Showing 141001 words to 144000 words out of 146065 words

Chapter 48 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

kalleta tace " Barka da warhaka."


Sannan tace " ban gane ba...."
Mairo tace " Yar gidan Barde ce."
Bilkisu tai murmushi, zatai magana Lantana tace "Mairo kin iso?"
Mairo ta gaisheta sannan tace " Umma fa?"
Lantana tace " tana ciki."
Mairo ta kalli Gimbiya tace " Zan shiga ciki."
Bilkisu tace " inkin fito zaki shigo?"
Mairo ta kalleta tace " zanzo, dama inatasan inga Matar Ya Turab, sai yanzu Allah yai, amma zanzo."


Bilkisu ta murmusa sannan tai gaba, da alama akwai shakuwa tsakaninta da Umma da kuma Turab.


Mairo ta bi bayanta da kallo, a ranta tace " Allah mai baiwa, gaskita tanada kyau, dan zata iya cewa tunda Allah ya halliceta bata taba ganin mace mai kyau irin na Bilkisu ba, duk da wani bangaren na zuciyarta na dan kishi saboda shi so ba farat d'aya yake fita gaba d'aya ba indai har san na gaskiya ne."


**************


Bayan ta gaida Umma kuwa ta nufi bangaren Gimbiya, Bilkisu har tayi wanka lokacin ta canza kaya, aka sanar da ita zuwan Mairo.
Fitowa tai taganta a zaune akan kujera, kusa da ita bilkisu ta zauna.
Mairo ta kalleta tace " Da har ina tunanin guduwa, ganin bansan mai zance miki ba in muka hadu."
Bilkisu tace " tunda nazo garin nan banida kowa sai mutanen gidan nan, shiyasa ganinki yasa naga kamar na samu wata."
Mairo tai murmushi tace " ga Ya Turab ba koda yaushe yake nan ba."
Bilkisu tace " sosai."
Murmushi sukama Juna.
Bilkisu tace " tun yaushe kikasan shi?"
"Ya Turab?"
Tace " eh."
Mairo tace " tun muna yara na dawo daga makaranta da gudu..............."
Nan ta bata labarin haduwarsu da abinda ta dingamai na tsokana ganin baya gani.....
Sosai Bilkisu take dariya tace " lalai kinyu kiriniya."
Mairo tace " hmmm ai a aji shi kullum yana zaune shiru dama Khadija ce..........."
Da sauri ta gumtse bakinta sannan ta wayance tace " Abdulmajid ne ma....."
Bilkisu ce ta katseta tace " kinsan Khadija ne?"
Mairo ta kalleta da sauri tace " Naam?"


*TURAB*
*KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


* SECOND TO D LAST PAGE*


*89*


Bilkisu tace " Mairo menene tsakanin shi da Khadija?"
Mairo tace " menene kuwa, zumunci ne na ya da kanwa kamar ni."
Bilkisu ta kura mata ido, da sauri Mairo ta mike tace " bari naje gida naga yamma tayi."
Kafin Bilkisu tai magana tayi wuf tayi waje.


""*******""""
Gimbiya ta dade a zaune tana tunani kafin ta mike ta shiga d'aki, tana shiga ya turo kofar tare da sallama.
Juyowa tai ta kalleshi tare da amsamai.
Karasowa yai inda take kawai sai jitai ya rungumeta tsam a jikinsa a hankali yake fitar da wani numfashi, murmushi tai sannan tasa hannu ta shafi bayansa tace " Weldone dear."


Sun dade makale da juna kafin ya d'ago tare da rike kafad'unta yana kallanta.
Wani sansanyan murmushi tamai tace " ya akai?"
Yace " jikinkinfa?"
Tace " na ware, sai kadan"
Ya kara rungumeta yace " Sannu, yau nasan kinsha wahala."
Tace "kaine kasha wahala, ni me nai? Ya hakurin mu? Ni ko ganin Hajiyar ban taba yi ba,Allah bai nufa ba."
Yace " Hajiya ta girma sosai wanda kowa yake mata tunanin mutuwa, sannan dan rashin imani matar nan ta nemi halaka mata rayuwa ba tare da tayi duba da tsufanta ba."
Bilkisu tai shiru, jiki a sanyaye.
D'agowa yai tare da kama hannunta suka zauna a bakin gado, kwanciya yai tare da d'aura kansa akan cinyarta yana kallanta yace " Kinji abubuwa na tashin hankali da mamaki yau ko?"
Hannunta tasa akan sumarsa tace " a'a, ni duk abinda ya faru abu d'aya yafi tadamin hankali, ganinka danai cikin wani yanayi kana neman fita hayyacinka."
Yace " abinda Magajiya tai fa?"
Tace "Magajiya? Hmm ko kad'an ban tsorata da ita ba saboda na tabbatar in har hankalinka da ta nemi gusarwa ya dawo to tabbas komai zai daidaita, sannan zaka juya kan akalar muguntar da ta shirya."
Murmushi ya mata sannan yace " Thanks alot for believing in me."
Tace " nima Thanka alot."
Yace " ke kuma for me?"
Tace " bakasan abinda yafi komai min dadi ba?"
Yace "a'a"
Tace " yanda nima ka yarda dani kake kuma sanar dani damuwarka."


Murmushi ya mata yace " ni kaina har yanzu ina mamakin yanda ke kadai zuciyata ke iya bod'ewa damuwarta."
Tace " ina rokon zuciyarka da ta kara sanar dani d'amuwa d'aya da na ke san ji."
Kallanta yai yace " name kenan?"
Kallansa tai sannan tai kasa da idanunta a hankali ta furta Khadija!"


Kallanta yai sannan ya mike daga kan cinyarta ya zauna yace " Khadija?"
Juyowa tai ta kalli kwayar idanunsa.
Mikewa yai hannu tasa ta riko hannunsa da sauri tace " Yarima."
Tsayawa yai sai dai bai juyo ba, tace " inada tsananin kishi hakan ne yasa nakesan na auri wanda yake sona sosai, sai dai duba da yanayin gidan dana fito nasan tabbas Mahaifina bazai bada ni ba sai ga wani mai matsayi na sarauta, sannan nasan Sarki bazai taba zama da mace 'aya ba, in har ka b'oyemin tsakaninku shine zai sani jin ba dadi a raina bawai shirunka ba."


Turab ya juyo ya kalleta sannan ya sakar mata murmushi yace " Later, zan sanar dake komai amma ba yanzu ba, banasan wani abu ya shiga zuciyarki a wannan lokacin, zan sanar dake in har kika sake tambayata, sai dai ba wannan lokacin ba."


Murmushi tai tace " nagode sosai."


Kusa da ita ya matso ya rikota jikinta.
Sai da sukai sallar isha'i sannanya sanar da ita hukunci sarki da kuma abinda suka yanke akan Abdulmajid sosai ta yaba da shawarar da suka yanke.


A ranar uku kuwa Mai Martaba Sarki ya tattara mutane ya sanar dasu hukuncinsa, sannan dama ya riga ya hana mutanen dake d'akin zancen Abdulmajid.


A lokacin ne aka nad'a Abu Turab a matsayin Sarkin garin Zazzau.
Kasancewar anyi rasuwa a gidan yasa ba'ai wani taro ba na biki a gidan Sarautar ba.


Turab na hawa kan mulki Sarki yace " kafin na bar gidan nan inaso ka yankema mutanen da ya kamata su amshi hukuncinsu a hannunsu."


Turab yace a fito da masu laifi su gurfana.


Abdulmajid na zaune jin ance a fito dasu yasa jikinsa yai wani irin sanyi.
Turab yace " a fara shigo da matar nan data mai sharrin fyade, dannan wacce take sama Sarki magani da kuma wacce take sama Hajiya, dan dama a kwanakin nan duk sai da aka kamosu."
Turab ya kalli Matar data mai sharri yace " duba da yanayin laifinki an yanke miki hukunci yin aiki a gidan nan, aiki na karfi na jiki na shekara biyu ba tare da an biyata komai ba."
Sannan ya kalli Sarki, murmushi mai martaba yai hakan yasa ya gane hukuncin yayi.
Turab ya kalli Matar da take sama Sarki magani.
Yace " kin aikata babban laifi na sa magani ga Mai Martaba, duk da bakisan maganin menene ba kinyi laifi na sakawa, sai dai rubutama Hajiya da kikai yasa za'a miki sassauci ke kuma zakiyu aiki kema na shekara uku ba tare da biya ba."
Sannan ya kalli matar da itace shaida a garesu yace " kema kinyi kuskuren sawa Hajiya magani duk kuwa da anyi amfani da rashin lafiyar kaninki gun umartarki da yin wannan aiki sannan kin kula da Hajiya kin kuma bada shaida akan abinda aka saki kika aikata hakan ne yasa za'a kaiki asibitin Abu inda kaninki yake dan yin aiki acan na karfi na shekara d'aya."
(In akacema Mace aikin karfi ina nufin, girki, wanki, wanke wanke, wanke band'aki, surfe, daka, sisika da sauransu.)


Shigowa akai da Jakadiya, kallabta yai sannan yace " Jakadiya kinsan laifin ki?"
Jakadiya ta sunkuyar da kai.
Turab yace " laifin sani tare da takewa, sannan laifin amfani da wannan sanin dan cikar burinki, na cireki daga matsayinki na babbar jakadiya a wannan gida, sannan zaki bar gidan nan batare da kin d'auki komai ba, ki koma kauyenku ki zauna."


Jakadiya kam jitai kamar tasa kuka dan tabbas tana cikin garari.


Hisham aka shigo da shi.
Turab ya kalleta sannan yai shiru, can yace "Waziri da farko dai daga wannan lokacin na cireka daga matsayinka na waziri sannan kai namiji ne wanda yake uba yake kuma da mutane a karkashinsa, sai dai bakai amfani da wannan matsayin da kake dashi ba, ka kashe mutane biyu a daura, wanda shikadai ya isheka karasa rayuwa a gidan yari, ka biyewa Magajiya kunyi ta tafka laififuka wanda bazasu irgu ba, hakan ne yasa za'a maidakai gidan yari ka karasa rayuwarka acan wato d'aurin rai da rai."


Hisham ya runtse idanunsa hawaye suka shiga zubomai, mai rayuwar nan ta dada mai? Kallan Abdulmajid yai wanda yai saurin d'auke kansa tare da juya kansa gefe dan yanaji wani abu na ratsashi.


Hisham yai murmushi tare da rusunawa yace " ina godiya da alfarmar dakama abinda na haifa, ina kuma rokon ka daka taimaka ka sassautawa matata ko dan kula da zuri'a ta."


Turab yace " a d'aukeshi."
Nan akai waje dashi yana kallan Abdulmajid.
Anje fita dashi ana kokarin shigo da Magajiya.
Gaba d'aya ta canza tana ganinshi tahau kakari alamar masifa, duk ta rame, ga wani azababban ciwon ciki da take kwana dashi kullum.


Ana shigo da ita aka fara gulmace gulmace.
Kalan kallo suka fara da ita, wani irin kakari take tana neman kwacewa ganin Turab akan kujerar mulki, sai wani kakari takeyi Tana girgiza kai ba kakkautawa.
Turab ya kalleta duk ta canza, nan aka tad'iye kafarta aka gurfanar da ita, Turab ya kalleta yace " Rashin godiya ga abinda Allah ya maka, rashin sanin darajar mutum, d'aukar rayuwar d'an adam kamar kaice kika bashi, halaka duk wani abu da yake neman kawo miki cikas a rayuwa, san zuciya da tsantsar san kan da kike dashi, laifufukan da kika aikata banaji zasu irgu, wayasan tun wani lokacin kike aikata laifufuka? Ba imani ko kadan a ranki. Sannan a wannan lokacin ma banaji zuciyarki tana dana sanin laifufukan data aikata, na tabbatar da za'a baki wuka to tabbas zaki nemi kawar da abinda bakyasan ganin a fadar nan."


Turab ya kalli Sarki wanda kallanta kawai yakeyi, Turab yace " Ina rokon Takawa da ya hukunta wannan matar, dan kuwa kai ta cutar cutarwa ta ruwan sanyi wacce tafi ciwo."


Sarki ya kalleshi sannan ya kalleta yace " abinda nake jira kenan, abin kuma da ya tsayar dani kenan, jira nake naga yanda matar nan zatai in zata wanda ta tsana a duniya zai yanke mata hukunci, sai dai inaso tasan abu d'aya a cikin mutanen nan, ni Abdussamad na yanke igiyar aurena da Magajiya, na yanke duk igiya ukun dake kanta."


Wani irin gurnani ta shiga yi.


Turab ya kalle ta sannan ya kalli Abdulmajid.


Magajiya ta shiga kokarin mekewa cikin tsananin tashin hankali, Turab ua runtse ido, a hankali muguntar Magajiya da tsantsar rashin imaninta ya dinga dawomai a zuciyarsa, tabbas ko gidan yari bata cancanta ba, a kalla acan za'a bata abinci zakuma a bata gurin kwana.


Gyaran murya yai sannan yace " Magajiya, daga wannan lokacin an saukeki daga matsayinki, sannan zakibar gidan nan ba tare da komau ba sai kayan jikinki, zan sanar a garin nan akan kar wanda ya kuskura ya bata muhallin zama, wannan umarni ne daga gun Sarki, abinda ya dace da ita shine ta shiga gari taga yanda mutane suke, taga yanda marasa muhalli suke rayuwa, yanda mahaukata suke rayuwarsa, su wad'an nan ba wai tsanarsu Allah yai ba ya gusar musu da hankali, a'a wasu kaddara ce ta Allah wasu kuwa irinku ne wad'anda suka haukatasu, kije kiga yanda ake rayuwa, kije kiga yanda abinci yake samuwa da tsananin wuya, wannan shine abinda ya dace dake, kije kiyi rayuwa wacce yan uwanki basu isa sun taimaka miki ba, in kikai irin wannan rayuwar ta shekara biyar daidai lokacin kin manyanta da yawa, sai a dawo dake gidan yari ki karasa rayuwarki acan."


Kakari take yi har muryarta ta kakari na neman d'aukewa, wani irin karfi take badawa kamar zata kamo Turab agun nan, yanda kasan mahaukaciya sabuwar kamu.


Nan akai waje da ita kakari take kamar zata ciro ranta........





*Turab*
*KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*LAST PAGE*


*90*


Yanda aka fito da Magajiya sai kallanta akeyi, kan kace me an cika ana zuwa kallanta labari duk ya baza akan maganin da take ba Sarki na hana haihuwa, sannan maganin da ta sama Hajiya dan kasheta, nan fa kowa ya fara tofa nashi albarkacin bakin.


Ana fitar da ita waje a ka tsaya da ita dan jiran umarnin daga sarki na asaketa.
Tahowa yai gadan gadan rike da wani makeken katako yayo kansu, kallo daya zakamai kaga bigegen d'am shaye shaye, dogarawan dake tsaye kanta kuwa suna ganin haka suka fyalla da gudu, yanda taga yayo kanta tasan tabbas sai ya maka mata, da sauri tai kasa ta tsugunna, yana karasowa kuwa ya d'aga katakon nan ya maka mata a gadan bayanta.
Ga ba baki bare ta calla kara, wani irin zakwadi na zafi ta shiga yi sai juye juye takeyi dan yauce rana ta farko da zatace a rayuwarta an mata irin wannan dukan, tsugunnowa yai inda take ya nuna ta da yatsa yace " menene damuwarki da Basira? ai na tambayi wanda ya kawoni garin nan bayan na karyamai Kafa akan wanda yasa aka kawoni shine yamin kwatance sannan naji labarin an kamaki, yau za'a yanke miki hukunci, yanzu nan da kika ganni gidan Sarkin nazo shiga kota wani hali ne dan sai naje gunki, sai naji ana cewa Magajiya, dan kut............. Dama amfani kikesan yi dani gun muzguna mata?"


Ya kara d'aga katakon zai mazga mata, da sauri ta rike kafafunsa dan ta tabbatar inya kara maka mata to fa lalai sai bayanta ya karye.
Da karfi ya fizge kafarfa sai gata a kasa ta fadi yace " kinsan masifar dana shiga bayan na mata fyaden, sam rayuwata lalacewa tai, banda shaye shaye banida aikin yi, kowa nawa ya gujeni, sannan kike kokarin jefani cikin masifa?"


Ina Magajiya ba bakin magana ga magana a ranta yana cinta, hannayenta ta hada tana bashi hakuri.
Yatsa ya nuna mata sannan yai kwafa.
A zuciye ya juya yai gaba, Magajiya sai ji tai hawaye ya zubo mata, da sauri tasa hannunta ta tabo hawayen cikin tsananin mamaki, yau itace take kuka? Ita Magajiya?


*************
A can fada kuwa Abu Turab ana fita da ita yace " Bazan maida sarautar Waziri gidan Hisham ba, sai dai zan nba babban dansa namiji wato Salihu wani mukami wanda bai kai Waziri ba."


Sannan magana ta karshe inaso kowa ya cigaba da girmama yayana Abdulmajid da bashi matsayinsa, banaso gulma akan Mahaifiyarsa ya shafeshi dan bazan yafema duk wanda aka kawo kararsa ba akan hakan."


Kallan juna sukai shida Abdulmajid, da sauri Abdulmajid ya maida kansa kasa yana tuno abubuwan da ya aikatama Turab a baya, lalai duniya abar tsoroce in ka bari santa ya shigeka to lalai kana cikin garari na rayuwa.


Sarki yana ganin haka yace " Alhamdulila komai yazo karshe, ina maka fatan alkairi ina fatan ku nacikin d'akin nan zaku bashi had'in kai kamar yanda ya kamata."


Galadima yace " Masha Allah, ba shakka komai yayi daidai, sai dai nima ina neman alfarma daga wannan lokacin inaso in ba wa Sabi'u mukamin mulkina na Galadima, ni dakai tare muka fara, haka kuma tare zamu gama, suma sai su fara a tare."


Sarki yai murmushi yace " Allah ya tayasu riko ya kuma kare mana su."
Nan akace Ameen.


Haka taro ya tashi, sai da mutane sukagama fita, Abdulmajid na kokarin fita Abu Turab yasa acemai ya sameshi a cikin falon Sarki wanda yake ta cikin fadar.


Nan Habu ya turashi zuwa falon.
Abu Turab na zaune a kasa, Sarki na kan kujera aka shigo da Abdulmajid.


Shiru ne yad'an ratsa falan kafin Sarki yai gyaran murya yace " Abdulmajid!"
Yace " Naam Ab......"
Sai kuma yai shiru, Sarki ya kalleshi sannan yace " Abu Turab!"
Turab yace " Naam Abba."
Sarki kallesu sannan yace "Abdulmajid mun yanke shawara nida Turab akan lamarinka, hakan ne yasa muka nemar maka aiki, Alhamdulila duba da matsayina da iliminka yasa ba'a sha wahala ba, dan an tabbatar min a wannan satin mai shiga komai zai kamala, anan cikin garin kaduna zaka fara aiki ba sai kayi nisa da gida ba."


Abdulmajid jiyai idanunsa sun ciciko yace " Na gode Allah ya saka da alkairi." yana karasa maganar hawaye na zubomai.
Sarki ya kalleshi yace " yanda kake da na matsayin d'a a gurina yanzu ma baka canza ba, sannan inaso in sanar maka har cikin raina a matsayin d'a kake a gurina har abada kuma bazan yada kai ba, sai dai ina fatan zaka cigaba da rayuwa kamar yanda kakeyi yanzu, rayuwa mai tattare da nutsuwa da kuma girmama mutane, tare da bin dokokin Allah."


Abdulmajid yace " insha Allah."
Sarki ya kalli Turab yace " inaso ku hada kanku, duk da ba a kusa kuke ba inaso ku rike zumuncin dake tsakaninku, Abu Turab mulki da kake gani yana tattare da jin dadi, samun babban matsayi da farin ciki na dayuwa sai dai wannan duba ne na mutanen da basa kan mulkin, kai da kake kan mulkin a hankali zaka fahimci rashin jin dadinsa, wanda mutane bazasu taba ganin haka ba."


Sarki ya numfasa yace " sannan kace akwai abinda zaka fad'amin, menene?"
Turab ya kalli Abdulmajid sannan yace " dama Abba maganar auran Yaya Abdulmajid ne."
Da sauri Abdulmajid ya kalleshi yace "Yaya?"
Sarki ma kallan mamaki yamai sai dai daga baya yai murmushi yace " Yaya? Hakan yayi kyau, ai da dadi mutum ya samu wanda zai kira da yaya."
Turab yace " akwai wace yakeso,itama ta sanarmin tana sanshi."
Sarki yace "Yar gidan Barde?"
Turab yace ya akai ka sani?
Sarki yai dariya yace " yanzu Turab kaf gidan nan waye bai san sanda yaran nan yakema Mairo ba? Bayan har fada yazo ya fada saboda rashin kara?"


Abdulmajid jiyai kamar kasa ta tsage ya shige saboda tsananin kunya.
Sarki yace " Tunda auran d'ana ne nine zanje neman auran, karka damu kaidai ka kula da abubuwan masarauta da kukan mutane, ni zan kula da Abdulmajid."


Turab yace " godiya muke."


Abdulmajid, kokarin mikewa ya shiga yi daga kan kujera dan taugunnawa, Sarki yace " bari mana karkaji ciwo."
Abdulmajid yace " Abba bansan ta ina zan fara bane."
Sarki yace " ba sai ka fara ta ko ina ba, ni dai ka zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login