Showing 84001 words to 87000 words out of 146065 words

Chapter 29 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

nid'in mutumin kirkine sai dai a zahirin gaskiya banida kirki ko kad'an."
Garzali yace "Ranka ya dade ta yaya zaka ce haka?"
Turab ya jingina kansa jikin kujera ya hard'e hannayensa tare da maida idanunsa ya rufe yace " Duk yanda yarinyar nan ke kula da Mahaifiyata da nikaina ace ko gidansu ban sani ba, sai dai ita tazo inda muke."
Ya karasa maganar tare da juyar da kansa gefe.
Garzali yai shiru kafin can yace " Ai kai kaga baka fiya fita ba, sannan yaushe ma ka warke Ranka ya dade?"
Turab bai ce komai ba, sai da suka isa gidan Garzali yai parking sannan ya kalli Turab wanda ya bud'e ido jin tsayawar motar yace " mun isa, a kira maka ita?"
Turab ya kalleshi yace " Cema akai zance nazo ko me? Ka sanarma Barde da zuwana."
Garzali yace to, sannan ya fita.
Yana fita Turab ya kalli waje, unguwar ya shiga kallo.


Garzali ne ya dawo da sauri yace " Kunye sab'ani ance d'azun nan ya tafi fada."
Turab yace "ayya, Mairo fa?"
Garzali yace "Ban tambaya ba dan nima dama bance kai bane kazo."
Turab yace " kira min ita, tunda nazo harnan mu gaisa."
Nan ya juya, yaron d'azu wanda da alama a gidan yake ya kara turawa yace "ya kida masa Mairo." yaran yace ince inji wa?
Garzali yace kace inji Yarima Turab.
Nan yaran yai ciki da gudu.


Mairo ta gama cin abinci kenan tana tattare kwanuka yaran dayake d'an babbar yayarsu ce da aka kawoshi hutu ya shigo da gudu ya rike mata riga yace " Ana kiranki a waje."
Tace " Khalid meye hakan? Waye yake kirana?"
Yace " Wai kije inji Yarima Turab."
Hararar sa tai sannan ta kwace rigarta tai kitchen tana cewa "Lalai Abdulmajid ma Ya raina mata hankali, taje inji Turab?"tai tsaki tace ko kunyar karya ma mutum bai iya ba.
Hannunta ta wanke sannan ta fito tai d'aki, kan gadonta ta kwanta, can kuma ta mike zaune tace karfa inje da gaske ya Turab ne.
Hijab dinta ta jawo tai waje.
Lekowa ta fara yi ganin duk suna cikin mota yasa ta kasa ganewa.
Ta kara lekowa, Abu turab ne ya zuge glass d'in window dinsa sai daya tabbatar itace sannan ya bud'e motar ya fito.
Mamaki ne ya kamata ganin shi d'in ne ya fito, kallansa kawai take d'auke da tsananin mamaki har ha iso soron.
Bayan kofa ta shige fa sauri tare da bin jikinta da kallo, ko kwalliya batai ba, jitai kamar ta ruga ciki.
Turab ya tura kofar yace " ko dai in juya ne?"
Tana bayyan kofar tace " Ya Tutab."
Takowa yai zuwa ciki yana cewa " Ba dai Abdulmajid har ya fara hanaki kula yayan naki ba."
Fito tai tare da had'e fuska tace " waye shi kuma?ni ai banaji a list d'in yayuna inada mai irin sunan."
Yace " To ko a kirashi sai a tambayeshi? Inga ko zaki iya tambayarsa."


Dariya tai mara sauti tace "Yaya kana tunanin bazan iya ba?"
Hannunsa yasa ya rufe bakinsa yace " Tab ai na manta ashe fa Mairo ce. mairon data yardani sau biyu."


Juyawa tai da sauri cikin shagwab'a tace "Haba yaya"
Murmushi yai yace " Barde nazo nema ashe bayanan."
Juyowa tai tace " ya tafi fada."
Turab ya kalleta yace "Are u okay?"
Yanayin fuskarta ne ya canza tace " akan me?"
Kallanta yai sai dai baice komai ba, murmushi ta masa tace " I am okay yaya."
Kara kallanta yai idanunsa d'auke da alamar kokonto, jitai idanunta na neman cicikowa, kanta ta d'aga sama tana neman maidasu, sannan ta kalleshi tare da girgiza kai tace " Yaya i am not okay, na rasa yanda zanyi, Abba yace bashida yanda zaiyi, kai baka nan, kunya nakeji in koma gun Umma sannan yaya bazan iya auren mutumin dana san ba sona yake ba, wlh yaya da ace Abdulmajid san tsakani da Allah yakemin ko da banasan sa zan jure na aureshi ko dan neman gyara halayensa." hawaue ne ya zubo mata ta girgiza kai tace "Sai dai yaya ni nasan Abdulmajid nasan irin kallan da yakemin, na tsani kallan da yakemin, na rasa ya....."
Kasa karasawa tai ganin tana neman yin kuka, gashi batasan Turab yaganta cikin wannan halin.
Tsananin tausayinta ne ya kamashi, kallanta yai sannan ya zaro handkerchief daga aljihunsa ya mika mata.
Ansa tai ta goge hawayenta sannan ta kakaro murmushi ta kalleshi tace " Ya yayar tamu? Ka barota lafiya?"
Murmushi ya mata yace " Bilkisu ce yayarki?"
Tace "eh mana, a yanzu dai ba yaha ta bace amma inta aureka ai ta zama yayata."
Kallan tsananin tausayawa ya mata dan tabbas yasan yanda take sanshi, yace " Tana garinsu, sannan Mairo ba kya ganin ya......."
Gabanta ne ya fad'i tana tsoron kar yace ya kamata ta daure ta auri Abdulmajid, da sauri ta katatshi tace " Yaya kasan me? Khadija fa ta d'auka ni kake so, tun kwanaki nakesan fadama sai in manta."


Kallan mamaki ya mata yace " mene?"
Daurewa tai tace " nima bansan ya akai tai wannan tunanin ba."
Iska ya d'an furzar yace " share wannan zancen sannan ni in tambayeki kinji na cemiki Khadija nakeso da bakina?"
Tace " Au sai ka furta? Banda abinda idanunka suka nuna?"
Handkerchief dinsa dake hannunta ya fizga sannan ya kwad'a mata akai, hannu tasa agun da ya daketa tace " Yaya da zafi fa."
Murmushi sukayi a tare, sannan ya saki wani hucci na tunowa da matsalar dake gabansa.
Kallanta yai yace " Karki damu, ke dai kicigaba da addu'a In Allah ya yarda komai zaizo da sauki."
Kai ta d'agamai tace "Nagode Yaya."


Juyawa yai ya fita, kallan bayansa tai har sai da ya shiga mota.

**********


A gidan Waziri kuwa, Khadija ce tsugunne gaban mahaifinta.
Hisham ya kalleta fuskar nan tasa ba wasa yace " Khadija mun riga mun yanke hukunci akan aurenki, dan Magajiya harta sa an sanar ma iyayen Saifullahi akan maganar sa rana, dan haka ki shirya, bazan tab'a yadda da wani zancen banza ba...."


Kallan mahaifinta tau idanunta fal hawaye tace " Abba tunda akai maganar Saifullahi ban tab'a cewa a'a ba ko wani abu, ni dai naji zan aureshi amma yaya Abdulmajid dan Allah ya janye auren nan na dole da yake neman yima baiwar Allah."


Kallanta yai ransa ya kara tun zura, mahaifiyarsa ya kalla da take zaune shiru, dan ko baki bata sa musu ba.
Yace " biyoni ke kuma."
Ya fad'a tare da yin ciki, Khadija na ganin haka tasan shikenan ta jama mahaifiyarta, da sauri tace " Abba...." bata soma fad'in komai ba Mahaifiyarta ta kalleta tare da girgiza mata kai alamar kartace komai.
Suna shiga d'aki ya kalleta yace " wai wani irin tarbiyya kikama Khadija? A da na d'auka duk gidan nan tafi kowa jin maganata da hankali amma yanzu na fara tunanin zugata kikai inba haka ba yarinyar da nasan komai nacemata tanayi akan me yanzu akan wani can sokon yaro ta nemi bijiremin, kece kike zigata kome?"


Kallansa tai ranta ya tunzuro dan itakam ta tsani yanda suke neman yima Khadija auren wanda bataso tace "Tunda nake dakai na tab'a musa ma? Ko a sanda ka d'auki d'an dana haifa ka kaima yar uwarka magajiya na hanaka? Ko har izuwa wannan ranar na tab'a kaucewa akan sharad'in daka gindaya min?ko kuwa kana tunanin banajin zafin ganin d'an dana haifa na fari agun kanwarka? Yaro bai san matsayin ba, ko suna uwa bai taba kirana dashi ba."

Hawaye take sosai, kallanta yai rai a b'ace yace " Bazakiyi shiru ba?"


Cikin b'acin rai tace" kana tunanin tsoronka nake daga kai har Magajiya? Sannan yanzu ni kun gama min abinda kukaga dama 'yar tawa ma haka kuke san juya mata rayuwa? Ko kana tunanin duk wani abu na makirci da kuke kai da Ma"


Da baya da baya ta fara ja tana girgiza kai, sam ta ma rasa me take ji, tahowa tai dan taba mahaifinta hakuri sai dai me?


Juyawa tai da gudu ko takalmi bata sa ba tai waje, ko mayafi babu a jikinta.
Tafiya kawai take bata ma san knda takesa kafar ta.


Sam bata kula da motar da take mata horn ba, jan burki yai da sauri ganin taki kaucewa, duk da haka sai da motar ta d'an bigeta kadan.
Turab ya kalleshi da sauri yace " lafiya?"
Garzali yace " bansan wacece ba, inajina bigeta. " ya karasa maganar tare da bude motar.

Kusa da ita yaje yana tambayarta lafiya?
D'agowa tai ta kalleshi ganin bibiyi take, mikewa tai kawai tana neman cigaba da tafiyarta.


Da sauri ya kalli Turab wanda ya bud'e motar ya fito yana tsaye rike da kofa, yace " Ranka ya dade Khadija ce."


Da sauri Turab ya kalli inda yarinyar take, ganin Khadija yasa ya taho da sauri yace "Khadija?"


Kallansa tai sai tai baya luu kamar zata fad'i da sauri yasa hannu ya tareta, suka tsugunna, kallanta yai cikin tsananin tashin hankali yace "Khadija?"


Kallansa tai sannan ta shiga girgiza kai tana cewa " Abba meke faruwa? Wani d'ane umma ta ba kanwarka? Abba...."
Jijigata yai yace " Khadija? Meke faruwa?"


Kai ta shiga girgizawa, ta shiga kankame jikinta alamar tsoro.


Turab ya rasa abinda zaiyi d'aukanta yai cak ya sakata a mota, ya rufe ya koma gaba sannan ya kalli Garzali yace " mu tafi mu kaita gida, da alama bata cikin hayyacinta."


Sun isa gidan ya rikota ya kalli Garzali ba sai ya tambaya ba dan kana kalla tsari da fentin gidan kasan gidan mai mukami babba ne na sarauta.
Nan ya nufi gidan da ita.
Hisham wanda ya fito ransa a b'ace da rainin hankalin da matarsa ta masa yai kicibis da su.


Mamaki da takaici ne ya kamashi yace " Malam wani irin iskanci ne haka zaka rikomin 'ya......."


Bayan Turab ta b'oye ta rikemai riga tana cewa " wayyo Allah, dan Allah tafi dani daga nan, wad'an nan......"
Tsawa Hisham ya daka mata yace " Khadija bakida hankali ne?meye hakan?"


Turab ya juyo ya kalleta yace "Khadija menene?meke faruwa haka?"


Kallan Turab tai sai yanzu ta gane shine, hannunsa ta kamo da sauri tace " Yaya Abba da Umma Magajiya..."


Hisham ya fahimci akwai wani sirri da take san fad'a, da sauri yasa hannu ya fizgota.


Tace " Kanwar Abba? magajiya kenan, kenan Ya Abdulmajid......"


Toshe bakinta yai ya sa hannu ya finciketa da karfi yai ciki da ita.
Turab ya kalli inda suka shiga yace " me ke faruwa?"




*ABU TURAB*
*KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*56*


Turab na zaune a cikin mota yai shiru yana tunani, me ya samu Khadija?


A can kuwa Hisham na shiga da ita cikin gida ya rike hannayenta duka biyu yace "Khadija, menene? Me kikaji?"
Kallansa tai tsananin tsoronsa taji ya shigeta, kai ta girgiza batace komai ba, kara jijiga ta yai yace " wanene ni?"
A hankali tace " Abba ne."
Yace " me kike kokarin sanar ma Abu Turab?"
Kai ta girgiza da sauri tace "bakomai."
Idanu ya kankance yana san gano abunda take b'oyewa, mahaifiyarta ce tazo gun tace " Khadija? Lafiya inata kiranki shiru?"
Kwace hannunta tai ta tafi gun Uwarta da gudu.
Hisham cikin zargi ya ke kallanta, Ummanta ta riketa tace "lafiya Khadija?"
Tattaro nutsuwarta tai sannan ta samun kanta da cewa " Bakomai Umma faduwa nai a waje."
Umma ta kama hannunta cikin kulawa sukai ciki.
Hisham ya bisu da kallon zargi sai dai bashida tabbas akan abinda yake zargi, sannan yasan Khadija da ace taji maganar da sukai da matarsa dazu da ciki zata shigo taji me suke nufi bawai waje zatai ba.


*****
Sun isa gida, Turab ya fito sannan ya nufi hanyar b'angarensa.
Abdulmajid ya hango yana tahowa shima da alama shima fita zaiyi, tsaya wai cak yana kallansa sannan yana maimaita kalamun Jakadiya, da kuma Khadija, da alama duk maganarsu a karkashinta dai maganace wacce ta shafi Abdulmajid, to amma me suke nufi? Sam hankalinsa bai kawo ba d'an sarki bane dan shi a ganinsa duk mugunta da makircin magajiya bazata taba tunanin yin wani abu mai kama da haka ba.


Abdulmajid ne ya iso inda yake kallan banza yamai yai gaba abinsa.
Turab ya bishi da kallo sannan yai gaba.


Har ya je zai shiga b'angarensa sai ya juya ya nufi bangaren Hajiya.
Yaje shiga yai kicibis damai kula da ita, sam bata san ya taho ba haka shima.
Bigetan dayai ne kufin dake hannunta ya fad'i kasa.


Turab ya kalleta yace " sannu....."
Ganin yanda ta shiga saurin dauke kofin da tayar sam tama manta da bigeta akai, tana d'aukewa tai hanhar fita, kasa ya tsuguna ya d'au yar karamar ledar data fad'o daga jikinta yana kokarin mata magana akan ta yarda abu sai gani yai ba kowa agun.
Mamaki ya kamashi ina tai? Kallan maganin yai sannan ya shinshina maganin, a aljihunsa ya saka sannan ya shiga ciki.
Sam jikinta ba sauki sai ma karuwa da yakeyi, kusa da ita yaje sannan ya riko hannunta yace " Hajiya nine Abu Turab."
A hankali ta bud'e idanunta ta kalleshi cikin karfin hali ta sakarmai murmushi.
Cikin kulawa da tausayawa yace" Hajiya kinganni shiru ko? Tafiya nai sannan abubuwa sunyi yawa dana dawo, ya jikin?"
Idanu ta lumshe sannan ta bud'e, kallan d'aki yai sannan yace " kin gaji da kwanciya ko?."


Tunani tai yanzu ne lokacin daya kamata ta yunkura ta fadama Turab abinda ta sani.
Bakinta ta shiga motsawa tana kokarin yin magana, kallanta yai yace " akwai abinda kikesan fad'amin?"
Kai ta d'aga da sauri alamar eh.
Matsowa yai da kansa kusa da bakinta yace "menene Hajiya?abu kikeso?"


Daurewa take sosai da kyar ta iya cewa "Maga...."
Yace "magani?"
Kai ta girgiza alamar a'a yace "Magajiya?"
Kai ta d'aga da sauri alamar eh.
Cikin mamaki ya kalleta yace " wani abun ta miki?"


Da kyar ta kara daurewa tace "Abb duu........"
Yace " Abdulmajid?"
Kai ta jijiga alamar a'a yai shiru yana tunani can a ransa yace Abdussamad?
Kallanta yai yace " Abba?"
Kai ta girgiza da sauri yace " me ya faru?"
Kokarin magana take sai dai ina ta kasa, ganin yanda take shan wahala yasa yace " Hajiya daina magana."


Yawo ne yashiga zubowa mai kumfa, cikin tausayawa ya mike da sauri yana neman mai kula da ita.
Yarinyar nan ya gani a waje tana ta dube dube cikin b'acin rai yace "bakiji ina kiranki ba?"
Tahowa tai gunsa, yace " Hajiya jikinta ya motsa nemo mai magani."
Ya fada tare da komawa ciki ya d'agata yana goge mata, sai far fari take da idanunta, mai bada magani tana zuwa ta shiga mata jike jike tana bata, sai dayaga ta samu bacci sannan ya mike cikin tausaya mata.


Dakinsa ya shiga ya kwanta akan gado kansa na kallan sama ya d'aura hannunsa akan goshinsa, me Hajiya takesan fada mai? Ya tabbatar yanzu kuma abu ne tsakanin Magajiya da Mahaifinsa.


Hannu yasa a aljihunsa ya d'auko wannan maganin, mikewa yai ya fito waje.
Garzali ya taso da sauri yazo gunsa, Turab ya kalleshi yace " ka kiramib jakadiya kace ta sameni a gun shakatawar Takawa."


Garzali ya amsa da to, juyawa yai ya fita.


A kan kujera ya zauna, bai dade ba sai ga Jakadiya.
Tana zuwa ta zube a gabansa ta shiga gaidashi, Turab ya amsa sannan ya kalleta yace " tambaya zan miki, banasan gulma ba kuma nasan had'i sannan kada ki kuskura kimin karya abinda na tambayeki shi kadai zaki amsa min bana bukatar wasu kalamai na daban."


Kanta na kasa tace " To ranka ya dade" a gaskiya tana ganin girma da kimar yaron tunda yake bata taba ji ance ya nemi jin magana daga bakin wani ba a masarautar, sannan ga kwarjini da izza ta sarauta da yake da ita.
Turab ne ya katseta da cewa " Menene tsakanin Magajiya da Abdulmajid da kuma Hisham? Wani sirri ne a tsakaninsu?"


Gabanta ne ya fadi ta kalleshi tace " Ranka ya dade."
Kallanta yai yace " jiranki nake."
Yawo ta hadiya sannan tace " Amsar d'an kaninta da juyawa a matsayin nata."


Idanu Turab ya zaro cikin tsananin tashin hankali, mikewa yai tsaye gabansa na wani irin fad'uwa gabansa yai, idanunsa ne suka kada sosai kallanta yai cikin kokonto yace " meye naki na sanar dani wannan babban sirrin? Sannan ta yaya ke kika san haka?"
Jakadiya ta kalleshi cikin tsoro tace " Tuba nake ranka ya dade amma wannan magana haka take sannan sanar dakai danai bawai da wata manufa na fadama ba......"
" Badai kina tunanin kin sanar dani hakan bane dan kar asiri ya tuno kiyi tunanin zan taimaka miki? Sannan meye dalilinki na b'oye wannan siriin bayan ked'in jakadiyar sarki ce?"


Tsoro ne ya kama Jakadiya jikinta ne ya hau rawa ta kalleshi tace " Ranka ya dade........."


Kallanta yai cikin takaici yace " ba dai dake aka shirya b......"


Tsugunawa tai cikin tsoro tace "wlh ba dani bane Ranka ya dade, wlh ba dani bane."


Komawa yai ya zauna sannan yace " jeki zan nemiki in nayi tunani."


Fita tai cikin tsananin fargaba.
Jiyai hannunsa na rawa, da sauri ya had'e hannayensa guri daya sannan ya bud'e idanunsa da sukai jawur.


Mikewa yai cikin takaici yai bangaren Magajiya.


Tana zaune a kilisarta aka sanar mata da zuwansa.
Murmushin jin dadi tai tace ace ya shigo dan ta tabbata yau dolene ya nemi ya fiyarta.


Turab ne ya shigo, tsayawa yai yana kallanta cikin tsananin mamaki.
D'agowa tai ta kalleshi tace " meye hakan? "
Murmushi yai sannan ya matso ya zauna tare da gaisheta.
Amsawa tai cikin isa sannan tace " kun yanke shawarar?"


Turab yace " sosai ma Umma shiyasa nazo miki da umarni."
Kallansa tai shekeke tace " Umarni? Kai zaka ban?"
Kai ya d'aga mata tare da yin murmushin gefe yace " inaso a satin nan ki fara shirya lefe na daga nan zuwa sati biyu ki gama hada komau dan zuwa kaiwa Masarautar kano, sannan in zaki saka lokacin biki banasan kijashi da nisa."


Kallan mamaki ta mai batasan sanda tasa wata dariya ba tace " me da me?"
Yace "kamar yanda kikaji na baki umarni hakan nakeso ki aiwatar min, sannan sirrin ki da nake rike dashi a hannuna zan aunashi a ma'auni, da namu sirrin da kike rike dashi zan duba inga da ni dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login