Showing 6001 words to 9000 words out of 146065 words
Chapter 3 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
" amma wannan shigar batai yawa ba? Ni fa na fara tsoro."
Baiwar tai kasa dakai tace " tayaya kaya zaiyi yawa bayan haka al'adar masarautar take? "
Cikin tsananin mamaki tace "Masarauta?"
Kallanta baiwar tai tace " eh mana duk abinda muke koya miki ai abinda zakiyi ko zaki tarar acan mukeyi."
Wani abu ne ya tsaya mata a makogaro, sarauta? Ba shakka ta gane yanzu, wato abokin yaya ne wanda kusan duk labarin yaya baya wuce na Sarki Abdulsamad lalai shine ya aureta kenan, to amma ina ita ina shi? Ta ina? Ita da ba cikakiya ba? Jitai an dafata hakan yasa tai firgigit daga tunanin data tafi.
Baiwar tace " Ranki ya dade ana jira."
Dakyar ta fara d'aga kafarta suka fita.
*******
Haka suka isa gidan tunani duk ya isheta.
B'angarenta aka wuce da ita suna tafe ana gaidasu danma bata ganinsu saboda fuskarta a rufe take.
Har suka shiga aka ajiye ta a kan bakin gado nan kowa ya fita aka barta da baiwarta guda d'aya.
A ka'ida bayan an daura mata aure akwai wasu bukukuwa daya kamata ayi agidan sarautar sai dai Abdulsamad ya turo a sanar da Magajiya akan kar ayi, tayi mamakin jin haka ta aika a tambayeshi dalili ganin al'adar gidance hakan.
Abdulsamad yace " Gani yai ba'a dade da yin taron suna ba shi bayasan almabazaranci."
Magajiya tayi dariya jin haka dan tasan lalai uzuri kawai yake nema na kar ayi amma wannan ai ba hujja bace, hakan kuma ya nuna mata lalai Sarki ba san auran yake ba da alama akwai wani abu a kasa ne.
Basira kam da yake mai san shiru ce zaman bai dameta ba.
Yau tana tashi baiwarta Ta sanar da ita zuwa gaida magajiya.
Batasan dalili ba sai dai tanajin sunan taji gabanta ya fadi, jiki a sanyaye ta fito suka nufi b'angaren Magajiya.
Bayan kowa ya zauna ita da ragowar matar nan ta gaidasu kowa na mata kallan wulakanci kallan wacce ba'aso.
Fitowar Magajiya yasa taga kowa ya nutsu, nan ta juya suka had'a ido kwarjini da cikar zati irin na Magajiya da isa da mulkinta yasa Basira tai saurin dauke ido, gabanta kuwa yaki daina faduwa, addu'a kawai ta shiga yi har Magajiya tazo ta zauna.
Basira ta d'ago suka kara hada ido, gani tai Magajiya ta mata alama da hannu, jiki a sanyaye ta isa gunta.
Magajiya cikib muryar rad'a tace "sau daya zan fada ki tsaya kiji dakyau, yau ya zama rana ta farko kuma ta karshe da zan juyo in ga idanuwanki a kaina banasan kallo."
Cikin inina tace "Tuba tuba nake."
Kowa ya gaida Magajiya sannan aka kawo abinci itakam dakyar ta ci kadab nan aka kawo musu ruwan zafi anmai had'a had'e, itakam Basira komai ya isheta a gun abincin ma da kyar taci ruwan zafi kam da kyar ta iya yin kurb'a d'aya.
Magajiya ta kalleta tace " shanyewa zakiyi ai."
Basira tai kasa dakai tace Ranki ya dade bana iyashan ruwan zafi tun ina karama."
Magajiya tai wani murmushi tace " inkinsha ya kasheki."
Basira gabanta na faduwa da tsoro gashi harga Allah batashan ruwan zafi dan tun tana yarinya datasha tai ta amai haka kuraje suka feso a bakinta tun daga nan aka hanata, an nemar mata magani amma ba'a dace ba sam.
Nan ta d'aga kofin ta fara sha kafin ta shanye kuwa sai amai ya feso, nan ta mike da sauri ta fita ta shiga kela amai kan kace me kuraje sun cika bakinta.
Tsoro ya kama Magajiya gashi ranar kwanan Basira ne, ya zatai in Mai Martaba ya tambayeta dalilin hakan???????
[truncated by WhatsApp]
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼♂*
_Alhamdulila an gama *Nayi Nadama* da *Hamal* Allah ya kara Baseera (Ameen) ni da ragowa 'yan kungiyar Haske na muku bangajiya, Allah ya kare mana ku😍_
*5*
Ganin yanda takeyi yasa Magajiya tace a maidata b'angarenta, nan kowa ya mike ya fita sakamakon sallamarsu da tai.
Suna fita ta aika a kira mata yayanta Hisham, bai dade ba ya shigo nan ta sanar dashi komai sannan ta d'aura da cewa " yanzu in Mai Martaba ya tambayeta ta fadamai tirsasata nai zaiyi zargin wani abu kasan halinsa sarai."
Hisham yai shiru sannan ya ce " bari na kira mai magani ya dubata."
Wani mugun kallo ta bugamai wanda yasa yace " tuba nake ashe fa babu namijin da ya isa shiga b'angaren matan sarki ba tare da izini ba ko an sanshi ba."
Kanta ta d'auke daga inda yake tace " Ka fad'ama Turaki ya tambayar mana kaninsa ko akwai maganin da zai warkar da ciwon tunda naga kanin nasa yasan kan magani."
Nan ya amsa da to sannan ta kara kallansa zatai magana yai saurin cewa "na fahimci komai kinaso kice shi Turakin ya rike maganar a sirri."
Murmusawa tai kad'an sannan ta juya kai.
Hisham ya mike ya fito yana fita waje yai d'an kwafa tare da kallan inda ya fito sannan yai gaba.
Basira kam kwanciya tai ta shiga bargo saboda sanyin dake ratsata itakam batasan gidan nan sam ita duk rayuwarma ba dadi take mata ba inta itace har gwara can inda ta fara zama akan nan dan a kalla a can gidan bayi insuna hira suna sata dariya amma nan kam tanaji tunda ta shigo haryau batai dariya ba.
Tana nan kwance aka aiko mata da magani, ko kallan maganin batai ba dan itakam ta sab ciwonta inta kwana washe gari zai baje.
Bayan tayi isha'i ne wasu bayi suka shigo suka tsaya a inda take, babbar cikinsu wacce suka zauna da ita a can ne, ta matso kusa da Basira tace "Ranki ya dade wanka zaki tashi kiyi."
Basira batai musu ba ta mike saboda a can an sanar da ita yin musu laifi ne kuma yana jawo a rage ganin girmanta.
Ban d'aki ta wuce, ruwan zafi ne aka saka a katan baho an saka abubuwan kanshi kala kala, kina shiga b'an d'aki wani dadad'an kamshi ne zai bugeki, nan ta sata a ruwan zafin.
Bayan sun gama wankan ne suka bata wasu kaya masu kyaubta saka sannan wannan matar ta miko mata wani ruwa a kofi ba musu ta amsa ta shanyi, maganin ba dadi bata koma san dame akayishi ba sai dai tasan akwai zuma a ciki.
Tana gama shiryawa wata mata ta shigo mai d'an jiki haka, tana shigowa suka gaisheta jin suna cewa Jakadiya yasa ta fahimci wacece.
Jakadiya ta kalleta sannan ta gaisheta tace "Ranki ya dade muje ko?"
Basira batai musu ha tabi bayanta.
Sun d'anyi tafiya kad'an kafin su shiga wani b'angare, sosai an tsara b'angaren gashi kato ita da tana tunanin b'angaren Magajiya yafi kyau sai dai yau ta gane wannan yafi, ga girma ga kyau,kofar wani d'aki suka isa sannan Jakadiya ta kwankwasa, daga ciki akace shigo.
Jakadiya ta kalli Basira nan Basira ta shiga dan ta gane hakan ake nufi.
Katon d'aki ne sosai ganinsa yasa tai saurin maida kanta kasa, murmushi ya saki sannan yace " Amarya karaso mana."
A hankali Basira ta karasa inda yake ta tsugunna nesa dashi sannan tace "Barka da dare."
Alama ya mata da hannu akan ta matso kusa dashi, idanu ta d'an zaro kad'an tana tsoron kar ta matsa ya kula da bakinta da ya ke ciki da kuraje har kan d'an leb'enta.
Ganin yanda yake kallanta yasa ta matsa kadan, hannu ya kara nuna mata akan ta kara matsowa, Basira ta rasa yadda zatai a hankali ta matsa sai dai ta sunkuyar da kanta.
Abdulsamad yasa hannu ya jawota kusa dashi yace " bakiga me ke gabana bane?"
Sai a lokacin ta kalli gun, abincinsa ne a gun da 'ya'yan itatuwa.
Ya kalleta yace "Zubamin."
D'agowa tai ta kalleshi wanda hakan yasa ya kalli bakinta, mamaki ne ya kamashi yace "Menene hakan a bakinki?"
Da sauri ta rufe bakin, matsowa yai ya fizge hannuta sannan ya ce bud'e bakinki, tsoro ne ya kamata dan Allah ya bashi kwarjini, bud'ewa tai cikin tsoro.
Idanunshi taga sun canza cikin fada yace "meye hakan?me ya faru da ke? Ai sanda kike can ba haka kike ba."
Bakinta ne ya fara rawa, cikin tsoro tace "banashan ruwan zafi ne sai dazu tsautsayi yasa nasha na dauka na warke."
Kallanta yau cikin kokwanto da sauri tace "tun ina karama na daina sha sam na dauka na daina."
Ta dauka zaiyi fada sai taji yace " kidinga kula yanzu bari nasa a samo miki magani."
Kai ta girgiza tace " ai gobe zai warke."
Jakadiya wacce ke makale a kofa ta saka kunne tana jin komai da sauri ta juya ta fara tafiya cikin sauri kamar zata kifa.
Shikam Sarki daga wannan matsowa ya shiga wani al'amarin daban ya manta da abinci......Lol!
Jakadiya kam bata tsaya ba sai a b'angaren Magajiya tana isa ta nemi izini ta shiga.
Zubewa tai a kusa da Magajiya nan ta zayyane mata komai.
Murmushi Magajiya tai tace "da alama tanada hankali."
Jakadiya tace "nima na kuka da hakan."
Magajiya tace " ya ya? Ya kusanceta?"
Jakadiya tsoro ya kamata itakam sam ta manta ma aiki biyu aka sata ta ji me zatace da kuma ko Sarki ya nemi Basira.
Kallanta Magajiya tai tace " menene?"
Yawo Jakadiya ta had'iya tasan halin Magajiya sarai ba tada kyau ko yayanta ba raga mai take ba hatta Sarki in ranta ya b'aci sai ta san yanda tai ta kona mai nasa ran ita kuwa ina ita ina yi mata laifi? Amma itakam tana ganin me zaisa Sarki ya kusanceta bayan ragowar Matan ma sai ya dade bai kusancesu ba?
Magajiya ta kafeta da ido.
Jakadiya ta saki murmushi tace "ina fa? Yana gama tambayarta yai kwanciyarsa dan ko abinci baicibama.
Magajiya ta saki wata bazawarar dariya tace " nikaina jikina yaban haka saboda Basira yarinyace bata wuce 16 zuwa 17 ba shi kuma na sanshi sarai bayasan kusantar yara ko ya auresu yafiso sai sun girma."
Jakadiya ta sake dariya tace"Ai Mai Martaba ke kadai ce a gabansa Hajiya Magajiya mahaifiyar Yarima Amdulmajid Magajin Sarki."
Kanta ta juya tana murmushin kasaita, nan Jakadiya ta mata sallama tai waje.
********
Magajiya ta yanke shawarar daina ba Basira shayin nan saboda taga abinda ya faru sannan taji Mai Martaba bai fara nemanta ba hakan yasa ta sa Hisham ya samo mata wani wanda ba sai a ruwan zafi ba, dan gwara a samo mata ta ajiye kafin Mai Martaba ya fara tunanin kusantarta.
Jakadiya kam bayan ta dawi ta tambayi wata baiwa wacce take ta hannun daman ta ce, ita ta bari a gun dama ta tafi kai gulma akan ko wani abu ya faru.
Baiwar ta fada mata ai tana tafiya akai abun.
Shiru Jakadiya tai tsoro fal ranta sai can tad'anyi tsaki tace "to ai ba abinda zai faru ma dan inaji Sarki Juya ne inba haka ba matansa nawa haryanzu ba haihuwa? Da ya kwanta dasu da kar ya kwanta duk d'aya ne."
Baiwar tace " wani juya kuma bayan Magajiya ta haihu."
Jakadiya tai dariya a ranta tace " sai dai a rainawa dolo hankali amma ni da nake zuwa gunta banga wani alamar ciki ba, wanda nake gani kuwa baimin kama da ciki ba sannan menene dalilin turani tafiya zuwa Masarautar Kano a daidai watan haihuwarta? Ni nasan akwai wata a kasa.
Murmushi tai a ranta, ganin komai ya zo mata daidai.
**********
_Bayan wata hudu_
Basira kam duk ta rasa me ke damunta bata iya cin abinci gashi shiru ba al'adarta sai dai bata kawo komai a ranta ba haka kuma tana kokarin yin komai daya kamata wanda hakan yasa ba wanda yai tunanin komai.
Sai dai a 'yan kwanakin nan ta fara zargin ko ciki ne ganin yanda cikinta yai tauri sannan ya dan fara tasawa kad'an.
Magajiya kam nasan Basira yanzu tunda taji abinda ya faru, haka zatai ta aika mata da abubuwa, itakam Basira har yanzu ta kasa sakar zuciyarta da matar.
Matsala ta fara faruwane daga sanda kanwar mahaifiyar Magajiya tai tattaki na ziyara ta kawoma 'yar yayarta, wanda a lokacin matan sarki duk suna zaune kwasar gaisuwa.
Kallo d'aya tama Basira tsoro ya kamata dan ta fada dashewa irin na masu cikin nan.
Ido ta kurama Basira wanda har tasan akwai matsala, da sauri Basira ta dauke idanta daga kan matar.
*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼♂*
_Where are u My Dear BillynAbdul? Here is ur special page, tnx for the care Tawan. Allah ya bar zumunci ya kareki daga sharrin masu sharri (Ameen)_
*6*
Suna fita Kanwar Mamanta wato Aunty Lami ta matso kusa da ita tare da cewa " Magajiya nikam waccan wacece?"
Ta fad'a tare da nuna inda Basira ta zauna, murmushi Magajiya tai tace "Ahhh Basira? Kema ta burgeki ne? Bansan meyasa ba amma yarinyar ta shiga raina."
Aunty Lami tai d'an shiru tana tunanin ta inda zata fara, can tace " amma dai ba matar Sarku bace ba ko?".
Had'e rai Magajiya tai tace " wace irin tambaya ce wannan? Baki ga kayan jikinta bane? Ko akwai masu sa kayan Sarki bayan matansa?"
Aunty Lami ta dafa kai, kanta na kasa tace "amma dai ba ciki ne da ita ba ko?"
Kallanta Magajiya tai cikin halin ko in kula ta girgiza kai cikin takaici sannan tace " da alama tsufa ya fara miki illa."
Lami ta d'ago ta kalli Magajiya tace " Magajiya wlh ba haka bane lalai ki binciki 'yar nan, kina me har ciki ya zauna a jikinta haka? Da alama ma cikin nan ya kai wata hudu in bai fi bama."
Kanta ta juya ba tare da ta bata amsa ba dan ta kula nema take kawai ta kona mata rai.
Lami ta kara matsowa tace " wlh Allah da gaske nake, Magajiya kinsan dai da yanda nake, indai naga mace da ciki ko wata d'aya ne sai na gane."
Tasan da wannan sarai sai dai tayaya zatace ciki bayan yarinyar haryanzu Sarki bai fara........
Tunaninta ne ya tsaya ta tuno sanda ita kanta waccan satin taga yanda tai haske har take tsokanarta akan lalai gidan sarauta ya amsheta ganin yanda take kyau haka.
Zumbur Magajiya ta mike cikin firgici ta shiga kwallama wata baiwarta kira, nan ta karaso da sauri.
Baiwar ta zube a kasa, Magajiya tace " jiku shirya zani b'angaren Basira."
Mamaki me ya kama baiwar dan tasan Magajiya bata zuwa b'angaren kowa hatta bangaren Mahaifiyar Sarki sai ta shafa watanni bata ko leka ba.
Basira kam tana dawowa daga gun Magajiya ta hau amai dan abincin dataci acan sam kawai dai ta tura ne amma bawai dan ranta yaso ba, kwanciya tai akan gado dan wani irin jiri takeji.
Mai kula da ita tana kusa da ita tana tambayarta akan ta kira mata mai magani na gidan?
Kai Basira ta jijiga zatai magana sai jin kirarin isowar Magajiya tayi ana yi a kofar ta.
Da sauri ta mike ta d'an gyara fuskarta sannan ta fito.
Magajiya ta gani a zaune tayi zama irin wanda ta saba, tun da ta taho Magajiya da Lami suka kura mata ido har kafarta ce ta hard'e ta kusa fad'uwa.
Da kyar ta karaso, Magajiya ta kalleta cikin dabara tace " ya akai? Bakyajin dadi ne?"
Kai ta girgiza alamar a'a, baiwar dake kula da ita ta matso ta zube a kasa tace " Magajiya dan Allah a kira mai bada magani ta duba Uwar gijiyata wlh ba lafiya ce ta isheta ba."
Gaban Magajiya ne yai wani wawan fad'uwa amma dayake isashiyace sai ta maze cikin gadara tace " je ki kirata."
Da sauri ta mike tai waje, Magajiya ta kalli Basira tace " na d'auke ki kamar kanwata ashe ke ba haka bane?"
Basira ta d'ago a hankali itakam tana tsoron matar nan, daurewa tai tace " ba wani abun damuwa bane kawai dai naci abinci dayawa ne a gunki."
Magajiya ta kafeta da ido, tsoro da fargaba ya cika mata ciki taf.
Suna zaune anan mai bada magani ta shigo.
Nan Magajiya ta bata umarnin duba Basira, hannunta ta kama ta bud'e tafin hannunta ta zuba musu ido, ta sake ta sannan ta bud'e idanunta na hago, nan ma ta saki ta sake bude na dama.
Tana gamawa ta zube a kasa tare da cewa " ina tayaki farin ciki yake Magajiya, babu wani gabanki ba wani bayanki, kece fitila wacce take haskaka gidan nan......"
Katseta Magajiya tai tace " ya isa ni fadamin meke damunta."
Mai magani tai murmushi tare da kara dukufar da kanta tace " Yarima Abdulmajid ya kusa samun kani ko kanwa ima tayaki murna Magajiya."
Ai ba Magajiya ba kowa na gun sai da ya zaro ido, itakam Basira kasa kawai tai da kanta.
Mamakin daya rufeni, gani nai Magajiya ta mata alama da hannu akan ta matso kusa da ita, nan ta taso ta iso, tana zuwa Magajiya ta jawota ta rungumeta tsam tace " Masha Allah! Lalai kinyi abin kwatance a wannan masarauta ba shakka ked'in ta dabance."
Basira kam addu'a kawai take dan gabanta sai fad'uwa yakeyi.
Magajiya ta saketa ta kalli Mai Magani tace " ki biyoni ki amshi tukwicinki mai tsoka.
Nan ta mike ta fito.
Abinda