Showing 117001 words to 120000 words out of 146065 words

Chapter 40 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

muka aikata? In haka ne kaine a ruwa dan kai kasan ni da kaina ban taba kaahe mutum ba haka kuma bantaba sawa da bakina a kashe wani ba."


Hisham kallan tsananin mamaki kawai yake mata, yace " mene?"
Tace " ni na saka kaje kashe Turab sanda aka haifeshi?ko nice na saka ka sama gidansu wuta ka kashe yayan mahaifiyarsa da matarsa?"


Abdulmajid ji yai kansa na wani irin juyawa, yanasan yai kara yace musu khadija na bandaki sai dai inaa, wani irin juyawa kansa yakeyi wanda gaba d'aya bakinsa ma ya kasa bud'uwa.


Hisham ya sa hannayensa biyu ya shake ma Magajiya wuya, kallansa tai tace "wani kisan kake san yi? A gaban d'an ka?"


Kallan Abdulmajid yai sannan ya saketa, nuna ta yai da yatsa sai dai baice komai ba sai idanunsa da fuskarsa da suka canza sosai.


Magajiya ta kalleshi shekeke tace " yaya baka isa ka gudu daga tarkona ba."


Kallan Abdulmajid tai sannan ta juya dan tambayar Likita halin da yake ciki.


Abdulmajid mutsu mutsu kawai yake akan gado.


Mairo kuwa harta hau kan mashin ta tuna tabar ledar kayan da zata canza in zata gidan bikin daga gun Umma.
Saukowa tai ta nufi ciki.


Tana shiga ta taradda Abdulmajid na kokarin faduwa, da sauri ta shiga ciki ta rikeshi tace " Abdulmajid!"


Jin muryar Mairo yasa ya bud'e idanunsa wanda suka canza kala sosai, hijab dinta ya riko bakinsa ya shiga rawa yana san magana.
Mairo duk ta gama rikicewa, kallansa take tana cewa " menene?"


Ganin ya kasa magana ta gyara mai kwanciya sannan ta zare d'ankwalinta ta shiga fifitashi, dan gumi yake kamar ba fanka a d'akin.


Wani irin ajiyar zuciya yai wanda duk wanda yake kusa sai ya juyo, Mairo ta kalleshi tace " Abdulmajid!"
Yace " Toilet, Mairo Toilet."


Toilet? Ta maimaita tare da yin hanyar, A kwance taga khadija shame shame a cikin bandaki, duk ta gama rikicewa nan ta shiga kokarin fito da ita, da kyar da jawota duk yanda ta jijigata ta kasa tashi, ga kayanta duk ya soma jikewa, a rikice ta shiga kokarin cire mata kaya, ta d'auko nata wanda ta manta, ta zare zanin ta sa mata siket dinta.
Ganin rigar bata jike sosai ba yasa fito da sauri dan neman nurse.


Wani ta gani da farar riga irin ta likita, tace " Dr wata ta fadi."


Likitan ya kalleta yace "a ina ne?"
Nuna mai d'akintai suka shiga.


Khadija na kwance, ya shiga da sauri inda take ya gyara ta zuwa rigingine.


Ya dade a kanta kafin ta farfado, kallan sa kawai takeyi, tana kuma bin d'akin da kallo.


Mairo na zaune ta baza tagumi Magajiya ta shigo.
Kallanta tai tace " ke kuma fa?"
Mairo tace " Khadija......."
Fita!
Abinda kawai tace mata kenan tare da nuna mata hanyar kofa.
Mairo ta kalli Abdulmajid wanda ke kwance idanunsa a rufe, kawai tai waje duk tsiwar mutum kwarjinin Magajiya daban ne.
Gidan Sarki kawai ta wuce, ga yamma tayi.


***********


'yan kawo Amarya kam sun sha hidima, dan ba shakka an musu tarba sosai, sai yamma suma sukai ma Bilkisu sallama suka kama hanyarsu.


Mairo ta iso sai dai bata samu ko ganin Turab ba dan yana cikin mutane, umma kuma tana ta fama da mutane, balle dama batama san me zatacema Basira ba.


Turab kam bai samu ya shigo ba sai bayan isha'i, shima tare yake da 'yan rakiya, yasha kwalliya sosai.
Bangaren Umma kawai lekowa yai ya mika kaya ya wuce, Mairo tana sallar isha'i ya shigo, tana idarwa ta tambaya akace ai ya tafi bangarensa.


Haka tai sallama da Umma ta fito dan tasan in aka rakashi shida fitowa sai gobe.


Gimbiya na zaune a d'aki, tasha had'adiyar alkyabbarta kayan jikinta masu tayi kyau sosai da sosai, sai dai an saka hular alkyabbar sannan an kawo mayafi an rufe fuskarta.
Jeren da aka mata kuwa, ko ban fadaba kowa yasan an kashe kudi dan ma dai lokacin ba kamar yanzu bane da kudinmu bashida daraja.


Da masu kula da ita wanda daga can kano aka raho mata dasu guda biyu saboda rashin sabo da batai da na nan ba.


Su Sabi'u manyan yan tsokana, haka sukai ta tsokanar shi kafin daga baya su bada kudin siyan baki, wanda rashin kawaye yasa sai ajiyewa sukai anan, da yake haka ta taso ba kawa sannan cikin maza ta taso bare tai abokantaka da yayunta, haka suka fita suka bar Ango da Amaryar sa.


Turab ne ya zauna kusa da ita sannan ya yaye mata mayafin dake yafe a fuskarta sannan ya kalleta yace " Gimbiya Bilkisu barkanki da shigowa gidan auranki, barkanki da sauka cikin wannan gida."


D'agowa tai ta kalleshi sannan ta maida kanta kasa, rabonshi da ita ya dade, haka itama, ba shakka yayi mamakin tsananin kyan da ta kara, itama a ranta taga yayi kyau sai dai kallo d'aya datamai ta ga ya fada.
A hankali tace "Barkanka dai Yarima Turab."
Murmushi yai yace "kinyi sallar isha'i?"
Tace " a'a."
Yace " ki tashi kiyi alwala sai muyi tare."


Kanta ta sunkuyar tana wasa da hannunta wanda yasha lale.


Jikinsa ne ya bashi da alama bata salla, sai yace " bari nai sallah ni tukunna, ga abinci nan ki fara ci."
Ya fada tare da shiga ban d'aki, sai dayai sallah yai shafa'i da wuturi sannan ya dawo inda take.
Ledar na gabanta sai dai ko bud'ewa batai ba.


Zama yai yace " Tunanin gida?"
Kallansa tai tace " kawai inajin abin ne kamar wasa."
Ledar ya bud'e tare da ciro ledar naman ya sauka kasa kan karamib carpet din tsakar d'akin ya zauna, sannan ya ciro ledar juice masu sanyi ya ajiye.
Alama ya mata da hannu akan ta sauko ta zauna, ya fada yana nuna mata kusa dashi kadan.


Murmushi tai sannan ta sauko ya tura mata gabanta sannan ya mike ya d'auko cup ya tsiyaya mata juice d'in yace " Bismillah."


Kallansa tai tace "banajin yunwa, ni kai naga ma kamar kaine bakaci abinci ba."


Fuskarsa ya taba yace " na rame ko?bayan amare aka sani da rama."
Tace " ka rame mana, badai matsalar bace har yanzu bata warware ba?"
Iska ya furzar yace " Abin ai ba karami bane."
Tace " Da alama an tsorataka?"


Dariya yai wanda harsaida hakwaransa suka fito yace " Tsoro? kuma fa kin fadi gaskiya an tsoratani."


Tace " an ba da ni."


Yace " ahh ya zakiyi yanzu? Gashi na riga na kwaceki bare a kasa ni?"
Kanta ta sunkuyar tace " Ni dai nace an badani, banaji ni akwai abinda zai tsorata ni."


Yace " hmm a hakan? Ke har zaki iya wani abun ma? Ni da na d'auka zan taddake irin ba wasan nan sai naganki mai saukin kai."


Wayau yake mata yaga inyana sata magana tana kara sakar jikinta dan gashi yanzu har naman ta fara dan ci.
Kallansa tai tace " a haka ne ka ganni mai sauki, amma in na rikid'e? Hmm ba wasa."


Ohhhh kice akwai wadi side ban sani ba, ko za'a gwadamin?
Murmushi tai tare da yin kasa da kai tace " Ka fadamin wanene yake baka matsala kaga abinda zan iya yi."
Yace " kice sai dai in koma baya in kallo?"
Tace " Magajiya ce?"


Kallan mamaki ya mata yace " me kika gani?"
Murmushi tai tace " Ka manta a inda na taso ne? Na kuma san d'anta taso ta had'a dani, sannan d'anta takesan tasa a kan mulki."


Turab yace " hmm lalai, na sha mamaki."
Kallansa tai sannan ta sunkuyar da kai tare da zare hannunta daga ledar, ya tabbata gida ta tuno, matsowa yai ya jawo ta jikinsa ya rungume ta tsam.
Yana shafa bayanta a hankali alamar lalashi, yace " i will try my best not to make u lonely, sannan ban manta da alkawarina dana miki ba, bazan nemi wani abu ba a tsakaninmu harsai na kammala abinda ke gabana, a lokacin ne zan nemi yardar na zamantakewa, a lokacin ne zaki yanke hukunci in zaki iya zama dani."


Luf tai a jikinsa, sun dade a haka kafin ya d'agota a hankali sannan ya shiga bata naman da kansa.
Da kunya ta ke amsa sai dai wata shakuwa na kara shiga tsakaninsu a hankali.
Yanajinta kamar kawarsa dan abinda zai gaya mata bayaji akwai wanda yake iya fadawa kai tsaye, bai san me yasa yakejin yardarta har zuciyarsa ba........




***********
*TURAB*
************
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*76*


Washegari.


Da asuba ya farka a kan kasan carpet din daya kwanta, salati yai sannan ya mike tare da kallan kan gadon da Gimbiya ke kwance, karasawa yai inda take ya gyara mata bargon data luluba dashi, sannan ya juya zai fita.


Jiyai ta kamo hannunsa, juyowa yai ya kalleta yace " idanki biyu?"
A hankali ta bud'e idanunta tace " yanzu dai na farka? Masallaci?"
Yace " eh, sai na dawo."
Sakeshi tai sannan tace " adawo lafiya."


Murmushi yai sannan ya juya yai gaba.


Alwala yai sannan ya fita, sun idar da sallah ya fito, jiyai ance " Yarima Turab!"
Yanda aka kirashi cikin rad'a yasa ya juya ba tare da ya amsa ba dan ganin me kiran.
Daga lungu ya hangoshi a tsaye jikin bango.
Turab ya karasa sannan ya kalleshi cikin mamaki yace " Waziri lafiya?"


Hisham ya kalleshi duk ya canza yace " Kaga Khadija?"
Turab yace " bangane naga khadija ba? Wannan wace irin tambaya ce?"


Hisham a rikice yace " Turab?"
Ya fada tare da riko hannayensa yace " ka taimakeni dan Allah bansan inda Khadija tai ba, tun jiya nake nemanta wlh ko barcin arziki ban samu ba."
Turab kallan mamaku yake masa yace " Ni fa nakasa fahimtarka, b'ata tai ko me?"
Hisham yace " da kanta ta tafi, sai dai bansan inda tai ba."
Turab ya kwace hannunsa yace " da kanta ta tafi? Kuma ko kunya kazo kana tambaya ta?"
Hisham yace " Turab na rasa inda zansa kaina, in ta fada hannun mutanen banza fa?"
"wannan damuwarka ce ba tawa ba, kaine ka lalata mata rayuwa ko menene ya sameta, sannan karkaga kaine ka haifesu kayi tunanin duk wani abu da ka aikata musu ba laifi bane, haifarsu kai ba hallitarsu kai ba."
Ya juya yai gaba.


Hisham idanunsa suka ciciko dan shikam yana cikin garari.


Turab tafiya kawai yake sai dai abin zirya yake tamai a zuciyarsa, ina taje? Menene kuma dalilin tafiyarta?"


Har yaje zai shiga bangarensu sai kuma ya juya, Garzali ya kira suka wuce asibiti.


Abdulmajid na kwance yana bacci, sai wata baiwa da Magajiya ta sata zama a gunsa, d'ayan gadon ya kalla wanda da ba kowa, amma yanzu yaga Khadija kwance.


Mamaki ya kamashi yaje kusa da ita, sannan ya dawo inda Abdulmajid yake yad'an tabashi.


Sannan yace " d'an tashi."
Abdulmajid bai bud'e ido ba sai dai yana jinsa.
Turab ya kalli wannan mai kula da su din da aka bari yace " bamu guri ko?"
Tace " to ranka ya dade." tai waje


Turab ya kalli Abdulmajid yace " magana zamuyi."

Abdulmajid a hankali ya bud'e idanunsa ya kalli Turab.
Turab ya zauna kusa dashi yace " ya jikin naka?"
Baice komai ba sai dai ya kawar dakansa.
Turab cikin wata irin murya yace " Nagode Abdulmajid."
Cikin tsananin mamaki Abdulmajid ya kalleshi, sannan yace " karkamin godiya dan ba saboda kai nai ba."
Turab yai murmushi yace " saboda ba saboda ni kai ba shi yasa nake ma godiya."
Abdulmajid yace " mene?"
Turab ya ce " Mu bar wannan maganar, me ya samu Khadija?"
"kana tunanin zan fadama?"
Turab yace " sosai, dan duk duniya yanzu ni kadai ne zaka iya fadama wannan sirin naka."


Wata dariya yai yace " bakai tunanin na gwammace na had'iye matsala ta ba?"
Turab yace " wannan tsarinka ne, zaka iya yadda zakuma ka iya kin yadda, sai dai in har kanaso ka ceto rayuwar mutanen dake kewaye dakai dolene mu had'a kai."
Abdulmajid ya kalleshi sai dai baice komai ba, Turab ya cigaba " haka zakabar matar da ta rikeka ta cigaba da tafka laifufuka? Haka zaka bar mahaifin daya haifeka ya cigaba da aiwatar da laifufuka? Ko kuwa rayuwar kanwarka dake neman tarwatsewa?"


Abdulmajid ya juya kai idanunsa suka ciciko, Turab yace " tunda ka zabi yin shiru, ni zan aiwatar da abinda naga shine daidai."


Ya mike zai fita, Abdulmajid a hankali yace " inajin kunyar hada idanu dakai, bansan abinda iyaye na suka aikata maka ba kenan, duk abinda sukai how can i face u?"
Turab ya juyo ya dawo kusa dashi ya zauna sannan ya kalleshi yace " bazance kaima bakada laifi ba dan kaima kayi abubuwa marasa kyau a baya, sai dai yanzu kana biyan laifin daka aitaka." ya fada tare da kallan kafarsa wacce ba hope din zata mike.


Turab ya cigaba " dole ne ka cire tsoron Magajiya in har kanasan ka taimaketa, kaine kadai wanda inka juya mata baya zataji gaba d'aya duniyar ta mata zafi domin dakai ta dogara sannan saboda kaine take ganin komai zatai ba zai zamar mata wani abu ba."


Abdulmajid ya share kwallarsa yace " haka ne, sai dai banaji ko ni Umma zata saurarawa, sannan Waziri ba tun yanzu yake kisa a kaina ba, na kula duk abinda ke faruwa saboda ni ne...."


Ya kasa karasawa saboda wani kuka daya taho mai.
Turab wani tausayinsa ne ya kamashi, daurewa yai yace " yanzu ba lokacin kuka bane, inhar ka yadda kana da hakki akan laifufukan da suke aikata wa to dolene ka nuna musu kuskurensu gun aikata abinda auka aikata."


Abdulmajid yace " hakane, yanzu me zanyi?"
Turab ya kalli Khadija sannan yace " da farko kasa Waziri ya maida yarinyar nan kano."
Abdulmajid yace " Khadija?"
Turab yace "eh, zuciyarta mai rauni ce duk da tasan mahaifinta da kanwarsa sun tafka kuskure intaga ana wahalar dasu zuciyarta bazata d'auka ba."


Abdulmajid yace " haka ne, zansa gobe amaida ita."
Turab yace " sannan ka nuna ma kowa ka farfado."
Yace " sai me?"
Turab ya matso daf da kunnensa ya rad'a masa wani abu wanda duk yanda nakai kunnena gun banji me yace mai ba, sai da ya gama sannan na kalli Abdulmajid naga yana kallan Turab.


Turab yace " me? Bazaka iya ba?"
Kai ya girgiza yace " ko d'aya kawai dai ina mamaki ne wanda yanzu na fahimci komai, a da ina kishin ko mai na rayuwarka, daga yanda Abba ke sanka zuwa yanda kuke hira da Mahaifiyarka cikin kulawa, zuwa yanda Kanwata da Wacce nakeso ke sanka bani ba, sannan zuwa yanda mutanen fada ke girmamaka, saj dai yanzu na fahimci dalili."
Turab yace " menene dalilin?"
Abdulmajid yai murmushin yake sannan yace " zuciyarka itace dalili."


Turab ya kalleshi ya murmusa, Abdulmajid yace " yanzu me yasa ka yarda dani? Baka tunanin zanci amanarka tunda abu ne na mahaifana?"
Turab yace " ko kadan, saboda yanzu idanunka sun canza, a da ambition da kuma kishi nake gani karara a idanunka sai dai yanzu ina ganin tsantsan guilty da kuma dana sani a idanunka."


Abdulmajid yai kasa dakai.
Turab yace " u have to do it right, karka bari kwarjini da tsoron magajiya yasa ka kasa."


Abdulmajid ya d'aga kai yace " nagode Turab."


Turab ya kalleshi ya dafa shi sannan ya juya.


Kallan Khadija yai ya juya ya fita.


Abdulmajid ya bishi da kallo idanunsa na zubda kwalla.


*********


Magajiya yau cikin baccinta ta tashi yakai sau uku, kalaman Hisham ne ke mata yawo, da kuma Turab, yau kam ta tabbatar Turab yasan Abdulmajid ba d'anta bane.


Ana sallar asuba kuwa ta aika a kira mata Jakadiya.


Tun 6 take zaune tana jiranta sai dai ba labari, har wajen karfe 8 abin ya gama damunta ta mike a zuciye ta fito.


Karfe 7:30 kuwa Turab ya iso gidan, yana sauka a mota Jakadiya ta taho da sauri.
Kallanta yai yace " Jakadiya lafiya?"


Jakadiya a rikice tace " Yarima tun dazu nake jiranka, Magajita ce ta aiko naje."


Turab yai murmushi yace " ai na d'auka tun jiya ta kiraki, ashe zata iya bari sai yau?"


Jakadiya ta mai kallan mamaki tace " Bam gane ba?"


Turab ya kalleta yace " kije in ta kiraki sannan ki sanar da ita abinda kika sani."


Jakadiya tace " abinda na sani? Ban gane ba?"
Turab yace " ba kiranki nai nace zan hukuntaki ba? Ki sanar ita duk abinda ya faru."
Kallansa tai tace " amma baka ganin zata iya lahantani?"
Turab yace " in ta lahantaki ma tsakaninku ne, ai kema kinyi laifi bawai wannan ne kawai abinda kika aikata ba, banaji inada damuwa akan abinda zai faru tsakaninku."


Hankalin Jakadiya ya tashi da sauri ta tsungunna a gabansa tace " Ranka ya dade kasan Magajiya."
Turab yai murmushi yace " na sani, saninta da kuma saninki ne yasa na fadi haka, ki kwaci kanki tunda kema da wayanki kuma ba ta yau bace."




Ya juya yai gaba yana murmushi.






Bangarensa ya nufa, yana shiga ya wuce d'akinsu, sallama yai yaji shiru hakan ne yasa yai tunanin ko bata ciki ko bacci taje har a lokacin.


Kofar ya tura tare da shiga da sallama, yana shiga ita kuma tana fitowa daga band'aki d'aure da towel, wani kamshin dadi ne ke fitowa daga ban d'akin wanda hakan yasa nasan lalai anyi wanka da kayayaki masu kamshi.


Da sauri ta juya baya, baisan sanda idanunsa suka shiga kallanta ba tundaga kafarta har zuwa kanta ba, abinda da zuciya ga Bilkisu mace ce mai tsananin kyau da kira.


Juyowa tai ta kalleshi da sauri ta sake juyawa tace " Ba ka fita ba?"
Turab yai murmushi sannan ya tako a hankali har zuwa inda take daf da ita yazo zuciyarsa na rayamai abubuwa, ita kuwa gabanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login