Showing 3001 words to 6000 words out of 146065 words
Chapter 2 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
ke rabon da mu fira waje kenan, sai dai ke ko magana ba yi kike ba sai in ta kamaki dole, bakya gani lokaci yayi da zaki cire wannan a ranki?
Murmushin dole tai sannan ta mike, ga mamakin Aunty Karima gani tai ta shiga had'a kayenta a akwati, mikewa tai jiki a sanyaye tai waje, ba shakka tana tausayin yarinyar nan gashi Amadu ya ki fada mata waye mijin itakam tana tsoron kar akai yarinyar nan inda zatasha wahala, dan ma dadinta d'aya ciki bai shiga ba sanda akai fyaden tunda har tayi al'adar ta.
Basira kam kayanta kawai take sawa a akwati tana gamawa ta shiga tai wanka tare da kwanciya akan gadon d'akin, ta rasa me yasa ko tunani ma ta kasa yi idanunta kawai ta rufe.
Bacci ne ya dauketa mai nauyin gaske.
**********
Wajen karfe 12 suka iso dan motar wannan lokacin sam ba gudu ne da ita ba kamar ta yanzu ba, hakan yasa suka dade sosai a hanya.
Basu san gidan Amadu ba hakan yasa suka shuga neman kwatance dan ma ya sanar dasu unguwar dan lokacin ba a sa sunan layi.
Sun dan sha wahala kafin su gane gidan dan ma abun mutane sai sunce gidan su Basira sannan ake ganewa.
Wajen karfe d'aya suka isa gidan lokacin Amadu na waje yana ta leke kudu da yamma ko zai gansu.
Yana hangosu ya saki ajiyar zuciya dan da ya dauka ko an samu wata matsalar ne.
Abdulsamad ko ciki bai shiga ba yace muje masallaci a ayi abunda za'ai in koma dan barin fada ba tare da kwakwaran uzuri ba matsala ne.
Amadu ya jinjina kai sannan suka nufi masallacin kusa dasu dama ya riga ya sanarma liman, bayan sunyi sallah ne aka daura auren Abdulsamad da Basira wanda Liman yama Abdulsalam walici shi kuma Amadu yama Basira an daura aure akan sadaki naira dari 200.
Wannan kenan.......
*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_Dan Allah wanda yamin magana ban mai reply ba yai hakuri jiya whatsapp d'ina ya samu matsala sai dana sake downloading sai dai sam yaki backup name messages d'ina_
*Na Ayusher Muhd🤸🏼♂*
*3*
Kafin su fito daga masallaci bayan an daura auren mutane har sun cika gaban masallacin, labari har ya kai musu cewa ga wani gara can da baisan me yakeyi ba ya auri Basira.
Sarki na kokarin fitowa wannan Bawan nasa ya sha gabansa ya rusuna tare da sanar dashi halin da ake ciki.
Jikin Amadu ne yai mugun sanyi, jiyai Abdulsamad yace " Ku fara fita in yaso ni sai in fito daga baya."
Amadu yace " ai Mai martaba bakasan gidan ba."
Yace ba komai zan biko a baya ne nima ai.
Jin hakan yasa suka fara fita, nan fa mutane suka saki baki suna kallan bawan, kowa da gulmar dake fada aransa, wasu cewa suke ai dole ya nemo ko ma waye ya bata da kuma alama ma fakiri ne, wasu kuma suce da alama sadaka aka bashi yaji banza shi yasa bazai iya bari ba.
Haka dai kowa da abinda yake tunani, sudai sukai gaba, Mai Martaba na baya cikin mutane yana kuma jin duk abinda kowa ke fada, jikinsa ne yai mugun sanyi lalai ba shakka yayi babban taimakon na auran yarinyar nan dan kuwa da alama ba mai auranta a garin nan.
Sai da mutane sukaga sun isa gida sannan kowa ya watse, shi kuma Sarki Abdulsamad ya shiga ciki.
Bayan sun zauna ne matar Amadu ta kawo musu fura mai sanyi tare da dambu na tsakin massara yasha gyada, Abdulsamad ya dan ci kad'an kafin ya kalli Amadu yace " Amadu ba zan kai Basira gidana ba yanzu."
Gaban Amadu ne ya fadi yace " kana dana sani ko? Na auranta? Ni kai........"
Katseshi Abdulsamad yai yace " ina tsorace mata a bubuwa guda uku shiyasa bazan kaita yanzu ba."
Yadan ja numfashi na manyan mutane kafin yace " in har taje gidan nan a haka zatasha bakar wahala ba tare kuma da sanina ba, ko Magajiya bazata barta haka ba, ganin jiya akai sunan d'anta ace yau na kawo mata? Sannan na saki yarinya jiya ashe wani nake san sakeyi? Sannan ban sanar dasu zanyi auren ba ma sam.
Kaga wad'annan dalilan sune zai sa su wahalar da Basira, gata ita kuma ko harkar gidan sarauta bata sani ba bare ta nemi kwatar kanta."
Shiru Amadu yai kafin yace " Gaskiya ne ni kaga sam banyi wannan nazarin ba nidai dadina Basira ta auri wanda nasan ko bani da rai zai kular min da ita."
Sarki ya d'an murmusa kadan kafin yace " Zan baka kwatancen gidana a cikin gari, zan kuma sanar ma ma'aikatan gidan in yaso kai zuwa gobe sai ka taho da ita ka kaita can, zan tura mata bayin da zasu dinga kula da ita da koya mata abubuwan daya dace, in yaso zuwa ko sati biyu ne sai ta dawo."
Amadu ya shiga godiya, nan Sarki ya mike yace zai wuce.
Amadu ya shiga kwallama Basira kira, da sauri Sarki yace " ya isa haka, bance ka kirata ba ai, ina sauri ne in tazo naje na ganta."
Amadu ya amsa da to, sannan yamai sallama yai waje.
Yana fita ita kuma matar Amadu wacce ta taso Basira da kyar tanata sharar baccinta suka fito, ganin ba kowa a gun yasa tace " Malam ina mijin?"
Basira ya kalla yace " Basira gobe zan kaiki shi yayi gaba."
Matar tace " a ina aka tabayin haka? Yaya shine zai kai yarinya?"
Amadu yace " ni ai da so nai tabi mijinta ma baki alekum to amma tunda haka yace ni na kaita goben"
Zata sake magana yace " kul! Mijin Basira baya magana a canzata dan haka ki kiyayi kanki."
Mamaki ya kamata sai dai bata sake magana ba, Basira kam tana jin haka ta koma ciki tai alwala tai azahar.
*********
A can gidan Sarauta kam ganin Sarki ya dade bai dawo ba yasa Hisham ya shiga amsar matsaloli da dai sauran abinda Abdulsamad ya kamata yai a ranar,dadi kuwa ya kamashi dan ba shakka yana san mulki sosai.
Sai wajen shida sannan suka isa zariya.
Kai tsaye wanka yai sannan ya zauna a kilisarsa aka shiga jeramai abinci kala kala da 'ya'yan itatuwa..
Sai da ya koshi sannan yai bincike akan abinda ya faru a ranar.
***********
Isar Magajiya da mulkinta yasa ta bada umarni bayan auranta dole ne duk matar sarki da kwarkwarori suzo su gaisheta da safe kafin suci abinci anan ne take sawa a kawo musu wani shayi wand sune suke tunanin shayi ne sai dai a zahiri naganin hana daukar ciki ne.
*********
Amadu kam ya kai Basira inda aka umarceshi sannan ya mata sallama akan zai tafi.
Kallansa tai idanunta suna neman cikowa tace " yaya ina ne nan? Na tabbata ba mai hankali mai kudin kuma da zai aureni."
Amadu ya girgiza mata kai yana murmushi yace " a naki tunanin kenan sai dai Basira inaso ki kasance mai godiya ga Allah dan kuaa ya baki mijin da babu kamarsa wanda baki taba tunanin ko gani ba bare aure ba."
Zatai magana taga ya juya baya yana kara kallan falon, daga nan ya kara mata nasiha ya fita zuciyarsa fes da ita.
*********
Sarki kam sam ya manta da Basira sakamakon hidimomin dake gabansa, yau ya cika satinta uku kenan da zuwa garin amma ko keyarsa bata gani va, sai wasu abubuwa da ake koya mata.
Gashi abin haushi komai sai ace sai dai a mata, magana wannan akwai mai nuna mata yanda zatai, itakam duk ta gaji da wannan sabon al'amarin.
Yau watanta d'aya cif, Abdulsamad harya kwanta bacci ya tuno da Basira da sauri ya mike cikin tsananin mamakin kansa da takaici ya fito daga turakarsa, Bayinsa ne suka matso suna tambayaraa ko yana bukatara wani abun ne?
Da sauri ya nemi bawansa Mudan ya kuma umarci bayin da wannan fitae ta zama sirri, nan yai waje shida Mudan.
Kayan fadawa ya saka sannan ya rufe fuskarsa ya hau doki, ba wanda yai tunanin Sarki ne har ya fita.
Gidansa ya nufa, a lokacin ita kuma an sa tayi wanka da wasu turaruka masu kamshi kamar yanda suke sata kullum wai hakane al'adar dole in zatai bacci tai wanka da wad'an nan turarukan sannan ta sha madarar shanu ta kwanta.
Ta fito kenan ta zira doguwar riga tana shan madara taji sallama.
Gabanta ne ya fad'i jin muryar namiji, a hankali ta amsa kamar mai rad'a, nam shi kuma ya shiga.
A zaune ya ganta sai dai idanunwanta sunyi zuruzuru.
Dama ya umarci bayin dake waje su tafi makwancin su, nan na cikin d'akin suma suna ganinshi suka zube suna gaidashi, nan suma ya sallamesu.
Itakam idanuwanta ne duk suka fito jin suna cewa " Mai Martaba barkada shigowa."
Batakai ga nemo amsar tambayar dake mata yawo akai ba taji yace " Basira ba gaisuwa?"
Kallansa tai sannan ta zube da sauri kamar taga mala'ika sai dai ta kasa cewa komai sai gabanta kawai dake mugun fad'uwa.
Murmushi yai sannan ya matso kusa da ita ya d'agata ya, itakam kafafuwanta rawa suke hakan yasa tsayuwar ta fara neman gaggararta, da sauri ya jawota jikinsa tsoro ne yasa ta zaro idanuwa, shikam Abdulsamad yana mamakin girman yarinyar.
Kamshin jikinta ne ya sa ya lumshe ido ba shakka kamshin Magajiya ya ninka nata dadi sosai sai dai baisan meyasa yakijin nata wanu daban ba, ji yake yana ratsa zuciyarsa.
Bata taba tunani ba haka kuma batau zato ba taji yace " kinyi al'ada ne?"
Da sauri ta matsa daga jikinsa ta kalleshi kadan sannan ta sunkuyar dakai, taya za'ai ya mata wannan tambayar? Ko kunya?"
Abdulsamad yace "dole ce ta sani yi miki tambayar."
Baya ta juya da sauri sannan ta d'aga kai alamar eh tare da shigewa uwar d'aka.
Hamdala yai sannan ya shiga ciki shima.
Itakam a bakin gado ta zauna tare da rike hannayenta biyu itakam wacce irin tambaya aka mata yanzu? Mijin da bata taba gani ba taya zai fara mata wannan tambayar?"
Shigowarsa ne yasa tai saurin kwanciya tare da rufe ido, murmushi yai sannan ya karasa kusa da ita ya zauna, hannu ya sa a kafadarta cikin maganarsa ta isa da sanyi yace " Basira na tambayeki ne badan komai ba sai saboda gaba."
Kallansa tai cikin mamaki yai dan murmushi yace "karki damu ni dama nasan ba matsala sai dai ya zana dole na tambaya."
Kasa tai da kanta ta maidashi kan filo, kanta ya shiga shafawa a hankali ya kwanto da kansa jikinta, tsoro ne ya shiga kamata ta tuno abinda ya faru da ita.
Da sauri ta mike ta zauna tare da matse kafafuwanta.
Hawayene ya shiga zubo mata, tana kuka tana girgiza kai.
Sarki ya shiga mata kallan tausayi, Basira cikin kuka tace " tsoro nake."
Matsowa yai kusa da ita ya rungumeta ta kara fashewa da wani kukan, nan ya shiga jijigata yana bata hakuri cikin salon soyayya a haka har yasa jikinta ya mutu nan shi kuma ya gabatar da abinda yake so........
Bayan ya nutsu ne ya jawota jikinsa itakam har yanzu kuka take, hakuri ya cigaba da bata, ta dade sosai tana kuka kafin bacci yai gaba da ita.
Shiru yai yana kallanta, ya sani sarai dolene gobe bayin dake kula da ita su bincika ko jinin da ya kamata ya fita a gabanta sakamakon farkon kusancin ta da maza ya fito, dan sune zasu zama shaidarta nan gaba.
Dubawa yai ya samo reza ya bud'e cinyarsa ya tsaga kad'an sannan ya sa a jikin zanin gadon, sannan ya mike ya fito bayan ya dan sumbaci Basira.
*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼♂*
*4*
Wajen Sallar asuba babbar mai kula da ita a cikin bayi ta shigo dan taimaka mata tai alwala.
Basira tana kwance tana bacci matar ta shigo ta tasheta, sam Basira ta manta abinda ya faru hakan yasa da karfinta ta nemi tashi, jin zafi a gabanta ne yasa ta tuna, saboda tasha wahala sosai sanda aka mata fyade dan sai da matar yayanta tai ta saka ta acikin ruwa mai zafi tana gasata tukun na, mikin daya warke ne taji ya motsa, hakan yasa ta dan ce wash.
Matar ta kalleta tare da yayi zanin gado da sauri, ganin jini yasa ta saki gud'a, Basira kam kallan jinin tai sam bata kawo ba daga jikinta ya fito ba saboda matan da ba ruwansu da zancen nan, hakan yasa batasan sau d'aya yake fitowa ba, itakam matar ce take bata mamaki ganin yanda take gud'a.
Kan kace me? Sai ga ragowar bayin sun taho da sauri, nan suka gani kowa ya fahimta, nan wata ta fita dan d'ora mata ruwan zafi, itakam matar zanin ta yayi ga mamakin Basira gani tai ta ninke ta saka a cikin leda.
Bayan ruwa yai zafi ta taimaka mata tai wanka tai sallah sannan aka kawo mata abinci, Basira nasan taji wai menene matsayin wannan mijin nata wanda yazo jiya sai dai tana kunyar tambayar hakan.
**********
Sarki ne zaune akan kilisarsa Magajiya na d'an nesa dashi tana cin 'ya'yan itatuwa shi kuma yana d'auke da Abdulmajid a hannunsa yana murmushi, can ya nisa yace " Magajiya nayi aure."
Kallansa tai cikin isa tace " aure kamar ya kenan?"
Ya dan murmusa yace " kanwar abokina Amadu ce zata tare nan da sati d'aya zuwa biyu."
Kallan mamaki tamai sai dai isa da ji da kai yasa batace komai ba, sai dai maganar ta kular da ita sosai tayaya kamar ita za'a mata kishiya ba tare da ta sani ba?lalai Abdulsamad yazo da rainin hankali.
Mikewa yaga tayi tare da kiran baiwarta, nan ta shigo da sauri, Magajiya ta kalleta tace "Amso Yarima zan koma."
Abdulsamad ya kalleta sai dai shima baice komai ba sai mika ma baiwa 'yar yai suka fita.
Tana fita ta tura a kira mata Yayanta Hisham.
Zaune take a d'aki ya shigo cikin sauri, ganin yanda fuskarta take a had'e yasa yace "Magajiya lafiya?"
Kofin dake hannunta ta jefo da karfi inda yake saura kiris ya jefeshi hakan yasa yasan lalai yayi laifi, da sauri ya matso cikin sanyin murya yace "kanwata........."
Wani mugun kallo ta bugamai tace " me kakeyi har Sarki yai aure ban sani ba?"
Gabansa ne ya fad'i cikin tsananin mamaki yace "Aure kuma?"
Wani kallo ta kara mai tace " ba nace ka dinga kula da duk al'amuransa ba? Yaya wai meke damunka ne? Ko ka manta da wasiyyar Baba yace?akan ka dinga bin duk abinda na fad'a?"
Yace "Yahkuri Sarauniya uwar Sarki duk wanda yaja dake shine a wahale, tayaya wata mata can da baki santa ba zata kona miki rai bayan ko ta shigo sahun ragowar matan zata shiga?"
Shiru tai tana kallansa, yace " menene naki na kishin wata macen bayan ba haihuwa zatai ba bare musa ran samun matsala nan gaba?"
Shiru tai kafin daga bisani tai ajiyar zuciya sannan ta d'an ja tsaki tace " ko menene dalilina na jin haka? Tunda yake aure ban taba jin haushi ba sai yau."
Hisham yai dan dariya ganin ya shawo kanta yace "kinada yarima magajin sarki sannan kina da ni waziri menene zai saki damuwa?"
Murmushin jin dadi tai sannan tace " zan baka sako ka aikama gidan matarka sannan itama ya kamata ta dawo."
Kai ya jinjina alamar gamsuwa yace " yanzu kam bamai gane ta haihu."
Sukai murmushin jin dadi.
_nikam nace hmmmmm_
Yau ranar kwanan Basira ne a yanda Mai martaba ya tsara sai dai kasancewar bata nan ya kamata ace shi kadai zai kwana, sai dai shikam da daddare ya lalaba ya fita.
Tana zaune ita kadai shiru, gefenta bayinta ne suke ta hirarsu, taji sallama.
Da sauri suka mike suka shiga kwasar gaisuwa sannan suka fita, ya rage saura su biyu.
Zama yai daga gefenta kadan yana shirin magana tai saurin cewa "ina wuni?"
Kallanta yai yace " da alama sai na sa an d'aure masu kula dake."
Dasauri ta kalleshi idanunta sun bayyanar da tsoro tace " me sukai?"
Yace " tunda haryanzu basu koya miki abinda ya dace ba."
Da sauri tace "Barka da dare."
Sannan ta cigaba "wlh na sha'afa ne ba laifinsu bane."
Murmushi yai sannan yace " ke bakya magana dayawa ne?"
Shiru tai batace komai ba, yana kallanta yace "kishirya zuwa jibi zaki koma gidana."
Kallansa tai batace komai ba itakam tana san jin shi d'in wanene.
Jitai yace "Abdulsamad sunana sauran bayani zaki gani inkin isa jibi."
Kai ta d'aga ba tare da ta kalleshi ba, hannu yasa ya rikota suka shiga ciki.
Duk da itakam tana tsoro sai dai bata isa bijire ma wanda ya taimaki rayuwarta ba.
Sai da komai ya lafa sannan bacci yai gaba dashi, itakam shiru tai dan baccin ya bar idanunta ta dade tana tunani kala kala kafin tai bacci.
***********
Magajiya da kanta tasa aka gyara b'angaren da zata zauna sannan tasa aka sanar da Sarki akan komai ya kammala, shikuma ya aika a sanar dasu lokacin da za'a daukosu.
Da daddare aka sata tai wanka, bayan tasa kaya aka miko mata alkyabba irin masu karfin gaske da nauyi irin na da, aka sa mata, mamaki sam ya hanata magana, sarka ta zinare aka sa mata aka sa mata abin kafa da awarwaro, kasa jurewa tai ta kalli baiwar tata tace