Showing 144001 words to 146065 words out of 146065 words
Chapter 49 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
mutum na gari wannan shine burina."
Turab yace " Abdulmajid akwai sauran hukunci d'aya da bansanar a fada ba wato hukunci Matar Waziri."
Abdulmajid ya kalleshi.
Turab yace " na aika da takardar hukuncin ta gida saboda banasan asan matsayin laifinta."
Abdulmajid ya kalleshi sannan yace " ina tayaka murna Turab hakika ba wanda ya dace da wannan mukami na sarautar garin nan sai kai, nayi mamaki kwarai da abubuwan da suka dinga faruwa, lalai kai namiji ne, kaine kadai kuma Magajiya take tsoro a fadin duniyan nan, sannan hukuncin daka yanke ma kowa yayi daidai, Umman Khadija kuna ba sai na tambaya ba dan nasan bazaka yanke mata hukuncin da ya wuce laifinta ba, sai dai kayi mantuwa baka yanke min nawa hukuncin ba, dan kuwa nima na biyewa Magajiya, na kuma wahalar dakai kana yaro."
Turab ya kalleshi yace " wani hukunci kake nema banda wanda aka maka? Ka duka nan an maka wanda haryanzu ba ka tafiya? Kamin abubuwa a baya, sannan bazan boyema ba a baya ko had'uwa banasan muyi, sai dai ahankali ka wanke duk laifin da ka aikata mana, sai tausayinka da mukeji yanzu a zuciyoyin mu."
Abdulmajid yai shiru....
Turab yace " Umma na yanke mata hukunci na zama a cikin gidanta tare da kula da 'ya'yanta, ban yarda ta fito wajen gidan ta ba sai da kwakwaran dalili, sannan ko da wasa naji ance yaran gidan yayi laifi to fa lalai wannan hukuncin ita zanyimawa, wannan shine hukuncinta."
Abdulmajid yace " nagode kwarai Turab, nagode sosai....."
Sarki yai murmushi yace "Allah ya kara hada kanku."
Nace Amin......
*********
Sarki sun tattara sun koma gidansu, Umma kam ta kara yima Bilkisu nasiha sosai, sannan ta kara bata labarin tashin hankalin da suka fuskanta a baya, tundaga cikinsa, nan ta bata amanar Turab tace " ga Amanar d'an ta nan tanaso ta kukar mata dashi."
Bilkisu kam jikinta ya yi sanyi, jin gwagwar mayar wahalar da Turab ya shiga yasa ta kara jin wani sansa da tausayinsa na kara ratsata, ta kuma d'au damarar taimakamai da kula dashi har karshen rayuwarta.
Haka aka rakasu mota suka tafi.
Kwanasu biyu da tafiya Sarki ya d'auko Galadima sukaje gidan Barde.
Yayi mamakin ganinsu, nan aka kawo musu abinsha, aai da sukai hira sannan yace " dama yazo ne akan maganar auran Mairo da dansa Abdulmajid."
Barde yace " Abdulmajid?"
Sarki yace kwarai, domin kuwa d'ana ne ada sannan d'ana ne a yanzu.
Wannan kalma ta sa Barde bai iya cewa komai ba sai cewa yai " ai 'ya'yana 'yayanka ne, kanada hakkin aurar dasu ga duk wanda kaso, ba tare da ka tambayeni ba."
Nan aka bada kudin gaisuwa tare da amincewa.
Mairo ana d'aki dama tunda taji sunzo tasan mai ya kawosu dan dama Abdulmajid ya sanar da ita yanda sukai da Sarki.
***********
*Bayan Shekara D'aya*
Idanunsa ya bud'e a hankali tare da kallanta, baccin ta take sosai murmushi yai tare da kokarin zare hannunsa.
Sa hannunta tai ta rike hannun tare da kara gyara kanta, a hankali yace " Princess idanki biyu?"
Kai ta girgiza alamar a'a.
Ya sake murmushi yace " ba idanki biyu ba amma kike magana?"
Kai ta d'aga mai alamar eh.
Yace " so nake in duba wasu takardu da aka kawomin jiya, sannan kinsan gobe zamuyi baki daga kasar America zasu shigo garin."
Idanunta ta bud'e ta kalleshi tace " Kullum fa baka kwanciya da wuri sannan da wuri kake tashi, baka tunanin babyn ka na san jin diminka?"
Jawota yai jikinsa sannan yasa hannu kan cikinta yace " in mace ce nasan zatawa mahaifinta uzuri dan tasan ba laifinsa bane, in namiji ne kuwa dama dolene yamin uzuri tunda dai lokaci ne zai juyo kansa."
Kallansa tai tare da dan harararsa na wasa, murmushi yai sannan yace " zan duba takardun na awa biyu kafin nan kin kara samun bacci sai muyi hira ta awa biyu, sai in fita fada, hakan ya wanke laifina?"
Tace " ya wanke kadan." ta karasa maganar tare da nuna karamin d'an yatsanta.
Mikewa yai ita kuma ta gyaamra kwanciyarta tana kallansa, kan carpet ya zauna inda karamin tebirinsa yake ya shiga duba takardu.
Tunowa tai da abinda ya faru shekaranjiya.
An turoma Turab wasikar hada aure tsakaninsa da masarautar Bauchi, jin hakan ne yasa ta tambaya akan Khadija.
Jitai ancemata ai Khadija tana nan agida, saurayin dake santa Saifullahi duk yanda yai taki amincewa dashi, ita tace zama zatai suyi hukuncin mahaifiyarta tare dan laifin iyayenta nata ne, jin wannan maganar ne yasa Bilkisu ta tabbatar da hankalin Khadija kuma tabbas dolene yau ta tuntubeshi da maganar.
Tana wannan tunani bacci yai gaba da ita......
Awa biyun na cika ya kalli agoggo sannan ya mike yai wanka, yana fitowa daga toilet ita kuma tana bud'e idanunta.
Kallan sa tai sannan ta kalli agoggo a hankali ta sakar mai wani murmushi, sannan ta mike tare da saukowa daga kan gado.
Towel ta d'auka ta cire kayan jikinta ta d'aura.
Yana tsaye yana kallanta, tana kokarin yin hanyar toilet ya sa hannu ya jawota jikinsa, d'agowa tai ta mai wani murmushi bakinsa ya saka a cikin nata..............
Sai da sukai wanka suna zaune akan kujera tana tayashi duba wasu takardu, ta kalleshi tace " in na tambayi labarin Khadija yanzu za'a sanar dani?"
Kallanta yai sannan yace " me kike san ji game da ita?"
Tace " ko mai."
Murmushi ya mata sannan yace " in kika ji haushi fa?"
Tace " hmmm nasan zanji haushi sai dai ba kamar da ba, a da banida hujjar amincewa akan inada wani matsayi a zuciyarka, sai dai yanzu nasan ko ya ya ne akwai ni a ranka, bazan nemi hada matsayin san da kakemin ba da wanda kake mata, sai dai zanyi kokarin fahimtar girma da darajjarta a gunka."
Murmushi yai sannan yace " kamar yanda kika sani sunanta Khadija............" haka ya kwashe labarinsu da Khadija da irin rabuwar da sukai.
Kallansa tai, gaba d'aya yanayinsa ya canza ba shakka itace First Love dinsa, sannan san da yake mata mai zafi ne, duk da dai yana kokarin b'oyewa sai dai yau ta fahimci dalilun da yasa yake san yarinyar dan tabbas labarinsu mai ban tausayine, ta kuma fahimci dalilin rabuwarsu.
Kallansa tai tace " saboda laifin iyayenta ka hakura da auranta? Abdulmajid yana can da matar da yakeso suna rayuwarsu ita akan me bazata samu farin ciki ba?"
Yace " me kikeso mu sanar ma 'ya'yan da zamu haifa tsakaninmu?"
Tace " Baka ganin bakuyi wa kanku adalci ba? Sannan shi aure rabone in har Khadija matarka ce to tabbas sai ka aureta ko ta wani hali ne."
Kura mata ido yai yana kallo kafin yace " Princess."
Tace " Kada ka nemi bijerewa ikon Allah, ni zan sanar ma Abba sannan za'a tura neman auranta, sai a d'aura auren tare da kanwar sarkin Bauchi, in har matarka ce zakaga abin ya faru in har ba matarka bace saikaga an warware cikin ruwan sanyi."
Turab ya kalleta sannan yai murmushi zaiyi magana tace " Please!"
Kasa magana yai sai jawota jikinsa dayai......
**********
Ajiyar zuciya yai cikin sakalci yace " Maryam ni wlh yau na gaji, ba gashi ina iya mikewa ba?"
Hararsa tai tare da had'e rai tace " zamuje ko sai nayi fishi na?"
Hannu yasa ya kamo kugunta tare da kwanciya akan cikinta yace " Maryam ni....."
Tace " sakeni."
Yace " naji mu tafi to."
Murmushi tai sannan tace " ko kaifa, bakajin rashin dadi in kaje gun aiki kullum sai Habu na kanka?"
Yace " haka ne, na dai so yau d'in ne inzauna dake....."
Tace " duk zaman da muke tare?"
Yace " to muje......"
Haka suke rayuwarsu cikin farinciki dan Abdulmajid na tsananin san Mairo so mai tsanani kuwa, ita kanta gaba d'aya ta maida hankalinta gun kula da shi.
Har dai wannan lokacin Allah bai bata ciki ba.
Dan yanzu wata na 6 kenan da auransu.
************
Yau 'yan America sun zo daga kasarsu, magana ce sukesan suyu da Mai Martaba Sarki Turab, bayan sun gama maganarsu ne suka fito gari dan zagaya wa dasu, akan irin kujerar nan ta doki yake suna tafe mutanen gari an taru ana kallan Sarki.
Tahuwa tai da gudu ba tare da an fargaba, dogarawa sam basu kula da ita ba sai gani sukai tana neman karasawa gun Sarki rike da wuka, kayan jikinta duk sun kode wani gun duk a yage yake, kakari take tana neman sukarsa, ana riketa, Turab jin hayaniya yasa ya juyo, Magajiya! Mamaki ne ya kamashi, gaba d'aya in ba ka santa ba sosai, bazaka taba cewa ita bace, ta rame ta gama fita hayyacinta, 'yan gari kam ganin za'a farma sarkinsu yasa suka fara jefanta da dutse.
Dogarawa suka hankadeta da karfinsu cikin takaici.
Jifanta ake, duk yanda Turab yaso ya hana ai inaa saboda yanda take kara yunkurowa zata kasheshi.
A take a gun rai yai halinsa, yana gani suka wuce ba tare da sun kalli gawar ba, sai turawa yai akan a mata sallah A kaita makwancinta.
Allah ya mana cikawa mai kyau Amin suma Amin.
***********
Bilkisu da kanta ta samu Umma ta sanar da ita sannan ta kara neman shawara, dafarko Umma tayi kokwanton amincewa duba da abinda ya faru, sai dai Bilkisu ta nuna mata shi laifin wani baya shafan wani ko a gun Allah ne, sannan iyayenta laifi sukai aka hukuntasu bawai yin kansa bane.
Wad'annan dalilai ne yasa jikinta yai sanyi itama ta duba yanda tasan Turab nasan yarinyar hakan yasa ta sanar da Sarki.
**********
Yau yana zaune acikin gun hutawar sa, a gaba da gidan Sarki Abdussamad kadan gun yake, Bilkisu ce ta takura akan sai ya kaita gun, shiyasa suka fito bayan magrib, gashi ta shiga gunsu Umma.
kwantar da kansa yai jikin kujera tare da lumshe idanunsa, rayuwa yake tunowa, sannan yau ya tura Sabi'u kauyen garin da suka zauna d'auke da sha tara ta arziki, shi da Lantana suka tafi dan kai musu tare da mika musu sakon gaisuwa da godiya.
Lalai rayuwa ba'a bakin komai take ba, karasowa tai gun tare da kallansa, ganin tabbas shi din ne yasa tai saurin juya baya zata juya, jin motsi ne yasa ya bud'e idanunsa.
Bayanta kawainya kalla ya gane itace, a hankali yace "Khadija!"
Juyowa tai ta kalleshi, kallan juna suka shiga yi dan tabbas raban da suka juna sun dade, daurewa tai tace " Aikowa akai akan inzo inji Umma Basira, sannan akace tana nan......."
Kallanta yake kamar bashida niyyar maganar, yawo ta had'iya sannan tace " kayi hakuri inaji ba'a nan take nemana ba."
Juyawa tai zata tafi, a hankali taji yace " Guna ta turoki, ganin ni hidimomi sun hanani zuwa sannan bansan me zance miki ba in mun hadu."
Juyowa tai ta kalleshi idanunta sun ciciko tace " ni kaina bansan da wace kalma zan fara ma magana ba, abubuwa dayawa sun faru wanda na hana kaina fita saboda hakan, raban da in fita waje ni kaina na dade, sai yau da Umma ta aika inzo."
Alama ya mata akan tazo ta zauna gefensa, kallansa tai tace " Ranka ya dade amma...."
Yace " haka kike kirana da?"
A hankali tace " Ya Turab."
Yace " zo ki zauna inji ya bayan rabuwa......"
Bata tako ba tace " Ya Turab mai zance?"
Hawaye ne taji suna neman zubo mata, da sauri ta juya bayanta.
Tausayinta ne ya kamashi dan tabbas taga rayuwa, ba ita tai laifufuka ba amma duk sun shafeta, hakika duk ta rame ta canza ba shakka tana cikin wani hali.
Mikewa yai ya dawo gabanta yace " Haryanzu saurin kukan na nan?"
Tace " Yaya ni......" sai kuma ta kasa karasawa, yace "ke me?"
Kallansa tai cikin kalar shagwaba tana san tai magana, yanda yake kallanta yasa tai murmushi, shima murmushin ya sakar mata...........
*ALHAMDULILA*
_Dukan Godiya ta tabbata ga Allah Ubanngijin talikai, muna neman tsari daga gareshi, Allah ya mana mai kyau, ya bamu ikon fin karfin zuciyoyin mu, ya sa mu a hanya madaidaiciya, shi ke shiryar da wanda yaso a kuma lokacin da ya so, ya Allah ka mana mai kyau ka kara karemu daga sharrin zuciya ka bamu ikon kyautatama iyayenmu.
Yanda zamu fara azumi lafiya Allah kasa muga karshensa lafiya, ya bamu ikon yin ibada yanda ya kamata._
(Ameen suma Ameen)
*Godiya ta musamman ga duk masu karanta littafin nan musamman yan Wattpad, da Whatsapp tnz alot, naji dadi kwarai yanda kuka kaunaci littafin nan.....*
Abinda nai kuskure a ciki Allah ya yafemin, abinda na fada daidai Allah ya bamu ikon yin amfani dashi.
Double thanks to all My Fans, I really appreciate ur love.....
*SARKI TURAB*