Showing 90001 words to 93000 words out of 146065 words

Chapter 31 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

wato bata d'auki Sarki da wani matsayi ba? Gani take tafi karfinsa.


Ba shakka ran Magajiga yakai gurin tunzura, lalai dole taga karshen yaron nan ita ganin sa ma ta tsani yi yanzu.




Haka ta fito rai a b'ace.


************


Abdulmajid kam yana tsaye a kofar gidansu Mairo sai data dade sosai dan sai da mahaifiyarsa ta tsawatar mata sannan ta fito.


Yana ganinta ya sauko yana washe baki.
Tsayawa tai tare da hard'e hannayenta ta juya mai baya a cikin soron.
Abdulmajid ya karaso ya kalleta ta baya sannan yace " Gimbiya irin wannan tsayuwa haka kamar mai shirin yin hoto?"
Juyowa tai ta kalleshi tace " Abdulmajid."
Da sauri yace " Naam."
Tace " dan Allah dan Annabi ka kyaleni, wlh wlh ni kam na gaji da wannam abun, ka sanni sarai banaso raina ya bace dan wlh xanyi abinda kaima sai kai dana sani."


Kalamanra ko a jikinsa yace " eh wlh, dan Allah Mairo kiyi abinda zanji jiki ni wlh so nake yi."


Wani banzan kallo tamai na takaici tace " wai kana d'an sarki me yasa kake abu kamar karamin yaro?"
Hannunta ya kamo, da sauri ta fizge tace " Wai Abdulmajid meke damunka ne? Na d'auka na sanar dakai banasan ka dinga tabani ko? Kaje can kun karuwan......."


Batai auni ba taji yasa hannu ya rufe bakinta.
Matsowa yai da sauri ta matsa jikin bango tana zare ido tace " meye hakan?"
Kallanta yai yace " Mairo me yasa kike tunani ni din dan iska ne?"
Harararsa tai batace komai ba.
Yace " nasan bazaki yarda da abinda zance ba amma wlh kinji na rantse ban taba sanin wata 'ya mace ba, ma sani sarai ina shafa bayin gidan mu dan jin dadi na sai dai ban taba bari abin yakai nan ba."


Kallansa tai tace " kana tunanin zina sai ka sadu da mace kawai take a matsayin zina?"


Kallanta yai yace " Mairo ni duk wannan ba sune a gabana ba, in kikace in daina taba mata zan daina nidak dan Allah ki auren, ko na aureki in kikaga dama kice sai kin amince zan kusanceki Wlh zam yarda ni dai dan Allah ki yarda ki auren, ina san......."


Katseshi tai tace " Ni dai dan Allah ka kyaleni na rokeka da Allah."


Murmushi ya sakar mata sannan yace" ma tafi yau, sai na dawo zuwa jibi."


Kafin tai magana har ya tafi, juyawa tai ta wuce gida.


*******






*TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*59*


Magajiya sam ta rasa yanda zatai, ganin ba mafita yasa ta nufi gun Sarki.
Yayi mamakin jin zuwanta bayan ta shigo ta zauna sannan ta gaidashi.
Kallanta yai tare da amsawa yace " Lafiya dai ko?" ya fada tare da d'aukan ruwan dake gabansa a kofi dan sha.
Fuskarta a sake kai kace cikin farin ciki take tace " dama maganar auren Turab ne, ina tunanin ya kamata in fara had'a lefe....."
Furzo da ruwan bakinsa yai tare da kwarewa, kallanta yai cikin tsananin mamaki yace " me? Me kika ce?"
Dariya tai na salo tace " me? Kana tunanin lokaci baiyi ba?"


Ido ya kura kura mata yace "Magajiya!"
Kallansa tai bata amsa ba, yace " kinsan me kike anan kuwa? Kin tabbatar a hankalinki kike ko kuwa wani tugun muguntar kika shiryo?"


Sansanyan murmushi ta sakar mai tace " ko d'aya na dai fahimci cewa aikinane wannan, sannan waye Turab? D'anka ne fa wanda daga shi baka kara samun wani ba, ta ya za'ai yara kwaya biyu ace mun kasa kula dasu? A wata masarautar sai kaga 'ya'yan sarki sunfi 30 amma mu a namu haryanzu biyu Allah ya bamu, me zaisa mu zauna muna samun sab'ani akan su?"


Wata banzar dariya yai dan ko magajiya zata dafa Al-qur'ani bayajin zai yadda da wad'annan kalaman nata, ya tabbatar da abinda take shiryawa.
Kallanta yai yace " yanzu me ake bukata?"
Nan ta fara mai bayani, yace zai bada kudi ayi komai cikin girmamawa da matsayi.


Tana fitowa yabi bayanta da kallo yana tunani, me ke faruwa? Ya tabbata Turab ko mai zai ce mata bazata taba yarda da zancen nan ba balle ma tasan sirrin mahaifiyarsa, me zai sa ta amince? Ya tabbatar akwai wani shirri da take yi.


*********


Turab zaune agun hutawar daya saba zama ya saka ledar maganin nan a gaba a hannunsa yana kallo cilla maganin yai sama kad'an sannan ya cafe yace " kai kuma aikin me kakeyi?"
Mikewa yai dan dole ne ya binciko maganin menene wannan.
Bangarensa ya nufa, yana shiga Garzali ya taso ya gaidashi sannan ya sanar dashi nemansa da mahaifiyarsa takeyi.
Mikamai maganin yai yace " so nake ka bincikomin maganin menene wannan yanzu, sannan ya zama sirri kar ka tambaya a gidan nan, kaje wajen gari"
Garzali yace " to" sannan yai waje.


Bangaren Mahaifiyarsa ya nufa, ta sa an shiryamai abinci, Turab ya zauna sannan ya gaisheta.
Kallansa tai cikin kulawa daga dawowarsa daga kano har ya d'an fada, Lantana ta kalla tace " Lantana zubamai abincin."
Turab ya kalli Lantana sannan yace " barshi zan zuba da kaina."
Nan ya jawo plate ya d'ebi fankaso guda biyu ya zuba miyar taushe wanda yaji kaza.
Hannunsa ya wanke sannan ya fara ci, sai da ya gama yasha zubo sannan ta kalleshi tace " ya kukai da Magajiyan?"
Murmushi yai mata sannan yace " karki damu Umma, sirrin nan sai dai ta tafi dashi har kabarinta badai ta sanarma wani ba."


Basira tace "me kake nufi? Kasan halin Magajiya fa?"
Yace " Nasani Umma sanin ne ma ya sani fad'in haka, sirrinki datake tunanin amfani dashi wajen hanani auren Bilkisu da kuma sa Mai Martaba yin murabus wannan sirrin ba wani abu bane akan sirrinta da nake rike dashi, ke dai kawai ki kula da lafiyar wannan shine kadai abinda nake nema daga gareki."


Kallansa tai cikin jin dadi da gamsuwa tace " maganar Mairo fa?"


Yana murmushi yace " Umman Mairo, wai ni Umma daga ni da alama ba wanda kikeso sai Mairo ko?"
Tace " Turab kenan, kasan yarinyar nan itace ta taimakeni har nakejin zaman gidan nan bai zaman min takura ba?itace ke d'ebe mana kewa daga ni har lantana, jinta nake kamar 'yata."


Turab ya jinjina kai yace " haka ne, shi yasa akoda yaushe nake godiya gareta, na sani ta kula dake wanda ni da nake d'anki ban baki wannan kulawar ba."
Basira ta kalleshi sai dai batai magana ba, sai dai yanayin kalamansa da yanda yake fitowa tasan magana ce wacce ke kwance a kasan zuciyarsa.


Turab ya d'ago sannan yace " karki damu Umma, Insha Allah ba abinda zai faru sai alheri."


Tace " Allah yasa."
Zama sukai shi da Lantana da Basira sukai hira sosai sai da yaji la'asar tayi sannan ya fito.
Yana shiga Garzali ya shigo falon, tare da mikamai maganin nan.
Turab ya kalleshi yace "Maganin menene?"
Garzali yai kasa dakai sannan yace " magani ne wanda zai halaka gab'obin jiki, ya hana mutum yin komai, ya kuma shanye mai b'arin jiki, a takaice dai guba ce mai illar gaske wanda samunta yake da matukar wahala."


Turab idanunsa ya runtse da karfin gaske dan ji yake gaba daya kamar an kwara mai ruwa.
Idanunsa a runtse yace " Ka yarda da sanin mai maganin daka tambaya?"
Garzali yace " kaf garin nan an san dashi dan nima kaini gunsa akai, shikansa yayi mamakin ganina da maganin, sannan ya sanar dani maganin a hankali yake lahanta mutum ba wai tashi d'aya ba."


Turab yace " jeka na gode."
Garzali ya mike yai waje.
Yafi minti goma idanunsa na runtse, wace irin matace wannan? Dan ya tabbatar itace tasa a ba Hajiya maganin nan, amma mahaifiyar mijinta? Wannan wace irin masifa ce?"




Jiyai kansa ya sara, ya mike yai sallah ya dade yana addu'oi kafin ya shiga bandaki ya sakar ma kansa ruwa.


Ruwa ne ke zuba a jikinsa hayi shiru yana tunani, ya dade sosai kafin ya fito.
Shiryawa yai sosai cikin wata dakakiyar shaddarsa ruwan madara, hula da takalmi ya saka sannan ua saka agoggo.
D'ankwalin khadija ya kalla ya dade yana kallan d'ankwalin kafin ya rufe kofar da karfi, takardar daya ajiye a gefen gado.


B'angaren Magajiya ya nufa yana tafe cikin isa.


Yayi sa'a Abdulmajid na zaune a gunta.
Tana jin ance yazo sai dataji gabanta ya fad'i, yauce rana ta farko data taba jin shakkar zuwan wani d'an adam gunta ba sai yau.


Ba shakka wannan abu ya kona mata rai.
Abdulmajid yace " ya shigo."
Turab ya shigo tare da sallama.
Abdulmajid ya bugamai banzan kallo yace "ina zakaje haka?"
Turab ya kalli Magajiya sannan ya kalli Abdulmajid yace " zance zanje."
Abdulmajid ya tab'e baki sai kuma ya zabura yace"badai gun Mairo ta ba ko?"
Turab ya kalleshi sannan ya maida idanunsa kan Magajiya datake kallansa yace" yau ba gunta zanje ba, gun Khadija zani."


Tashin hankalin daya bayyana a idanuwan Magajiya ba'a magana, Kallansa tai tace " me? Khadija? Ba dai Khadija wacce take 'ya ga yayana ba?"
Turab ya d'aga mata gira sannan yace " ya? Kin sanar ma Sarki akan maganar lefe na?"


Abdulmajid ya sheke da dariya yace "Lalai Turab amma kai ba karamin had'amamen mutum bane, kana tunanin soyayya da aure wata a lokaci d'aya?"
Turab yai murmushi yace " ba'ayi ne? Da farko dai ni d'in mijin mata hud'u ne banda kwarkwarori."


Abdulmajid yace " wannan damuwarka ce sai dai ka fita hanyar kanwata dan badai yar uwata ba kai ko kunya ma damu zaka had'a zuri'a?"


Magajiga kam kallansa take cikin idanunta da suka canza kala wanda bakin ciki ne karara ne d'auke a idanun.


Turab ya kalli Abdulmajid sannan ya kalli Magajiya tare da ciro ledar maganin nan. Ruwan dake gaban Andulmajid ya jawo ya zuba a kofi sannan ya zuba maganin nan.
Magajiya ta kalleshi tace " meye hakan kuma?"
Mika mata kofin yai yace " Umma sha."


Wani banzan kallo tamai tace " a gabana ka zuba magani kace insha? Nasan ko maganin halaka ne?"


Kai ya d'an langwab'e yace " kuma fa haka ne, kar in baki maganin dazai kwantar dake ya kashe miki gab'obin jiki sannan ya hanaki magana, ya kuma hana kwakwalwarki aiki yanda ya kamata."


Gabanta ne ya shiga fad'uwa, daurewa tai ta saki murmushi zatai magana Abdulmajid yace" ansha karya, yanzu kai kana tunanin akwau irin wannan maganin a duniya? Sannan in akwai ma mai zai sa ka saku?"
Turab ya kalli Abdulmajid yace " shine ai abin tambayar, Umma ya akai kika samu wannan maganin?"


Kallansa tai tare da fito da idanuwanta, daurewa tai tai wani dariya tace " Turab kenan, kanasan zolaya, yanzu ka shigo da magani kace ni na baka?"
Turab yace " kin manta? Ke kika bani a sanda muka had'u a b'angaren Hajiya?"


Magajiya tace " ni bansan wannan zancen ba, sannan mai zai sani in baka?"
Yace " shine abin tambayar? Mai zaisa ki bani? Sannan me na tare miki da zaki bani irin wannan abin? Karfa ki manta nid'in d'a ne a gunki."


Idanu suka kafama juna dan magana ce suke yinta a juye wanda su biyu ne suka san me suke nufi, ita tasan Turab sanar da ita yake abinda ta sa akeba Hajiya, shi kuma so yake yaji menene dalilinta na neman halaka kakarsa? Wacce take uwa a gareta?


Abdulmajid ne ya kallesu, kana kallan yanda suke kallan juna kasan kallo ne mai tatare da ma'anoni kala kala, hannu yasa ya daki kafadar Abu Turab yace " Turab bakada hankalu ne? Umma kakema wannan kallan?"


Magajiya ta juya kai sannan ta kalleshi tace " bansan me kake cewa ba Turab."


Yace " wasa nake yi nima, ya maganar lefen?"
Tace " na d'auka mungama wannan maganar hakki nane a matsayina na mahaifiyarka ai inyima lefe."
Yace " haka ne, yauwa bari na kira Gimbiya na tabbata ta damu da jina shiru tunda na dawo, bari nai amfani da wayar b'angarenki."


Magajiya ta gama cika fal, Abdulmajid mamaki ma ya hanashi magana, kallan sa yai harya mike yai falonta, sannan ya kalli kofin ya d'auka yana kallan ruwan ciki, yace "Umma me wannan yaran yake cewa?"


Sam bataji ma me yake cewa ba dan ta tafi dogon tunani.
Kallanta yai ganin yanda ta tafi tunani ya sa jikinsa yai sanyi, bai taba ganin ta haka ba, me ke faruwa? Me zaisa Ummansa tama Turab lefe bayan tasan yanda ta tsani auren nan?








*TURAB*



🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*60*


Abdulmajid ya kara kallan Magajiya yace " Umma wai meke faruwa?"
Tsawa yaji ta dakamai tace " Fita ka bani guri."
Tsananin mamaki ne ma ya hanashi d'auke ido daga kanta, me yai? Yauce ranar daya tabaji tamai tsawa haka balle ma akan wani Abu Turab?
Mikewa yai rai a b'ace yai waje.
Ko bi ta kansa batai ba ta sa kafa tayi ball da wannan kofin, mikewa tai ta nufi falonta.


Turab kam number Bilkisu ya danna, ta dade kafin a d'aga, gaisheshi akai sannan akace wanene?"
Turab yace " Ina Gimbiya?"
Daga can akace bari a sanar mata, waz'ace?" yace "Abu Turab."
Da sauri mai maganar ta gaisheshi sannan ta ajiye kan wayar a gefe tai cikin d'aki da sauri.
Gimbiya na Kwance rike da wani littafi tana karantawa.
Bayan yarinyar ta nemi izini ta shigo ta tsugunna sannan tace "Gimbiya, yarima ne ya kira waya."


Mikewa tai zaune da sauri tace " Turab?"
Yarinyar tace " eh Gimbiya."


Da sauri ta juya zata sauko, sai kuma ta koma ta zauna tace jekinkice ina zuwa.
Yarinyar ta amsa da to sannan ta mike.


Bilkisu sai da ta d'an dade a zaune sannan ta sauko a hankali ta fito.


Sallamar duk masu kula da ita wad'anda ke falon tai sannan ta d'auki wayar, cikin kasalaliyar murya tace " Barkanka da Warhaka."
Turab wanda yasan dolene ya jira saboda mulki, yai murmushi sannan yace " na d'au lokaci kafin na kira Gimbiya, ina fatan za'amin afuwa."


"Hmmm za'a duba uzurunka sai a maka."
Turab ya kalli kofa dan yasan tabbas Magagiya zata leko dan ganin me yake yi.
Gefen fuskarsa ya d'am shafa sannan yace " Abubuwa ne wad'anda nikaina banyi tsamanni ba suka dinga bulbulowa wad'anda suka rike tunanina."
Tace " Hmm yanzu fa? Ka warware komai?"
Yai shiru, hakan yasa tace " Karka damu nasan zaka iya, koma menene, kardai kacemin baka yarda da kanka ba?"


Turab ya kalle gefen kofa inda ya hango inuwar Magajiya, yiyai kamar bai ganta ba, murmushi yai sannan ya gyara zamansa irin mai jin shaukin nan yace " Kuma fa haka ne, ya kamata in zama mutum na farko mai yadda da kansa."
Tace " A koda yaushe ka dinga tunawa ina tare da kai akan komai, duk da ayanzu bazan iya taimaka maka ba, bazan kuma iya kula da kai ba sai dai inaso kasa a ranka akwai wacce take tare da kai a koda yaushe."


Har zuwarshi sai da yaji wani sanyi ba shakka Bilkisu macece wacce ta san kanta ya tabbata zasu zauna lafiya, sannan yana ji a jikinsa ita alheri ce a gareshi.
Jiyai tace " kayi shiru? Ba dai kalamai na......"
Katseta yai da sauri yace " wannan layin nawa ne bance ki fada ba."
Tace " layin me?"
Yace " Kalamanki sun ratsani na kuma ji dadi, ba haka zaki ce ba?"


Bata san sanda tai dariya ba, tace " mene? Haka nace ma?"
Yace " sosai ma."
Gani inuwar Magajiya yai ta juya.
Fuska ta rufe kamar yana ganinta, Turab yace " zan kiraki zuwa ko zuwa anjima ko zuwa gobe."
Tace " Karka damu dani, yanzu ma da mukai magana ya isa, duk sanda ka samu sarari ka kirani."
Yace " Nagode, ki gaida Munnira."
Bai jira ta amsa da to ba ma ya ajiye kan wayar sannan ya mike.


Magajiya kam ta gama kuluwa da alama ma soyayya suke da yarinyar, itakam duk duniya ba wanda ta tsana yanzu irin wannan dan banzan yaran, ko ganinsa batasan yi, wai kamar ita ace ta zauna yaro yana raina mata hankali? Dolene ta nemi abinda zatai amfani dashi ko da yake ai ta shirya da auransa hmmm tai kwafa tace a ranar aure ka zai kasance jana'izar ka.
Ta na kokarin shiga d'akinta yace " Umma me kike anan?"


Juyowa tai fuskarta a had'e sai kuma ta saki fuska tace " Na d'auka ka tafi ai, ashe kana ciki?"


Turab yace " na d'auka zakizo ku gaisa da sirikarki, ko zaki koma in kira miki ita?"
Idanunta ne suka canza har fuskarta sai data nuna bacin ranta, daurewa tai ta saki yake tace " Meye abin azarbabi bayan nice shugabar kai lefe?"


Kai ya jinjina sannan ya dawo gabanta, fuskarsa a hade tare da kallanta.
Kallansa tai tace " ya akai kuma?"


Wani banzan murmushi yai yace " maganinki da kika sa a dinga sama Hajiya ina tunanin sai kinsa a nemo wani."


Idanunta ne sukai rawa alamar mara gaskiya tace " me kake fada?"
Yace " ba abinda nake fada ina dai sanar dakeni duk wanda ya maida Hajiya haka wallahi wannan rantsuwa ce nai bazan taba kyaleshi ba, sai na sa anmai hukunci daidai da abinda ya aikata, ko da kuwa Umma tace Basira ta aikata hakan, duk da nasan bazata taba zalintar d'an adam ba kamar wasu."


Magajiya ta kalleshi sannan ta saki wanj banzan murmushi na rainin hankali tace " Ko nima zan tayaka d'aukan hukuncin, sai dai ka tabbatar kana da karfi na hukunta mai laifin? Ba wai karfi na jiki nake nufi ba."
Turab ya kalli kwayar idanunta yace " Ahhh to wa ya sani?" sannan ya murmusa yace " kece kika sa aka fara game d'in, sai dai ni nake da ikon tsayar dashi, sannan inaso ki tabbatar idanunki na nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login