Showing 126001 words to 129000 words out of 146065 words
Chapter 43 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
Hisham ya kallu Turab sannan ya kalli Alkali dasu Galadima da Barde wansa suka saki baki dab tsananin mamaki.
Hisham ya gama sadaukarwa yau kam tashi ta kare.
Idanu ya runtse yace " nine na aikata, ni ne nasa a kamaka, tsautsayi ya fada kan Abdulmajid."
Dolene ya fadi haka ba wai dan Magajiya ta sashi ba sai dan yasan yau kam tashi ta kare, ko ma menene dolene ya kare rayuwar Abdulmajid.
Inalilahi wa ina ilaihi raji'un.....
Abinda kowa ya shiga fada kenan a fadar.
Turab yace " kana so kacemin kai kadai ne ka shirya wannan abin?"
Hisham yace " ni kadai ne, da dani dawa nake yanke shawara ta?"
Turab yace " ni na kasa fahimtar menene ribarka a ciki in Abdulmajid ya hau mulki, dan yana d'an kanwarka? Ko kuwa da wani abun?"
Gaban Hisham ne ya fadi ya kalli Turab, tsananin tsoro ne karara a idanunsa.
Sarki a kufule yace " kai da wa kuka aikata? Magajiya?"
Kasa yau da kansa da sauri yace " ko d'aya bata ma san da wannan zancen ba, ni kadai na aikata bawai kuma saboda mulki na aikata ba sai dan ina bakincikin yanda Khadija ke san yarima Turab shi kuma yana murnar auransa."
Turab ya kalleshi a ransa yace taban ka biyo? wato so kake har karshw kar ka nuna dana sani ko? Zuciyarka ta gama kekashewa wanda ko kayi dana sanin bazaka taba sanarwa mutane da ka yi ba? Kunyar duniya ce bakasan kaji?
Ran Sarki ya baci yace " Alkali inaso a kewa Hisham daga wannan lokacin sannan ayi bincike sosai akan kaf laifufukan daya aikata inaso a sanar dani nan zuwa kwana uku."
***********
Magajiya kam ta rasa ina zata sa ranta, a zaune dai take kusa da Abdulmajid amma sam hankalinta baya gun, tashi hankalinta bai wuce sanda ta tuna abinda Abu Turab ya mata ba bayan sun rabu da Hisham.
Tana kokarin shiga d'akin taji muryarsa a bayanta yace " kin gama tsaramai?"
Juyowa tai ta kalleshi batace komai ba, sai wani kallo da take mai wanda ni kaina bansan manufarta ba.
Turab yace "shawara nazo baki, kiyi gaggawar zuwa ki sanar da laifufukan da kika aikata, dan wannan karan bazan taba bari kici galaba akaina ba."
Murmushi tamai tace "bari? Kana nufin kai kake bari nake yin nasara akan al'amurana? Sai dai ya zakayi Turab? Har karshen rayuwarka baka isa kai nasara akai na ba, ka sa wannan a ranka."
Ta shige d'akin, idanunta ta runtse sannan ta mike da sauri, bataga ta zama ba.
Kallan Abdulmajid tai wanda shi kansa a kwance kawai yake tace " zan je gida."
Bata jira amsarsa ba tai gaba.
Da kallo ya bita.
Baga dade da fita ba yaji an turo kofar, idanunsa ya maida ya rufe dan ya d'auka itace, sam baiji sallamara datai ba.
Kusa da gadon taje a hankali tace " Malam kaci abinci?"
Idanunsa ya bud'e da sauri sannan ya kalleta, ji yai wani sanyin dadi ya ratsashi sai dai yana tunanin ko ita taji sirrinsa kila kallonsa ma bazata sake ba.
Had'e rai tai tare da cewa " karma kai tunanin damuwa nai dakai nazo dubaka, asibitin nazo shine na karaso inga Khadija."
Murmushi ya sakar mata yace " ko ma menene dalili naji dadin ganinki."
Baki tad'an tabe tace " ya jikin Khadija?"
Yace " ta koma gida."
Tace " yayi, kai fa? Ka daina pretending d'in baka farfado ba?"
Murmushi yai yace " me? Kin damu ne akan rashin cin abincin da nake? Kullum ina kwance?"
Kai ta kawar da sauri tace " inji wa kenan? Tab!"
Dariya ya d'anyi ganin yanda tai saurin bashi amsa...........
**************
A can bangaren Turab kuwa, Gimbiya na zaune a kan gado ita kadai a cikin d'aki, ba shakka ya dade bai dawo ba, dan ita ma bata dade da dawowa daga bangaren Umma ba.
Jitai an kwankwasa kofar tare da yin sallama.
Amsawa tai sannan ta mike jin muryar Turab.
Kallan kofar tai a hankali taga ya shigo.
Tana ganin yanayinsa tai saurin karasowa inda yake tace " lafiya?"
Jitai ya jawota jikinsa ya rungume ta tsam.
Mamaki ne ya kamata, sai dai bata nuna ba, a hankali takai hannunta bayansa.
Ajiyar zuciya yai a hankali......
*TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼*
*81*
Ya dade a jikinta kafin ya d'ago ya kalleta yace " i'm sry."
Abinda ya fada kenan yai fara takawa zaiyi waje.
Takunsa biyu yaji ta riko rigarsa, tsayawa yai ba tare da ya juya ba, a hankali ta tako zuwa inda yake itama ta sake rigarsa sannan ta kwantar da kanta a bayansa.
Yayi mamakin jin ta a bayansa dan shi har yanzu gani yake auren had'i ne tsakaninsu shi kuma bazai taba shiga hakkinta ba.
Cikin wata murya mai sanyin gaske tace " Thanks alot for showing me ur weaknesses."
Jiyai wani abu ya tsirgamai, murmushi tai mai sanyi sannan tace " ban san me ke zuciyarka ba game dani, sai dai at least nasan abu d'aya wanda inaji shikadai ya isheni zama dakai cikin farin ciki."
" menene shi?"
Kanta ta d'aga daga bayansa tana murmushi tace " nasan u are comfortable in kana tare dani."
Murmushi yai sannan ya juyo ya kalleta yace "Hmm abinda kika ce......"
Kallansa tai cikin mamakin dan yanda yai maganar alama ce ta zai musa abinda take tunani, da sauri ta juya bayanta tace " ba sai ka fad..
.."
Kansa ya sako ta bayanta saitin kunnenta yace " abinda kikace hakan yake."
Sam ta manta da kanta na gefen kunnenta ta juyo da sauri jin amsarsa.
Numfashinsu ne ya sarke dan fuskarsu tayi daf da juna, a hankali ya saukar da idanuwansa ya kalli bakinta wanda yake dan karami mai kyau, gashi tasa jan baki jaa amma bai turo ba.
Wani abu ne yaji yana tsirgamai, dif sukai kamar an d'auke wutar nefa sai shi da yake dan kokarin kara karkatar da kansa wanda ita kuma tai kasa da idanunta saboda kunya.
(mai kake shirin yi Turab? Me zuciyarka take neman saka? Ina alkawarin?)
Jisukai an kwankwasa kofa, juyasa yai da sauri ya nufi kofar ya bud'e.
D'aya daga cikin masu kula da Gimbiya ne, ta gaisheshi sannan tace "Yarima an turo Mai Martaba na banana. "
To kawai, yace yai waje.
Yana fita ya furzar da wata iska sannan ya d'anyi fifita da hannunsa yace " why am i feeling hot?"
Itama yana fita ta fada kan gado ta kwanta tare da saukar da ajiyar zuciya itama.
Bangaren Mai Martaba ya nufa, a waje yana jiran kafin a sanar ma Mai Martaba zuwansa ya kalli wani yace " Jakadiya fa?" yace " ai yau da safe tace wai yarta ba lafiya, shine aka dawo da wannan nan, ita kuma ta tafi." ya karasa maganar yana nuna mai wata.
Murmushi yai dan ya tabbatar guduwa tai, nan ya shiga bangaren Sarki.
Yana zaune ga abincin nan a gabansa da alama yanzun nan ya gama ci.
Sai da ya kara gaisheshi sannan ya zauna tare da lankwashe kafafunsa yace " gani."
Sarki ya kalleshi yace " me kake tunani game da Waziri?"
Turab yace " ban fahimceka ba..."
" na rasa me yasa nake ganin kamar akwai abubuwa da dama da kake b'oyemin."
Turab yace " me yasa kake tunanin haka? Ni kam ba abinda nake b'oyema."
Takawa ya kalleshi sannan yace " Turab? Kana tunanin zaka iya kama Magajiya da kanka?"
Turab ya d'ago ya kalli Sarki sannan yace " Abba me yasa ka ke kokonto a kaina?"
Sarki ya girgiza kai yace " Abu Turab!"
Kallansa Turab yai jiki a sanyaye, yace " Hajiya ta farfado, sannan naji abinda ya ke faruwa."
Idanunsa ne suka canza yana kallan Mahaifinsa saboda tausayawa.
Sarki yai murmushi yace " alokacin da naji abinda ya faru lokacin ne na tabbatar da Magajiya tafi karfina sannan babu ko dan d'igon imani a zuciyarta, a da nayi tunanin rashin nuna mata kulawa ne yasa ta rikid'e ta koma haka, sai dai abinda naji sam ya hanani bacci, hankalina ya tashi. Ban taba tunanin a duniya akwai wanda rashin imani zai sa ya aikata hakan ba, sannan bayan abinda ta aikatamin har ta nemi halakamin mahaifiya, a wannan rana nayu dana sani sosai na zamantowata Sarki dan da ace ni ba Sarki bane banaji duk wad'an nan abubuwan zasu faru dani."
Turab yace " Kaddarar ka kenan Abba, sai dai fatan Allah yasa kaci jarabawar da ya maka."
Sarki ya kalleshi yace " wato ita daga d'anta bata san in sake haihuwa kenan?"
A ran Turab yace " Abba shima ba naka bane."
Sarki ne ya cigaba, Turab kai Kainuwa ne dashen Allah, shi yasa duk wani makirci da kiyayya bata hanaka takawa duniya ba, bata kuma haka bud'e ido ba a duniya, wannan itama Baiwa ce da Allah ya bani wanda nake gode masa."
Turab ya d'ago ya kalli Mahaifinsa yanajin wani tsananin tausayinsa na ratsashi, cikin takaici yace "Abba wai kana sarki ke zai hana ka hukuntata daidai da laifukanta, barinta fa da akeyi shi yasa ma take abubuwan dataga dama."
Sarki ya dade kafin ya murmusa yace " Turab kenan, bakasan me nene nauyin dake d'aure akan kujerar nan ba, sannan abu ko ya shafeni dole sai na fitar da shaida sannan nai hukunci cikin jama'ar fada, sai dai matsalar itace Magajiya bata barin abinda zaisa a gane tayi abu, sannan duk wani wanda yake da hannu akan abun to fa sai ta san yanda tai ta kawar dashi."
"Hajiya fa?"
Sarki yace " wa zai yadda da shaidar tsohuwa? Sannan suruka?"
Turab yace " haka ne na tabbatar zata iya juya laifin kanta."
Sun dade suna tattaunawa kafin su rabu.
Turab na fitowa ya bi d'akin mahaifin nasa da kallon tausayi, tabbas dolene ya hanzarta sanin abinda ya kamata yai da Magajiya.
Magajiya kam tana dawowa taji labarin killace Hisham da akai, wannan abu ya tabata sosai ya kuma kara tada mata hankali domin ta tabbata Turab sai tayi da gaske akansa, wannan shine karo ma farko da aka kada ita da dan uwanta akoda yaushe sukecin riba bawai su a ci riba akansu ba.
Bayan La'asar ta aika a kira mata Basira.
Basira kam ta gama had'a kayanta kenan da Turab yace ta koma can ko sati d'aya zuwa biyu ne tayi, sannan Sarki yace za'a maida Hajiyarsa can gidan.
Jin wannan sakon yasa tai shiru kafin ta fito, dan a ka'idar mulki Magajiya ce Sarauniya wacce duk matan sarki ke karkashinta dolene ta amsa kiran data mata.
Magajiya na zaune kan kilisarta kai kace ba wani abu dake damunta sai dai zuciyarta fal take da tsoro da shakkar abinda ke faruwa.
Basira ta gaisheta sannan ta zauna.
Magajiya ta kalleta cikin izzarta tace " Basira kin san ko ni wacece ko?"
Basira ta kalleta cikin mamaki da rashin fahimtar abinda take nufi, Magajiya ta murmusa sannan tace " ba wai wani abun nace ba, tuna miki dai kawai nakeyi, ni d'in macece wacce banida yafiya akan duk wanda ya nemi tozartani, inaso kisa hakan a ranki sannan ki sanarma na kusa dake abinda na fada, daga ke har abinda kika haifa banaji kunyi kaurin wuyan da zai sani na tsugunna muku, tunani yakeyi shine yake cin galaba akaina shiyasa na kiraki ke wacce kika haifeshi in sanar dake hakan."
Basira ta kalleta sannan tace " Magajiya ni na kasa fahimtarki, Turab ne ya tozartaki kike sanar dani in gargad'eshi ko me?"
Ran Magajiya ya b'aci sai ta saki dariya tace " me? Tozartawa?au har an hallici d'an dazai tozartani a duniyar nan?"
Basira ta murmusa sannan tace "nima abinda na gani kenan, shi yasa nake mamaki danaga kin kirani kika neman sanarmin in jaa ma Turab kunne, bayan yaran nan naki ne."
Magajiya ta kalleta a ranta tace " wato kema kin rika ko?"
Basira tace " zan koma in ba wani abun."
Bakin ciki baisa Magajiya ta kara tanka mata ba.
Tana fita Magajiya tasa kafa ta ture tiren inibin dake gabanta cikin b'acin rai, sannan tai wani dan karamin kara ma takaici, me yasa yanzu sam bata iya shanye bakin ciki? Mikewa tai cikin takaici tace " ke aika a kiramin Waziri."
Baiwar ta sunkuyo tace "Ranki ya dade kin manta an........."
Matsowa tai ta kifama yarinyar mari sannan tai ciki ranta na soyuwa.
Tafiya ta kamayi a d'akin cikin b'acin rai, yanzu ba Hisham wanda sai dai tana daga zaune tasashi aiwatar mata da duk abinda take so, sannan ba Abdulmajid wanda take tunkaho dashi Yana can a kwance.
Kanta ta dafe sannan ta d'ago idanunta cikin tsananin bacin rai, tace "Abu Turab!!! Ka jirani, zan shayar dakai abinda har karshen rayuwarka bazaka manta dani ba, wannan shine zai zama fad'anmu na karshe dakai, in har nai kuskuren halaka rayuwarka to tabbas nasan tawa rayuwar zatai rawa."
Kurama kasa ido tai cikin tsananin takaici, rabon datasamu bacci mai dadi ta manta, kullum sai tai mafarkin Turab na neman illatata, tabbas dolene suyi fito na fito yakin karshe a tsakaninsu.....
(😂😂😂😂nace Allah yaba mai rabo sa'a)
Khadija kam ta gaji da jiran Mahaifinta tana zaune a waje akwatinta na gefenta, ganin yamma tayi yasa ta mike ta fito waje.
Tsayawa tai ta kira mai kula da kofar su, ta tambayeshi " ina Abba wai yaje?"
Yace "wlh ban sani ba na dai san ya fita."
Juyawa tai ta koma ciki kawai, Umma na kwance a d'aki tunda sukai maganar nan da Khadija ta shiga d'aki bata fito ba, tanaji kannan Khadija da yayyinta na shigowa su fita amma ta kasa tashi, saboda tsananin dana sani dake damunta.
Wannan kenan..........
*KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*82*
Bayan tayi sallar magrib ta yafa mayafinta katon gaske, lulubi tai sosai da sosai, wanda inba kaga fuskarta ba bazaka taba cewa Magajiya bace, ta fito, tara bayinta tai ta sanar dasu zata fita sai dai batasan kowa yasan ta fita sannan ko anzo nemanta a tabbatar ance tana bacci.
Ita kadai ta fito ta nufi inda aka killace Hisham.
Tana zuwa ta sauke mayafinta sannan ta kalli masu tsaron gun tace "yana ciki?"
Kallanta sukai bayan sun gaisheta sukace " Ranki ya dade Sarki ya umarcemu akan kar kowa......."
Wani kallo data buga musu shine ya hana su karasa maganar, tace " nice kowa?"
Da sauri sukace " ba haka bane......"
"ya isheni, bud'e."
Jikinsa na rawa ya bud'e kofar ta shiga."
Hisham na zaune ya had'a kai da gwiwa saboda abin duniya da duk ya taru yamai yawa, ba shakka yana cikin tsaka mai wuya.
Ta window ta tsaya tace "Yaya!"
D'agowa yai ya kalleta, ba shakka wannan itace wacce ta ruguzamai rayuwa, dan itace ta kawo shawarar d'aura d'ansa akan mulki wanda hakan ne yasa ya bata d'an ba tare da yin wani dogon nazari ba, sannan wannan shine dalilin daya sa sam idanunsa suka gama rufewa yakejin koma meye zai iya zuciyarsa ta zarme indai akan hawan d'ansa mulki ne to tabbas zai iya koma menene.
Kallansa tai cikin zafi tace " magana nake."
Mikewa yai ya iso inda take, kallanta yai yace "ya akai?"
Tace " baka tambayeni jikin d'anka ba?sai kacemin ya akai?"
Kallanta yai yace " d'ana? Bayan kece kika hana wannan maganar?"
Tace " yaya ai duk hanawar danai jini ai jini ne, sannan karka damu da gida, zan kula dasu kamar yanda zan kula da kaina, kai dai ka kara hakuri."
Kallanta ya sake yi yace " me ya kawoki? Dan na tabbata bazaki taso nan ba bayan kinsan abinda ke faruwa kizo nan ba tare da kwakwaran dalili ba."
Tace " Yaya ka san kome nakeyi a yanzu saboda Abdulmajid nakeyi ko?"
Kallanta yai dan yama kasa magana, tace "yaya karka damu da duk abinda ke faruwa, koda wani abun ya sameka ni ina nan, sannan in har ina duniya tofa kamar kai kana cikinta ne, d'an mu da 'yayanka ni na d'au alkawarin rikesu amana......."
Katseta yai da cewa " me kikazo fad'amin."
Juyowa tai ta kalli waje, can ta hangoni rakube jikin window rike da takardata da birona, kallo d'aya ta sakarmin na fita a guje kamar wacce aka biyo da wuka, dan tabbas na tsorata, wannan dalilin yasa sam Bansan me tace masa ba.
Sai dai tana gama maganarta na kalli Hisham, kallan da Hisham yake mata kadai zaka kalla ka tabbatar da lalai shi kansa yasha mamakin kalamanta.
Kallansa tai tace " Yaya bansaka dogon tunani ko dogon nazari ba dan abinda na sanar maka shi za'a aikata indai kana san kanka da lafiya, ni kabarni da waccen yaran, kai dai kayi abinda ya dace."
Yama kasa magana sai kallanta da yakeyi, tace "ni na wuce, ina kuma jiran ganin abinda nace."
Ta juya ba tare da taji asarsa ba.
Tsananin mamaki kawai yake, sai binta da kallo kawai da yai.
Tana fitowa ta ciro abu a jikinta ta mikama masu kula da kofar tace "waye ya ziyarci Waziri?"
Da sauri sukace " ba kowa ranka ya dade."
Juyawatai tai gaba abinta.
Tana shiga bangarenta cikin d'aki ta yaye mayafin ta shiga zirya a d'aki, Hisham zaibi abinda tace? A fili tace dole ne ai.
Ya zatai in bai bi ba?? Kai take girgizawa da sauri in zuciyarta ta nemi kawo mata wannan tunanin, sai tace innaaaa....."
*******
Basira kuwa da yama ta wuce gidan dan Turab dashi da Garzali ne sukazi suka rakata, hmm Umma anga Lantana.
Nan suka shiga hirar yaushe gamo bayan ta dan zauna gun hajiya ta dubata da jiki.
Turab ya zauna gun Hajiya wanda jikin nata dai to, sai a hankali duba da yanayin tsufan datai, sannan dama in girma ya kama dama ciwo kad'an ke zaunawa a jikin mutum, ita kadaice wacce take da wannan shekaru a cikin masu mukami dake gidan, dayake duk kishiyoyinta basa gidan sai ita wasu matan nasa sun mutu wasu kuwa sun bar gidan.
Turab ya kalleta duk ta rame ta kara motsewa, tace " Ina cikin farincikin ganinka, a koda yaushe tambayata d'ayace kana ina? Kana lafiya? Dan gaba d'aya hankalina yana kanka