Showing 114001 words to 117000 words out of 146065 words
Chapter 39 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
da banso kisan abinda na sani ba sai dai kunnuwana sun gaji dajin muryarki tana cewa d'an da batasan zafinsa ba da sunan d'anta."
Idanu Magajiya ta zaro, a tsorace tad'anyi taku biyu baya.
Turab yace " me? Kina mamaki ne? Wato kinaso ki halaka asalin d'an sarki ki saka d'an d'anuwanki akan mulki shiyasa kika sa a kasheni?"
Magajiya bakinta ya fara rawa tace " bansan me kake cewa ba, sannan zance kasheka bansan wannan maganar ba, sai dai ka tambayi Hisham."
Turab ya kalleta yace " banyi mamaki ba, dan dama nasan cewa zakiyi shine ya aikata hakan."
Shiyasa ana sanar dani zuwanki nasa Garzali ya kirashi, bari yazo sai muji wanene yasa a kasheni, daga nan sai mu nufi turakar Sarki."
Magajiya tsoro da fargaba ne suka dinga ratsata, inza'asan komai nata bazai dameta ba amma banda sirrin Abdulmajid, komai zata iya kwatar kanta inhar d'anta nada matsayinsa.
Abdulmajid dake kwance a kan gado a hankali wasu zafafan hawaye suka gangaro mai.
Turab ne ya kalli kan gadon, ko tunanin me yai sai ya kalli Magajiya yace "ahhh yau Gimbiya zatazo banaji ya kamata in zauna anan, ina tunanin maganar a gida ya kamata muyi."
Ya juya da sauri yai waje.
A can gefe ya hango Khadija, gunta ya nufa fuskarnan a d'aure yace " Abdulmajid ya farka bayan na tafi?
Tace "a'a."
Bai jira mai zata kara cew ba yai gaba.
Dawowa yai inda take, kallansa tai, hannu yasa a aljihunsa ya ciro d'ankwalinta ya mika mata.
Ya juya yai gaba, bakinta ta saki tana kallansa.
Kallan bayansa tai har sai da ya bace mata, kwallar data zubo mata ta share.
Sannan ta kurama d'ankwalin ido, ita kanta dan dai ya bata d'ankwalin ne yasa tasan nata ne, amma ita kanta ta manta dashi.
Hawaye ne suka shiga zubo mata, in har Turab zai ajiye abinda ita kanta ta manta dashi to ba shakka yana santa.
Amma meye amfanin san da bata tashi sani ba sai lokacin da bazai mata amfani ba, ko da yaks da can ma ko ta sani ma ba zai musu amfani ba.
Jingina tai da bango tanajin zuciyarta na mata wani irin rad'ad'i na azaba........
*******
Magajiya kuwa Turab na fita ta rufe kofa da makulli ta zauna kusa da Abdulmajid tace " Uban waye ya isa ya ce ba ni na haifeka ba?"
Inhar kana tare dani ba abinda ba zan iya ba, dan haka ka gaggauta mikewa, Mairo kake so ko? Ka farka zan baka ita, mulki? wannan dama dole ne, sai me? Turab? Karka damu ko me zai faru sai naga bayansa, bazan taba bari yafadama wani sirrin nan nawa ba.
Ko mai zai faru banaso kasan komai, ni dai kawai ka tashi.
Sam hankalinta ya kasa kwanciya ganin Abdulmajid ko motsi baya yi.
Shi kuwa Abdulmajid samun kansa yai da Addu'a mara amfani, baisan sanda yace " Allah ka d'auki raina......"
*******
A can kano kuwa anata shirin zuwa kawo amarya, dan wasu ma yau da wuri suka taho dan kara gyara gidan Amarya da kara duba jeren da akai, Amarya Gimbiya Bilkisu kuwa yau tun safe ake ta gyarata, gyara mai sunan gyara na gargajiya bawai irin na xamani ba......
*TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*74*
Turab gidan Umma ya wuce inda take, yana isa ya tadda ta shiryamai abinci, nan yaci sannan ya kwanta akan kujerar falo.
Fitowa tai daga d'aki ta kalleshi tace " Turab meye hakan? Ta ya zakaci abinci ka kwanta?"
Mikewa zaune yai yace "Wlh Umma kaina kemin ciwo."
Zama tai gefensa tace " Ba dole kanka yai ciwo ba, tun da ka tafi d'aurin aure har yanzu banaji ka samu isasshen hutu na awa biyu cikake, ni na kasa gane me kake tayi a waje haka, gashi ni kace in zauna anan."
Turab ya kalli falon sannan yace "Umma ni dama ki dawo nan da zama."
Kallansa tai tace "akwai abinda kake b'oyemin ko?"
Turab yai kasa dakai yace " Ni Umma haryanzu Abba bai fad'amiki inda Hajiya dasu Lantana suke ba?"
Umma tace " Bai fad'amin ba, sai dai inaji kamar fa har yanzu jikin Hajiya ba sauki."
Turab yace "dama nayi tunanin haka, dan da ta warke da ta sanar dashi wani abu."
Basira ta kalleshi tace " me kenan?"
Kai Turab ya girgiza sannan yace " In kawo miki masu aiki daga can? Naga waccan kamar aikin zai mata yawa."
Tace " karka damu, ni ma zaman haka kawai damuna yakeyi, yanzu kai haka zaka zauna har a kawo Amaryar?"
Turab yace " name?"
Tace " ko ma dai menene, ka samu ka huta sosai kafin suzo, kar suzo suganka a haka."
Murmushi yai yace " a haka kamar ya?"
Tace " oho dai nidai na fad'ama in ba so kake su juya da ita suce dama Ashe Angon ba shida jini a jika."
Dariya ya saka sosai, yace " lalai Umma, kawai kice kinaso in huta amma wannan sharhin babu shi."
Tace " haka kace?"
Yace " hmm, ni kam Umma akwai abinda nakesan sanar dake."
Tace " name kenan?"
Yace " Umma so nake idan komai ya kammala in d'aukeki da Bilkisu muje kauyen da na taso."
Umma ta kalleshi cikin jin dadi, tace " Ni kaina inasan zuwa sai dai ina tunanin me zance ma Sarki."
Yace " ki jira in gama abinda nakeyi, sannan ki kara min addu'a akan Allah ya bani ikon gurfanar da masu laifi, ya kuma kareni daga sharrinsu, sannan karya bani ikon cutar da wasu saboda wani buri nawa."
Basira cikin kulawa take kallansa tace " Insha Allahu Allah na tare dakai, sannan muma bazamu daina maka addu'a ba."
Haka sukai ta dan hira sama sama kafin daga baya ya kwanta.
Bacci sosai ne ya d'aukeshi wanda shi kansa bai san jikinshi ya gaji haka ba.
Bai tashi ba sai karfe biyu na rana.
*********
A can gida kuwa Magajiya ce zaune a kuryar d'aki ita da Hisham ta kalleshi tace " Yaya Yaran can yasan komai."
Hisham yace " name kenan?"
Magajiya tace " yasan Abdulmajid ba d'ana bane."
Hisham yai kasa dakai wato shiyasa ya ce mai haka? Sanda ya koreshi daga asibiti?"
Magajiya ta kalli Hisham tace " yaya duk yanda za'ai inaso ka tabbatar baka bari an san nice na sa a kama Turab ba, inaso ka yarda akan kaine kai komai, ni zan san yanda zanyi karyai magana akan Abdulmajid."
Tsananin mamaki ne ya kama Hisham ya kalleta yace " ban gane ba?"
Tace " inaso ka ce kaine kasa a kama Turab in Sarki ya tambayeka, ni zansan yanda zanyi kar a hukuntaka."
Tsananin mamaki yama hanashi magana sai kallanta kawaj da yakeyi.
Magajiya tace " Sannan inaso a maida Khadija Kano, duk sauran matsalar daga baya ni zan san yanda zanyi, kai dai kai wannan abun guda biyu."
Ta mike ba tare da ta jira amsarsa ba tace " bari naje na kara shiryawa asibiti zan koma, dan bazan iya barin D'ana a can ba."
Hisham yabi bayanta kawai da kallo Baki a bud'e.
Ya dade a zaune kafin ya mike yai waje cikin tsananin takaici.
Gida ya wuce, ya shiga d'aki ya baza uban tagumi.
***********
Mairo kuwa tana gama aikin gida da takeyi tai wanka ta shirya ta cema Ummanta zataje gun Umma Basira, nan ta fito, sai dai me? Asibiti ta fara wucewa.
A jikin windown d'akin ta tsaya, ba kowa a d'akin, batai niyyar shiga ba dama, gani tai yana kokarin motsi da hannunsa da alama idanunsa a bud'e yake kuma abu yakesan d'auka.
Da sauri ta shiga ciki, yana jin motsi ya koma ya kwanta tare da rufe ido.
Mairo ta karasa gunsa da sauri tace " me kakesan d'auka?"
Ta fad'a tana kallan gefe, ruwa ta gani a jarka da alama shi yakesan d'auka.
Tace "Ruwa zaka sha?"
Jin shiru yasa ta matsa daf dashi tace " nice bakasan gani?"
Ganin bashida niyyar bud'e ido yasa haushi ya kamata ta juya zata tafi, jitai an riko hannunta.
Tsayawa tai ba tare da ta juya ba, Abdulmajid a hankali yace "Karki fad'awa kowa na farfado, na rokeki."
Cikin mamaki ta juyo ta kalleshi, gani tai yayi wani mugun fadawa, tace " bakasan asan ka farfado?"
Kai ya d'aga mata, tace "ban gane ba? Abinci fa? Ruwa fa? Kashe kanka kake sanyi?"
Maimakon taga ya bata amsa gani tai yana murmushi, tace " murmushi ma kake?"
Yace "in kina fada kyau kikeyi."
Kallan mamaki tamai, sannan ta d'auko ruwa a cup ta mikamai tace ungo.
Sam ya ma manta abinda ke gabansa ganin Mairo, yace " bazan iya tashi ba."
Harararsa tai sannan tace " ta ya ya ma zaka sha ruwa? Ai kullema ciki zaiyi."
Ta karasa tare da ajiye ruwan.
Inda kayayyakinsu yake ta shiga dubawa, kular abinci ta bude ta zubo shinkafa miya wacce taji naman kaji.
Abdulmajid yace " so kike inaci wani ya shigo?"
Tace " wai me ke faruwa?"
Idanunsa nd suka kada yace " ban cancanci cin abinci ba, magana ma bancancanci yimiki ba, Mairo."
Mairo ta kalleshi tace " nima ce maka akai ina san yi maka magana?"
Yace " haka ne, amma yanzu in wani ya shigo fa? Dan Khadija ma fita tai taje ta dawo."
Bata amsa mai ba kawai yaga ta kukule window ta sa sakata a kofa, sannan tazo ta taimaka mai ya zauna ta mikamai abinci.
Hannunsa ya nuna mata tace " to me kakeso ai?"
Yace " shiyasa nace bazan ci........"
Abincin data samai a baki ne ya hanashi karasa abinda zai fada.
Haka ta shiga bashi abinci, tana bashi ruwa, daga zaiyi magana zata ballamai harara.
**********
Turab na farkawa yaga Sabi'u a kujerar gabansa.
Kallansa yai yace " kai kuma fa?"
Sabi'u yace "gaskiya ban taba ganin ango irinka ba, ana can ana ta hidima a gidan sarauta amma kai baka nan, Ummanka bata nan, yayanka bayanan, nikam yau an ka wahalar dani."
Turab yai murmushi yace " dama ko muna nan ai jama'a ne masu hidimar ba mu ba."
Sabi'u yace " ka tashi ka shirya mu tafi, 'yan uwan Amarya sun fara zuwa.
Yace" to ni mai kake nufi inje?"
Sabi'u yace " au bazaka ku gaisa ba?"
Turab yace "amma lalai kafi kowa, a ina aka taba haka?"
Sabi'u yace " haba? Ba haka ake ba?"
Turab ya girgiza kai yace " kai in anzo naka kayi, yanzu ina Umma?"
Ya fada tare da mikewa.
Sabi'u yace "ta tafi gun 'yan uwan Amarya, tace in fadama inka tashi, insun watse ta taho."
Turab ya d'aga kai alamar gamsuwa.
Sabi'u ya kalleshi yace " dazu waziri ya aiko inje."
Turab yace " me yace?"
"yace zaiyi tunani akan abinda kace mai."
Turab yai murmushi a ransa yace " ko kayi tunani dolene ka amince da abinda nace dan nasan halin magajiya maida komai kanka zatai, in har kanasan taimakon d'anka da kuma kanka dolene kabi abinda nace."
Sabi'u ne ya kalleshi yace "me kace mai wai?"
Turab yace " ba komai."
Yai ciki.
Wanka yai ya saka kayan da Sarki ya aikomai.
Yadi ne mai masifar kyau, kallo d'aya zaka mata kasan tsadarsa.
Farin yadi ne, ya saka aikin babbar rigar kayan, yasa hula da takalmi ya fito.
Tafi Sabi'u ya saka yana ganinsa yace "kai Ango, yaufa ba dama, da alama Gimbiya yau sai an tausaya mata."
Turab ya kalleshi yace " yo ai dole a tausaya mata tunda Amaryar Sabi'u aka kai."
Sabi'u yace "anma kafadamin magana."
Haka suka taso suka fito.
""********
Zaune take a cikin mota, sai kuka takeyi, kanwar Fulani na gefenta da kishiyar Fulani.
Wani had'ad'an leshi na da mai nauyi da tsada, ta sanya, tayi kyau sosai da sosai sai dai kukan da takeyi yasa duk kwalliyar fuskar tata ta tafi.
Haka har suka isa garin na zazzagawa.
Suna isa gidan aka saki wani busa na sarauta.
Su Magajiya dama sun shirya dan tarbar ta, tana isowa suma suka fito suka zo inda suka tsaya.
Magajiya ta dafa ta saboda fuskarta a lulube take ruf.
Nan suka shiga har bangarenta, ana tafe ana zabga guda.
Magajiya na ajiyesu ta tabbatar komai ya kammala ta fito.
Tana san ganin fuskar Amarya amma hankalinta na gun Abdulmajid.
********
A asibiti kuwa Mairo tana gama bashi abinci, tana bashi ruwa aka fara kwankwasawa.
Nan ta tattare kwanukan ta ajiye a kasa, shikuma ya kwanta.
Kofar ta bude tana addu'a Allah yasa ba Magajiya bace.
Ajiyar zuciya tai ganin Hisham ne da Khadija.
Khadija ta kalleta tace " saukar yaushe?"
Mairo tace " d'azu, har abinci ma naci, dan sanda ma taho ban tsaya naci abinci ba."
Hisham ta gaida, jiki a sanyaye ya amsa ya shiga ciki ya duba Abdulmajid sannan yai waje.
Mairo ta kalli Khadija tace " are u okay?"
Khadija tace " name kenan?"
Mairo tai murmushi tace " yau ake tariyar ya Turab."
Khadija kanta ta sunkuyar sannan ta d'ago tace " ke zan tambaya ai duba da yanayin dake tsakaninku na shakuwa, ni dama mun dade a haka."
Mairo ta kamo hannunta cikin tausayawa ganin yanda idanun Khadija suka ciciko, tace " Khadija ya Turab na bala'in sanki, in nace so tofa so d'in gaske nake nufi, tun kina karama yake sanki sai dai da alama har zuwa wannan lokacin bai bayyana miki ba."
Kallanta khadija kawai takeyi, idanunta na zubo da kwalla.
Mairo tace " Ya Turab a matsayin kanwa ya d'aukeni, kece zabin ransa ban san me yasa soyayyar ku ta koma haka ba."
Khadija ta runtse ido tare da share kwallar ta tace " Mairo inaji dama can Allah baiyi akwai wata rayuwar jin dadi ta soyayya ba a tsakaninmu, soyayya ta zamantakewa bazata taba shiga tsakanina da yaya ba, mahaifina da Kanwarsa sun zalunceshi sunmai abinda na tabbatar bazai iya mantawa ba (nace wanda ma kika sani kenan), ta ina kuwa zamu iya zaman aure dashi?"
Mairo tace " to amma ai ba ke bace kikai, kuma laifin wani ai baha shafar wani."
Khadija tai murmushi tace " haka ne sai dai........."
Kallan Abdulmajid dake kwance tai, a lokacin ta tuno da kalaman Turab, a sanda take juyawa zata tafi d'azu daya ce ta fita.
Kamar Magajiya yake tambaya akan ciwon yaya.
Mikewa tai da sauri tai waje da gudu, Mairo cikin mamaki ta kalleta.
Abdulmajid na kwance duk yana jinsu, hawayen tausayin kansa dana kanwarsa ne ya ziraro mai ta gefe.
Khadija can ta hango mahaifinta da karfi ta kwalla mai kira, ko takalmi babu a kafarta.
Tsayawa yai yana kallanta, da gudu ta karaso tana hakki tace " Baba kai da Umma Magajiya kuna da hannu a ciwon Yaya?"
Kallanta yai sai dai baisan me zaicw ba, tace " Ya Turab kukaso ama haka, amma Ya Abdulmajid ya tare?"
Hisham ya kalleta yace " Khadija..." ya fada tare da kokarin kai hannu ya riko ta, da sauri tai baya tana zare ido tare da girgiza kai, dan yanda ya kira sunanta ta ya bata amsar tambayarta.....
*TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*75*
D'akin da Abdulmajid yake ta koma, tana shiga ta taradda Mairo dake tsaye tana jikin kofa da alama nemanta take.
Yanda ta ganta yasa tasan ba a hayyacinta take ba, Mairo ta ja hannunta ta shiga da ita ciki sannan ta zubo ruwa a kofi ta mika mata, tace " naga kina bukatar kad'aicewa ni bari na wuce."
Khadija bata tanka mata ba haka kuma bata sha ruwan ba sai daj yana rike a hannunta.
Tashi tai taje kusa da Abdulmajid tana kallansa, hawayene kawai yake zubo mata, ganin kukan na neman kamata tai ban d'aki da gudu.
Tana gama kukanta ta fara wanke fuskarta, taje zata bud'e kofa ta fito taji muryar Hisham na cewa Khadija? Da alama shigowa yai nemanta, bayan kofar bandakin ta labe da sauri, shi kuma jin shiru yasa ya d'an bud'e ban daki, da yake a rikice yake bai yi tunanin zata iya b'oyewa ba, kawai sai yai tunanin bata ciki.
Juyowa yai zai fita, Magajiya ce ta shigo, ko ta kanta baiyi ba ya fara kokarin wucewa, ba abinda ta tsana irin a ganta ai kamar ba'a ganta ba, a xuciye tace " Waziri meye hakan?baka ganni bane?"
Yace "na ganki, sai dai abinda ke gabana yasa idanuna suka rufe."
Ganin yana neman fita a xuciye tace " Yaya Tsaya!"
Tsayawa yai sannan ya kalleta yace " bakiji nace idanuna sun rufe ba? Alama ce ta ba lafiya ai."
Tace " wannan ba damuwa ta bace, damuwar ka ce, sai dai inaso in sanar ma inma ka nuna baka ganni bane saboda abinda na fadama na cewa ka tabbatar kace kaine sanadin komai, kake neman yadda ni to kada ma ka soma, ka fi kowa sanin nice yar uwarka kadai a duniya nice sirrinka kuma nice reshenka."
Ran Hisham yakai makura yace " reshen da bai dade ni da komai ba sai wahala? Sanar dani me wannan reshen yamin a rayuwa?"
Magajiya tace "mene? Ni kake fadama haka yaya? Ni kake tambaya me na maka? Duk daula da jin dadin da kake zaune a ciki waye sanadi? Kana tunanin karfinka da matsayinka ne yasa?"
Cikin takaici yace " daular banza daular wofi, daular data sa 'ya'yana suka tarwatse? Daular da ta ke rinjayata nake aikata abinda bashi bane? Daular da tasani kisan kai?"
Jikin Khadija ne ya kaure da rawa, batasan sanda ta tsugunna a bandaki ba, kisan kai?
Abdulmajid kam gaba d'aya jiyai gab'obin jikinsa sun daina aiki.
Magajiya ce ta sa dariya tace " ashe kasan da wannan, na d'auka ka manta da mumuman abinda ka aikata."
Hisham fuskarsa ta canza sosai yace " kina tunanin duk abinda nake miki kyaleki nake ko dan ina tsoranki? Dama ina jurewa ne saboda d'ana, yanzu kuwa abinda nake jurewa dominsa na kwance ba lafiya, kina tunanin akwai abinda zai tsayar dani?"
Kallansa tai tace " me zaka iya yi in baka jure ba? Sanar da abinda