Showing 120001 words to 123000 words out of 146065 words
Chapter 41 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
ne ke faduwa dan ma tasan ba sallah take ba.
Harta runtse idanunta tana tunanin zatajishi kusa da ita ko wani abu.
Toilet ya shiga sannan yace " A shirya lafiya."
Ya karasa maganar tare da tura kofar.
Kallan kofar tai sannan ta saki wani ajiyar zuciya kafin tai wata yar siririyar dariya.
Turab shima yana rufe kofar ya saki wani ajiyar zuciya, yana mamakin me ke damunsa? Bayan bai tabajin haka ba,yaji wai zuciyarsa na kwadaitamasa taba mace?
*********
*TURAB*
**********
.🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*77*
Tana shiga kilisarta Magajiya dake zaune ta mike tsaye sannan tace " biyoni.
Sai da suka shiga cikin d'akinta Magajiya ta zauna akan kujerarta sannan tama Jakadiya alama da hannu akan ta matso inda take.
Jakadiya ta karasa gun ta zauna sannan tace " Barkanki da Safiya...."
Magajiya ta kalleta tace " Me kuka kulla ke da Turab?"
Gabanta ne ya fad'i tace " ban fahimt......"
Kinaso in sake maimaitawa?
Jakadiya tace "Ai ban fahimceki bane Magajiya."
Magajiya tace " ba sai kin fahimceni ba, sannan nayi kuskure ma dana tambayeki, abinda ya dace shine ki jira kiga yanda wanda ya ci amanata yake kasancewa, dan wlh sai na baki mamaki."
Jakadiya tai kasa dakai tare da fashewa da wani irin kuka tace " Magajiya ni na isa naci amanarki?bansan komai a abinda kike fadaba, ni dama wata magana nazo sanar dake banyi tunanin neman da kikemin da biyo kike min ba."
Magajiya ta kalleta tace " magana?"
Jakadiya ta juya ta kalli kofa sannan tace " naji wani abu wanda ya tsoratani."
Magajiya ta kalli kwayar idanunta.
Jakadiya ta dan had'iyi yawo tace " Jinai Abu Turab yana magana wacce ta tsoratani tsantsa, ta yaya akai kika bari yaran nan yasan sirrin nan namu?"
Magajiya ta kalleta tace " me kike nufi?"
Jakadiya ta matso tace " Jinai yana cema Basira wai Abdulmajid d'an Waziri ne, wannan labarin ya tadamin hankali tsantsa, ta ina yaji? Garin kuma yaya?sirrin da mukai alkawarin rikeshi har bayan ranmu?"
Magajiya jitai hannunta na rawa, ta daure ta kalli Jakadiya tace " bani guri."
Nan Jakadiya tai wuf tai waje kai kace dama jira take ace ta fita.
Tana fita Magajiya ta dafa kanta, tabbas yasan sirrin nan, garin yaya? Dolene ta b'olo da hanyar da zatasa ya kasa fadan komai, amma Basira ta sani ai, tabbas sai tayi dogon nazari.
**********
Sai daya cire kaya ya gama wankan sannan ya tuna ba towel a cikin toilet din.
Tsayawa yai, yai shiru yana tunanin mafita.
Ita kuwa Bilkisu ta shirya tsaf cikin wani had'ad'en leshi mai kyau, peach colour tayi kyau sosai, tana kokarin kame kanta da ribbon ne taji alamar kwankwasa kofa, kallan band'akin
tai tana mamaki, sannan ta mike tazo kusa da toilet din tace " Daga nan ne?"
Turab yai gyaran murya, tace " wani abu kake so?"
Iska ya furzar sannan a ransa yace sai ince bani towel?
Itace ta katseshi da cewa " Yarima?"
Turab yace " towel zaki d'an bani."
Idanu ta zaro sannan tace " to."
BJuyawa tai ta d'auko sabon towel ta kwamkwasa a hankali ya d'an bud'e kofar tare da zuro hannu, ita kuma ta juya kanta tana ta mikamai, yana kokarin kamo towel ya kamo hannunta, shiru ne ya biyu baya batare da ya sake ta ba, a hankali ya shafa zuwa kasan hannunta ya ja towel din.
Itakam gaba d'aya jikinta yayi sanyi tanaji ya turo kofar band'akin ya rufe.
Juyowa tai ta kalli toilet din sannan ta murmusa.
Turab kam shima a ciki yana rufewa yai murmushi sannan ya sa towel din, tana jin alamun zai fito ta fita falo.
Sai da ya shirya tsaf sannan ya fito falon, tana zaune kan kujera, kasan carpet din an jera musu kayan abinci kala kala, kamshin turarensa ne yasa tasan ya fito.
A hankali ta lumshe idanunta.
Kallanta yai yace " Amarya kin tashi lafiya?"
Murmushi tai tace " ina kwana? Kaga ka sa ban gaisheka ba sai daka fara tambaya ta ya na tashi?"
Yace " daga masallaci na biya wani guri ne."
Tace " ayya! Kaci abincin sai muje gaisuwa."
Gaisuwa?
Tace " eh, zaka kaini in gaida matan Sarki."
Yace " ohh lalai, to sauka muci abincin."
Tace "nasha madarar shanu ni sai anjima zanci."
Bai ce komai ba ya zauna a kasan carpet din, yana kokarin bud'e kula ta sauko tare da d'aukan plate ta zuba mai.
Kallanta yai fuskarsa d'auke da murmushi yace " masu aiki nawa kikeso a turo nan bangaren?"
Tace " amin uzuri da masu aikin nan, tun ina karama komai sai dai amin banasan a gidan mijina ya zamana komai sai dai amin, ni ba abinci na iya ba ba shara na iya ba balle wanke wanke, banaso akawo mutanen da zasusa ya zamana kula da kaina da mijina sai dai amin."
Kallanta yai cikin jin dadi yace " Kina tunanin zaki iya?"
Tace "ummm"
Yace " shikenan zan sanar ma Umma."
Ya gama cin abinci sannan suka nufi bangaren Matar sarki ta biyu, sai da suka gaisa sannan sukaje gun ta uku, duk inda sukaje sai kowa yai mamakin tsananin kyau irin na Gimbiya, sannan suka nufi bangaren Magajiya.
Tasa an had'a abincin sha da kayan marmari an jera a falon ta dan dama tasan da zuwansu, taci kwalliya na gani na fada kai kace wani had'ad'en taro zata hallarta.
Sai da suka zauna sannan ta fito cikin isa da izzarta.
Gimbiya tayi zama irin na 'ya'yan mulki a gaban iyayensu Kanta na kasa ta shigo.
Magajiya ta zauna tare da kallansu, Turab yace "Umma Magajiya Barka da Safiya."
Tace " Ango na d'auka zaka bari sai zuwa jibi, irin wannan wahalar da amarya haka?"
Ta fada tana kallan Bilkisu.
A hankali ta d'ago ta kalli Magajiya, idanunsu ne suka had'u, Bilkisu ta sakar mata wani sansanyan murmushi tace " Barka da Safiya."
Magajiya idanunta na kanta tace " Amarya barka da shigowa masarautar Zazzau, dafatan zaki samu kwanciyar hankali kamar yanda kike samu a can."
Tace " Karki damu indai farin ciki ne Umma dan na tabbata d'anki zai kula da ni sosai."
Ta rasa meyasa taji zafin kalamanta, bayan ba wani abun ta fada ba, amma me yasa takeji kamar magana ta fada mata?
Daurewa tai tace " Haka akeso, ai Turab yaro ne na gari."
Bilkisu tace "Godiya muke, dan yabonki yana nuna hakan take a gun al'uma."
Magajiya ta kara kallanta, me yasa yanzuma taji maganar ta bata mata rai?
Turab kam murmushi yai yace " na d'auka kina gun Abdulmajid."
Tace " dama ku nake jira mu gaisa sai in fita."
Yace " ohh amma da sai naji kamar kince da mun bari sai nan da kwana uku."
Ta kalli Bilkisu tace " hmm ai da dai ka barta ta huta d'in."
Bilkisu tace "godiya nake da kulawa, amma Umma duk wani hakkina ina ganin gwara nayishi lokacin daya dace."
Tace "haka ne."
Turab kallan Magajiya yake yana mamakin yanda take amsawa Bilkisu duk da dai yasan da bakunta amma yasan dukda haka wannan ba style dinta bane.
Basu wani dade ba suka fito, har ya kai falo tace " Turab."
Dawowa yai ya shigo d'akin, kallansa tai tace "Magana nakesan muyi."
Yace " banaji akwai wata magana data rage a tsakaninmu a wannan lokacin, sannan asibiti nakeso na tafi dan kuwa naji labarin Abdulmajid ya farfado inada bukatar jin wanene a kuma garin ya ya aka aikata mai hakan."
Magajiya zatai magana yai gaba.
Yana fita ta mike tare da matse hannayenta, Abdulmajid?
Yana fita itama ta mike ta sanar da masu kula da ita akan zuwa asibiti.
********
Hisham ya gama galabaita gaba d'aya ya wuce asibiti dan ganin Abdulmajid da jikinsa, yana zuwa ya tadda khadija a zaune ta had'a gwiwarta da kanta a kan sallaya.
Yana shiga ya tafi da sauri inda take ya rike hannayenta ya d'agota yace " Khadija!"
D'agowa tai sannan ta kura mai idanunta da suka kumbura, wanda har fuskarta itama ta kumbura.
Muryar Abdulmajid yaji yace " Khadija zaki iya komawa gida da kanki?"
Kallansa tai batace komai ba, yace " kije gida ki jira Waziri, ko kuma kije waje ki jirashi yazo kuje gida, magana zamuyi."
Mikewa tai kamar wacce ba tada laka a jiki tai waje ko kara kallan Mahaifinta batai ba.
Tana fita Hisham ya matso yace " Abdulmajid yaushe ta dawo....?"
"Ba wannan bane abinda yasa nace zamuyi magana, tambayarka nakesanyi."
Hisham ya kalleshi gabansa na faduwa.
Abdulmajid yace " menene tsakanina dakai?"
Hisham ya had'iyi yawo yace " naam?"
Abdulmajid yace " ni d'anka ne?"
Hisham kallansa kawai yake dan bashida amsar da zai bashi.
Abdulmajid yace " inaso daga rana irinta yau ka cire batun nan a ranka dan bazanci amanar Umma ba, ban damu da wanene ya haifeni ba wacce ta raineni itace Uwa a gareni, akan Umma zan iya juya ma baya zan kuma iya tozartaka, kaine ka d'aukeni ka bata dan haka babu damuwata akan duk wani abu da zai shafeka."
Hisham bai taba tunanin abinda zaiji daga gareshi ba kenan, yace " Abdulmajid kanaso kace ni dana haifeka banida matsayi a gunka?"
Yace " matsayi? Kai kasan wannan, sannan ka gaggauta maida Khadija kano inhar kanasan rayuwarta ta daidaita, sannan in har kanaso in d'inga ganin kimarka da darajarka a matsayin wanda ya haifeni ti ka tabbatar ka fita hanyar Umma ta, sannan ko da wasa naji labarin ka aikata abu irin kwatankwacin abinda ka min banaji zan iya yafe maka."
Hisham da sauri ya d'ago ya kalleshi yace " naji bazan aikata ba ko kadan amma laifin dana aikata a baya fa?"
Abdulmajid ya ce " au akwai abinda ka aikata irin wannan a baya? To a wannan d'akin inaso ku warware a lakar dake tsakaninmu."
Hisham ya matso da sauri yace " Abdulmajid kayi hakuri wlh....."
Idanu ya runtse sannan yace " naji amma kada ka kuskura abinda ka aikata ya fito fili dan bazan iya kallan mutane ba in har abinda ka aikata ya fito fili, ciki kuwa harda abinda kamin."
Hisham da sauri yace " naji, naji."
Abdulmajid yace "kaje gun Khadija, ba dadi take ji ba."
Nan yai waje.
Yana fita ya kalli kofa sannan yai ajiyar zuciya, yace " anya Turab wannan hanyar zata bule?"
Tunowa yai da kadan daga cikin kalaman Turab dayace " ka tabbatar ka nunama Waziri kai a bayan Magajiya kake sannan ka nuna masa in har ya amsa laifinsa to lalai kai dashi har abada........"
Tunowa da ragowar kalaman yai a ransa sannan yace a fili " Turab kenan, wato in Waziri ya ki amincewa da laifinsa sannan ya fahimci ni a bayan Magajiya nake lokacin ne kishi zai afko a tsakani, ita zataji haushin kin amsa laifinsa wanda za'ai ta bincike gun gano gaskiya, sannan shi kuma zaiji takaicin bijerewata zuwa gun magajiya, idan ya raba tsakaninsu sai ya sani nasa Umma ta fadi laifukanta da kanta cikin ruwan sanyi ba tare da tasan abinda takeyi ba, saboda yardarta gareni ganin na ki mahaifina saboda mulki............"
Murmushi yake yai ganin ya fara hada kan puzzle din da Turab ya bashi, a fili yace " daidai nake aikatawa??????"
Nikam da sauri nace " Kwarai😄😂"
*TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*78*
Hankalin Hisham yayi tsananin tashi yana fita jiyai jiri na neman d'aukansa sai daya dafa bango.
Daga nesa ya hango Khadija a zaune a jikin bango tana bin mutane da kallo, tsananin tausayinta ne ya kara ratsashi, shi dai bai ga ranar da wannan buri nasa ya masa ba, ina amfani gaba d'aya ya tarwatsa rayuwar 'ya'yansa?
Kusa da ita yaje yace "Khadija "
Kallansa tai sai dai ba magana, yace " tashi muje."
Mikewa tajeyi da yake batada karfi tai kamar zata fadi, da sauri yasa hannu ya rikota yace "yi a hankali."
Hannunta ta fizge sannan tai gaba.
Kallabta yai jiki a sanyaye suka shiga mota, ya ja sukai gida.
Har suka isa ba wanda yai magana a cikin motar, tana shiga gida ta wuce d'aki ta sauko da akwatinta ta shiga had'a kayanta.
Umma ce ta shigo cikin kulawa tace "Khadija ya jikin Yari......"
Ganin tana had'a kaya yasa maganarta ta tsaya, kallanta tai tace " Khadija me kenan?"
D'agowa tai ta kalleta sai dai bazata iya cewa komai ba dan ta tabbata tana magana kuka ne zai zo mata, kurama Umma ido tai a ranta tace " me yasa kikai haka Umma? Me yasa baki hana Abba aikata munanan aiyukan nan ba?"
Kallanta Umma tai tace " Khadija lafiya?"
Khadija ta maida kanta kan kayan ta cigaba da shiryawa, ganin batada niyyar magana yasa ta fito.
Hisham ta tarar a d'aki ya baza uban tagumi, ko sallamar da tai bai amsa ba, tace " Baban Khadija me ke faruwa?"
Kallanta yai shima sororo, tace " ba shiru zakai ba me ke faruwa naga Khadija duk ta canza sannan tana ta faman hada kaya? Sannan ni bakacemin komai game da ciwon Yarima ba kadai cemib kawai bayajin dadi ne......"
Ya isheni haka nan, ki barni da abinda ke damuna dan Allah, haba! Kinsan ya nakeji a zuciyata a wannan lokacin? Komai na neman rugujewa a rayuwata, d'an da nake tunkaho zai ramamin rashin mutunci da cin zarafin da Magajiya tamib yanzu ya rikide yace shi ba wani abu tsakanina dashi, itace uwarsa, sannan Khadija ko kallona basan yi take ba ke kuma zakizo ki sani a gaba kamar wanda ya amshi bashinki?"
Umma tace " ban gane me kake nuf......"
"ba sai kin gane ba, dama ina kanki zai yi aiki? Kwakwalwace dama kamar ta kifi?"
Umma ta juya jiki a sanyaye tai waje, dakin Khadija ta koma ta tsaya kawai tana kallan ikon Allah.
Khadija kam dama tun jiya idanunta biyu taji sanda Turab yace ta koma kano, sannan dama itama bataji zata iya cigaba da zama a wannan garin, Umma ta kalla tanasan mata magana sai dai ta kasa.
Umma idanunta duk sun ciko dan itakam kalaman Hisham sun kona mata rai, inda sabi yaci ace ta saba amma duk sanda ya mata sai ta dingajin ba dadi.
Hanyar band'aki ta nufa bayan ta dau zanin wanka, ta daure tace " kano zan koma."
Ta shige ban d'akin, kallan kofar Umma tai jiki a sanyaye sannan ta mike hartaje zata shiga d'akinsu kuma ta fasa saboda takaici, juyawa tai ta koma d'akin khadija ta zauna.
**********
A bangaren Basira kuwa su Gimbiya anata kunyar suruka, Umma sosai ta yaba da hankalinta, nan tasa aka kawo mata abincin safe jin Turab yace bataci abinci ba, duk da bataso ci ba sai da Umma tasata taci, sun dade kafin Garzali ya turo a sanar da Turab akan zata fita.
Abinda kawai aka ce kenan shiyasa Basira bata fahimcesu ba, Gimbiya kuwa kallansa tai sai dai bata tambayeshi ba, ya kalleta yace " in barki anan ko in maidake can kafin in dawo?"
Tace " ina nan."
Yace " ok, ba dadewa zanyi ba."
Umma ta kallesu tai murmushin jin dadi.
Turab ya juya ya fita, Garzali ya tarar a waje yace " ta fito?"
Yace " yanzun nan."
Turab yace " muje, ka tura a sanar mai?"
Garzali yace " eh Ranka ya dade."
Mota suka shiga suka tafi asibitin, suna kallan motarta daga gaba su kuma suna baya, har suka isa.
Magajiya ta fito ta nufi d'akin da aka kwantar da Abdulmajid.
Turab yana kallanta ta shiga shikuma ya tsaya a bakin kofa.
Tana shiga aka ajiye kayayyakin data kawo, kallan danta tai cikin jin dadi ta matso tace " Abdulmajid? Idanunka biyu?"
Kallanta yai sai dai baice komai ba.
Magajiya ta zauna kusa dashi cikin jin dadi tace " na sani ai, nasan d'ana ta ina magajin sarki zai kwanta kamar bara numfashi?"
Abdulmajid ya murmusa yace " Umma kiyi hakuri na saki damuwa."
Kanta ta girgiza tace " wa ke wannan zancen? Ai farfad'owarka shine komai nawa."
Kallanta yai sannan yace " Umma kinsan Kawu yanada hannu akan abinda aka min?"
Idanu ta zaro sannan tasa hannu a kirji tace " mene?kanaso kace shiya ja maka wannan abun?"
Turab ya murmusa yace " GOOD JOB ABDUL"
Abdulmajid yai kasa dakai cikin rashin jin dadi, Magajiya tace " karka damu ba yayana ba ko Sarki ne ya kuskura ya tab'amin kai bazan taba yafemai ba."
Abdulmajid ya kalleta yace " na sani dama........"
Turo kofar da akai ne yasa shi yin shiru, Turab ne ya shigo tare da sallama.
Bata juyaba amma tanajin sallamarsa sai da gabanta ya fadi, me ya kawoshi?
Turab ya matso yana cewa "Umma ashe kin garzayo."
Juyowa tai ta kalleshi tace " Au Turab kaine?"
Yace "ni ne, kinsan dolene nazo duba Abdulmajid tunda ni aka je halakawa tsautsayi.........."
Katsesh tai da sauri cikin tsoro tace " ina amaryar? Badai barinta kai ba?"
Yace " ya zanyi? Dolece ta sani zuwa ai, naje gunki akan zamu gun Mai Martaba dan yin wata magana ashe ke kina nan?"
Idanunta ne suka fito, duk yanda taso b'oye tsoronta sai da ya nuna tace " ban gane ba?"
Turab ya matso yace " magana ce wacce ya dace ayi gani gaki ga Abdulmajid sannan ga Waziri."
A rikice ta d'ago ta kalleshi sannan ta kalli Abdulmajid tace "Turab wai kwanan nan meke damunka ne? Wuce muje gida mayi maganar a can."
Murmushi yai sannan yace " Bakyaso muyi a nan?"
Hararsa tai tace " muje ko?"
Ta na kokarin mikewa Zagi ya sanar da isowar Mai Martaba.
Kallan Turab tai dan tabbas tasan yasan da zuwansa, murmushi ya mata sannan ya d'an d'aga gira kadan ya juya kai.
Sarki ne ya fara shigowa bayansa kuma Waziri ne ya shigo.
Abdulmajid ya kalli Turab dan baisan me yake shirin aikatawa Ba.
Sarki ya nemi fadawa daau fita dan zai duba d'ansa.
Nan kowa yai waje, kallan Abdulmajid yai cikin tausayawa yace " Ya jikin naka?"
Abdulmajid ya dan sunkuyar dakai yace"Barka da war haka Takawa."
Kallansa sarki yai sannan ya kalli Turab wanda ya rusuna tare da gaidashi, Magajiya ma tace " Barkanka da war