Showing 129001 words to 132000 words out of 146065 words
Chapter 44 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
tunda na riga nasan abinda ke faruwa."
Yace " me kika sani hajiya?"
Tace " kasan komai ko? Wannan shine yasa nake tsoro saboda wannan matar batada imani ko kad'an, na tabbata bazata taba kyaleka ba."
Yace " Hajiya karki damu, ba ta isa tamun abinda Allah bai mun ba, in har wani abu kuma ha sameni to tabbas kaddara tace bawai wani abun ba, karkisa wannan a ranki."
Tace " Turab kana tunanin taimakawa yarinyar nan da kake hakan shine daidai? Karfa ka manta itace ta dinga zubamin magani
"
Yace " na sani hajiya hakan ne ma ya sa naji taimakon take bukata, Da ace mun farga ko munsan halin da take ciki mun taimaka mata da wuri banaji Magajiya ta isa ta sa ta wannan abin, sai dai ganin tana cikin hali na bukata yasa takejin zata iya yin komai.....
Hajiya kallansa kawai take cikin jin dadi.
********
Yau ma a kasa ya saukar da filonsa ya kwanta, tana kan gado a zaune ta kalleshi tace " ka dawo nan, ni sai in sauka kasa."
Kallanta yai yace " so kikeyi gobe in ziyarci asibiti?"
Tace " saboda me kenan?"
Yace " kin taba kwana a kasa?"
Tace " zan fara yau."
Murmushi yai yace " ke dai ki kwanta a inda kike kafin ki tada mana hankali da ciwon baya da gab'obi."
Kallansa tai tace "kai ma ciwon bayan kakeyi?"
Gani tai ya kwanta sannan ya ce wash Allah na, cikin irin muryarnan ta marasa lafiya.
Hankalinta ne ya tashi, da sauri ta sauko inda yake ta zo ta sa hanny tad'an d'agoshi tace " Lafiya? Menene?" duk ta rikice."
Idanunsa ya bud'e sannan ya mike ya zauna yace " yanzu in ni ina namiji daga kwanana a kasa na fara ciwon baya ai na zama rago."
Harararsa tai tace " yanzu nan d'in kenan zolayata akai?"
Dariya ya guntse yace " a'a"
Hannunta data ririkeshi ta nemi zarewa tare da had'e rai, hannu yasa ya rike hannun yanda ba yanda za'ai ta zare, kallanta yai ita kuma tai saurin juya kanta gefe.
Yace " ta ya za'ai ina namiji na barki ki kwana a kasa?"
Kallansa tai tace " ni ma tayaya za'ai in dinga barinka kana kwana a kasa?"
Murmushi yai yace " ke bakisan wahala ba......"
Kallansa tai saurin yi tace " kai sani kai?"
Murmushi yai yace " Bilkisu ni a kauyen kayau na taso."
Kallansa tai da sauri tace " kauyen ina?"
Murmushi yai sannan ya kwanta a kan filo din sannan ya jata itama fa kwanta a kan filon ta gefensa, duk suna kwance a rigingine.
yace " kinsan nayi makanta ko?"
Kai ta d'aga tace " eh"
Yace " da ita aka haifeni."
Shiru tai dan jin tausayinsa ya kamata, a hankali ya shiga sanar fa ita rayuwar da yai a kauyen nan.
Har zuwa dawowarsu garinan, hawaye ne ya gangaro ta gefen idanunta wanda ita kanta bata farga da zuwanshi ba.
Ya karasa zancen tare da juyowa yace " kinga kuwa ni a kasa ma wanda ba carpet zan iya kwana."
Kallanta yai yaga hawaye ya zubo mata, komawa yai ya kwanta sannan ya sa hannu ya riko hannunta.
Kallansa tai tare da sunkuyar dakai, yace " Kiyi hakuri na barinki kina yini ke kadai."
Murmushi tai batace komai ba, shiru ne yad'an ratsa kafin can tace " Umma......"
Sai kuma tai shiru, juyowa yai kalleta ta saitin inda take, yace " me ne?"
Tace " Na jinjina mata ne a raina."
Yace " jinjinar me?"
Tace " duk yanda ta shiga cikin wannan halin bai hanata kula da baka tarbiyya ba."
Murmushi yai sannan a ransa yace " shiyasa bazan taba yafema wad'anda suka ruguza mata rayuwa ba." ji yai tace " basu cancanci yafiya ba, sannan duk da bansan me suka mata ba na san d'anta zai hukuntasu daidaj laifikansu."
Murmushi yake yana kallanta,
Sund'an dade suna hira kaffin bacci ya d'auketa, shiru yai yana tunani shikam, a wani hali Khadija take jin abinda ya sami mahaifinta? Dan ya tabbatar bata tafiba tunda ya tambaya.
Bilkisu ya kalla sannan ya mike ya d'auketa ya d'aurata a kan gado ya rufeta da bargo dannan ta mike ya zai sauka, jiyai ta riko hannun rigarsa.
Idanunta a rufe tace " baka tunanin kaine ya dace ka kwanta akan gadon?bayan kasha wuya kana karami?"
Yace " ba bacci kike ba dama?"
Bata bud'e idon ba sai kara kasa datai dakai, yace " zan kwanta ta can bayanki, zan kuma sa filo a tsakaninmu, shikenan?"
Kai ta d'aga cikin jin dadi.
Mikewa yai har ta d'aukama yayi gaba, sai jin muryarsa tai saitin fuskarta yace " in mutum ya hauro inda nake garin bacci, duk abinda ya biyo baya ba ruwana...."
Ya juya yai gaba yana murmushi.Filo ta janyo ta rufe fukarta tana murmushin kunya.
*********
Khadija kam ana sallar asuba ta fito waje, tana ganin gari ya waye ta taho gidan sarki cikin tashin hankali.
B'angaren Magajiya ta nufa.
Tana kwance tana bacci taji ana kwankwasawa.
Cikin mamaki ta mike a d'an zabure, jitai gefen cikinta yad'an amsa, tai tsaki sannan ta mike ta zo ta bud'e.
Khadija ta gani, tace" Khadija?"
Masu kula da ita ne suka shiga bada hakuri, tace " kuje."
Khadija ta shigo sannan ta kalli Magajiya tace " Umma ina Abba?"
Magajiya tace " Yaya? Ina yaje?"
Khadiya ta kalleta tace " ke zan tambaya ai, banaji akwai wani dayasan inda yake bayan ke."
Magajiya ta kalleta tace " khadija! Ni kike tsarewa da magana?"
Khadija ta kalleta tace " wanda ake kasa magana a gabansa wanda yasan girma da darajarsa kenan bawai wanda ya halaka rayuwarsa, ta 'yayansa da kuma ta 'ya'yan yayan nasa ba sannan ya ruguza rayuwar duk wani wanda bai mai ba."
Magajiya tace " mene?"
Khadija wacce hanayenta da kafafunta duk sun sunyi shakaf sabida tsoro tace " kina tunanin kullum cikin samun nasara kike?"
Ba abinda Magajiya ta tsana irin a dinga nuna mata abinda ta ke tunani ba daidai ba.
Wani kallo ta mata tace " karki bari raina ya baci, ina raga miki ne saboda san da nake miki da kuma darajar sunan naki."
Khadija bata damu ba tace " Ya Turab bazai taba barinki kice nasara ba, domin kuwa Allah na tare dashi sannan gaskiya tana da adalci na yawo a jikinsa, in kinga Abba, ko inya dawo daga aikin sharrin da kika sashi ki sanar dashi ni na wuce."
Ta juya ta fita da sauri saboda karkaraa da jikinta keyi..........
*Turab*
*KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*83*
Kanta ta dafe a waje tana tunanin abinyi, bazatace bata damu da inda mahaifinta yake ba, sai dai ganin mahaifiyarta yau da asuba ta yabbatar bata samu bacci ba jiya.
Ya Turab? Abinda yazo mata kenan, sai dataje bangarensa ta kalla, ganin kofar ba mai kula da ita yasa ta tuna da ashe fa yanzu ya tashi daga nan, tunda yanzu yayi aure.
Haka ta juya jiki a mace ta koma gida.
Magajiya tai shiru tana tunani, tafi awa d'aya a zaune shiru kafin ta mike sannan ta shiga wanka.
Sai data cancad'a kwalliyarta kamar yanda ta saba sannan ta saka alkyaba mai tsananin kyau, wanda ya kara fito da kyanta.
B'angaren Sarki ta nufa.
Yayi mamakin jin ance itace ke nemansa, kuma wai a kilisarsa bawai a bangarensa ba.
Tana zaune, irin zaman data saba na isa da mulki.
Mai Martaba ne ya shigo sai daya zauna sannan ta gaisheshi.
Abinda ya bashi mamaki, yana zama sai ga Alkali ya nemi izinin shigowa, nan ta bada izini ya shigo.
Ko zama baiyi ba sai ga Abu Turab, Sabi'u sun shigo, shikam Turab ya d'auka ma Sarki ke nemansa.
Yayi mamakin ganin Gimbiya a zaune, shikansa Sarki kawai kallan kowa yake cikin mamaki, Turab na ganinta yasan akwai abinda ta shirya.
Sai da suka gaida Sarki da Magajiya sannan suka zauna.
Magajiya ta kalli Sarki tace " Ranka ya dade muna bukatar Hisham a gun nan."
Kallanta yai sannan yace " Ba yanzu ba, sanar dani me ke tafe dake sannan inyi tunanin kiransa."
Ta numfasa sannan tace " jiya naji duk abinda ke faruwa, dan ni bansan abinda ke faruwa ba, duk yanda na tambayi Abdulmajid bai sanar dani ba."
Sarki yace " meke tafe dake yanzu?"
Murmushi tai sannan ta kalli Sabi'u t ace " Abinda na kasa fahimta shine na d'auka Sabi'u shikadai ne shaidar abinda ke faruwa?"
Turab kallanta kawai yakeyi, haka kawai zuciyarsa take raya masa abinda take shirin yi.
Alkali yace " eh shikadai ne."
Magaijiya tai murmushi sannan ta kalli Sarki tace " Sabi'u kowa yasan aminin Abu Turab ne, me yasa mutane suka yarda da maganarsa ba tare da bincike ba? Me yasa ba wanda ya kawo Turab shine ya sa a kama Abdulmajid shikuma Sabi'u ya tafi inda aka killaceshi, wanda bai sani ba ashe Waziri ya bishi a baya?"
Turab ya kalleta baisan sanda wani murmushi na takaici yazo mai ba, lalai matar nan bala'i ce.
Sarki kallan mamaki shikansa yake mata, ita kuwa ta kalli Alkali tace " Turab d'ana ne sai dai ko d'ana ne naga zaiyi abinda bai dace ba dole ne na maidashi kan hanya."
Alkali yace 'm" haka ne, kuma sai da kikai magana naga ya kamata kam a sake bincike."
Kallan Sarki tai tace " Takawa tuba nake in na b'ata ma rai, sai dai Abdulmajid yaji magana a lokacin da yake kwance agun, kuma tabbas sunan yarima suka kira, banaji kuma akwai wani yarima wanda yake masarautar nan bayan Abdulmajid to Abu Tutab ne."
Sarki ya kalli Turab wanda kallan Magajiya kawai yakeyi.
Sarki yace " Turab!"
Abu Turab ya kalli Magajiya bai d'auke idansa daga kanta ba yace " haka ne, ba shakka Umma kinyi gaskiya, Sabi'u abokinane sannan ni da Abdulmajid bama shiri."
Magajiya tace " Banso nai maganar nan ba sai dai ina ganin dolene a sake bincike saboda ina tsoron kar wani kazamin sirri ya fito daga bakina."
Turab ya kalleta yace " me kike nufi?"
Kallan Sarki tai sannan tace " Banasan ragewa wacce ta haifeka daraja a idon duniya wanda nake ganin shine dalilin.......
Sarki ne ya katseta " me kike shirin cewa??"
Ta kalleshi tace " ba wai dan Hisham yaya na bane sai dai dan bazan baro a hukunta mara laifi ba."
Kallanta Turab yake zuciyarsa na wani irin kuna, ji yake kamar ya tona asirin Abdulmajid a gun nan, sai dai abu biyu ne ke hanashi, na farko yana tsoron yanda Sarki zaiyi inyaji wannan maganar duba da yanayin girmansa, sannan yana tausayawa rayuwar da Abdulmajid zaiyi nan gaba."
Alkali ne yace " me zai hana a kira Abdulmajid da Hisham aji abinda ke faruwa daga garesu?"
Magajiya tace " Abdulmajid na asibiti amma za'a iya tambayar Hisham."
Sabi'u wanda ransa ya gama b'aci yace " wallahi da idona naga Waziri yaje gun, sannan nine na bishi ba shine ya bini ba."
Tace " wanene zai yadda da hakan? Bayan ba kada shaidar da zata nuna hakan?"
Turab ya sa hannu ya dafa cinyarsa yamai alama dayai shiru.
Sarki tsananin mamakin ta ma yasa ya kasa magana.
Daurewa yai yace " gobe za'a sake zama saboda wannan maganar, zakuma a sake yin shari'a akan wannan al'amari."
Magajiya tai kasa dakai tace " Godiya muke ranka ya dade."
Nan ta mike cikin isa tai gaba.
Tana fita alkali yai sallama ya fita, Turab ya kalli Sabi'u yace " dan bamu guri."
Nan Sabi'u yai waje.
Turab ya kalli Sarki wanda gaba d'aya fuskarsa ta canza, tsananin bacin rai ne bayyane a fuskarsa.
Kallan Turab yai.
Turab ya kakaro murmushi yace "Abba ba wani abu "
Sarki yace " Turab ina matsayin mahaifinka? Nasan duk abinda ke faruwa amma banida ikon bin bayanka? Banida ikon kareka? Ina zaune za'a maka sharrin da baka sani ba?"
Turab yace "karka damu Abba, muna wani stage ne na wanda ko ni ko ita, wani mataki muke wanda in har bata nakasa rayuwata ba ni zan nakasa tata, dolene dukanmu mu fito da b'oyayen ajiyar da mukama junan mu dan gogawa, karka damu Allah na tare da mai gaskiya."
Sarki ya kalleshi cikin kulawa yace "kada ka kuskura kai mulki irin nawa wanda zaka sakarwa matarka komai, ka kuma bari ta dinga cin galaba akanka."
Turab ya jinjina kai kafin ya mike ya fito.
Yana fita yai waje mai makon ya koma cikin gida.
******
Magajiya kuwa tana shiga bangarenta ta saki wani murmushin jin dadi tace " Takawa ya kaji a zuciyarka? D'an da kake masifar so na cikin halaka?"
Turab kam gidan da Umma take ya nufa.
Suna zaune a waje suna yar firarsu da Lantana.
Ya shiga, sai da suka gaisa sannan ya kallu Lantana yace "ina yarinyar nan?"
Tace "wa kenan?"
Yace " mai kula da Hajiya."
Tace " au Marakisiya? Tana gun Hajiya."
Shiga yai ciki kai tsaye tana shara, Hajiya ya kalla wacce ke kwance tana bacci, yace " zo."
Tace "to."
Falo suka dawo ya zauna kan kujera ita kuma ta nemi kasa ta zauna, kallanta yai yace " baki manta abinda kika cemin ba ko?game da ko a gaban waye zaki fadi gaskiya akan Magajiya?"
Tace " eh."
Yace " kinsan waye ya saki ba hajiya magani?"
Tace " eh wacce tafi zama kusa da Magajiya ce."
Yace " Yauwa."
Mikewa yai ya fito.
Bai ko zauna gunsu Umma ba ya fita.
Bayan ya shiga mota ya dade a zaune a bayan mota shiru yana tunani, kafin yacema Garzali su tafi Asibiti.
**********
A gida kuwa Mairo ta gama cin abincin safe kenan tai wanka, ta hau kan gado, tunowa tai da abinda Abdulmajid yace mata da zata tafi.
Yaushe zaki dawo?
Tsaki tai a fili tace " harda wani tambayar yaushe zan dawo ko kunya, ko mai zan koma in mai?"
Can kuma tace " ni biki ma zamu tafi gobe zuwa cikin garin kaduna, kaga wacce zata zo."
Kara gyara kwanciyarta tai.
Abinda yaban dariya shine batafi binti biyu da kwanciya ba naga ta sauko daga kan gadon tace " hmm bari dai inje neman lada kafin mu tafi kaduna."
Hijab d'inta ta janyo ta fito.
Abdulmajid na kwance akan gado, yana tunanu, wanda kwanan nan aikinsa kenan, gaba d'aya tunani sun kasa barin zuciyarsa, gani yake duk yanda rayuwa zata juyamai bayaji zai taba samun jin dadi wannan rayuwar, bata ubansa ba ba kuma ta uwar data rike shi ba.
Sallamarta ce tasa ya kalli kofar.
Shigowa tai fuskarnan a had'e tare da kallan d'akin tace " hmm da alama yauma Khadijan bata nan"
Abdulmajid kallanta kawai yake yana murmushin jin dadi. Tace "Sannu da jiki, ni na tafi in ta dawo ma had'u."
Juyawa tai kamar mai shirin fita.
Da sauri yace " Maryam!"
Tsayawa tai cak sai dai bata juya ba, yace " Maryam!"
Yanda ya kira sunan ta ne yasa taji ta wani iri.
Abdulmajid yace " Maryam dan Allah karaso nan."
Juyowa tai a hankali ta kalleshi sannan ta karasa inda yake.
A jikin gadon ta tsaya tace " gani, menene?"
Yana kallanta yace " bazan tambayeki komai ba, ko magana in bakyasan na miki bazan yi ba, so nake kawai na kalleki ko na minti biyu ne, please."
A hankali ta d'ago idanunta ta kalleshi, sannan cikin sanyin murya tace " meke damunka kwanan nan?"
Yace " ba komai, ko ince ko me ke damuna inaji in har ina ganin fuskarki kullum ko na minti biyar ne zan iya jurewa."
Maida idanunta kasa tai batace komai ba.
Zaiyi magana Turab ya kwankwasa kofar Tare da sallama.
Da sauri ta matsa daga jikin gado tare da kallansa.
Yana kallan kofar yace mata "tsoro kike kar yai tunanin ko akwai wani abu tsakanin mu?"
Harararsa tai batace komai ba.
Turab na shigowa ya kallesu, Mairo ta kalleshi sannan ta d'an matso da sauri ta gaisheshi tace " Ya Turab na shigo asibitin ne shine na leko neman Khadija."
Turab ya kalleta yace " au ba dubiya kika zo ba?"
Kallan Abdulmajid tai wanda ya juya kai, kasa magana tai.
Turab ya kalli Abdulmajid wanda ya kula shima yad'anji ba dadi yace " Mairo kenan, da alama kunyar yayan nan naki kikeyi, me zaisa in miki fada dan kinzo duba shi?"
Kallan Turab tai sannan ta sunkuya kai tai gefe da sauri tai waje.....
Murmushi Turab yai, duk da dai yana tunani akan wannan lamarin nasu sai dai yana musu addu'a dukansu.
*TURAB*
.🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*Gaisuwa Gareki Maman Abrar wannan shafin naki ne, Allah yabar zumunci Ameen.......*
*84*
Ajiyar zuciya yai sannan ya kalli Mairo, kanta ta sadda kasa sannan tai hanyar fita.
Abdulmajid ne ya bita da kallo, sai dataje jikin kofar zata fita sannan ta juyo idanunsa na kanta dan Ji yake kamar kartaje ko ina.
Murmushi tamai sannan taja kofa tai waje Tare da rufo musu.
Tana fita ya maida kallansa gun Turab yace " Waziri fa? Ya aka kare?" dan tun jiya abin nan ke damunshi.
Turab yace " yana gida sai dai Sarki yasa an killaceshi kafin a gama shari'a."
Mairo taje zata gangara ta hango Magajiya na nufo gun.
Gefe ta matsa tare da juya baya har ta wuce, har taje zata sauka ta tafi sai kuma ta fasa.
Turab ya kalleshi yace " Magajiya ta bu'lo da wani sabon al'amari."
Abdulmajid yace " na me kenan?"
Turab zaiyi magana yaji Garzali na sanar da isowarta.
Tura kofar tai ba tare da sallama ba, dama tunda taga Garzali tasan Turab na nan.
Tana shiga ta kalleshi sannan ta kall Abdulmajid.
Murmushi Tai sannan ta karasa ciki.
Kallan Turab tai tace " kana nan ashe?"
Turab ya kalleta sai dai baiyi magana ba.
Girarta ta ja