Showing 102001 words to 105000 words out of 146065 words
Chapter 35 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
tace " a'a."
Kallanta yai zai yi magana aka dallesu da fitilar mota.
A tare suka kalli motar, Turab ya sa hannu ya rufe idanunsa dan sam bayasan a haskashi irin haka saboda idanunsa.
Mairo ta juya kai tare da jan tsaki.
Turab ta kalla ganin yanda ya rufe idanunsa yasa ta taho dan nufo mai motar.
Har ta iso sannan ya kashe, tare da fitowa daga motar.
Kallansa tai tace " Abdulmajid me ke nan?"
Kallanta yai fuskarsa a d'aure yace "me kike a can?"
Tace " ko ma me nakeyi banaji ya shafeka amma wannan dallenin da kai da fitila fa?"
Kallan inda Turab yake yai bai amsa mata ba taga ya nufi inda Turab yake.
Abdulmajid na zuwa ya d'aga hannu zai naushi Turab, Abu Turab ya sa hannu ya tareshi.
Kallo kallo sukai kafin turab ya sakar mai hannu sannan yace " ka kiyayi kanka da san duka, sannan ka kiyayi kanka da saurin hawa Da kuma kishi "
Abdulmajid yace " Kai waye da zaka bani shawara?"
Turab ya kalleshi ba shakka yana tausayamai alokacin da yasan sirrinsa shiyasa baya neman fada dashi a wannan lokacin.
Mairo ce ta karaso ta kalli Abdulmajid, zatai magana Turab yace " Bari na wuce."
Ya karasa maganar tare da wucewa ta gaban Abdulmajid.
Biyoshi tai tace"Yaya kama Umma godiya."
Juyowa yai ya kalleta sannan ya kalli Abdulmajid dake tsaye yace " Mairo."
Kallansa tai bata amsa ba, yace " karki dinga zafaffama Abdulmajid."
Tace " Yaya na fadamai ba so nake ba, na rasa dalilin takurar."
Shiru yai tare da cigaba da kallan Abdulmajid yace " ba yanda za'ai?"
Kallan mamaki tamai tace " yanda za'ai me?"
Kai ya girgiza da sauri yace "ba komai."
Ya karasa mota ya shiga.
Shiru tai tana kallansa har sukai gaba, ba yanda za'ai? Me yake nufi?"
Karasawa tai inda Abdulmajid yake.
Kallanta yai yace " Mairo mai ya kawoshi?"
Ledarta ta nuna mai tace " abu ya kawomin, ko da wani abun?"
Abdulmajid yai murmushi yace " Mairo lalen ki yayi kyau sai kika fito kamar amarya."
Harararsa tai tace " kamar Ango ne ba amarya ba."
Dariya yai yace " in kika zama kamar ni Angon ki ai ba wani abin bane."
Baki ta d'an murguda tace " Ka manta."
*********
Turab kam kansa ya kama a cikin mota wanda yaji yana sarawa, yace " Ya Allah! Ka kawo komai da sauki, kada ka bani ikon cutar da wanda bashida hakki akan al'amarin nan, ka bani ikon aiwatar da komai yanda ya kamata.
Nace Ameen
*TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼*
_Haly(Mom Farhan) Allah ya kara lafiya yasa kaffara ne....Wish u quick recovery_
*66*
Abu Turab idanunsa ya bud'e a hankali ya shiga kallan d'akinsa kafin a hankali ya furzar da wata yar karamar iska daga bakinsa.
Sannan yasa hannu ya dafa gadon ya mike ya zauna, idanunsa ya rufe ya shiga karanto addu'oin safiya, kafin ya sauko daga kan gado.
Yau saura sati 3 bikinsa, dayake gidan maza ne ba wani abu special ake aikatawa ba, an dai kammala ginin bangaren da zasu zauna da gimbiya.
Saukowa yai daga kan gadon sannan ya nufi bandaki dan kama ruwa da yin alwala.
Bayan ya dawo daga masallaci ya zauna yai ta tilawar al-qur'ani har sai da gari yai haske, wannan al'adar haka yake yinta dan koyar wace ta ma'aiki S.A.W.
Sai wajen karfe goma yaci abincin safe sannan ya fito.
B'angaren Mahaifiyarsa yaje sukai 'yar hira kafin ya fito.
Yana kokarin komawa bangarensa ya hango Baiwar da take kula da bangaren Abdulmajid wanda ya shine ya sakata a bangaren dan kawomai rahoto akan Hisham.
Karasowa tai cikin hanzari sannan ta gaisheshi, tana yi tana kalle kalle.
Turab ya kalleta yace " lafiya da safen nan?"
Tace "banga d'an aike bane, dama Waziri ne ya zo yanzun nan, sannan rike yake da lefa katuwa, da ya shiga ciki na amshi laidar sai naga kula ce sannan ga kamshin abinci nan."
Turab yace " yayi kyau, koma bakin aikin ki."
Tace "Yarima Abdulmajid ya......"
Dakatar da ita yai yace " na tambayeki rayuwar Abdulmajid? Ko kuwa a sanda na baki aikin nan nace ki dinga kawon zancensa? A iya sanina ce miki nai kawai in Waziri yazo ki sanar dani."
Tace " Tuba nake ranka ya dade."
Turab ya sallameta sannan shikuma ya shiga ciki.
A bakin kofa ya tadda Garzali da alama fita zaiyi.
Turab ya kalleshi yace " in zaka fita ka biya bangaren Sarki gub Jakadiya."
Garzali ya kalleshi yace " Jakadiya?"
Turab yace " ka sanar da ita Hisham na bangaren Abdulmajid."
Garzali cikin rashin fahimta yace " to." dan bazai iya tambayarsa dakili ba.
Garzali ya garzaya yaba Jakadiya sako.
Ita kanta kallab Garzalin tai tace " abinda yace kawai ka fadamin kenan?"
"iya kacinsa kenan."
Ya juya.
Jakadiya tai shiru tana kara maimaita kalmar kafin daga baya ta fito.
Bangaren Magajiya ta nufa, Magajiya na karyawa ta shigo.
Sama sama ta amsa gaisuwarta tanayi kamar bataso.
Sannan tace " me ya kawoki?"
Jakadiya ta miko mata leda tace " maganine aka kawo na gyaran fata."
Magajiya ta kalli maganin dake cikin farar leda sannan ta kalleta tace " ni ce miki akai ko wani kare da doki ya bani magani amsa nake?"
Jakadiya tace "badai haryanzu baki hakura ba?haba Hajiya Magajiya, matar sarki, uwar sarki, kakar sarki."
Magajiya ta wani juya kai sannan tace " Me ya kawo ki? Dan na tabbata ba wannan bane kadai abinda ya kawoki."
Jakadiya ta dan shafi fuska sannan ta matso tace " hmm dama na kasa fahimtar wani abu ne, Na rasa me yasa nake ganin Waziri yanzu yana zirya bangaren yarima Abdulmajid."
Magajiya ta kalleta tace " ban gane ba.."
Jakadiya tace " Tuba nake Ranki ya dade amma nifa hankali ya kasa kwanciya da zuwansa."
Ruwan da ta gama sha ragowar cikin kofun tai kamar zata zubo mata har ta rufe idonta ta d'auka ita zata zuba ma.
Magajiya ta ajiye cup din sannan ta kalleta tace " najiki inaso kuma ki fita."
Jakadiya ta had'iyi yawu sannan ta mike tai waje.
Magajiya tai shiru tana tunani, dama kwanaki Turab ya sanar da ita ya ganshi amma shi ha musa, sannan an fada mata rannan an ganshi, sannan yau Jakadiya ta fada mata, me Hisham yake tunani? Tamai magana akan kai Khadija Kano ma ya mata burus sannan yanzu ya fara kewayewa yana zuwa gun D'anta?
Turab kam zama yai a falo yai zama cin abinci sannan ya rufe idanunsa, yana kada 'yan yatsun hannunsa, Magajiya! Ki jira juyawar bayan duk wani na kusa dake, a hankali zan ruguza miki duk wani abu da kike takama dashi....Slowly ya saki murmushi sannan ya bud'e idanunsa, ta ya zakuyi kisa ku cigaba da zama kamar wad'anda basuyi komai ba? Kun halaka rayuwar mutane dayawa amma ko tunawa bakwayi.
Hannunsa ya dunkuke sannan ya kalli bakin kofa cikin tsananin kunar rai.
********
Abdulmajid na mikewa daga kan gado aka sanar dashi zuwan Hisham, baiyi mamaki ba dan ya kula yanzu wata gulma ce take damunsa, inba haka ba da can me yasa bai mai haka?
Sai dayai wanka sannan ya fito.
Hisham ya sa an jeramai abincin dayasa matarsa tai, ita kuwa tanayi tana farinciki dan yauce rana ta farko da zatai abinci domin d'anta Shikadai.
Kallan abincin yai sannan ya karasa ya zauna, ya gaisheshi.
Hisham ya amsa fuskarsa a washe yace "Ashe bacci kake?"
Abdulmajid yace " eh wlh, kayi hakuri na barka kai kadai kawu."
Hisham yace ba komai, zauna kaci abinci, goggonka ce ta dafa ma.
Abdulmajid ya kalleshi sannan ya kalli abinci yace "Kawu me kakeso?"
Hisham yace " name kenan?"
"na tabbatar abu kakeso a gareni shiyasa kake nunamin kulawar da baka nunamin da, badai so kake in auri Khadija ba ko wani abun ba?"
Da sauri Hisham ya zaro ido yace "ka auri khadija kuma? Wannan wani irin shirmene? Auzubillah."
Abdulmajid yayi mamaki yanda yaga yayi, sai dai bai kawo wani abu ba yace " to inba shiba menene? Na tabbata akwai dalilinka na yin haka balle ma kace kar na dinga sanar da Umma zuwanka."
Hisham yai shiru yana tunani kafin yace " ko d'aya kawai dai ina ganin ya kamata mu saba da juna ne, na ga ko aboki baka dashi."
Abdulmajid ya kalleshi baice komai ba ya fara cin abincin.
*******
Magajiya kam Jakadiya na fita hankalinta ya kasa kwanciya, mikewa tai ta shirya ta fito ta nufi bangaren Abdulmajid.
Da yake ta baya ne bata wani dadeba ta isa.
Ana kokarin sanar da isowarta tace ayi shiru.
Kai tasa tare da tura kofar a hankali.
Hisham taji yana cewa " Na d'auka wancan sati zaka zo, sai naga baka zo ba."
Abdulmajid wanda ya gama cin abinci ya kalleshi tare da wanke hannu yace " ya su Umman da Khadija?"
Hisham yace " suna lafiya, zakazo ran juma'ar?"
"Yaje ina?" abinda sukaji kenan da ga bayansu.
A tsorace suka mike, Abdulmajid ya kalleta yace " Umma."
Kallansa tai sannan ta kalli abincin da ya gama ci tana gani tasan Hisham ne ya kawo dan ga kuka nan a gabasa, sannan ita ba irin abincin da aka kawo mata ba kenan.
Ba shakka ranta ya baci sosai, dan idanunsa sun canza fuskar nan tata ta had'e ta tamau.
Kallan Hisham tai tace " Yaje ina?"
Hisham ya kalleta sannan ya kallu Abdulmajid, kallan Abdulmajid tai tace " ina zaka?"
Abdulmajid yace " Umma."
Kallan abincin tai sannan ta kallu Hisham tace " me kenan? Waye ya baka ikon kawomai abinci?"
Hisham ya kalleta yace " dan na kawo mai abinci wani abin ne?"
Cikin d'aga murya wanda ni kaina sak dana razana tace " wani abin ne babba ma kuwa, yaya me ke damunka?"
Abdulmajid wanda ransa ya dan sosu ya daure yace " Umma dan ya kawomin abinci wani abun ne? Kawu nane fa na tabbata bazai cutar dani ba."
Kallan Abdulmajid tai tace " ta ya kasan bazai cutar dakai ba? Dan yana kawunka kawai?"
Hisham yace " mene? Kina nufin ni zan cutar dashi?"
Cikin bacin rai tace " yaya biyoni inasan magana dakai."
Tai gaba.
Abdulmajid ya dafa kai, sannan ya kalli Hisham wanda yama rasa mai zaiyi.
Yana kallan Hisham yai waje.
Komawa yai ya zauna jiki a sanyaye.
Ita kuma suna shiga d'akinta ta juyo cikin tsananin bacin rai zatai magana.
Hisham ne yai saurin cewa me kike nufi da zan cutar da abinda na haifa?
Wata irin dariya ta saki mai razanarwa, sannan ta tsuke bakinta lokacin d'aya ta matso kusa dashi tace " me? Abinda ka haifa? Inji wa kenan?"
Hisham yace " mene?"
Tace " ahhh dalilin kenan da yasa kake neman kula dashi yanzu? Saboda d'anka ne? Ko saboda kanasan amfani dashi nan gaba?"
Hisham yai kasa dakai.
Tace " idan har kana san kanka da arziki ka fita harkar d'ana, shine magajin sarki banasan wani abu ya faru har sai ya hau mulki, in kuma har kana tunanin wani abu kama daina dan zan iya sa Abdulmajid ya daina ko gaidaka ne kai kasani."
Kallanta kawai yake yama rasa mai zaice.
Hannu tasa ta shafi fuskarta sannan Tace " Yaya banaso muna fada akan abinda bai kai ya kawoba, ban hanaka kula Abdulmajid ba amma bance ka shishigemai ba, d'ana ne banasan wani abu na shakuwa ko sama da haka ya shiga tsakaninku."
Sam yama kasa magana, sai mamaki kawai da yake na kalamanta.
Magajiya tace " Yaya na aika da kayayyakin bikin Abdulmajid gida, sannan karka manta da shirin mu na ranar d'aurin aure, wannan shine abinda ya kamata muyi ba fada ba."
Ta karasa maganar tana murmushi kamar ba abinda ya faru.
Hisham " to." kawai yace ya mata sallama ya fita.
Tabbas daga Abu Turab sai ke zakisan ni kikama haka, ba uwa d'aya uba d'aya ba ko 'yatace ke wlh sai kinsan nikikama haka.
*TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼*
_I sincerely apologize to u 😌_
*67*
Basira ce ta kalli mai martaba tace " Barden ya amince ne?"
Takawa yai shiru alamar tunani sannan ya kalleta yace " Basira kiyi hakuri, nasan yanda kika d'auki Mairo na kuma san halin Abdulmajid, yanda Magajiya ta raineshi a haka yake, yaro ne wanda bai yarda da babu ba, sannan duk abinda yakeso gani yake dolene sai ya samu, hakan ne yasa nake nunamai ba haka ba, nake kuma janyeshi daga jikina saboda banaso yai tunanin komai nasa ne kamar yanda Uwarsa ke koyar dashi, sai dai nayi tunani dakyau yaran yanasan yarinyar sannan Mahaifiyarsa ba so take ba, ko dan Magajiya taji ciwon bijire mata da d'anta yai ina tunanin Amincewa."
Basira tace " ba wai naki aminta da kai bane sai dai meyasa nakeji kamar kanasan had'a auren ne bawai dan farincikin d'anka ba ko dan karfafa zumunta da Barde ba, ya nakeji kamar dan cikar burinka na kuntatama Magajiya kake san had'a su?"
Sarki ya kalleta yace " wannan tunanin shine babban dalilin dayasa na dage akan auren Turab da Bilkisu."
Tace " bangane ba."
Yace " a masarauta dolene ka sadaukar da wani abu dan samun wani abun, bazai yiwu ka samu komai ba, inhar inaso Turab ya zama Sarkin da naso na zama dolene na samarmai mace jinin sarauta wacce tasan sadaukarwa."
Basira ta kalleshi tai murmushi dan ta fahimcu a fakaice magana ya gwab'a mata, tace " Allah ya baka hakuri."
Hannunta ya kamo duka biyun yace " inaso ki zama mai karfafamin gwiwa akan al'amurana, bawai dan Magajiya ba kawai nake san had'asu, inaji a jikina zata zama mata ta gari agareshi."
Shiru tai dan batasan me ma zatace ba, amma itakam dan ba yanda zatai ne, bataso Magajiya ta zama sirika a gun Mairo.
************
Yau kwanan Abdulmajid biyu kenan Magajiya bata kulashi, gaisuwarsa kawai take amsawa.
Yau dai abin ya dameshi bayan ya gaisheta yaki tashi.
Ya dade a zaune kafin yace "Umma nikam sai yaushe zaki huce ne?"
Bata kalleshi ba bare yasa ran amsawa, yace " kema kinsan ba ji nace ya kawomin abinci ba, sannan gani nai Kawu Hisham yaya yake a gunki kinga kuwa Uba yake a gurina......"
A gun wa yake uba?"
Kallan mamaki ya mata yace " Umma kinsan kwanan nan kin canza kuwa?"
Kallansa tai tace " na canza ko ka canza?"
Yace " Umma yanzu na kula kamar akwai abinda ke damunki, abinda bai kai ya kawoba sai inga kinji haushi, a da kuwa kina dadewa kafin inga b'acin ranki."
Shiru tai ita kanta tasan haka ta rasa me yasa takejin ta akoda yaushe kamar intai sake Abu Turab zai ruguza mata rayuwa.
Abdulmajid ya taso yazo gabanta yace " Umma meke damunki?"
Murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace " Abdulmajid."
Naam Umma.
"inaso kamin alkawari a koda yaushe cikin ko wani hali zaka zama a bayana, bazaka taba juyamun baya ba."
Murmushi yai wanda sainda hakoransa suka bayyana yace " bakyasan indinga shiga jikin Kawu?"
Kai ta girgiza alamar a'a tace " kawai dai banasan inga wani yana neman janye min kai ne."
Yace " Umma kenan, wa ya isa ya janye miki d'anki? Nifa d'anki ne ba kuma wanda ya fimin ke duk duniyar nan."
Tace"ka tabbatar ka ajiye wannan kalmar a kasan zuciyarka."
Kallanta yai yace " Umma na kasa fahimtar dalilinki na yin hidimar bikin Turab, akan me wacce ta haifeshi bazatai ba sai ke?"
Magajiya tai shiru a ranta tace" kwalliya zata biya ai kud'in sabulu."
Amma a fili tace " karka damu nice uwargidan Sarki, hakkinane na kula da hidimar bikin 'ya'yansa."
Abdulmajid ya dai kalleta ne kawai amma zuciyarshi bata gamsu da wannan sharhin nata ba.
Haka ya taso ya fito.
Da yake juma'a ce massalaci ya wuce, bayan an idar da sallah Abu Turab na cikin mutane suna ta gaigaisawa ana tsokanarsa akan ya kusa zama ango.
Abdulmajid na zaune yana hangoshi, shi kansa Abu Turab baya minti biyu sai ya kalli inda Abdulmajid yake saboda yanasan ganin Hisham kusa dashi.
Abdulmajid ya miko yazo shima aka fara gaisawa dashi.
Hisham ne ya karaso gun, yana zuwa Abdulmajid na gaisheshi ya juya zai yi tafiyarsa.
Hisham ganin haka yabishi da sauri tare da kiransa, tsayawa yai tare da juyowa, Hisham ya iso yace " gida zaka?"
Abdulmajid ya kalleshi yace " eh, da wani abun ne?"
Zaiyi magana Abu Turab ya karaso yace " Abba barka da juma'a."
A tare suka juya suka kalleshi, Hisham yace " ni?"
Turab yace " Kai Abba, zumunci akeyi shine kuka taho gefe?"
Abdulmajid yace " a yaushe ya zama Abbanka?"
Turab ya kalli Hisham irin jin kunyar nan yace " Waziri baka sanae dashi ba?"
Hisham ya had'e rai yace " me zan sanar dashi?"
Turab yai murmushi yace " Abdulmajid ai munkusa zama surukai."
Kallan Hisham yai cikin mamaki, yace " me? Sirikai? Badai Khadija ba?"
Turab yai kasa dakai yace " da alama kuna bukatar keb'ewa ko kwa zanta na maganar, ko gun Khadijan zaka kaji komai?"
Abdulmajid ya cika yai fam, yace " Kawu me kenan?"
Hisham ya kasa magana.
Turab ya kalli Abdulmajid yace " ka tambayi kanwarka."
Ya juya yai gaba, sai dai hankalinsa na kansu.
Baisan me sukace ba sai dai yaga sun juya a tare sunyi hanyar fita.
Turab ya kalli Garzali yace " dubamin ko gida sukai."
Yace to.
Bai dade ba ya dawo yace " ya gansu sum shiga mota a tare."
Murmushi Turab yai yace " Bari muje muga Hajiya Umma Magajiya."
Yai gaba.
Tanaji an sanar da ita zuwan Turab sai da gabanta ya sake fad'uwa.
Mike wa tai ta shiga cikin d'aki, gyara kanta tai sosai, sannan ta fito.
A zaune ta ganshi yana cin ayaba.
Karasowa tai ta zauna, Turab ya kalleta yace " Umma barka da rana."
Ta amsa cikin izzarta sannan tace " banyi tsammanin ganinka ba."
Yace " nima bansan zanzo ba sai