Showing 63001 words to 66000 words out of 146065 words
Chapter 22 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
shigo ya gaida Magajiya da matan mahaifinsa sannan yaja ya zauna, a gun zamansa.
Can aka sanar da Zagi ya sanar da isowar Mai martaba.
"Lafiya Sarkin yakin Sarkin musulmi
Lafiya maida garin wani kango
Lafiya Barden mahadi
Lafiya Sukukun bakaka
Lafiya Darzaza amalen sarakuna
Lafiya ba hau da wani ba sauke wani
Lafiya hana kangara
Lafiya Sakaka babban bako
Lafiya Bango madafar bayi
Lafiya hadarin kasa maganin mai kabido........."
Mai Martaba ne ya shigo Abu turab na bayansa.
Yana shiga kowa yagaidashi.
Sai da ya zauna a gun zamansa.
Gyaran murya yai sannan yace " Nagode kwarai da zuwanku taron nan na taya murnar samun saukin Abu Turab, Allah ya saka da alkairi."
Nan sukace Ameen.
Abu Turab na zaune gefen hagunsa sai tunsu d'aya da Abdulmajid wanda ke zaune a bangaren dama.
Sai daya gaishesu shima kamar yanda Abdulmajid yai sai dai shi sai daya gaida kowa.
An d'anyi shiru kafin Magajiya tace " D'ana Abu Turab fatan alkairi gareka da kuma rayuwarka, yanda idanunka suka bud'e ina maka fatan kyakyawar rayuwa mai d'orewa."
Nan kowa yace "amin."
Abu Turab kallanta yai sannan yai kasa dakai yace " ina godiya Umma Babba na kuma gode da addu'arki."
Murmushi tamai wanda hakan ya d'ansa shi kara kallanta.
D'auke idanunta tai daga kansa ta kalli basira sa nan ta kalli sarki tace " Haikawa Basira ce tace abar mata harkar girke girke."
Murmushi ya saki sannan ya kalli Basira yace " ai ba laifi, hakan yayi."
Mamaki abin yad'an ba Basira dan kuwa ba ita ta nema ba, itace ta ba ta, to meye na fadama ma Sarki?"
An d'anyi hira kad'an kafin Lantana ta shigo ta fara jera abinci, wanda masu kula da bangaren Basira ke rike da tire manya manya.
Da yake abin a tsare yake ,Lantana ta ajiye ma kowa nasa a gabansa.
Nan Mai Martaba ya bada izinin aci abinci.
Sai daya fara ci kafin kowa ya bud'e nasa.
Abu Turab kam ko bud'e nasa bai yiba sai kallan kowa yakeyi yana san yaga inda wani shiri da takesan tadawa.
Kallansa tai ta saki murmushi dan ta fahimceshi. Nan ta bud'e nata itama hankalinta a kwance.
Kafin ta faraci sai data kalli Turab tace " D'ana ya naga ko bud'ewa bakai ba?"
Kallanta yai tare da d'an rage girman idanunsa, sannan yace " yanzu zanci."
Bud'e nashi yai, kallanta ya sakeyi, gani yai tana tacin abincinta hankalunta a kwance, kowa ya kalla yaga kowa yana ci ciki kuwa harda Basira.
Yana kokarin kaiwa bakinsa sukaga Magajiya ta fara wani abu, da sauri Abdulmajid ya mike cikin tashin hankali.
Nan fa kowa ya yo kanta, kumfa ne ke fita ne daga bakinta, idanunta sai farfari suke.
Abu Turab ya runtse idanunsa da karfin gaske, sanna ya bud'esu sun kada sunyi ja, hannayensa ya saka duka biyun ya shafi fuskarsa abinda ta shiya kenan?
Mai Martaba ne cikin tashin hankali ya kalli Abu Turab sannan ya ce " Turab yi sauri kasa a kira mai magani, ya sameta a bangarenta, bari a maidata can."
Nan akai waje da ita, sai amai kawai takeyi.
Basira kam gaba d'aya ta gama rikice wa sai yanzu itama ta fahimci dalilin dayasa tace tai girki.
Abu Turab ya kira mai magani suka isa bangaren Magajiya.
Nan aka shiga mata magani, amai take har yanzu, mai maganin ta d'ago ta kalli mutanen gun tace " guba ce, guba taci."
Hankalin kowa a tashe aka kalli Basira.
Abu Turab yana rasa mai zaice.
Abdulmajid ne ya shigo da gudu cikin dabara ya tura mata wani abu a bakinta.
Aman ya tsaya sai dai da alama hankalinta baya jikinta dan a sume take.
Abu Turab ya kalleta cikin tsananin mamaki, yau abin harya kai ta nemi halaka kanta? Akan mulki? Akan ta hanashi auren Bilkisu? Ya tabbata yanzu basuda mafita, in zance ya yado zaije har masarautar kano, wani sarkin ne ko wani uban ne zai bashi aure?
Fitowa yai waje dakyar yake sa kafarsa.
Khadija ce ta karaso da sauri, itada Mahaifiyarta.
Yana kallanta ta shiga ciki kamar bata ganshi ba.
Kallan waje yai mutane sun cika gun sosai, sai gulmar Basira akeyi, kowa na fadan albarkacin bakinsa, shikansa yana fitowa ya fahimci gulmar hardashi.
Wato Basira dan taga d'anta ya warke shine take kokarin halaka Magajiya, sannan ta halaka Abdulmajid ta d'aura nata akan mulki.
Inka ganta kamar bazatai haka ba.
Gulma dai kala kala...
Basira kam tana zaune a falo cikin tashin hankali, ta tambayi masu aikinta kowa yace baisan meya faru ba.
Mairo duk ta rukice itama ta shiga kitchen sai dube dube takeyi cikin tashin hankali.
Kan kace me? Zance har ya fita daga gidan ya shiga cikin gari......
*TEAM ABU TURAB 🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*_Wannan shafin naku ne 'yan Zauren BieBie Isa, tnx alot 4 ur support....Much luv_*
*42*
Abu Turab ya shiga bangaren mahaifiyarsa, ba kowa a falon sai Lantana dake zaune jugum.
Tana ganinsa ta mike ta gaisheshi, kallanta yai yace " Umma fa?"
A hankali tace "tana d'aki."
Juyawa yai ya fita, dayake magrib ta duso massalaci ya nufa.
Ana idar da sallar wasu dan gulma tun a cikin massalacin suke yan gulmace gulmacen maganar, mikewa yai ya fito.
Bangaren Mahaifinsa ya nufa.
Jakadiya tana ganinsa ta iso gunsa ta gaidashi.
Kallanta yai yace " Mai Martaba fa?"
Tace " Yana ciki, a ma iso?"
Kai ya d'aga mata alamar eh, har ta fara tafiya sai ta dawo gunsa tace " Hmm nikam Yarima naji abinda ya faru, sai dai kuma hmm tuba nake ranka ya dade amma ni nasan akwai alamar tambaya a al'amarin nan."
Gefe da gefe ta kalla tace " Sai dai neman Allah ya fitar da ku lafiya."
Kauda kansa yai daga kanta dan shi sam bayasan harkar gulma tunda kuwa yaga yanda take wani juye juye yaji ransa ya baci.
Juyawa tai, bata dade ba sai gashi ta dawo tace ya shiga.
Abu Turab ya shiga.
A zaune ya tadda mahaifinsa sanye da tabarau, rike da wata takarda da alama karantawa yakeyi.
Abu Turab ya shiga sannan ya kara gaidashi.
Sarki ya zare tabarau din ya kalleshi yace " Turab ya akai?"
Abu Turab ya kalleshi yace " Abba, na tabbata kasan Umma bazata aikata wannan laifin ba."
Murmushi yai sannan yace " bansan komai ba Turab, bansan ko zata aikata ba ko bazata aikata ba."
Kallan mamaki Abu Turab yamai yace " Abba."
Sarki ya kalleshi kallo wanda bazaka tana fahimtar yanayin da mutun yake ciki ba yace " Abu Turab ba dai so kake kacemin in yarda da Basira ba, bayan a gabana Magajiya ta fadi?"
Abu Turab cikin mamaki ya kalleshi yace " Amma......"
Katseshi yai yace " In har kanaso in yarda da Mahaifiyarka to inga evidence wannan shine kadai abinda zan fadama."
Abu Turab yai shiru" nagode." Kawai abinda yace kenan yai waje.
Mai Martaba ya bi bayansa da kallo cikin tausayawa a fili yace " Abu Turab dolene sai ka yaki weakness dinka, Magajiya ta riga tasan Basira tace lagwanka, tunda nake bantaba ganinka cikin damuwa kamar tayau ba.
Abu Turab yana fita ya nufi bangarensa, sam ya rasa dalili zuciyarsa ta kasa bashi wata mafita, kwakwaran tunani ma ya kasayi, mahaifiyarsa kawai yake hangowa lokacin da ta kalleshi cikin wani yanayi, kallo d'aya yamata ya fahimci tsantsan tashin hankali karara a idanunta.
Wannan rana ta zame musu ranar tashin hankali, Abu Turab da Basira.
Magajiya kuwa ta daina amai sai dai har alokacin bata bude idanunta ba a haka a ka kwana, khadija ce ta zauna a gunta.
Washe gari da safe yana zaune a d'aki Garzali ya kwankwasa mai kofa.
Mikewa yai ya bud'e, kallansa yai yace " Garzali ya akai?"
Garzali yace " Sabi'u ne ya zo Ranka ya dade."
Bai koma ciki ba kawai ya jawo kofar d'akin ya fito falo.
Garzali yabi bayansa.
A zaune yaga Sabi'u.
Kusa dashi ya karasa ya mikamai hannu sukai musabaha.
Sabi'u ya kalleshi cikin kulawa yace " Mutumina are u okay?"
Murmushin yake ya masa yace " ya akai da safen nan?"
Sabi'u ya kalleshi yace " maganar Gimbiya Bilkisu ce."
Kallansa Abu Turab yai yace " ta fasa aurena?" Murmushi yai yace " nasan haka zata faru ai."
Sabi'u yace "no ba haka bane." Ya fada yana girgiza kai.
Abu Turab ya kalleshi sai dai baice komai ba.
Sabi'u yace " nemanka takeyi."
Cikin mamaki Abu Turab ya kalleshi yace " nema kamar ya?"
Sabi'u yace " bansani ba ni kaina, bansan me ya faru ba d'azu da safe wambai ya kira gida a landline ya ce abani, ina amsa ya sanar dani, kasan Wamban kano shike auren kanwar Mamana."
Abu Turab yace " shikenan a satin nan naje."
Sabi'u da sauri yace " da alama neman na gaggawa ne fa, kasan ana asuba aka kira wayar? Bansan meke faruwa ba amma tabbas yanda aka sanar dani da alama neman gaggawa ne."
Mikewa yai yace " Kana tunanin zan tafi inbar Umma na da take cikin wannan halin?"
Sabi'u yace "haka ne sai dai ina ganin ka nemi shawararta, ita kanta nasan cewa zatai kaje."
Abu Turab yace "zan nemeka duk yanda mukai da ita."
Daga nan ya wuce ciki.
Tun dare yake tunanin mafita, sau biyo yana komawa bangaren mahaifiyarsa amma har a lokacin bata fito ba wannan dalilin shi ya kara d'agamai hankali sosai.
Har ya zauna sai kuma ya mike ya fito bangaren mahaifiyarsa.
Lantana tana ganinsa ta taso ta gaidashi.
Kallanta yai cikin damuwa yace " ta fito?"
Lantana ta girgiza mai kai alamar a'a sannan tai kasa da kanta alamar damuwa.
Kofar d'akin ya nufa, ya kwankwasa, shiru yaji ya kara kwankwasawa.
Jin ba alamar motsi yasa ya murd'a kofar d'akin.
A kan gado ya hangota a kwance lulube da bargo.
Da sauri ya karasa ciki.
Bacci takeyi sai dai kana kallanta da yanda take futar da numfashinta zakasan ba tada lafiya.
A hankali yakai hannunsa kan goshinta.
Zafin dayaji ne yasa hankalinsa ya tashi.
Da karfi ya kwallawa Lantana kira.
Da gudu ta shigo dan yanda ya kirata tasan da matsala, Lantana ta kalleshu cikin tashin hankali ta kalli basira.
Cikin fada yace " Lanata me kike yi jikin Umma yakai haka?"
Lantana ta kalli Basira cikin yanayin na ban tausayi tace " Uban gidana jiya da zata shiga tace kar inbar kowa ya shigo mata ciki kuwa harda ni, sannan ko abinci in na kwankwasa mata sai tace min kar na sake shiyasa ban kara dawowa ba."
Idanu ya runtse cikin tashin hankali yace " kira mai magani."
Hannu Basira tasa ta rike hannun Turab cikin a hankali tace " a'a Turab inba so kake magana ta kara karfafa ba ka bar zancen mai maganin nan
"
Kallanta yai cikin tausayawa idanunsa duk sun rine yace " Umma?"
A hankali tace " Lantana kisa a kira Mairo kice ta tahomin da magani, hakan ya isheni Turab
"
Rasa abin cewa yai, jiyai tace " Ya jikin Magajiyan?"
Kallanta yai cikin wani yanayi, yace " wake zancen wannan? Matar da ita tajama kanta ciwo dan ganin bayana? Meyasa in zatai sharrin bazai tsaya iya kaina ba? Menene dalilinta na had'awa dake?"
Kallansa tai, jiyai zuciyarsa ta kara karaya, mikewa yai da sauri ya fito daga d'akin, bakin ciki ya addabeshi.
Bangaren Magajiya ya nufa rai a bace.
Tana kwance, Khadija ce kawai a gunta tana zaune tana matsa mata kafa.
Kallo d'aya yama khadija ya maida dubansa kan Magajiya, yana kallanta yace " Ta farfado?"
Khadija ta kalleshi ba shakka tafi kowa sanin yana cikin wani hali sai dai ita kam ta rasa inda matsalar take, ta tabbata Umman Turab bazata taba yin haka ba, to meya faru? Daga ina aka samu matsalar?
"A hankali ta amsa mai baya farka ba yaya."
Idanunsa nakan Magajiya yace " d'an bamu guri."
Mikewa tai jiki a sanyeye tai waje, zuciyarta a karye, ba shakka tasan jiya ya turab ko bacci bai samu ba.
Juyowa tai ta kurama kofar d'akin ido, ya zatai da ya Turab?ya zatai ta taimaki mahaifiyarsa?"
Abu Turab bayan ta fita ya kalli Magajiya yace " Kina kokari, na kuma jinjina miki a salo na makirci da iya tugu, kinfi mahaifiyata girma amma saboda kinasan ganin bayana kika ajiye girmanki."
Gani yai ta bud'e idanunta.
Kallan mamaki ya mata yace " Idanki biyu?"
Murmushi ta saki ma tsantsar mugunta tace " Turab naji da ka fahimci na girmi uwarka, kaga alama ce ta ko ita bata isa taja dani ba, duk sanda ka nemi izinin durkusawa da bani hakuri lokacin zan saurareka."
Tana gama fad'ar haka ta maida idanunta ta rufe, tsananin mamaki ya hanashi magana, kallanta yai cikin takaici yace " zan baki mamaki, wlh wahalar da mahaifiyata da kikai, zagin da kikasa a ka mata......"
Kasa karasawa yai jin an turo kofa.
Abdulmajid ne, yana shigowa ya ce " malam yi waje ko? Tayaya ma Khadija zata barka kai kadai a ciki? In ka karasata fa?"
Abu Turab ya kalleshi kamar zaiyi magana sai kuma yai waje.
Khadija tana tsaye taga ya fito, kallansa tai cikin tausayawa, ko kallanta baiyi ba yai gaba.
Kansa ya dafe cikin tsananin takaici.
Sabi'u ne ya nufoshi cikin hanzari.
Yana karasowa gun Abu Turab ya kalleshi, kafin yai magana Sabi'u yace " Yarima ko zuwa zamuyi kuyi magana da Gimbiya? Na d'auko number data kira da ita muje dan Allah ka kirata, yanzun nan ta sa aka sake kirana tace ko magana ne a hadaku kuyi."
Abu Turab yace muje to.
Da yake akwai landline a bangaren Basira nan suka nufa.
Sabi'u ya danna numbobin, bayan sun gaisa da wace ta d'aga yace " Gimbiya suke nema ga Yarima Turab din."
Nan tace to.
Ba'a dade ba Bilkisu ta amshi wayar.
Nan ya mikama Abu Turab bayan ya gaidata.
Abu Turab ya amsa, Sabi'u kuma ya fita.
Shiru ne ya d'an ratsa kafin Abu Turab yace " kuna lafiya?"
A hankali tace " naji abinda ya faru, ya Umman taka?"
Mamaki ne ya kamashi dan baiyi zatan abinda zaiji daga gareta ba kenan.
Bata jira amsarsa ba tace " ance bazaka samu damar zuwa ba."
Yace " Bilkisu kinsan halin da ake ciki sannan Umma batajin dadi."
Kai ta jinjina tace " na fahimta, Abbana yace zai sake tunani akan auranmu."
Yasan hakan zai faru sai dai baiyi tunanin ji daga bakinta ba.
Murmushi yai yace " Nasani dole ne hakan ya faru, duba da yanayin da muka shiga, ko nine mahaifinki dole ne na sake tunani akan auran."
Jiyai tace " abinda yasa na kiraka shine inaso in tunama abu 2, kada ka bari wannan abun ya kwantar dakai, bansan meke faruwa a masarautarku ba sai dai nasan abu d'aya in har ka bari akaci galabarka a kan wannan abun banaji zaka farfado daga kuncin abin, zan duba ingani zan kuma sanar da Abbana akan mujira mugani in zaka iya warware matsalar nan daka shiga, na san zuciyarka dakakiya ce, zuciyace kuma ta 'ya'yan da suka kasance jarumai dan wannan dalilin ne yasa na aminta dakai, sai dai jin muryarka yanzu ya nunamin Mahaifiyarka itace lagwanka, inhar aka biyo ta bangaren Mahaifiyarka alamace ta angama cutar ka, an kuma rufema tunaninka da jarumtarka."
Idanunsa ne suka canza daga kalar tausayawar da suke dazu, Murmushi ya saki yace " Nagode Bilkisu jin kalamanki yasa na fahimci dalilin dayasa aka biyo ta bayan mahaifiyata, dan ansan bazan iya yin komai ba, zuciyata zata raunana ta hanani tunani komai, ta sani cikin rudo da tausayawa."
Zai sake magana yaji ta katse wayar.
Ajiye wayar yai yabita da murmushi lalai Bilkisu jinin sarautace ta asali, har daga jin muryarsa ta fahimci abinda ya kamata ta fadamai? Mikewa yai ya nufi waje.
Mairo wacce ta taho da magani ta ganshi.
Ta d'auka xata ganshi cikin yanayi na tashin hankali.
Kallanta yai yace " Mairo kin iso?"
*TEAM ABU TURAB 🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
_Tuba nake plz na jina shiru da kukai ✌🏻dayz_
*43*
Mairo ta tsaya kawai tana binsa da kallo, kai yad'an lank'wasar kadan yace " Lafiya?wannan kalan fa?"
Cikin mamaki ta amsa mai " Yaya Umma ta warke ne?"
Kai ya girgiza alamar a'a yace " baki taho mata da ganin bane? Ko samu ne ba'ai ba?"
Tace " to ko an gano gaskiya ne?"
Kallan rashin fahimta ya mata yace " menene?"
Tace " naganka ne kamar abin ya daina damunka, sannan idanunka suna d'auke da confidence."
Murmushi taga ya sakar mata yace " ni kaina bansan ya akai ba bayan nayi wata 'yar karamar waya na samu kaina cikin wannan yanayin."
Tana kokarin tambayarsa wace irin waya yai jitai yace " shiga ciki, inada abinyi."
Kafin tai kokarin magaa ma yayi gaba.
Komawa yai b'angarensa yai wanka ya d'auko kaya had'ad'u ya saka, shadda ce bugagiya light brown, yayi kyau sosai da sosai.
In har ka ganshi to fa lalai zaka d'auka wani taro na mahimmanci zaije.
Haka ya fito hankalinsa kwance, Garzali na ganinsa ya mike ya biyoshi yana tambayarsa inda zasu.
Turab yace " Bangaren Umma Babba zamu."
Bayan ya shiga ne yaga ragowar matan sarki da kuma matan kannansa a zazzaune suna gulmar abin, da alama dubiya sukazo suka bige da gulma.
Ganinsa yasa kowa ya ja bakinsa ya tsuke, Abu Turab fuskarsa d'auke da murmushi mai sanyi ya gaishesu, haka kowa ya dinga amsa gaisuwar a kunyace dan sun tabbata yaji me sukace.
Kowa sai dayai mamakin ganin yanda ya d'au kwalliya duba da yanayi da suke ciki.
Kwankwasa kofa yai, Khadija ta taso.
Tana tura kofar tai ido hudu da Abu Turab, tana rike da kofar take binsa da kallo, kallanta yai kallo na bege sai dai bayanda zaiyi, da sauri ta katse