Showing 99001 words to 102000 words out of 146065 words

Chapter 34 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

wani halin ga tsufa, ya san hakan ne yasa ya d'auketa.
Magajiya ta gama had'a lefe wanda ta yishi na gani na fada dan ita d'in yar kwallisa ce ta gaske, an kashe kudi kam, hankalin Magajiya a kwance take had'a kayan nan, dan itada Hisham sun gama tsara yanda zasu shirya komai.


A b'angaren Turab kuwa jira yakeyi a tsaida rana dan shima ya fara aiwatar da nasa shirin kamar yanda suma suke nasu shirin, Magajiya ta gama yanke hukunci akan Halaka Turab dan wannan ita kadai ce hanya, ganinsa ma batasanyi sam.




An tsaida lokacin biki nan da wata d'aya.


Magajiya ta sa Hisham ya hana Khadija fita, yanzu ko nan da nan ba a barinta fita.




Wannan kenan.





*Turab*
πŸ•Š *KAINUWA*πŸ•Š
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)





*HASKE WRITERS ASSOCIATION*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*Na Ayusher Muhd🀸🏼*


*64*


Abdulmajid yau tun safe yai wanka tsaf ya shirya ya nufi bangaren Sarki, Mai Martaba ya bashi izinin shiga.


Ya dade rabon da ya keb'e da mahaifinsa irin haka, shiga yai a hankali kamar ba shi ba sannan ya gaisheshi.
Sarki ya kalleshi yace " Ya akai?"
Ba shakka har cikin ransa sai dayaji ba dadi, ya akai? Abinda uba ya kamata ya fara tambayar d'ansa kennan sannan kuma fuska a d'aure?


D'agowa yai jiki a sanyaye yace"dama maganar Mairo ne....."
Katsehi Mai Martaba yai yace " maganar Mairo a me kenan? Kana tunanin kayi daidai a zuwa cikin tsakiyar fada kace kana san auran Mairo? Bayan ni naka sameni ba?"


Abdumajid yai shiru, Sarki yacigaba " Na rasa wani irin hali ga reka, gani kake komai naka ne kamar Magajiya ko?"


Abdulmajid ya d'ago idanunsa sun ciciko sosai da kwalla yana tsananin ganin kwarjinin mahaifinsa amma ya daure yace " menene laifina? Abba ni ba d'anka bane? Me yasa komai sai dai Abu Turab? Ka samomai mata yar mulki, gashi yanzu har an tsaida rana ana ta shirye shirye, nine fa babba ba shiba, amma bance komai ba, sannan nace ga wacce nakeso itama an kasa bani, ko itama Abu Turab din za'a ba?"


Sarki ya kalleshi yace " Kana tunanin duk abinda kukeyi kai da mahaifiyarka sani ne banyi ba ko ka d'auka karfina tafi? Sanda kukama Turab sharri kana tunanin bansan ku kuka aikata ba?"


Abdulmajid yai shiru, sai dai zuciyarsa na tafasa da tsanar Abu Turab tsantsa.
Sarki yace " Maganar auren Mairo ni har yanzu ban yanke hukunci ba, zamu zauna da mahaifinta muga wanda ya dace da ita."


Abdulmajid ya d'ago sai dai baice komai ba amma kana kalla idanunsa zakaga tsantsar b'acin rai.
Mikewa yai yama mahaifinsa sallama ya fita.
Cikin tsananin takaici ya nufi bangaren Magajiya.
Tana zaune tana shan madarar shanu, wanda takesha duk safiya dan gyara mata fatarta.
Ko sallama baiyi ba ya afka ciki.


Magajiya ta kalleshi har ya zauna, baigaisheta ba yace " Umma nikam na gaji da abinda Abba yakemin, wlh zan d'au mataki a kaina."


Magajiya bata daina shan madarar ta ba ta kurb'a sannan tace " me ya faru?"
Abdulmajid ya kalleta yace " Umma ni kam na tsani yaran can, me yasa ne komai nake so a rayuwa sai ya kwacemin?"


Tace " karka damu ka kara hakuri na wasu 'yan lokuta, sannan ka shirya nan da wani satin dan zuwa ganin yar sarkin daura."


Kallanta yai yace " inganta in mata me?"
Kallansa tai tace " tambaya kake?"
Kansa ya maida kasa sannan yace " Amma Umma kinsan ai ni M......."


Kallan data masa ne yasa yai shiru, ajiye kofin tai sannan ta juyo ta kalleshi tace " me yasa kake neman canzawa? Da baka tambayata akan abinda na sharadda maka amma yanzu naga alama yar iskar yarinyar nan tana neman canza maka hali, a kanta ka fara neman canzamin."


Kansa na kasa yace " Amma Umma."


Mikewa tai tsaye tazo kusa dashi ta sa hannu a kafadarsa tace " Abdulmajid ka zama mai bin duk abinda na sharadda maka, komai da kakeso a rayuwa ni zan baka, in nace komai ina nufin komai d'in, kai dai kabi ni."


Shiru yai, ita kuma tana gama magana ta juya tai ciki, ya dade a zaune kafin ya mike ya fita.


********


Turab yau da kansa yaje fada ya dade a can sai dayaga fitowar Waziri sannan shima ya mike ya fito.
Yana kallan Hisham ya shiga mota ya wuce gida, shima ya shiga tasa motar wanda dama ya sa Garzali ya jirashi ya bi bayansa.
Hisham na kokarin shiga gida, Turab ya fito da sauri ya biyoshi.
Hisham na shiga aka cemai wai yayi bako, yayi mamaki sai dai bai yi tunanin Turab bane yace " ace ya shigo."


Turab ya shiga cikin falo ya zauna, sannan Hisham ya shigo.
Mamaki ne ya kamashi na ganin Abu Turab.
Karasawa yai ya zauna yace "Yarima lafiya?"
Turab ya gaisheshi sannan yace " biyoka nai ai daga fada."
Hisham yace " wani abin ne ya faru da baka sanar dani a can ba sai da ka biyoni gida?"


Turab yai kasa dakai yace "ai yanzu a matsayin siriki mai neman 'yarka nazo."


A zabure ya kalli Turab cikin raahin fahimta yace " me kake nufi?"
Turab ya d'ago idanunsa yace " zuwa nai maka da abinda zai taimakeka ya kuma taimakeni."


Hisham ya bishi da kallo, Turab yace " khadija zaka auramin kaga nan gaba ko da komai naka ya kare a kalla 'yarka tana da matsayin da zata kwace ka."
Ran Hisham ya b'aci yace " Ta karemin kamar ya?"


Turab ya d'an furzar da iska irin damuwar nan yace " Badai kana tunanin in Abdulmajid ya hau mulki Magajiya zata barka da matsayinka ba ko ta barka kayi yanda kakeso da d'anta ba?"


Hisham yace " wannan banaji yana daga cikin damuwarka."
Turab yace " Hake ne sai dai inaso kayi tunani sosai kaga mafakar da zata bul'ema, ka fini sanin kanwarka ka kuma san halinta, kana tunanin zata barka ko shawara ne kaba Abdulmajid? Inka bada ma shawarar kana tunanin zata bari yai aiki dashi?"


Hisham ya mike tsaye cikin takaici yace " koma menene damuwatace ba taka ba, sannan kana tunanin ni zan kai 'yata a ta biyu gidan wani? Sannan ni ban taba tunanin had'a zuri'a dakai ba kuma bazan yi ba har abada."


Turab yace "kumafa gaskiya ka fada, ni kaina bansan me yasa nazo ma da zancen ba, inaso ka sanar da 'yarka hukuncinka saboda mu hakura da juna."
Ya mike yamai sallama ya fito daga falon.
Yana fita yai wani murmushin gefe yace " nazo neman iri ne na auran 'yarka? Inji wa? Kai dai na tabbatar abinda na saka a kwakwalwarka ya shiga zai kuma fara aiki."
Ya juya, Karo suka kusa yi da Khadija wacce ta taho da tirw daga kitchen rike da tire wanda yake d'auke da juice.


Kaucewa tai saboda ganin zata bugeshi, garin kaucewa bata kula da kafarsa ba ta taka ta tafi kamar zata fadi, da sauri ya rikota ta baya.
Ajiyar zuciya tai da karfi dan tabbas ta d'auka fad'uwa zatai.
Juyowa tai a hankali, nan taga wanene idanunsu ne suka had'u da juna.
Sai da 'yan wasu dakiku suka wuce a haka kafin Turab ya daure yace " Baki bige ba?"


Gyara tsayuwarta tai sannan ta kalleshi, a hankali ta d'aga kai, kallanta ya sakeyi yaga ta rame, ita kuma tana san tambayarsa abinda ya kawoshi, a tare sukace "Nace me......"
Ganin yanda sukai maganar a tare basu san sanda sukai dariya ba, Turab yace " fara magana."
Kallansa tai tace " a'a ka fara." yana kokarin tambayarta yaji murya ance " Khadija me kikeyi anan baki kai ba?"
Juyowa tai ta kalli Ummanta tace " yanzu zan kai."
Kallan gun yai, mahaifiyarta ya gani, suna tsananin kama da Khadija sosai, da ace itace Abdulmajid to fa yasan tabbas zargi zai bayyana.


Gaisheta yai sannan ya fita, Hisham kam Turab na fita ya kumburo baki yana tunani, tabbas dolene ya fara jan d'ansa a jikinsa dan sai yanzu ya farga ya san Magajiya sarai tabbas gaba ma neman ma hanashi zuwa gidan zatai.


Ko tabin bayan Khadija data shigo baiyi ba ya shiga cikin d'aki.


**********


A can kano kuwa shiri sosai akeyi na auren Gimbiya, auren da babu kamarsa agunsu domin ita kadai ce 'yar sarki mace, shiri ake sosai wanda yasa kishiyoyin Fulani jin kishi dan komai ita keyi, Bilkisu kuwa an shiga gyara, dama ba zancen zance dan in suka fara gyaran jiki to ango bazai ga amarya ba saboda so ake inya tashi ganinta yaga kamar ba ita ba.
Turab kam na kiranta sosai suna waya.





Hisham ya gama tsarawa dan yau yana tashi daga fada ya nufi bangaren Abdulmajid........


*TURAB*
πŸ•Š *KAINUWA*πŸ•Š
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)





*HASKE WRITERS ASSOCIATION*


*Wattpad :-AyusherMohd*


_Sakon ta'aziyya gareki kawar arziki BillynAbdul Allah ubangiji ya jikan Mahaifinmu yasa Aljanna ce makomarsa.....(Ameen)_


*Na Ayusher Muhd🀸🏼*


_Masu san karanta Matar Fayrouz na AsyKhaleel da sauran litattafanta su duba ta a wattpad @asykhaleel.😘😘_


*65*


Hisham yana fita yai bangaren Abdulmajid, baya nan ma sai ya zauna a falo ya aika a nemoshi, yace " in an ganshi kar acemai shine yake nemansa.


Abdulmajid ya fito daga bangaren Magajiya kenan aka sanar dashi yanada bako.


Yana shiga yaga Hisham, ya karasa ya zauna sannan ya gaidashi, Hisham ya washe baki yace " Abdulmajid sai ka ganni ko?"
Kallansa yai yace " Kawu me ya kawoka? Naga baka taba zuwa bangarena ba."
Hisham yai murmushi tare da kallansa yace " yauma wucewa nazoyi sai na fahimci ban taba shigowa ba."


Kai ya d'aga kawai baice komai ba, yau ce rana ta farko da suka kebe su biyu haka shiyasa yakejin abin wani banbarakwai kamar ba kawunsa ba.
Hisham ya kalleshi yace " ya maganar auren naka da Mairo? Har yanzu Magajiya bata sauko ba?"


Hisham ya kalleshi kallan mamaki, cikin rashin fahimta yace " eh kasan halin Umma ai "
Hisham yace " karka damu inaso kome ke damunka ka dinga sanar dani, ni zan yi iya kokarina wajen ganin na taimaka maka, Magajiya bazata taba bari ka auri yarinyar ba, sai dai ni zan san yanda zanyi in har kanasanta."
Ya kasa fahimtarsa, mamaki yake na yanda yake mai, Abdulmajid yace "Nagode, amma kana tunanin Umma zata yarda?"
Hisham yace " karka damu, kai daj ka yarda dani, duk wata matsala taka ka dinga zuwa kana sanar dani, ni zan taimakeka akan komenene, kawai dai ka dage kar ka taba bari Turab ya kwacema mulkinka."


Abdulmajid kallansa kawai yakeyi, Hisham ya matso yace " inaso a sati ka dinga zuwa gidana cikin gari, zansa Maman Khadija ta dinga shiryama duk abincin da kakeso, kaga sai kazo ayi hira, hakan zai ragema kewa ya kuma kara mana zumunci."


Shekarata nawa da haihuwa? Da can ba'ai zumuncin ba sai yanzu? Abinda ya fada kenan a ransa, sai dai a fili kallan Hisham yai kawai baice komai ba.


Hisham ganin yanda Abdulmajid yake yi yasa ya mike yace " ni zan koma sai mun ganka ko ran Juma'a ko asabar,sannan karka fadama Magajiya zuwana da zancen da mukai, ka santa."
Uhm hmm, kawai yace.
Hisham yai waje.
Kallansa Abdulmajid yai sannan ya mike yai ciki.


Hisham kuwa na fita ya jinjina kai yace " a hankali zan jawoka jikina, ai tsakanin Uba da d'a sai Allah."


Yana fitowa yai wuf yai kwana ya wuce, Abu Turab wanda yana shiga bangaren aka sanar dashi zuwansa ya fito dama yana jiran fitowarsa.
Yana hangoshi ya taho kamar irin bai ganshi ba d'in nan, Hisham na hangoshi ya tsaya tare da neman inda zai b'uya, dan dai girma ya kamashi ne amma da gudu zai saka, juyawa yai da sauri dama abinda yasa ya bi ta baya saboda bangaren Magajiya ne ta gaba, yana tsoron kar aganshi.
Abu Turab yana kallan ya juya yai wani murmushin jin dadi.


Hisham ya shiga bangaren Magajiya.
Tana kishingide ta bashi izinin shigowa.
Hisham ya shiga yana dariya yace " Magajiya ikon Allah hutawa kikeyi ne?"


Wani banzan kallo tamai hakan yasa yai shiru sannan yace " Magajiya barka da yamma."


Idanu ta d'an juya bata amsa ba, zama yai sannan yace " na lekone mu gaisa."
Tace " ka sandai muna da abinda ya kamata mu shirya na ranar auren yaran nan ko? Ga lokaci yana matsowa amma sam ka ki shigowa ayi magana."


Yace " haka ne, nima ai ba mantawa nai ba, yanzu ya kikeso ayi?"


Ta bud'e baki zatai magana aka sanar da ita zuwan Abu Turab.


Fuska ta canza tare da yin wata karamar kwafa, ba shakka itakam ta gaji da jin ko sunan yaran nan.
Shigowa yai ganin batada niyyar bashi izini.
Yana shigowa yace " Umma bakiji isowar d'anki bane?"


Murmushi ta saki sannan ta koma ta gyara zamanta tace " banyi tsamannin zuwan ka bane."


Zama yai sannan ya kalli Hisham yace " da alama sirri kukeyi da Kawun namu au ko ince Babana."


Magajiya ta had'e fuska, shima Hisham yaci mazu, Turab ya d'aga hannayensa yace " Tuba nake Babana kar in bata ma sirikin nawa rai kafin abani Khadija."


Magajiya ta kalleshi cikin takaici tace " kai dai ka nutsu akan auranka da Bilkisu ka daina wata banzan magana wacce bazata amfaneka ba."


Turab yace "Haka ne Umma, nayi..." yai alamar zip a bakinsa.
Kallan Hisham yai yace "Amma waziri kamar daga bangaren Abdulmajid na ganka ko?"


Hisham ya zaro ido, da sauri ya kauda kai gefe irin mara gaskiyar nan yace " a'a wucewa nai ba shiga nai ba."


Turab ya jinjina kai yace " kayi kokari sai naga kamar tacan yafi nisa."
Hisham yace "Hmm." da sauri ya kuma cewa " bari nikam na koma." ya fada dan kawar da zancen.


Turab yace " a'a bari ni na tafi da alama Umma akwai abinda zata cema, da na d'auka ma d'anka kazo ba gun Umma ba shiyasa na shigo."


A tare gabansu ya amsa da rass, Magajiya cikin tsananin tsoro tace " D'ansa?"
Hisham kam har zufa ta fara afko masa, Turab yasa dariya yace " menene hakan? Da ba d'ansa bane?"


Ai tuni Hisham kansa zuwa wuyansa ya cika da zufa, Magajiya kam a ranta tace "shikenan ta faru ta kare."
Turab ya karayin dariya yace " lalai Umma ba kara? Na d'auka d'anki a ka'ida d'an Waziri ne saboda jininku d'aya."


Bakin Hisham har rawa yake gurin cewa " sosai ma haka ne."


Magajiya kam idanu ta bud'e ta kurama Turab tana kokarin ganu abinda ke b'oye a ransa da gaske abinda yake nufi kenan?"
Turab ya kalleta yace " Umma lafiya? Naga kinata kallo na."
Idanu ta d'auke tare da cewa " ba komai, ya shirye shiryen biki?"
Yace "Thanks to you, komai na tafiya daidai."
Kai ta d'aga tace " yayi kyau."
Turab yace " Ayi hira lafiya."
Ya juya ya fita, yana fita ya kara kallan kofarsu ta gefe, "Haka ne nima ba mantawa nai ba, yanzu ya kikeso ayi?" kalaman Hisham da yaji sanda ya iso gun ne ya kara dawo mai, tabbas akwai wani mugun abu da suke kara shiryawa, ya tabbatar.


Juyawa yai ya fita.


Yana fita Hisham ya saki wata ajiyar zuciya ya kalli Basira yace " kinji hanjin cikina?"


Magajiya ta kurama kasa ido kafin tace " Inaji ya kamata mu maida Khadija kano."
Yace " Kano? Kamar ya?"
Tace "kasan Mahaifiyar Saifullahi ta kirani jiya da daddare tace wai Khadija tace ma Saif akwai wanda takeso, dolene mu maidata kano in taga bata gani yarancan sai ai auren, inba haka ba intaga mutuwarsa abin zai baci, ka san dagar da akai da ita sanda tana karama ma bare yanzu."


A ransa yace " ni da 'ya'yana sai dai a dinga sharada min abu, da girmana amma a dinga kaskantar dani"
A fili yace " hakan yayi."
Nan suka cigaba da tsarinsu.....


*********
Basira zaune a falonta, gabanta kuma leda ce irin mai karfin nan, da alama kaya ne a ciki.
Amsa sallamar Turab tai sannan ta kalli kofar da ganin shigowarsa.
Turab ha shigo sannan ya zauna yace "Umma gani."
Kallansa tai tace " Dama aikenka zanyi."
Kallanta yai sannan ya kalli ledar gabanta, sai kuma yar murmushi yace "Gun 'yarki?"
Tace " eh, Mairo zaka kaimawa, sa wa nai a d'inka mata na bikinka."


Murmushi yai yace "Umma kenan."
Kallansa tai tace " Amma baka tunanin hakan yazo da kamar wulakanci ko?"
Turab yace "wulakancin me?"
Tace " Na kaimata kayan da zata sa a bikinka bayan akwai wata a kasa."


Turab yace " Lalai Umma, ni bansan wannan ba ki tambayi Lanta....."
Da sauri yai shiru tare da kallanta, Kallansa tai itama tace " Turab har yanzu ba labarin inda Hajiya take? Bare Lantana?"
Kai ya d'aga alamar eh.
shiru sukai ganin haka yasa ya jawo ledar yace " Zanje in anyi Magrib."


*********


Garzali ne ya kaishi, yana cikin mota Garzali ya fito ya aika a kirata.
Ta gama kunce lale kenan wanda tayi a hannunta, aka sanar da ita zuwan Turab.
Wankewa tai dama ba sallah zatai ba ta saka hijab ta dan murza hoda sannan ta fito.
Tanaji 'yayan kishiyar babarsu na mata habaici, ko ta kansu bata biba tai waje.

A jikin soro ta tsaya dan bata fita waje zance, ka'idar gidansu ne haka.
Turab sai da ya hangota sannan ya bud'e motar ya fito, rike da ledar.


Tundaga nesa take murmushi har ya iso, Kallanta yai sannan ya karasa cikin soro yace " Hajiya Maryam an fito?"
Kallansa tai tace " Yaya ina wuni?"


Bai amsa ba sai cewa dayai " kwana dayawa?kin bata bat."
Fuska ta d'an rufe tace " wlh inasan zuwa gaida Umma magana ce banaso."
Leda ya mika mata yace " ga sakonki inji Ummanki."
Amsa tai tana murmushi tace " oh ni, me na samu?"
Yace " kayan bikin yayanki ta d'inka miki."


Gani yai ta d'ago da sauri, sannan yanayinta ya canza, yace " Badai Umma tayi lefi ba?"
Ya ke tai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login