Showing 135001 words to 138000 words out of 146065 words

Chapter 46 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

yanata lumshe ido kamar mai bacci sannan ta kalli Basira tace " Basira? Me zakice?"


Umma kam jikinta duk ya fara rawa, Magajiya tace " ina neman izinin shigowar mai bada shaida."


Sarki ba yanda ya iya dole yace " ya bada"


Shigowar mutum ne yasa gaba d'aya jikin Basira ya hau rawa, Bilkisi dake kusa da ita tasa hannu ta rike hannunta tana kallanta, kallan Turab tai wanda gaba daya ta rasa meke damunshi dan kamar baya baya cikin hayyacinsa.


Basira kam duk ta gama rikicewa. Ganin haka yasa hankalin Sarki ya tashi.
Magajiya tai murshi sannan tace " Basira kin gane wannan? Badai zaki mance da wanda ya amshi budircinki ba?"


Cikin tashin hankali kowa yaji maganar, nan fa aka fara kananan gulma, Sarki ya runtse ido saboda tsananin takaici.


Turab wanda ke kokarin maido da hankalinsa ne ya kalli wanda ake magana, cikin layi.


Kallo d'aya zakamai kaga alamar shaye shaye da talauci a jikinsa, tsugunne yake yana dan cicila ido.


Kallan Basira yai wacce gaba d'aya jikinta rawa yakeyi.
Bilkisu ganin ba wanda yai magana yasa ta kalli Turab da sauri, gani tau kamar baya hayyacinsa.


Khadija itama kallan Turab tai dan kowa ya san zaiyi magana, yanda taga yanayi da kansa ne yasata kuramai ido tana san gano meke faruwa.
A zuciyar sarki kuwa addu'a kawai yake akan Turab yai magana.


Bilkisu ce ta kalli Magajiya wacce ta saki wani murmushin mugunta tare da kallan agoggon hannunsa ta gefe, a tsorace Bilkisu ta kara kallan agoggon tabbas bata karasa sanar dashi ba dazu aka kwankwasa kofa.


Matsowa tai gun Basira da sauri ta rada mata abu a kunne.
Basira ta kalleta sannan ta kalli Turab wanda idanunsa ke juyewa.


Mikewa tai ta zo inda Turab yake, tunda wannan mutumin ya hangota ya taso da sauri ya biyota yana neman rikota yana cewa " kece ko? Kamar kece? Kai na tabbatar ma kece."
Da sauri Dogarawa suka rikeshi, nan aka shiga tambayar wanene wannam din? Kowa fuskarsa dauke take da tambaya.


Basira ta daure ta karasa inda Turab yake, kowa yana jira yaga mai zatai, da karfinta ta dage ta wanka mai wani wawan mari wanda yasa kowa kallan Turab.


Bilkisu da sauri ta mike ta isa inda yake, Turab kallanta yai.
Basira tace " bakada hankali ne? Ta ina zaka bari magani ya rinjayi jikinka? Bayan ni ina cikin tashin hankali? Ta ina......."


Kuka ne ya nemi kamata, da sauri Bilkisu tasa hannu ta balle agoggon ta zareshi daga hannunsa, sannan ta kalli Turab wanda ya ke kallan Mahaifiyarsa gaba daya idanunsa sun canza.







🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*86*






Kansa yainta girgizawa saboda gaba d'aya hankalinsa na neman gushewa, Bilkisu idanunta ne suka kada ta taso daga inda suke sannan tazo gaban Mai Martaba ta tsugunna, tare da ajiye agoggon akan tebirin gabansa, tace " Tuba nake Ranka ya dade amma zaka iya gane agoggon nan?"


Magajiya ce tai saurin katseta tace " Bilkisu wani irin banzan tarbiyya ce wannan? Bakiga magana muke akan wannan dake gaban mu ba?" ta fada tare da nuna wannan namijin da aka rike.


Bilkisu ta kalleta sannan ta sunkuyar dakai bayan ta juyo bangaren Sarki tace " Tuba nake ranka ya dade amma dan Allah ka bani amsar tambayar nan."
A kasan ranta kuwa addu'a kawai take akan Allah yasa abin ya sakeshi kafin ta gama maganar nan, dan tana tambayar ne dan neman karin lokaci dan ya wartsake.
Magajiya zata sake magana sarki ya katseta tare da kallan agoggon yace " Agoggon menene?"
Bilkisu tace " dazu aka aiko ma Yarima akan kaine ka bada a kawo mai."
Sarki yace " ni kuma?"
Bilkisu tace " haka ne Takawa, yarinyar ta kawo akan kaine ka bada a kawoma Yarima."


Sarki ya daga agoggon sannan yace " menene dalilin aika agoggon nan da sunana bayan bani na bada ba?"
Bilkisu ta kalli magajiya kadan sannan ta kalli Turab wanda yake ta kokarin bud'e idanunsa da kyar tace " ni kaina shine abinda ban sani ba."
Magajiya tace " to yanzu menene? Abinda ya kawomu shine abinda ya kamata muyi ba wai wani zancen agoggo ba wanda bai damemu ba, da a aikamai da agoggo da kar a aika menene namu?"


Galadima yace " Takawa ni wannan mutumin nake san sanin wanene? Da matsayinsa."
Magajiya ta kalli Bilkisu tace " Gimbiya dawo ki zauna ko?"


Bilkisu ta mike tare da kallan Turab.
Sam hankalin Khadija ya kasa kwanciya ganin halin da yake ciki, idanunta duk sun ciciko da kwalla.


Basira kam gaba d'aya ta rasa ina zata sa kanta, Magajiya ta kalli mutumin tace " kai ka nutsu a gaban Sarki kake, sannan wannan da kake neman yima magana mata ce a gun Sarki ka kiyayi kanka kafin a kamaka."
Mutumin yasa dariya yace " mata?"
Galadima yace " kai! Meye tsakaninka da matar Sarki?"


Kallan Basira yai yace " Basira in sanar dasu?"


Kallansa Basira tai idanuwanta sun cika da tsoro, Abdulmajid ne ya kalli Turab ganin har yanzu ba a hayyacinsa yake ba kawai ya fara tari kamar irin ya kware din nan sosai.


Da sauri Magajiya tace a kawo ruwa.
Nan aka kawomai ruwa, da yake hannunsa ba kwari sai yai kamar irin rikewa ya kasa kawai ya juye ruwan a kan Abu Turab.


A firgice Turab ya mike tare da rike kansa.
Magajiya tace " meye hakan kuma?"
Turab ya kalleta sannan ya kalli mutumin nan, sai a yanzu maganar take kara dawo mai daya bayan d'ayan.


Lokacin shi kuma mutumin yana kara cewa " Basira in fada?"
Turab ne ya taho da sauri basu ankara ba ya kai mai naushi.


Karfinsa ya sake sosai dan har saida gefen leb'ansa ya fashe.
Dif d'akin yai da wuta saboda mamaki.
Turab ya kalleshi sannan cikin murya mai sauti yace "Ka fad'i me?"


A lokaci d'aya mutane biyar sukace Alhamdulila Turab is back (nasan kun sansu....Lol)
Magajiya kam takaici ya kamata, Turab ya kallesu sannan ya kalli mai shari'a yace " a shaida da tambaya, mutane nawa ne ba'a yarda da amsarsu?"


Kallansa yai yace " da mahaukaci da......"
Turab ya katseshi yace " wannan hankali gareshi?"
Kowa ya kalli mutumin.
Turab ya kalli Sarki yace " Takawa kayan jikinsa kawai nakeso a kalla, wannan mutumin hankali gareshi?"


Sarki ya kalleshi sannan yace "da alama babu."
Turab ya kalleshi yace " bawan Allah ya sunan ka?"
Mutumin ya kalleshi yace " wani rai...."
Turab yace " bakasan sunan ka ba ko?"
Yace " na sani mana."
Turab yace " meye sunanka to?" yace "wannan wani irin tambayar rainin hankali ne?"


Turab yao murmushi yace " me kuka gani anan? Zakuce wannan nada hankali? Mutumin da ko sunansa bai sani ba?"




A zuciye mutumun ya kwace tare da yowa kan Turab.
Nan aka kamashi da sauri, Turab yace " Galadima mai zakuce game da wannan mutumin?"
Galadima da Barde suka kalleshi, wanda shikuma takaicin abinda Turab yamai yasa abin ya motsa ya shiga yin gurnanin ihu na manyan 'yan shaye shaye akan lalai sai ya kashe Turab.


Ba shiri akai waje dashi.
Turab ya kalli Magajiya yace " Umma me zakice ke kuma akan kawomana mahaukaci gun shari'a?"
Magajiya ta kalleshi sannan tace " ban gane ba....."
Yai dariya yace " baki gane me ba? Kinaso kicemin mahaukacin nan shi ya kawo kansa......"
Cikin tsawa tace " kai Turab! Kasan da wa kake magana, ko ka manta wacece ni, ko wacce ta haifeka bata isa ta dinga min magana haka ba."


Sarki ne ya kalleshi yace " Turab a daidaita kalamai, kar ka manta mahaifiyarka ce."


Turab ya kalleta sannan ya koma ya zauna tare da sunkuyar da kai yace " tuba nake ranka ya dade, zuciyatace take tafasa."


Magajiya ta bishi da kallon takaici.
Sarki yace " munajiran mai shaida na gaba dan jin asalin meke faruwa."
Turab yai gyaran murya sannan ya zubawa Magajiya ido yace " bansan me yasa ake tunanin nine na sa akama Abdulmajid ba, sai dai ni da bakina bazan taba cewa ba ni bane, sai dai kafin a kawo wata shaida da zata nuna nine nai wannan laifin inaso in gabatar da wani laifi wanda yake bukatar bincike, ina fatan za'a bani dama."


Mai shari'a ya kalli Sarki yace " mai kake gani?"


Sarki ya kalleshi yace " menene?"
Magajiya ta kalli Turab cikin takaici da san jin me yake shirin yi."


Turab ya d'ago yace " godiya nake, magana ce game da Hajiya."
Da sauri Magajiya ta kalleshi.
Yai murmushi sannan ya cigaba " Bayan mun kai Hajiya asibiti likita yayi bincike gun warkar da ita, a lokacin ne ya gano cewar guba ce aka bata wacce ta nakasar mata da duk gab'obin jiki."


Inalilahi wa ina ilaihi raji'un, abinda yake fitowa daga bakin jama'ar gun kenan, Abdulmajid da sauri ya kalli Magajiya.


Turab ya mika ma dogarin dake tsaye akan Sarki takardar yace " ga abinda likitan ya rubuta."
Duk da sarki yayi mamakin jin wannan zancen wai likita? Bayan har Hajiya ta warke Turab baisan inda take ba, sai dai bai bari mamakin ya bayana ba a fuskarsa.
Amsar takardar yai ya gani sannan ya mika aka bi kowa aka nuna mai.
Sarki nuna bacin ransa yai kamar irin baisan komai din nan ba, yace " Guba kenan aka shayar da Hajiya?"


Turab yace " sosai, sannan inada shaidar da zata sanar damu hakan."
Nan yace shigo.


Yarinyar dake waje aka ce waye xai shigo?
Nan tace nice, tare da shiga.


A tsorace ta shiga, tana shiga ta zube a kasa tare da gaisuwa.
Sarki yace " kece shaida akan abinda ke faruwa?"


A rikice tace " Tuba nake ranka ya dade na cancanci hukunci mai tsanani."
Galadima yace " tashin hankali."


Turab yace " sanar damu abinda ke faruwa."


Yarinyar ta d'ago tana kallan Turab a tsorace.
Turab yace " sanar damu abinda kika sani."


Magajiya ta kalleta duk ta rasa me zatace.
Hisham kam idanunsa kawai ya runtse dan yasan yau kam sai dai Allah.


Yarinyar ta kwashe komai ta sanar dasu.
Mai Shari'a yace " yarinyar data baki maganin tana nan?"
Kai ta girgiza alamar a'a, dan mai baiwa ce."
Sarki yace " wannan alama ce ta kenan wanda ya bada umarnin mutum ne mai mukami."
Turab yace " a wani bangaren take aiki?"


Magajiya ta kalla sannan ta sunkuyar da kai.


Magajiya tace " kanaso kace guba aka ba Hajiya? Wani mara imanin ne zai in aikata hakan?"
Turab yace " ina muka sani, ko mara imanin na cikin d'akin nan?"
Bai bi takan me zatace ba ya kalli Yarinyar yace " a wani bangare take aiki yarinyar?"


Yarinyar ta nuna da yatsa, yatsar kowa yabi sukaga ta tsaya akan Magajiya.


Magajiya tai murmushi tace " ba dai ni kike nunawa ba ko?"


Kallan Magajiya kowa yai.


Yarinyar ta sunkuya sannan tace "a bangareki take aiki sannan tace inhar ban sa maganin ba......."

A zuciye ta mike tace " ke dan gudanku sharri zakimin?"


Sarkin yace " Magajiya me kikeyi hakan?"
Tace " ban gane me nakeyi ba, bayan ina zaune ana neman ace nine nake neman halaka Hajiya, meye dalilin da xai sani halaka mahaifiyarka?"


Turab yace " shine yanzu zan sanar."
Tace " mene?"
Turab ya kalleta sannan ya kalli ragowar matan sarki yace " ko zaku iya tuna shayin da Magajiya ke baku a shekarun baya?"
Kallan juna sukai dukansu harda Basira, sannan sukace eh.
Turab ya kalli Magajiya sannan yace " Magajiya tana saka magani a ciki wanda zai hanaku d'aukar ciki a wannan shayin, bansan dalili ba wanda yasa daga baya ta canza tunani ta koma shayar da Sarki wannan shayin."


Mikewa tai sannan tai wani murmushi tace " mene?"
Turab ya kalleta sannan ya kalli Hisham yace " Waziri me zakace game da sharhi na?"
Hisham ya kalli Magajiya sannan ya tuna ziyartarsa da Turab yai jiya, ya sanar dashi abinda ke faruwa da Hajiya da abinda ta sani har Magajiya ta mata hakan, Hisham yace tabbas shine ya amso maganin dan akan matan sarki aka fara.


Magajiya ta kalli Hisham tace " Yaya me kenan?kana nufin kaine ka sanar dashi wannam kagagen labarin?"


Hisham ya kalleta yace "Magajiya sai yaushe ne zaki daina san kanki?"


Kallan sarki tai tace " bansan wannan labarin ba, sai dai in shi Hisham din shine ya aikata hakan."


Gaba d'aya d'akin kowa kallanta yakeyi.
Khadija kuwa gaba d'aya jitai kanta na wani juyawa, Abdulmajid kam idanunsa kawai ya rufe, ita kanta mahaifiyar Khadija ta girgixa da jin wannan muguntar.


Bilkisu kam kallan Magajiya tai cikin tsananin mamakin wannan muguwar zuciyar tata.


Sarki ya daka mata tsawa yace " ashe bakida imani?"
Kallansa tai itama tace " dama abinda kake fata kenan ya faru, ko kana tunanin bansan so kake kaga bayana ba?"
Sarki yace " mene?"
Tace " da kai da danka kun hada kai kuna neman mun sharri, shine yanzu zakace wai banida imani?"


Hisham yace " Magajiya!"
Kallansa tai tace " yimun shiru tsohon munafuki, ni zakaci amana?"
Khadija tace inada magana.
Kallo ne ya dawo kanta, Turab ya zuba mata idanu.
Khadija tace "tuba nake ranka ya dade amma Umma Magajiya da Abba sun aikata laifin dayafi wannan."


Magajiya ta kalleta sannan tai dariya tace " khadija ke kam wa kike tunanin zai yarda da maganar ki? Bayan kowa yasan yanda kike bala'in san Abu Turab? Banaji akwai abinda zai saki da bazaki aikata ba."
Da sauri Bilkisu ta kalli Khadija sannan ta kalli Turab wanda hakan yayi daidai da kallanta dayai.


Murmushi ya sakar mata sannan ya d'auke idanunsa da sauri ya kalli Magajiya yace " Umma bakya tsoron incigaba da magana? Ko zaki fad'i sauran laifin da kanki?"


Tace " laifi?ni ba laifin dana aikata."


Turab yai murmushi yace " idan har zan sanar da laifufukan da kika aikata banaji wannan rana xata ishemu."


Magajiya tace " good kun kyauta, sai kuce yau ba ranar bincike bace akan abinda akama d'ana, ranar yimun sharri ne."


Turab ya kalli Sarki yanasan tona d'ayan sirrin sai dai inya kalli Abdulmajid ya kuma kalli Sarki sai ya kasa.


Kansa ya sunkuyar yana tunanin abinyi.


Muryar Andulmajid ce ya katseshi dayace " Umma ya isa haka nan, sao yaushe ne zakiyi nadamar abinda kika aikata?"
Tace " mene?"
Cikin murya mai sauti yace " Umma please ki tsaya haka nan, a da ina tunanin san da kike mun ne yasa kike aikata abinda kike aikatawa sai dai yanzu jin abinda kikema matan sarki da kuma shi kansa yasa nasan san kaine kawai naki, sai yaushene zuciyarki zata gamsu da abinda take so? Sai na zama sarki? Ko sai kin ganki akan gangarar mutuwa?"


Tace " Abdulmajid."
Abdulmajid yace " kin rabani da Mahaifana, tunda nake ban taba kiran matar data reni cikina da sunan uwa ba, ban taba kyautata mata ba a matsayin wacce ta d'au cikina na wata tara ba......."


Da karfi tace " YA ISA HAKA!"


Turab ya runtse ido tare da cewa thanks Abdulmajid.


Inalilahi wa ina ilaihi raji'un.......
Ba shakka wannan kalaman sunfi tadawa kowa hankali, Hisham kam hawaye ne ya zubo masa, Turab Sarki ya kalla wanda gaba d'aya zuciyarsa tayi wani nauyi, kallan Abdulmajid kawai yake yana nanata kalamansa.
Bilkisu ce ta daure ta kalli Abdulmajid cikin mamaki tace " kana nufin ba Umma Magajiya bace Mahaifiyarka? Ba kuma Sarki ne ya haifeka ba?"


Gaba d'aya zubama Abdulmajid ido akai cikin mamaki.
Khadija kam hawaye ne ke zubo mata, itakam Umman Khadija jitai hawayen ma sun kafe kaf sun kasa ma zubowa........






*TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*


*Wattpad :-AyusherMohd*




Gaisuwa da fatan alkairi gareku masoyan littafin nan gabaki d'aya, ina godiya kwarai da kaunar da kuke ma littafin nan, nagode da hakuri dani na rashin posting akai akai da kuke, ni kaina ba hakan naso ba.
Always love u.......




*86*


Wani irin ihu Magajiya ta saka da karfi tace " ABDULMAJID....."


Mikewa tai a zuciye ta isa inda yake, ta d'aga hannu zata zabgamai mari, da sauri Turab ya tsaya a gabanta.


Kallansa tai idanunta duk sun kada sunyi jaa, kallan juna suka shigayi, tana mai wani irin kallo wanda ba komai a ciki sai tsantsar kiyayya.
Mai Martaba idanunsa a rufe kawai suke saboda jin abin yake kawai yana mai yawo akai.
D'akin yayi tsit kowa da abinda yake sakawa a ransa, wani dogari ne ya shigo da gudu ya tsugunna, Barde ya kalleshi yace " lafiya kai kuma?"


Cikin in in na yace " mai kula da kofar gidan mai martaba ne na cikin gari."
Galadima yace " to ya akai?"
Bakinsa ya shiga motsawa ya kasa magana, Basira tace " ya akai Hadi?"


Da sauri ya ya maida kansa kasa ya sa kuka, Turab ya kalleshi ganin yanda yake kuka yasa Turab ya matsa daga gun magajiya ya taho inda yake yace " Hajiya......"
Wani kuka dogarin ya saka, da sauri Sarki ya bud'e idanunsa wanda gaba d'aya sun yi jaa, mikewa yai yana kokarin takawa baya yai da sauri dogarawan dake bayansa suka tareshi, kallansu yai sannan ya kwace jikinsa ya koma ya zauna saboda jirin da yakeji, Dogarin yace " Allah yama Hajiya cikawa yanzun nan......"


Inalilahi wa ina ilaihi raji'un......Abinda kowa dake d'akin ya shiga fada kenan, Banda Magajiya wacce take tsaye, sai Sarki wanda gaba d'aya yaji kansa ya kulle ya kasa tunanin komai.
Turab ya karasa inda yake da sauri yace " Abba!"
Idanunsa ya sauke akan Turab cikin tsananin tausayawa, ba shakka lalai bai cancanci mulkin nan ba, lalai laifinsa ne na kyale Magajiya tun farko ta dinga yin abinda taga dama.
A hankali ya fara karanto

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login