Showing 9001 words to 12000 words out of 146065 words
Chapter 4 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
zai baka mamaki kan kace me? Labari har ya cika gidan, Jakadiyar Sarki kam tana jin wannan labarin ta garzayo gun Basira sai data tabbatar sannan ta tafi gunsa yana fada ta sa a sanar mai.
Magajiya kam tana shiga d'akinta ta dafa kanta wanda ke sarawa, idanunta sunyi jaa sosai lalai dabadan tun tana karama an hanata kuka ba lalai yau da sai tayi, sai dai itakam batasan kuka ba, ko da mahaifinta ya rasu batai ba.
Lami ta kalla tace a kira Ya Hisham.
Nan Lami tai waje da sauri ta aika a kirashi.
Hisham na fada ya samu sakon kanwarsa da sauri ya mike ya nemi izini ya taho, a waje yaga mai magani hakan yasa yai tunanin ko batada lafiya ne.
Murmushi yai sannan ya shiga, a tsaye ya ganta ta juya baya.
Nan ya canza fuska cikin kalar damuwa ya matso kusa da ita ya zauna yace " Magajiya lafiya?"
Juyowa tai cikin takaici ta zauna a gun zamanta sannan ta kalleshi tace " ciki gareta."
Cikin rashin fahimta yace " wa kenan?"
Lami tai caraf tace " Basira Amaryar Sarki."
Tashin hankali Hisham ya mike da sauri cikin tsananin mamaki da tsoro yace " ban gane ba? Magajiya ba kince bai kusanceta ba?"
Sosai ya damu dan babban burinsa bai wuce yaga d'ansa akan mulki ba, Magajiya ta runtse ido cikin takaici tace Jakadiya ce ta fadamin.
Shiru sukai kafin daga bisani Hisham yace " ya zama dole a zubda cikin kafin yai kwari."
Magajiya tai shiru sannan tace a kira mata mai magani.
Mai Magani ta shigo cikin farin ciki, gaban Magajiya ta tsugunna.
Magajiya ta kalleta yace " shekararki nawa kina aiki a gidan nan?"
Cikin zumud'i tace "40."
Magajiya tai murmushi tace " muhallin zama fa?"
Tace " a wani d'an daki muke takura nida mijina da 'ya'yana."
Magajiya ta kalleta tace " Zubar dashi."
D'agowa tai da sauri tace " me fa?"
Hisham yace " ke kika dubo tana da ciki hakkinki ne kisan yanda kikai kika zubar dashi, in har kinasan ki cigaba da aikinki kuma kinasan muhallin zama mai kyau ke da iyalanki."
Cikin tsoro tace " Waziri tuba nake amma tayaya zan zubar da kwan Sarki?"
Hisham yace " ruwanki ne ki zubar ruwanki ne ki barshi sai dai 'ya'yanki ina tabbatar miki zasu fuskanci gararin rayuwa dan ko aure basu isa suyi ba in har sun zauna da ransu kenan."
Cikin tsananin tashin hankali ta d'ago ta kalli Hisham.
Lami tace " kinaso mahaifiyarki dake kwance ba lafiya ta rasa inda zata zauna? Ke kuma ki rasa sana'arki?"
Kai ta shiga girgizawa, Lamibta cigaba " in har kinaso bakin ciki ya kashe mahaifiyarki kar kiyi abinda aka saki."
Ganin ta rikice tana roko yasa Magajiya tace " kwana bakwai, kwana bakwai kacal na baki ki tabbatar kin kawon magani mai karfin da zai tafi da cikin, kar kuma kiyi tunanin bazan gane ba dan sai nasa ankai gun mai maganni ya tabbatar da hakan."
Kanta ta shiga d'agawa nan aka sallameta.
Tana fita Lami tace " zatabi umarnin mu?"
Magajiya ta juya kai batace komai ba.
Magajiya tasa a nemo Jakadiya sai dai sama ko kasa an nemeta an rasa bat ta bata dan bata gidan sam.
**********
Sarki kam yana tasowa daga fada yasa a kiramai Basira, dan da shi yaso zuwa ma sai Barde yace in yaje za'ai tunanin yafi san Basira ne wanda hakan zaisa matan su fara tsanarta.
Farincikinsa ma yau kwanan ta ne, tunda yai sallah ya kasa tsaye ya kasa zaune sai jeka ka dawo yakeyi, yana nan a tsaye har ta iso.
Tana shigowa tun bata karasa ciga cikin d'akin ba ya karaso ya rungume ta tsam wani irin nishadi da jin dadi na ratsashi.
Bayan ta zauna ya sa hannunsa akan cikinta cikin tsananin murna, itakam kanta na kasa tana murmushi, cikin tsananin farin ciki yace " in Allah ya saukeki lafiya in har Mace kika haifa zan sa mata suna Fatima Zahra wato 'yar Manzon Allah in har kuma Namiji ne zan sa mai *ABU TURAB*."
Cikin muryarta mai sanyi tace " Har ka zabi suna?"
Yana murmushi yace " sunayen dana fi so kenan haka kuma fatana in ga na saka wad'an nan sunayen."
Murmushi tai sannan tace " meyasa baka sama d'an ka na farko ba?"
Yace " ai shi magaji ne shiyasa na samai Abdulmajid, tun daga kan mahaifinmu ake sa ma Magaji Abdul a gaba."
Murmushi tai sannan ta kara sadda kanta kasa.
Dadi ne ke ratsashi hakan yasa ya kara jawota jikinsa lalai baiji haka ba sanda Magajiya zata haihu, yau jinsa yake daban lalai yana cikin farin ciki.
_Hmmm Allah yasa farincikin ya d'ore_
*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼♂*
*7*
Magajiya tasa Aunty Lami akan duk wani magani datasani ko wani mai bada magani data sani ta je ta amso mata maganin da zai kawar da wannan cikin, babu makawa sai ta sa cikin nan ya bi shada dan itakam bataga wanda ya isa ya haihu ba a gidan, dan kuwa bazata tab'a iya jurar ganin yaro na yawo a gidan ba a matsayin d'an wani ba, ba nata ba.
Basira tana kwance a d'aki tun safe ta kasa cin abinci, sallamar baiwar ta ce wato lantana yasa ta mike zaune, Lantana ta karaso ta gaidata sannan tace " Ranki ya dade Magajiya ta aiko miki da magani da kuma abinci."
Basira tace " nakoshi Lantana sam banajin cin abinci."
Lantana ta matso tace " Kinsan bazataji dadi ba in taji bakici ba kinga na jiya ma data aiko bakici ba sai dataji ba dadi."
Basira tace " to ke kici mana?"
Idanu Lantana ta zaro tace " so kike a yanken hukunci mai karfi? Magajiya ce fa ba wani ba."
Zata sake magana sai ga Aunty Lami ta shigo ba ko neman izini, tana shigowa ta matso kusa da Basira fuskarta a sake aosai tace " haba 'yata tashi ki daure kici mana, ko so kike hankalin Mai Martaba ya tashi?"
Da sauri Basira ta jijiga kai alamar a'a, Aunty Lami tasa aka kawo abincin da kanta ta bata sai dataga taci sosai sannan ta bata maganin da aka kirashi da sunan maganin dazaisa taji karfin jikinta."
Ta dade a zaune ganin Basira ma baccinta take shara yasa ta fita daga d'akin.
*******
Zaune take gaban Magajiya wacce itama shiru tai tana tunani, can Aunty Lami tace " amma Mai maganin nan na kan tudu ya rainamin hankali, sai fa daya tabbatarmin cikin minti 15 zata fara fitsari akai akai in har naga haka inbata kwana d'aya cikin zai zube dan dama nacene ya bada wanda zai dan d'au lokaci kafin cikin ya zube kar a gane."
Magajiya tai tsaki tace " mai Yaya yakeyi?"
Da sauri Lami tace "ya tafi Daura anso wani maganin."
Magajiya tace " itafa matar nan ga gidan nan?"
Lami tace " ita kuma tace a bata zuwa gobe."
Magajiya tai d'antsaki tace nifa banasan jan abin nan dan ji nake kamar akan bushiya nake a zaune."
Lami ta matso tace " karki damu 'yata....."
Wani kallo Magajiya ta mata wanda yasa tai shiru, kanta Magajiya ta juya gefe sannan tace "kayan abincin dana aika ya karene?"
Lami ta d'aga kai, Magajiya tace " zan aika da wani amma sai hankalina ya dawo jikina." dan dama ta sani da zarar taji Lami ta fara cewa 'yata tasan abu take nema.
Basira kam ta fahimci Magajiya ce kawai ke santa a matan sarki dan su kiri kiri suke nuna mata kishin cikin nan, dan haka duk abinda aka aiko mata daga bangaren Magajiya bata wani kokonto take ci.
Mahaifiyar Sarki wacce ta tsufa itama bata gazawa gun aikoma Basira kayan marmari.
Shikam gogan wato Sarki kullum sai yayi aike sau uku akan a dubo lafiyarta, wannan al'amari ya kara dugunguza hankalin Magajiya dan kuwa an sanar da ita, to ita ke yasa sanda akace tana da ciki baya mata wannan aiken? Tsanar Basira da abinda ke jikinta ya kara tsananta a ran Magajiya.
Yayanta ya dawo d'auke da magunguna kala kala nan ya zauna yama Lami bayanin komai, nan ita kuma ta shiga yin hidimominta.
A ranar da aka fara bata maganin an saka mata shine a cikin miyar kubewa d'anya, san tuwo da takeyi yasa taci tuwon nan sosai, sai dai me? Tunda ta kwanta bacci ta ke juyi a kan gado, tsananin ciwo da mararta keyi yasa tai ta murkusus, da sauri Lantana ta fita ta karasa b'angaren Sarki nan ta aika a sanar mai.
Ranar kwanan matarsa ce ta biyu, ai ko fadamata baiyiba yai waje da sauri, sun iso bangaren Basira lokacin ciwon ya mata yawa dan ta fad'o ma daga kan gado, jini ne ya fara zubo mata wanda hakan yasa hankalinta yai tsananin tashi.
Sai dai tsananin ciwon da takeji yasa ta kasa magana, shigowar Sarki ne yasa ta daurw ta fara kokarin mekewa, da sauri ya karaso ya rungumota jikinsa, hawayene kawai ke zubo mata a hankali take cewa "shikenan cikin nan ya tafi shikenan nikam na baka kunya...."
Hannu yasa da sauri ya toshe mata bakinta sannan ya kara jawota jikinsa, d'aya daga cikin bayin Basira wacce Magajiya ce ta turota b'angaren dan kai mata rahoto.
Da sauri ta zame jikinta tai bangaren Magajiya.
Tana shiga ta zayannema Lami halin da ake ciki, da sauri Lami ta shiga ciki ta sanar da ita, ajiyar zuciya Magajiya tai tace " yau da alama zan samu bacci mai dadi."
Lami ta saki dariya tace " nikuma gobe za'a sallameni ko?"
Kanta ta juya gefe bata amsa mata ba sai murmushin jin dadi data saki.
Basira kam tana jikin Sarki ganin ciwon ya lafa yasa ya kira Lantana yace ta taimaka mata ta gyara jikinta.
Basira tana mikewa Lantana taga yanda jini ya zuba sosai, salati ta shiga yi, Sarki ya kalli gun dan harshima ya b'atashi, Lantana ya kalla ya mata alama da ido akan tai shiru hakan yasa tai shiru itakam Basira hawaye kawai take yi.
Shiru yai bayan sun shiga b'and'aki, ji yai idanunsa na neman canzawa, kallan jinin yai yanajin wani abu na tasomai na bakin ciki, ba shakka yasa rai sosai akan cikin nan, yana nan a zaune Lantana ta fito ta debi kaya ta koma.
Can sai gasu sun fito, kuka sosai Basira takeyi wai tana bashi hakuri, mikewa yai yaje kusa da ita ya jawota jikinsa yace " karki damu Allah zai bamu wani."
Shiru tai batace komai ba, ya daure yai murmushi yace " kishirya gobe insa a maidake gida gun Amadu inkin warware sai insa azo a d'aukeki.
Kallansa tai cikin mamaki tace " akan me?sakata kai?"
Dariya yai sannan yace " wani irin saki kuma? Ai ba saki a auranmu cewa nai dai kije inda zaki samu kulawa sosai sannan za'a dinga d'ebe miki kewa, sai ku shirya ku tafi da Lantana."
Murmushi tai sannan ta sunkuyar da kanta kasa.
Magajiya kam an tabbatar mata ciki ya zube shine ma dalilin tafiyarta gida, nan ta aiko mata da kaya kala kala wai ta kai gida, masu murna nayi masu bakin ciki na yi na tafiyar cikin nan.
Sarki ya cika musu mota da kayan abinci ya kuma bata kudi sosai yace " zai zo sai dai bai san yaushe ba."
Sun shirya sun kama hanya.
**********
Matar Amadu kam bata yarda cikin nan ya tafi ba ita kanta basira ganin cikinta na kara tasowa yasa tasan cikin nanan, sai dai ba yanda zatai ta sanar da Sarki tunda dai ba salula babu kuma wanda zata aika, sai dai ta zauna zuba ido akan sanda zai zo.
Matar Amadu dashi Amadun tunda sukaga cikin Basira nanan suka d'aura himma sosai na kula da ita hakama Lantana sosai take kula da Basira.
_Wannan kenan_
( _Dan Allah kuyi hakuri da wannan wlh yau abubuwa ne suka cud'emin da kyar na samu nai wannan, Nagode kwarai_)
*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼*
*8*
Shiru shiru ba sarki ba labarinsa wanda hakan ya kara d'agama Amadu rai gashi lokacin Basira cikinta yakai wata 9, ganin kar Basira ta haihu ba tare da sarki yasan komai ba yasa Amadu ya shirya tsaf ya nufi garin Zariya a akuri kura.
Sai yamma liss suka isa, gidan Sarki ya wuce.
A b'angaren Mai Martaba kuwa aiyuwa sun cab'e mai a fada wanda ya rasa yanda zaiyi, yaso ya aika aje q dubo Basira sai dai Barde ya bashi shawara akan ya kara jinkirtawa ganin kar a gane tsananin san da yake mata wanda kan iya jawo mata tsangwama in ta dawo.
Yau ma kamar kullum yana zaune a fada ana ta fama kawo kara yana hukunci, wasu kuma neman taimako suka zo yi wasu kuma sulhu da dai sauransu, ganin yamma tayi sosai yasa ya sallami kowa akan a dawo gobe, shigowar bafadansa ne yasa ya kalleshi, bafadan ya sanar dashi zuwan Abokin nasa kuma sirikinsa, nan ya bashi izini da sauri.
Amadu ya shigo kansa na kasa sai daya gaidashi tukunna, Sarki ya nemi a basu guri, suna fita ya kalli Amadu yace " Amadu ka jini shiru ko? Wlh al'amura ne suka c'abe min gaba d'aya.
Amadu yace bakomai sannan ya d'ura da cewa " dama zuwa nai na sanar dakai Basira ta shiga watan haihuwa."
Mamaki ne ya kamashi wanda sai da ya bayanna a kan fuskarsa yace "Haihuwa kamar ya?"
Amadu yai murmushi yace "ai cikin bai zube ba."
Mikewa yaga Sarki yayi da sauri ya shiga matse hannayensa yama rasa mai zaiyi can ya matso jusa da Amadu ya d'agashi tsaye ya rungumeshi kam yace " Basira ta kusa haihuwa kenan?"
Amadu yai murmushi yace "kwarai kuwa dan tama shiga watan, haihuwa yau ko gobe, nima sai da Matata ta sanar dani ta kula Basira ta kusa haihuwa sannan nace to ya zama dole yanzu kam inzo in sanar dakai."
Abin mamaki kwalla ne ya taru a idan sarki hannu ya d'aga ya shiga godema Allah.
Abin mamaki fadawa da bayinsa dake waje nan a ka fara zamewa kadan kadan an tafi kai gulma (lol.....)
Sarki yace "aikam yanzu dakai zamu tafi muje in d'aukota."
Amadu yai dariya yace " kai da kake fama da aiki sai dai ka tura kawai a d'aukota."
Shiru yai yana tunani can yace " ka kwana anan zuwa gobe zansan yanda za'ai."
Magajiya na zaune zance ya zo mata, tashin hankalin da ba'a kwatantashi, ba shakka tashin hankalin data shiga ya wuce duk yanda mai karatu zaiyi tunani tana tsaye jitau jiri ma na neman d'ebanta, Hisham kam ba kanta dan kuwa magana ra baci, tsantsan tashin hankalin da ya shiga ya wuce misali.
Gun Magajiya ya taho a sukwane, sunyi jugum jugum su biyu a d'aki, can Magajiya tai d'an ajiyar zuciya sannan ta kalli Hisham tace "duk laifinka ne, kaine ka tabbatarmin maganin nan ba karya ko wasa a ciki."
Hisham yai shiru can yace " duk ba wannan bane abinyi yanda zamuyi yanzu shine abinyi."
Magajiya tai shiru tana tunani, Hisham yace " bafa zai yiwu mu bari a haifi yaron nan ba in ma mace ce da sauki to amma ina muka sani?"
Magajiya cikin kufula tace " aikin gama ai ya riga ya gama kanaji ance ta shiga watan haihuwa?"
Da sauri Hisham yace " to sai me? Ai ko haifarsa tai sai mu halakashi."
Kura mai ido tai can tace " kisa kake so muyi kenan?"
Hisham ya share zufa sannan yace " ai da din ma kisa ne, in kuma kina ganin ba wani abu to shikenan kinfi kowa sanin Abdulsamad haka kawai bazai ba Abdulmajid mulki ba dan yana na fari ko yana d'anki ba."
Shiru tai tana tunani kafin tace " banasan irin wannan maganar ka fita ka bani guri in na gama yanke hukunci zan kiraka."
Mikewa yai ya fita rai a b'ace.
Magajiya ta dade tana tunani kafin daga bisanj ta mike ta fito.
B'angaren Sarki ta nufa, yana turakarsa banda farinciki ba abinda yakeyi, neman izini da akai akan isowar Magajiya yasa gyadan had'iye abinda ke fuskarsa.
Magajiya ta shigo cikin tafiyarta ta isa,zama tai a inda ta saba zama sannan ta kalleshi tace " ina cikin tsananin farin ciki Mai Martaba, nasan ban kaika ba amma natabbata ina bayanka."
Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa na tsantsan farinciki yace " nagode Magajiya."
Murmushi itana tai sannan tace " ka gode dame? Abinda za'a haifa kamar d'ana ko 'yata ne zan kula da abinda aka haifa kamar nice na haifesu."
Kallanta Sarki yai sai dai yau idanunsa ya rufe har ransa yake jin dadin maganar ta.
Magajiya ganin ta kamo lagonsa ta cigaba " shine nake tunanin kai ka zauna saboda hidimar dake gabanka inyaso waziri sai yaje ya taho da ita."
Sarki ya kalleta zaiyi magana tace " menene amfanin waziri? Dole ne ya wakilceka ko ya taimaka maka alokacin da kai kake wani abun, banaso mutane su fara tunanin kafinsan matarka a kan talakawa da mutanenka."
Shiru yai yana tunani ba shakka hakan data fa'a shine gaskiya, ya kalleta yace "haka ne sai dai bakya tunanin Hishan zaiji ba dadi ganin kishiyarki ce?"