gaskiya kam, ai hakan zata iya faruwa, amma ni a sanina Sabi'u baiga alamar bincike a tattare da kai ba."
Hisham ya kalli Galadima cikin takaici sai dai bai amsa ba.
Turab ya mike ya dawo gefen da Hisham ke zaune ya kalli sarki yace "Ranka ya dade menene dalilin daya sa Abdulmajid ya shiga motar da ta kasance mota ce wanda Ango zai shiga?"


Kallan Hisham yai yace " Waziri mai kake tunani?"
Hisham ya kalleshi dan bai fahimcu me yake nufi ba.
Turab yace "baka tunanin yaji wani abu game da abinda zai faru?"
Idanu Hisham ya zaro yace " kanaso kacemin Abdulmajid yasan abinda zai faru a ranar?"
Turab yace " ranar? Wace rana kenan?"
Hisham kallansa yai sannan yace " bansan me kake so kace ba."
Turab yace " zata iya yiwuwa, sai dai da alama bakwa tunanin abinda Abdulmajid yakeji a wannan lokacin, ace yayan mahaifiyarsa shine ya nemi halaka mai rayuwa, ko meye ribarka........"
Cikin zafi Hisham yace " kai yaro, ya isheka haka, har yaushe aka haifeka da zaka zo ka dinga d'aure magana? Hauka nakeyi da zan nemi halaka Abdulmajid? Tsautsayi ne dai ya afka ya shiga motar da bai kamata ya shiga ba, amma ni ban yarda ya ji ba, ni ina tunanin kai ne ka sashi ya shiga motar ma."


Kallan Turab sukai, Shikam bai san sanda ya sa dariya ba, yana dariya ya sunkuyar dakai yace " tuba nake ranka ya dade, bansan sanda dariya ta kwacemin ba, ni? Meye ribata in nayi hakan?"
Hisham yace " ka hau mulki ba tare da matsala ba mana."
Turab yace " kana so kace in har d'aya ya kauda d'an uwansa a tsakaninmu d'ayan zai hau mulki ba tare da matsala ba kenan?"
Hisham yace " Sai ka tambaya?"
Turab yace "ahhh na gane, amma in na kusa damu ne suka neman taimaka mana gun rage mana iri fa?"
Hisham yace " ban fahimceka ba."
Turab ya kalli Alkali yace " ina so a duba maganar Hisham kamar haka, na farko yace Tsautsayi ne dai ya afka ma Abdulmajid ya shiga motar, na biyu zuciyarsa tana tunanin halaka junanmu shine hanyar da ya fi cancanta d'ayan mu ya hau mulki, sannan bai musa ba akan shi da wani sun aikata wani abun tunda sanda na cemai Abdulmajid yaji bai musa ba akan bai san me yaji ba sai cewa dayai wai bai yarda yaji ba."
Ji sukai " Abu Turab kuka so ya shiga motar?"
rq
Gaba d'aya kallan mai martaba sukai wanda idanunsa ke kan Hisham, ya cigaba " motata dana bada ta ango ce, menene dalilin dayasa ba'a tare ko wace mota ba sai ta Ango?"


Turab Murmushi yai dan dama shi bai isa yai tambayar nan ba, fatansa d'aya mahaifinsa yai.


Hisham ya rikice ga tsananjn kwarjini na idob Sarki, kalaman Khadija ne kawai suke mai yawo, meye ribarsu?meye ribarsu? Duniyar ma nawa take?
Sarki a zafafe yace " Dakai nake magana Hisham."


Hisham ya kalli Sarki a tsorace sannan ya kallu Alkali.
Turab ya kalleshi, Hisham duk ya rikice.
Turab ganin ya gama rikicewa yai sauri yace " Waziri nine bakasan gani a duniyar? Me na tare ma?"
Kallan Turab yai yana huci yace " tambaya kake? Zuwanka duniya shine abu na farko da mukai dana saninsa."
Sarki yace " mene?"
Hisham ne ya kalli Sarki a tsorace sannan yai saurin sukunyawa duk jikinsa rawa yake, ina zai sa kansa?me zaice wanda bazai taba rayuwar Abdulmajid ba.


Turab jiki a sanyaye yace " kai da wa kukai dana sanin zuwana duniya?"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login