Showing 51001 words to 54000 words out of 146065 words

Chapter 18 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

Turab kam yana shiga d'aki ya kule ya zauna a kan gado, sai dai ba wanda yasan me yake tunani yake kuma sakawa a ransa, daga shi sai mahallicinsa.




**********


A kano kuwa Bilkisu da kanta ta sanar ma Mahaifinta tana kaunar Abu Turab hakan yamai dadi dan shi kansa ya mai.


Shi kuwa Hisham ya isa kano bayan azahar, bangaren Gimbiya Sadiya wato Amarya ga mai martaba, bayan an masa iso.


Bayan sun gaisa ne kansa na kasa yace " Gimbiya nazone dauke da sakon Gimbiya."
Murmushi tai tace " Magajiya ikon Allah wani sakon ta aikoka dashi?"
Yace " Maganar auren Gimbiya Bilkisu da Yarima Abdulmajid"


Kallan mamaki tamai tace "Me kake nufi? Na da'uka ai an bar wannan maganar ganin yau d'innan Abu Turab yabar gidan nan, kuma inada labarin Bilkisu ta amince dashi."


A razane ya d'ago yace " Gimbiya ta yaya Yar sarki guda zata amince da Makaho? Na tabbata asiri suka mata."
Kallan rashin fahimta tamai tace " waye makahon kenan?"
"ABU TURAB mana." Ya fada kansa tsaye.
Tace " ban fahimta ba, a iya dai sanina banji ancemin yaran nan makaho bane."
Murmushin jin dadi yai yace " kisa a tambayo miki gimbiya."
Tace " in kuwa hakane na tabbata Mai Martaba bazai aminceba."
Nan ta aika a kira mata Jakadiya.


Bayan Jakadiya ta gaisheta ne Gimbiya Sadiya ta kalleta tace " Nikam ya Abu Turab yake ne? Yanada wani nakasu ko abin kushewa a tattare dashi?"


Jakadiya tace " ban fahimceki ba Gimbiya."


Gimbiya Sadiya tace " hakkinane a matsayina na matar Sarki intambayi wanda Bilkisu zata aura."
Jakadiya tace " Tuba nake ranki ya dade, amma Yarima Turab bashida wani nakasu a jikinsa."


Da sauri Hisham yace " idanunsa fa?"
Tace " idanunsa kuma? A iya sanina bashida wata matsala na gani da idanunsa."
Hisham ya kalleta yace " Jakadiya ki tuna da kyau, baki ganshi da sanda ba?"


Kallan mamaki tamai tace " Na kasa fahimtar wannan tambayar taka, ni dai a iya sanina bashida wata sanda kuma sunyi magana ta fahimta da Gimbiya, ya kuma shiga gun Takawa."


Gimbiya Sadiya ta kalleta tace " tashi kije Jakadiya."
Zufa ne ya shiga ketoma Hisham tsananin tashin hankali, kasa yarda yai da wannan zancen ya mike yace " bari naje gun Mai Martaba mu gaisa."
A ransa kuwa so yake yaje ya dan tambayeshi a dabara.


Yana mikewa yaji kafafunsa sun mai nauyi, da kyar ya iya d'agasu.
Haka ya garzaya fadar sarki.
Bayan ya shiga ne suka gaisa da Mai Martaba.
Sarki ya kalleshi yace " Waziri ba dai biyu Abu Turab kai ba?"
Hisham ya dan yi yake yace " a'a na dai shigo garin ne naga ya dace inzo mu gaisa."
Sarki yace " hakan yayi, Abu Turab sun tafi yau."
Hisham yace " ai na d'auka ma sai zuwa gobe zasu taho, ko dai abin bai yiwu bane?"


Sarki yai murmusa yace " zamu aiko da amsa cikin wani satin."
Hisham ya rasa ta inda zaiyi tambayar ganin yanayin Sarki alama ce ta gamsuwa da yai da Abu Turab.
Sallama yamai sannan ya mike ya fito.
Sai da ya kara tambayar wasu fadawa kowa ya tabbatar mai ba sanda a hannun Abu Turab sannan ya juya ya shiga mota.
Jiyai kansa ya dau wani zafi yana rasa ta inda zai fara tunani.
Me ke faruwa?
Kenan kallansu kawai yake?
Tabbas lalai yau yanada mumunan labari, suna mai kallan dan tsako ashe kura ne?????




Nace Daga Baya kenan Hisham....😝




*TEAM ABU TURAB 🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*33*





Hisham ya iso Zariya cikin tashin hankali, ana magrib yana shiga bangaren Magajiya.
Zaune take gefenta kuma Khadija ce tana duba mata wasu kayayyaki, Abdulmajid kuma na gefenta na hago.
Hira sukeyi da Abdulmajid sama sama, itakam Khadija bata sa musu baki a zaune kawai take tana aikin da aka sata.
Can cikin hirar tasu ne Abdulmajid ya kalli Khadija yace " ke dama inada magana dake."
Kallansa tai batace komai ba.
Fuskarsa a had'e yace " haryanzu baki daina zuwa b'angaren Abu Turab ba ko? Kina mace ko kunya."
Magajiya ce ta kalleta tace " Khadija me kenan?"
Kanta ta maida kan kayan tace " meye amfanin ma in naje tunda ba kulani yake ba?"
Dariya Abdulmajid yasa yace " kinji kunya wlh, kina mace kina bin namijin da baya sanki."
Zatai magana Hisham ya banko kofa cikin hanzari.
Jin yanda a ka bugo kofar yasa duk su ukun suka maida ha kalinsu kan kofar.
Hisham na shigowa ya kalli Khadija yace " bamu guri."
Mikewa tai tsam dan dama ba san zaman takeyi ba sai dai jikinta ya bata ba maganar arziki zasuyi ba.
Tana fita ta tsaya a jikin kofar d'akin.
Hisham ya kalli Magajiya cikin tashin hankali yace " Magajiya!"
Ita kanta hankalinta ya tashi ganin ita data aikashi maganar aure kano? Ya dawo mata a haka?"
Kallansa tai tare da tattara hankalinta kansa.
Yawo ya had'iya sannan yace " yaran nan yana gani Magajiya."
"Yaro? Wani yaro kake nufi kenan?"
Yace " yaron nan mana da baya gani."
Idanu tad'an juya tace "wai wani yaran kake nufi? Nibansan wani yaro ba."
Abdulmajid ma yace " wani yaro kake nufi Kawu?"
Hisham yace " Yarancan Abu Turab."
Dariya Magajiya tai tace " Waziri? Ko dai gajiya ta fara ratsaka ne? Me kake san fada takamaimai?"


Hisham ya kallesu cikin wani yanayi yace " Wlh da gaske nakeyi, yarancan Abu Turab idanunsa garau suke."
Abdulmajid ya mike tsaye yace " ni wlh na dauka maganar arziki zaka fada ashe tsokana kazo da ita, ni nayi masallaci."


Hisham ya kalli Magajiya yace " Magajiya na taba miki karya akan harkar dana san bazata amfanemu ba?"
Wannan lokacin kam ta kalleshi kallan nutsuwa, Abdulmajid ma ya ja ya tsaya.
Khadija kam da baya da baya ta juya tai waje cikin tashin hankali, me kenan?


Hisham ya kalli Magajiya sannan ya kalli Abdulmajid yace " dayaje kano a garau yaje musu."
Magajiya ta kanne idanuwanta tace " ban fahimta ba."
Nan Hisham ya zayane mata kaf abinda ya faru na zuwansa.
Tashin hankali karara ne ya bayyana a idanun Magajiya, kallansu tai cikin tashin hankali tace " ku bani guri."
Nan suka mike suka fita.
Abdulmajid ma bangarensa ya wuce cikin d'emuwa da rashin sanin abinda zaiyi.
Shi kuma Hisham yai waje.
Magajiya ta kasa zaune ta kasa tsaye ba shakka in har hakan ne lalai kaf duniya ba wanda ya taba rainamin hankali irin yaran nan.


Kwallawa wata mai kula da ita tai, cikin hanzari ta iso.
Bata ko juyo ta kalleta ba tace " kiramin Abu Turab."
To tace kawai tai waje itama.


Abu turab yana zaune kan sallaya tilawa yakeyi cikin daddadan muryarsa, yau ko masallaci bai je ba dan bayasan ganin kowa.


Garzali ya mai sallama, sai daya kai aya sannan ya amsa mai.
Garzali ya matso ya tsugunna sannan ya sanar dashi sakon Magajiya.
Ya dade kafin yace " ace mata ina zuwa."
Nan yai waje.
Sai dayai sallar isha'i sannan ya mike ya fito, Garzali ya mikamai Sandarsa wacce Lantana ta kawo.
Amsa yai sannan yai gaba Garzali yabi bayansa.


Bayan an mai iso ya zauna a kilisarta sannan ta shigo cikin takamarta.
Idanu ta kafa mai har ta zauna shikam fuskarsa a had'e take yana zaune kansa a kasa.
Bayan ta zauna ne ta kalleshi tace " Abu Turab ka iso?"
"Barkanki da warhaka Umma Babba."
Murmushi ta sakarmai sannan bata amsa ba tace " kiranka nai in baka wani labari."
Shima bai amsa mata ba dan lalai ji yake bazai iya kallanta ba saboda tsananin tsana.
Magajiya tacigaba " Wani dan tsakone kurma ya taso karkashin kulawar kura, ita kurar dama tanada nata d'an hakan yasa ta had'asu duka ta rike, a kwana a tashi sai kurar nan ta tsufa, ta fahimci dole tana bukatar barma d'anta mukaminta a daji.
Kasan abin mamaki?"
Abu Turab ya d'ago suka had'a ido, bai d'auke idanunsa daga cikin nata ba yace " bazai wuce wannan d'an tsakon kurma yace shi yake san aba wannan mukamin ba."


Ta kuramai ido itama tace "Haka! Ashe ka harbo jirgin, sai dai kasan wani abun tsoro a labarin?"
Kallan ban fahimceki ba ya mata tace " Tun daga sanda Kurar nan ta fahimci kudurin wannan d'an tsakon har yau ba wanda yasan inda wannan d'an tsakon yake."


Wani lalausan murmushi ne ya bayyana a fuskar Abu Turab yace " sai dai ban fahimci abu d'aya ba a labarin, d'an tsakon dama can kurma ne ko kuwa yayi hakan ne da saninsa ya noke bakinsa?"


Idanun Magajiya ne suka d'an canza sai dai da sauri ta maida fuskarta cikin yanayin hankali a kwance tace " hmm wannan shine abinda ya sa kurar nan dana sani."


Gani tai ya saki wata yar karamar dariya har hakwaransa suka bayyana ya kalleta yace " Tuba nake Umma Magajiya, na saki a duhu danai na nuna miki nidin bana gani."


Wannan karan kam duk yanda taso ta b'oye bacin ranta ta kasa, karara ya nuna a fuskarta.
Abu Turab ya rangwadar da kai yace " umm ya zamuyi yanzu?"
Tace da me kenan?
Yace " dan banaji zan iya yafemiki."


Kallo tamai cikin mamaki tace " bakaji xaka iya yafemin kamar ya kenan?"


Fuskarsa ce ta canza idanunsa sukai jaa, ya kalleta yace " bazan taba yafe miki ba daga ke har yayanki, abinda yama yayan mahaifiyata da matarsa da ke da kika umarceshi a sanadiyar kokarin rabani da duniya da kukai kuka jamusu mutuwa, ni Abu Turab in har Basira da Abdussamad sune suka haifeni sai na sa an muku hukunci daidai da laifinku."


Wata muguwar dariya ta saki, wanda ya sashi tsayawa yana kallanta tace " kai a suwa kenan?"
Yace " a wanda yake da damar zama Sarki."


Ta ja tsaki tace " Shekaruna d'aya da mahaifinka, hakan na nuna nid'in batayau bace, ba kai ba hatta mahaifinka bai isa yaja dani ba."


Abu Turab ya d'an juya bakinsa sannan ya had'a lab'ansa yace " well, shi daban nid'in daban, mu zuba mu gani."


Tace " shikenan mu zuba mu gani, na baka sati biyu kacal, ina zaune anan zakazo gwiwowinka biyu ka nemi gafarata."


Yace " ina fatan hakan ta kasance."
Kallan juna sukai, kansa ya saukar kasa ya juya kansa gefe tare da d'aukan sandarsa yace " Umma Babba nagode ni zan wuce, ki huta lafiya."
Kallan mamaki tamai, gani tai ya sa sanda a gaba kamar makaho.
Idanu ta kuramai har ya fita, ta murmusa tace " hmm a kashi 100 na baka 40, ba laifi ka iya b'oye fuskarka da abinda ke ranka, ko dayake d'an Abdussamad ne."


Fuskarta ta kuma had'ewa tace " kai har ka isa? Kamar ni? Kamar ni Magajiya ka rainan hankali?"
Kwafa ta saki.
Abu Turab kam na fita ya juyo ya kalli bangarenta sannan ya juya ransa a b'ace.






*********




Itakam Khadija ta shige d'aki ta kwanta akan gado, me ke faruwa? Ya Turab yana gani? Anya kuwa? Ta yaya? Yaushe?
Itakam ta kasa yarda da abinda taji, ba dai wani sharrin zasu kullama bawan Allah ba?
Da sauri ta mike zaune tace " dole in fadama Yaya gobe akan abinda sukace."




*TEAM ABU TURAB🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*34*

Washegari.


Da safe zaune yake a gaban Mai Martaba a cikin Turakarsa.
Mahaifinsa ya kalleshi cikin kulawa yace "Turab me yasa ka dawo tun jiya? Sannan tundaka dawo baka zo ba."


Fuskarsa a d'aure take dan sam ba fara'a a cikinta kallansa yai yace " Dama zuwa nai na sanar dakai zan auri Bilkisu yar gidan Sarkin kano."


" Alhamdulilah nagode kwarai na kuma ji dadi daka fahimceni."


"Bayan umarnin auranta daka bani a yanzu auranta yana tattare da amintata, a da auranta zanyi saboda umarninka, sai dai yanzu zan aureta ne dan kaina."


Fuskar mai martaba ta kara fadada da farinciki yace "naji dadi yanda kuka fahimci juna."
Kallan Mahaifinsa yai yanajin wani radadin takaici a ransa, yace " zan koma."
"Abu Turab!"
Komawa yai ya zauna sannan ya kalli Mahaifinsa dan yanda yaji ya kira sunansa yasan yana bukatar nutsuwarsa.


Mai Martaba ka kalleshi cikin kulawa yace " Abu Turab me yasa kake so ka b'oyemin abinda ke ranka? Me yasa bakasan mudinga raba damuwar dake zuciyoyinmu?"


Shiru yai sai dai zuciyarsa tadan raunana.
Sarki yace " Meke damunka?"
Shiru ya kuma yi sai dai a wannan karan ya d'ago ya kalli mahaifinsa da idanunsa da suka canza launi.
Sarki ya cigaba" Shikenan mubar maganar inhar zuciyarka bata san inji."
Abu Turab yace " zan koma Abba."
Mai Martaba ya murmusa yace " to Turab."
Mikewa yai ya fito daga bangaren mahaifinsa, ba shakka yanasan ya sanar dashi damuwarsa da kuma neman shawararsa sai dai ba yanda zaiyi domin kafin ya kasance mahaifinsa sarki ne shi a wannan garin dole kuma yai abinda ya dace a matsayinsa na sarkin garin.


Bangarensa ya nufa rike da sandarsa yana gana Garzali da wani na gefensa.
Sunsha kwanar da zata kaisu bangarensa yaji muryar Khadija tace " Ya Turab."
Haka kawai ta samu kansa da kin tsayawa dan abinda Mahaifinta sukamai bayaji ko ganin Khadija yana kaunar yi a wannan lokacin.
Ganin bai tsaya ba yasa ta kara sauri, har tazo inda suke, tace "Ya Turab."
Tsayawa yai sai dai bai juyo ba.
Gabansa ta dawo ta kalli Garzali tace " dan Allah kudan matsa kadan zanma Ya Turab magana."
Nan suka gaisheta suka matsa.
Kallansa tai tace " Yaya."
Bai kalleta ba sai dai yace " ya akai?"
Tace " yaya kana ganina?"
"Me kike nufi da hakan?"
Ta kara matsows tace " Yaya ninasan baka ganina, sai dai na rasa dalilin Abba na na zuwa ya fadama Magajiya wai kana gani."


Kallanta yai, ta kalleshi hakan yasa ya kauda idanunsa, tace " Yaya Please ka kula da su wlh sam hankalina ya kasa kwanciya dasu, na tabbata da abinda suke shiryama."


Jitai yace " yanzu kinaso ki cemin zuwa kikai kiban shawara akan kula da Mahaifinki? Ko kuwa zuwa kikai ki sanar dani Mahaifinki zai cutar dani?"
Cikin rashin fahimtar kalamansa tace " Ban fahimceka ba..
.."
" in mahaifinki zai cutar dani tayaya nake da tabbas din ke bazaki cutar dani ba?"


Kallansa tai a zabure cikin tsananin mamaki tace " Yaya."
Yace " da mahaifinki da ni wanene mafi kusanci dake? Wanene wanda yake jininki? Tayaya zan yarda zaki juya ma mahaifinki baya akan wani makaho wanda bakuda hadi dashi?"


Gaba daya ta ma kasa magana dan batada amsar da zata bashi, tana neman amsar da zata bashi taga ya fara tafiya.
Idanunta ne suka ciciko a hankali wasu zafaffan hawaye suka xubo mata, me yaya yake nufi?
Gani tai ya tsaya a jikin kofar bangaren Mahaifiyarsa da alama magana yake da wani, gani tai ya saki fuska ba kamar yanda ya cukule mata ba.


A hankali ta tako har gefen da suke.
Mairo ta gani a tsaye a gun rike da kula suna magana, juyawa tai zuciyarta sam ba dadi.


A bangaren sa kuwa, bayan ya taho daga gun Khadija zai wuce yaji tace " Ya Ina Kwana?"
Juyowa yai ya kalleta yace " Mairo kece?"
Tace " nice, Umma ce ta sani in kawo mata abu yau da safe."
Murmushi yai yace " Mairo kinaji da Umman nan."
Ta kalleshi tace " Da cemaka akai Ummanka ce kai kadai?"
Kallanta yai yace " Yar gidan Umma ce ke dama ai."
Zatai magana yace " ki gaisheta."
Tace " bazaka shiga ba?"
Kallanta yai fuska a sake yace " Later."
Daga nan yai gaba.
Kallansa tai cikin mamaki dan taga ba haka suka saba ba.


************




Abdulmajid ne zaune gun Magajiya yace " Umma ya kukai Jiyan? An bincika yana ganin?"


Magajiya ta kalleshi tace " Abdulmajid, ka nutsu sosai kaji abinda zan fada ma."
Kallanta yai sannan yace " inaji."


" Ka shiga hankalin sosai da Abu Turab ka daina masa kallan wanda bashida wayau ko bai san komai ba, wlh wnnan yaran hmmmm"
Tai shiru sannan tacigaba " kadai bi a hankali karka kuskura ka fada tarkwansa."


Abdulmajid ya dan tabe baki yace " ni Umma har wannan yaran ya kai in shiga hankalina a kansa?"
Ta kalleshi cikin isarta sannan ta ce " Abdulmajid kenan."
Kara tabe baki yai yace " ni Umma dama maganar aurena nazo muyi, nace tunda dai Bilkisu an riga an hadata da Turab mai zai hana mu juya akalar auran kan Mairo."
Ya karasa maganar yana dan sosai keya.


Kallansa tai tace " Mairo? Wacece hakan?"
Yadanyi kasa dakai yace " Mairo 'yar gidan Barde."
Barde?bakada hankali ne?"


Yace " Umma to...."
Katseshi tai cikin fada tace " nimeyasa baka tunani ne a al'amuranka? Abu Turab zai auri Gimbiya Bilkisu kai kuma dan hauka kacemin wata Mairo? Me yasa ne bazaka dinga abu da tunani ba?"


Fuska ya hade dan maganar ta batamai rai, Magajiya ta cigaba " kada ka kuskura ka karamin wannan banzan zancen."
Tana kaiwa nan ta maike tai ciki.
Kallo ya bita dashi da alama zai je gun Sarki ya fadamai kuwa dan shi kam Mairo yakesan aura ko ta wani haline kuwa, dan kwanan nan har mafarkinta yake wai sunyi aure.




🤣




**************




Kwana biyar da dawowarsu kuwa Mai Martaba Sarki Shu'aib mahaifin Bilkisu ya aiko mutane daga Masarauta akan amincewa da aure da sukai.


Wannan labari ya tadama Khadija hankali, sai dai duk yanda taso ganin Abu Turab abin ya faskara, itadai ba dama ta shiga bangarensa dan ya bada umarnin hana kowa shiga bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login