Showing 87001 words to 90000 words out of 146065 words

Chapter 30 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

wanene nashi sirrin yafi nauyi, inhar naki yafi nauyi dole ne kiyi tabin umarnin d'anki Abu Turab har sai sirrinki ya kai daidai d'aya da namu inyaso sai kowa ya tona nashi sirrin a lokacin ne zamuga wanda zai ci galaba."


Gabanta ne ya shiga fad'uwa dan yanda idanunsa suke nunawa tasan tabbas akwai wani babban sirrinta daya sani, menene? Wanene daga ciki?"
Daurewa tai tace " kana tunanin zan yarda da wannan shirman naka?"


Kallanta yai cikin tsana yace " to ko in sanar ma Abdulmajid?"
Gabanta ne yai wani wawan faduwa cikin rawar murya tace " Abu Turab."


Murmushi ya sakar mata sannan ya mike ya kalleta yace " kiyi gaggawar sa d'anki ya janye auren Mairo, ahh ba......" sai kuma yasa yatsa a baki alamar yin shiru yace " sry" ya fada tare da nuna alamar zip a bakinsa.
Juyawa yai yai waje.


Yana fita ta shiga kakkarwa, mikewa tai da sauri cikin tsoro me ya jiyo? Me ke faruwa?


Turab na fita ya kalli bangarenta cikin takaici sannan yace " kin cuci Abba yanda kika ci amanar sa da cutar da mutane sai na nuna miki abinda kika aikata babbam kuskurene, babu babban yaki sai wanda kika yarda dashi yaci amanarki, kijira juya miki baya da zansa Hisham yai, sai kinyi dana sanin abinda kika aikata."
Darajar mahaifinsa kawai taci amma da....Yai kwafa ya tuna yanda aka bashi labari dadin da mahaifinsa yaji a lokacin da aka haifi Abdulmajid.


Kallan bangarenta ya karayi cikin tsananin takaici sannan yai gaba.


*TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*57*


Turab na fita Magajiya ta d'auki kofin da ke gabanta ta jefi madubin dake manne a kilisar.
Mikewa tai cikin tsananin tsoro da fargaba tai cikin d'akinta.
Me ya sani? Me ya sani? Me ya sani?
Wannan kalmar ita kawai take mata yawo a kwakwalwarta gaba daya ta rasa inda zatasa kansa, fitowa tai ta bada umarnin a kira mata Jakadiya cikin gaggawa.
Jakadiya na zaune tasa kwanan abinci agaba sam ta kasa ci akazo aka sanar da ita kiran Magajiya.
Zufa ce ta shiga karyo mata, mikewa tai ta fito.
Haka ta karasa tana ta tsoron abinda zai faru.
Magajiya na zaune a kan gadonta yayi shiru tare da kurama kasa ido.
Ko sallamar Jakadiya bata amsa ba, har Jakadiyar ta zauna tare da gaisheta.
Magajiya bata amsa ba sai dai ta kalleta cikin wani yanayi na zargi, sai kuma ta murmusa tace " Jakadiya ba tin yau ba nasan tabbas sai gulna da tsautsau bakinki yasa kin sanar ma Turab sirrin Abdulmajid."
Jakadiya ta zaro ido sannan ta tuno kalaman Turab a yayin da ya mike zai fita bayan ya gama mata fada " Kada ki kuskura ki nunama Magajiya munyi maganar nan dake, duk yanda taso ta bugi cikinki ki tabbatar baki bar wata hanya ba dazai sa ta fahimta, nagode da sanar dani da kikai."
Ya juya ya fita, tunowa datai da kalamansa yasa tai saurin zubewa tace " Gimbiya Magajiya ta yaya zakimin wannan shaidar? Bayan shekaru sama da ashirin ina rike da wannan sirrin? Sai yanzu ne zan tona? Inci ribar me?"
Magajiya ta kalleta tace " Amma ai kwanaki kin min birga akan sirrina da kike rike dashi sannan banida tabbas ke d'in yanzu a bangarena kike duba da abinda kikamin."
Magajiya ta daure tace " Gimbiya bani bace, me nene ma zaisa in fadamai?"
Ganin yanda Jakadiya tai yasa ta gamsu akan ba ita bace, ta kalleta tace " bani guri."
Fita Jakadiya tai, tana zuwa waje ta saki wani ajiyar zuciya.
Magajiya kam tana fita ta dafa kanga cikin tashin hankalu tace " ba wannan bane, tunda duk gidan Jakadiya ce kawai tasan wannan sirrin, tunowa tai da Hajiya, ba dai Hajiya ce ta fad'i dayan sirrin ba?"
Mikewa tai da sauri ta fito, ta sanar ma Bayinta akan zuwa bangaren Hajiya.


Tana shiga wannan baiwar ta taho gunta da gudu ta gaisheta.
Magajiya ta kalleta bata amsa mata ba tai ciki.
Mai kuka da ita wacce tafi kusanci da Magajiya ce ta kalli Baiwar tace " kina zubawa?"
Cikin tsoro tace eh, dan bazata iya cewa ta batar da maganin ba dan ta tabbata inhar ta fada to lalai kwananta ya kare.
Magajiya na shiga ciki ta rufe kofa.
Kallan d'akin tai a wulakance sannan ta toshe haccinta wai wari.
Zama tai daga nesa da Hajiya sannan ta kalleta cikin jin dadin yanda take shan jiki ba damar magana tace " Hajiya? Kin ganeni?"


Kallanta Hajiya tai, tana ganin Magajiya ta shiga yunkuri tanasan magana ta kuma kasa, Magajiya tace " Lalai Hajiya kiji da jikinki har kike wani yunkurin magana? Da nadauka ko kinsamu sauki ne harkinyi tsautsayin yin magana amma yanzu naga ba haka ba, bakya tunanin ya kamata ki sallama komai na duniya ki jira mutuwa tazo ta daukeki?"


Hajiya yunkuri take sosai, ganin ba dama yasa tai shiru sai hawaye da yake ziraro mata ta gefen ido, tunowa tai da abinda ta gani.


{
" Wasika aka ba da akawo mata tashin safiyar yau, amsar wasikar tai ta bud'e, kana kallan rubutun kaga rubutu ne na 'yan koyo, sai dai da yake bata iya karantawa ba yasa ta ajiye wasikar a tunaninta ba mai amfani bace.
Sai dai me? Kwana hudu kenan ana aiko mata da wannan wasikar sannan yaro ne yake kawowa kuma daga ya bada yake sa gudu yai waje, yau abin ya fara damunga dan da alama magana mai mahimmanci ake san sanar da ita.
Sawa tai a kira mata Rabi'a, bayan tazo sun gama gaisawa ta d'auko wasikar ta bata tace " Karantamin."
Rabi'a ta amsa tare da bud'e wa.
Na farko an rubuta "Hajiya d'anki na cikin matsala."
Na biyu " Hajiya ki yafemin sai dai ba yanda zanyi dolene na cigaba da zuba maganin nan inba haka ba Magajiya halakani zatai."
Na uku "Hajiya ki taimaken ki d'au mataki ko na samu zunubina ya tsaya anan."
Na hudu " Hajiya kiyi wani abu dan Allah."


Hajiya ta amshi takardar a taorace tace "Rabi'a kin tabbatar da abinda aka rubuta kenan?"
Rabi'a tace "Hajiya wlh abinda akace kenan amma me hakan yake nufi? Magajiya tana ba sarki magani? Akan me?"


Hajiya tace " jeki gida sannan maganar nan ta zama sirri tsakaninmu koda wani abu zai sameni kimin alkawarin bazaki taba fadan wata kalma ba."
Rabi'a tace "Na miki alkawari, nan ta mata sallama ta fita da tsananin mamaki, bazata taba iya ma Hajiya musu ba."


Tana fita Hajiya ta kona takardar sannan tai shiru tana tunani, ba wanda ta yarda dashi bare suyi maganar dashi, sannan batasan wacece tayo mata wasikar ba, gashi ita ta tsufa ba wani abu da zata iya yi.


Abu d'aya ne ya dace tai shine taje gun Magajiya dan nuna mata ba tsoronta ake ba sannan ga fadamata inhar bata daina ba zata sanarma Sarki.


Yau da safe tasa aka kira mata Magajiya, tun safe aka sanar da ita amma sai yamma liss sannan tazo.
Hajiya na zaune da charbi, zama tai akan kujera sannan tace" Hajiya kim wuni lafiya?"
Hajiya cikin takaici ta kalleta tace " me kike bawa d'ana?"
Magajiya ta kalleta cikin mamaki tace "me nake ba d'anki kamar ya kenan?"
Hajiya tace "Kamar yanda kikaji haka yake, wani tuggun kike dubgawa Abdussamad, nasan dai ba maganin mutuwa kike bashi ba tunda zamansa a mulki shine zamanki kema a mulki, sanar dani me kike masa?"
Dama Magajiya na tsananin jin haushin Hajiya dan tunda aka aureta tasan ba santa takeyi ba, fuska ta canza ta d'aure fuska tace " koma me nake bashi ai mijinane sannan bakida ikon shiga tsakanin mata da miji."
Ta mike zata fita, Hajiga abin ya bata mamaki tace " waye ya haifa miki har kika aura? Sannan ni dama tunda na fara ganinki wlh nasan ke ba alheri bace a gareshi ba kuma matar zama bace ta amana, ko kiyi gaggawar daina abinda kike bashi ko kuma wlh in sanar dashi, zakiyi mamaki inkika ganki a gidan yayanki da takardar saki, ba'a saki a gidan sarauta bari sakin uwargida wacce take sarauniya sai dai ina sanar miki za'a fara akanki."


Wata banzan dariya Magajiya tai tace " Me? Ni za'a saka?"
Hajiya ta kalleta sai dai yanda taga Magajiya tayi yasa tsoro ya d'arsu mata dana sani ya kamata me yasa bata fadama d'anta ba ta sanar ma Magajiya?"


Magajiya tazo kusa da ita ta sakar mata murmushi tace " ina jiran lokacin da za'a bani takarda, ki kuma tabbatar an bani, sannan maganar magani maganin hana d'aukan ciki ne ki tabbatar kin sanar dashi haka."
Ta juya ta fita, tana kallan Hajiya duk ta rikice jikinta ya d'auki rawa.
Bayan Magrib tanashan ruwa shikenan ta kasance ba lafiya tun daga wannan rana har yau ba baki ba zama bare tafiya."
}


Magajiya ta mike tazo saitin kunnen Hajiya tace " Kijira d'ana ya hau mulki in har kinada rai ni zan taimaka a fitar dake daga gidanan akaiki can bayan gari ki zauna kyafi jin dadin zaman duniyar, in kuma kinaso in hada da jikanki da kuma uwarsa Basira ku zauna tare acan."
Ta mike tai waje.
Tsayuwa tai a wajen gidan, me turab ya sani? Bataji akwai wanni babban sirri dazai tsoratata da ya wuce wad'an nan biyu, sauran duk sai dai tasa a aikata amma badai ita dakanta ba, inma zancen kashe yayan Basira ne ai ba ita bace tai Hisham ne.

Dolene ta nemi Turab ta kuma bihi cikinsa da jin sirrin da ya sani.


Turab zauna akan kujera yana d'an kada dan yatsansa d'aya tunani yakeyi wace hanya ce mafi sauki da kuma bakin ciki da zai sa Magajiya ta fita hayyacinta in taji Yayanta Hisham yaci amanar ta? Ya tabbata Hisham da Magajiya kowa amfani yake da dan uwansa.
Ita tana amfani dashi dan cikar burinta, shi kuma yana amfani da ita dan samun matsayin da zai wuceta nan gaba, murmushi yai yace " Badai tana tunanin in Abdulmajid ya hau mulki komai na burinta ya cika ba?"


Mikewa yai ya fito waje.
Hango Abdulmajid yai a zaune yana shan iska jiyai tausayinsa ya dan darsu mai, ya zaiji in yaji wannan sirrin? Yauce rana ta farko dayaji tausayin Abdulmajid ya kamashi.


Ya zaiyi ya sa Magajiya da Hisham su tunama junansu asiri da kansu?
Khadija!
Shiru yai jin sunan daya zo mai, tabbas itace a tsakanin mutanen biyu, ita da Abdulmajid, sai dai me? Zuciyarsa zata iya jure amfani da ita?


Juyawa yai ya koma ciki tare da furzar da iska mai zafi.......




*TURAB*

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*58*


Duk yanda Magajiya tai akan samun mafita ta kasa, da sassafe kuwa ta aika akan a kira mata Hisham.
Ko gaisuwarsa bata amsa ba tace " Yaya inaji fa yaran can yasan wani abu namu."
Gabansa ne ya fad'i kallanta yai sannan ya tuna kawo Khadija gida da yai, ba dai wani abu ta fada mai ba?
Daurewa yai yace " bangane ba? Me ya sani?"
Ta girgiza kai tace ban sani ba sai dai daga yanda yazomin da kuma yanayin kalamansa inada tabbacin yasan wani abu wanda yafi fyaden da akama Basira."
Hisham ya sauke ajiyar zuciya jin da alama ba Khadija bace yace " amma kinsan yaran nan shegen yaro ne anya ba dan karkiyima Mahaifiyarsa wani abu bane?"


Magajiya ta girgiza kai cikin yanayin tunani tace " Yaya bakaga idanun yaran nan ba alokacin, sannan cemin fa yai in fara hada kayan lefensa yaban zuwa sati biyu, kamar ni dan karamin yaron da ko uwarsa na girma yazomin da zancen rainin hankali irin wannan?"


Hisham shi kansa yayi mamakin jin haka yace " da kuma bakinsa ya fad'a miki hakan?"
Tace " anan gun kuwa, sannan harda cemin in sa Abdulmajid ya janye auren Mairo, umarni fa yazo ya bani wanda ko ubansa bai taba ban umarni akan abinda yasan ina duk wani abu na ganin na hana wannan abun."


Hisham yace " da alama yasan wani abun to amma ta yaya?"
Magajiya ta juya kai tace " wannan shine abinda ke damuna."
Shiru sukai kafin can ta kalleshi tace " Yaya"
Kallanta yai yace " ya zakiyi?"
Murmushi ta saki tace " kamar ni? Abinda yafi damuna kenan dan jiya ko baccin kirki ban samu ba, kamar ni Magajiya ace wannan yaran zai kalla ya bani umarni?"
Hisham a ransa yace " an tabo Masifa."
Magajiya ta kalleshi cikin iza tace " zanyi abinda yace bayan na tabbatar da akwai sirri na a hannunsa, zanyi lefe zan kuma sa a sa rana, zan nuna ma jama'a Turab ma d'anane."
Hisham cikin tsananin tsoro ya kalleta dan ya tabbata wank mugun abun zata fada daga karshen abin arzikin datai, dan yasanta haka take in har aka bata mata rai sai ta nuna bakomai Sai kuma tayi abinda baki bazai fadu ba.


Magajiya ta kara wani murmushin jin dadi tace "Aure? Auren Bilkisu?" sai kuma ta sa dariya tace " lalai nayi gangancin barinka da rai."
Hisham ya kalleta yace " me kike tunanin yi?"
Kallansa tai sannan ta wani juya ido tace " sai muga ranar auransa waye zai je gun, mai makon kaga ai aure da shi a d'aura da Abdulmajid sannan su gama d'aura aure suzo su tadda angon da aka shirya za'ai dashi a kwance ba numfashi."


Hisham ya kalleta yace " ban fahimceki ba....."
Tace "Zaka fahimceni, dan kuwa kaine zakasa a kamashi a hanyarsa ta zuwa d'aurin auran, sannan musa abokinsa dole ya sanar akan bazai samu zuwa ba dan shi ba auran yake so ba, kaga ran Sarki zai b'aci matuka ya aura ma Abdulmajid Bilkisu sannan mai makon mu sakeshi lafiya sai mu juya abin a matsayin 'yan fashi ko kuma hatsarin mota, kaga mun jefi tsuntsu biyo da dutse d'aya."


Mamaki ya hana Hisham magana kawai kallanta yakeyi.
Kallansa tai tace " ya? Wasan nawa ya had'u?"


Idanunta ya kalla yace " Magajiya kenan, duk duniya Allah bai taba hadani da mai kaifin basira irinki ba, da ace Basirarki a abu mai kyau kike sa ta lalai da ancigaba a gidan nan."
Harara ta makamai tace " mai kake nufi?"
Jinjina ya mata da hannu yace " komai yayi nake nufi."
Tace " Uwata fa?"
Sai daya had'iyi yawo yace " tana gida ba lafiya."
Cikin kulawa tace " da alama sam yaya baka kula da Khadija, inaji zan dawo da ita gabana har tai aure, munyi magana da Mahaifin Saifullahi yace tunda yara sun daidaita zasu kawo kudi."
Hisham yai murmushi yace "Allah ya kaimu."
Kallansa ta kuma yi tace " Ya ake ciki a fada akan maganar auran Abdulmajid da wannan sakaryar?"
Hisham yai tsaki yace " kwana biyu dai anyi shiru da maganar dama Galadima ne uban san kawo maganar da Turaki."
Magajiya tai shiru kafin tace " Gun Abu Turab zani yanzun nan dan in tabbatar da abinda yake dashi."
Hisham ya kalleta yace " da kanki zaki? Ba gwara ki aika yazo ba?"
Murmushun jin dadi tai tace " ai tun yanzu za'a kulla abotar d'a da uwa saboda gudun zargi da zai biyu baya."
Kallanta yai sannan yai kasa dakai.
Mikewa tai ta fita sannan shima ya fito.


B'angaren Turab suka nufa, mai kula da kofarsa ne ya bud'e tsananin mamaki ya kamashi na ganin Magajiya.
Su kansu mutane duk wanda yazo wucewa alokacin sai dayai mamakin ganinsu.
Bud'e mata kofa yai tare da gaisheta.
Magajiya ta shiga tana kanta tsaye.
Garzali ne ga taho da sauri tare da gaishesu.
Magajiya ta kalleshi tace " Turab fa?"
Yace " yana d'aki."
Nan ya nuna mata hanyar falo ta shiga.
Tsayawa tai tana kallan bangaren, abinda ko bangaren Abdulmajid tunda ya tasa bata zuwa.


Garzali yai ciki dan kiran Turab.
Abu Turab ya gama sa kaya kenan yaji ana kwankwasawa, yace waye? Garzali yace "nine kayi baki ne."
Bai tambayi waye ba sai huka da ya saka ya sa turare ya fito.


A zaune ya ganta tayi zamanta na isa akan kujera.
Mamaki ne yasa ya ja ya tsaya tare da jingina kansa da bango, yace " Umma Magajiya da kanta?"
Alama tama bayin da su fita daga falon,saj da suka fita sannan ta kalleshi tace " tsayuwar anan ta menene? Abun mamaki ne in uwa tazo ganin d'anta?"


Kallanta yai sannan ya tako a hankali yana cewa " inafa abin mamaki, dama ai hakkinta ne na ta kula da d'anta."
Ya karasa maganar tare da zama.
Kallansa tai tace " nayi tunani akan maganar ka sai dai banaji kai ka isa ka bani umarni sai dai In zaka canza yanda kamin magana daga umarni zuwa roko."


Kallanta yakeyi har saida tazo karshe, gani tai ya sakar mata wani bazawarin murmushi yace " ko?"
Ranta ne ya d'an soso ta kalleshi.
Yace " kin fara had'a kayan? Ko dayake jiya mukai maganar bazai yiwu ace kin fara ba, amma ina sanar miki sati biyu na baki kacal in har kika wuce ina tausayin halin da zaki shiga dan banaji Sarki zai barki da ranki, in kuwa har ya barki to lalai a kurkuku zaki karasa rayuwa daga ke har yayanki."


Gabanta ne ya fadi, ta daure tare da kakaro dariya tace " inji wa kenan? Kai kana tunanin duk duniya akwai wanda ya isa ya hukuntani? Sarki? Hahah lalai yaro yaro ne."


Turab kallanta kawai yake, jin kalamanta yasa ya mike tsaye yace " Ba sarki bane zai hukuntaki Umma mantawa nai, nine nan d'anki wanda zai hukuntaki, ya kuma hukunta duk masu hannu a abinda kuka aikata."


"Ahhh, bansan me yasa nake tausayin mutanen da kukai amfani dasu gun cimma burinku ba, sai dai ina tunani anya zasu yafe muku? Sannan Hisham da kike takama dashi...."
Sai kuma yai shiru tare da yin kasa da kai yana dariya yace " ke kina tunanin zai cigaba da bin umarnin ki har sai sanda kika jefashi halaka?"
Kallansa tai cikin mamaki tace " mene?"
Kafada ya d'aga mata ya girgiza kai yace " Bansan komai ba."
Juyawa yai yace " in kin gama ganin gidan d'an naki kya rufomai kofa."
Ya juya yai ciki ransa a b'ace,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login