Showing 12001 words to 15000 words out of 146065 words

Chapter 5 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

Kai ta jinjina tace " zaiji mana, sai dai ai a karkashinka yake, sannan in munaso mu girmama Basira shi din ya kamata a tura."


Sosak Sarki ya gamsu haka kuma ya amince da wannan shawara.


Bayan Magajiya ta dawo b'angarenta tasa aka kira Hisham, ta kalleshi tace " gobe ka shirya kai zaka taho da Basira sai dai inaso ka sani banaso inga Basira a gidan nan daga ita har abinda zata haifa."


Tana gama fadar haka ta sallami Hisham ba tare da ta jira abinda zai ce ba.




**********


Washegari kuwa da sassafe Mai Martaba yasa suka kama hanya, mota biyu sukau saboda in an tashi d'aukota yace a taho da Matar Amadu saboda ta kula da ita inta sauka, ganin ita ta gidace ba wai dan baza'a bata kulawa a gidan nasa ba.




A can garin Katsina kuwa Basira tun dare take nakuda mai azabar wahala, banda juyi ba abinda takeyi duk sun jigata daga ita har abinda ke cikinta har matar Amadu, sai asuba ta sauka, ta haifi d'anta santalale mai tsananin kama da Mai Martaba, duk da dai ance jariri ba'a gane kamarsa sai dai wannan kam kallo d'aya zakamai ka san ba Basira bace.


Tana haihuwa wani nannauyan bacci yai gaba da ita, Matar Amadu ta gyara d'an tas sannan ta gyara gun, ganin yaron ya tafi bacci yasa ta zo ta tashi Basira ta gyara ta, sannan tace ta koma ta kwanta bayan ta d'anci dumame.


Shiru Matar Amadu tai tana tunani, ga Amadu bai dawo ba gashi Basira ta sauka, ganin zaman ba shine mafita ba yasa ta mike ta fito tai gidan yayanta dake nan kasan layinsu.


Babban d'an yayan ta samu tace maza yaje ya samu motar da zatai Zariya ya hau, ta bashi sako akan yaje gidan Sarki ya nemi Amadu in bai ganshi ba yace a sanar ma Sarki Basira ta sauka ta haifi Namiji.


Sai dataga ya hau motar sannan ta juyo gida, kazarta ta kama ta yanka ta shiga gyarawa, Lantana na aikin gida.


Rashin sani sam itabatai zaton Amadu na hanya ba.

Su Amadu sun iso wajen azahar nan ya tarar da abin farin ciki wanda ya kasance na babban bakin ciki ga Hisham, sai ma da aka miko mai yaron yana bacci ganin katon yaro nau kama da AbdulSamad yasa hankalin Hisham ya kara tashi, jiyai kamar ya shake yaran ya mutu.


Matar Amadu ce ta kawo musu ruwa da abinci ganin yanda Hishan yake kallan jaririn ne yasa ta tsorata ba shakka kana gani kasan kallo ne na saka mugun abu a rai.


Hisham jin motsin ajiye tire yasa yai saurin kallanta sannan ya canza fuska, itakam tana ajiye wa ta juya tai ciki, zuciyarta fal da tunani.


Bayan yaci abinci ne yace zaije ya samu hakimin nan garin ya kwana a gunsa zuwa gobe tunda bai kamata su kama hanya yau ba.


*******


A can kuwa Sani ya isa Zariya ya sauka ya gangara masarauta, a bakin kofar shiga dogarai suka tambayeshi inda zashi, nan ya sanar dasu gun Kawu Amadu yazo wato yayan Basira wanda yazo jiya, nan suka sanar dashi ai ya koma katsina yau, jiki a sanyaye ya juya, har ya d'anyi nisa sai kuma ya dawo yace " ku sanar da Mai Martaba dama Yafendo ce ta sauka yau da asuba, an samu d'a namiji."


Kallan mamaki dogaran sukamai suka ce Yafendo?wacce kenan?"


Sani cikin halin ko in kula yace "Basira."


Kallan juna dogaran sukai sannan suka kalleshi sukace " da gaske ta haihu?"


Kai ya d'aga alamar eh, gani yai sunyi ciki da sauri ko kulashi basu sake yi ba, tsayawa yai yana mamaki, ganin ba kowa a kofar shikam ya shige ciki.




B'angaren Magajiya sukai tana zaune a kilisarta dan ko abinci ta kasa ci, bayan sun nemi izini ne suka shiga ciki suka zube a kasa suka kwashe komai suka sanar da ita, zumbur ta mike cikin tashin hankali sai dai ganin su waye a gabanta yasa ta daure ta saki fara'a tace " Alhamdulila kun sanar da Sarki?"




Sukace "munje baya fada shiyasa muka garzayo nan."


Tace " dakyau ba sai kun fadamai ba bari ni na sanar dashi da kaina, ko kuma dukanmu kar mu fadamai sai dai kawai mu bari in ta dawo gobe ya ganta da d'a lalai zai sha mamaki."


Kai suka jinjina alamar gamsuwa sannan ta basu tukuici ta sallamesu.


Shikam Sani ciki kawai yai ta shiga har ya ganshi a wajen wasu mutane, a tsatsaye a waje da alama magana mai nahimmanci suke tattaunawa kuma yaga duk wani mutum akewa maganar.


Gun ya karasa ya gaishesu, kallansa sukai cikin mamaki,Barde wanda ke tsaye ya kalleshi yace " Lafiya?"


Sani ya kara sanar dashi yanda ya fadama dogaran.


Barde cikin zakuwa yace " ka tabbata?"


Yace " sosai nidin ai d'an yayar matar Kawo Amadun ne."


Barde ya kama hannunsa cikin sauri sukai gaba.


Gun Mai Martaba ya kaishe yace ya tsaya a waje shi kuma ya shiga ya sanar da Sarki.




Sarki kam wani irin dadi ne yake ziyartarsa ji yake kamar zaiyi me dan dadi, nan ya bada umarni a ba Sani tukuici mai tsoka.


Magajiya ta rasa abinda zatai da sauri ta aika a kira mata Inna Lami(sry zamusa Inna Lami tunda a lokacin ba Aunty.)


Lami tana shigowa ta tsinci labari a sama yana yawo akan haihuwar Basira.


Cikin hanzari ta juya tai waje, gun malaminta ta nufa ta sanar dashi komai.


Kallanta yai sannan yace " yanzu me kikeso ayi?"


Tace "an riga an haifeshi ni kuma ban taba kisa ba kuma itama Magajiya nasan bazataso muyi kisa ba dan haka so nake a nakasar dashi.


Kallanta yai yace" Nakasa wace iri?"


Tace waccece zata hana mutum yai tunanin hawa mulki? So nake a nakasar dashi a yau yanda in sukazo gobe za'a dauka a haka aka haifeshi."


Dariya yai sannan yace " na baki ko na ido? Sune babban nakasu da zasuma mutum."


Lami tai shiru can tace " ido, a hanashi gani yanda ko uwarsa bazai sani ba balle ubansa sai dai muryarsu, tunda munyi iya yinmu akan karyazo duniya amma sai da ya zo."


Tana zaune anan ya gama abubuwansa sannan ya bata wani yace ta binne, nan ta bashi sallama ta mike ta fito cikin farin ciki.


Sai daya gama komai sannan ta shiga gun Magajiya ta sanar da ita.


Magajiya ta kalleta tace "kina ganin zai kama?"


Tace kwarai kuwa kuma nina fada miki gobe ba ido zaizo gidan nan.


Ajiyar zuciya Magajiya tai cikin damuwa......




_Hmmmmmm_




*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)





*HASKE WRITERS ASSOCIATION*


*Wattpad :-AyusherMohd*



*Na Ayusher Muhd🤸🏼*




*9*




Sosai Barde ya ba Sani tukuici sannan ya kamo hanya.


Shikam Hisham tun da suka isa masauki ya kasa zaune ya kasa tsaye can ya gaji ya koma ya zauna tare da bubuga 'yatsarsa a guda d'aya a kasa alamar yana cikin dogon nazari ba shakka dolene ya d'au mataki sai dai ta ina?kuma ta yaya? Ganin yaron ma yasa hankalinsa ya kara tashi matuka, ba shakka in har Mai Martaba yaga yaran nan to fa su tasu ta kare, tunda shi jininsa ne.


In mun tafi a hanya in jefar dasu a tsakiyar daji ne? Abinda ya fara fad'o mai kenan a zuciya, kai ya girgiza da sauri yace in nai haka kuma ai zasu koma gidan a hankali tunda da kafarsu kuma zasu iya samun taimako.


Insa a je gidan a kashe su yau? Kai ya girgiza yace na tabbata in nai haka sai an zargeni tunda dai ina garin.


Idanunsa ne ya kada sosai na bakin ciki, gashi dare yayi bare ya tafo daura gun mai magani.


Ko guba zan....... Kai ya kada da sauri alamar rashin gamsuwa, idanunsa ya rufe cikin bakin ciki, jiyai daga wajen d'akin da yake wasu na hira "wlh jiya ai munga abin mamaki, tas fa wutar nan ta cinye gidan daga mata da mijin har yaranta biyu ba wanda ya tsira."


Zumbur ya mike yace wuta.....Wani murmushi ya saki na gamsuwa da shawarar data zo mai a yanzu.




Turawa yai a kiramai wani bawansa wanda ya sa aka bashi matsayi a gidan sarauta saboda tsabar yardar da yamai, bawa ne wanda baya ko tambayarsa dalili in ya saka shi abu, baya taba musa mai ba kuma ya neman sanin dalilinsa na sashi abun.




Yana zuwa ya jashi cikin kuryar d'aki ya sa bakinsa a saitin kunnensa alamar rad'a ya fara mai bayani wanda ni da nake tsaye a gun ma bansan mai ake cewa ba.




Itakam Basira da Babynta bayan Magrib suna kwance akan gado Lantana na kasa tana ninke kayan data wanke tana ta shirya musu jaka matar Yayanta ta shigo.


Basira na ganinta ta fara kokarin mikewa, da saurin tace " koma ki kwanta."


Itakam Basira mikewa tai ta zauna, kallan Lantana matar tai tace "Lantana d'an bamu guri."


Da sauri Lantana ta mike tai waje.


Kallan Basira tai sannan tace " Basira."


Yanda ta kirata yasa Basira ta tattara hankalinta gaba d'aya kanta.


Ta cigaba " Wani irin zama kukeyi da Yayar wanda yazo?"


Basira tace " zaman mutunci mukeyi."


Ido ta kura mata sannan tace " gaskiya nakeso ki fadamin."


Basira taja numfashi sannan tace " wlh da gaske nake tana kula dani nidin ce zuciyata taki yarda da ita."


Meyasa? Abinda taji ta fada kenan.
Basira tai shiru kafin can tace " gabana fad'uwa yakeyi in na ganta."


Shiru tai sannan tace " ki nutsu kiji mai zance, tun bayan zuwansu hankalina yaki kwanciya da yanda naga yayanta yana kallan yaron nan, kallo ne na tsana tsantsa."


Basira tai murmushi tace " kedai kila baki fahimceshi bane amma......"


Katseta tai da cewa " Basira zaman gidan sarauta ko ba'a fada ba kasan ba wai zama bane wanda kowa zai soka, bare ke da kika haihu, ki kasance mai hakuri sannan kar ki bari ko kad'an a cutar miki da d'anki."


Murmushi Basira tai tace " ki daina damuwa ba komai insha Allah."


Sun dade a d'akin kafin ta mata sai da safe ta fito.




Wajen karfe 1 na dare Basira ta farka sakamakon kukan da Jaririn yake mata, kuka yake sosai ta mike tana bashi mamma, Lantana ta amsheshi tace kawoshi na fita dashi na lallabashi ki samu ki kwanta.


Nan ta amsheshi tai waje dashi, kamar wasa tana jijashi taga hayaki sosai yana tasowa daga wajen d'akin Amadu.


Cikin tsoro ta koma ciki dayakr ta kofar baya ta fito a kuma nan d'akin Basira yake, Basira ta gani tana ta tari cikin bacci.


Nan ta fara tashinta, dakyar ta samu ta tasheta, ganin yaron nata tari shima yasa Lantana tasa zani ta goyashi.


Basira cikin tsoro tace " menene hakan?"
Lantana tace bansani ba nima sai dai hayaki na tasowa daga can.


Da sauri Basira ta mike ta nufi ciki, tana bud'e 'yar karamar kofar da zata sadata da wajen su Amadu, da yake gini ne irin namu na da, kowa da inda yake sai dai shi yayi dabarar ginewa tsakanin nasu da inda Basira take sai yar 'yar kofa a gun.


Basira na bud'ewa taga wuta sosai tana ci ta b'angaren su Amadu, ihu sosai ta kwalla wanda yasa Lantana tahowa da sauri.


Ganin yanda wuta ke cin b'angarensu Amadu har ta fara gangarowa inda suke yasa ta saki ihu itama, daga waje sukaji mutane an fifito, Basira kam neman cusa kai takeyi b'angaren su Amadu, ganin yanda ta fita hayyacinta tana ihu tana kiran yayanta da matarsa yasa Lantana ta fara jan hannunta.


Fizgewa tai da karfi ta kara nufar ciki, Lantana ta kara riketa tana ihu akan a kawo musu a gaji, nan wasu maza sukai tunanin bi ta baya, suna shiga sukaga yanda Lantana ta kankame Basira tana ihu, nan fa suka kamo Basira sukai waje da ita, ihu take sosai akan a taimako mata yayanta.


Suna kaiwa waje gidan ya kara kamawa sosai ihu sosai Basira take ana ririketa, can ma kawai sai gani akai ta suma.




Mahaifin Sani wanda yazo gun yasa aka kaita gidansa, sosai ranar anga tashin hankali a unguwar, daga Amadu har matarsa sun kone a ciki, dan da alama bacci suke wuta ta taresu.


_Nace Allah ya jikansu Ameen_


*******


Itakam Basira sai wajen asuba ta fardo, kuka kawai takeyi, sai wajen hantsi bayan anyi jana'iza mahaifin Sani ya kalleta cikin tausayawa yace "Basira ya akai wuta ta kama haka?"


Kai ta shiga jijigawa akan bata sani ba, shiru yai sannan yace " da matsala."


Kallansa tai cikin mamaki tace name?"


Yace " Basira wanda suka zo gidanku jiya masu rawani dan bansan matsayinsu ba."


Kai ta gyad'a alamar ta sansu, yace "kinsan ko jana'iza basu zo ba, kawai tambayata yai akan kina raye? na sanar dasu kina raye kina gidana, sai ya tambayan yaron fa? Ni kuma sam banga yaro ba alokacin sai nace mai ban sani ba gaskiya dan nima a rikice nake, abinda yaban mamaki yanda naga idanunsa sunyi alamar bakin ciki na kasa gane bakin cikin namenene a ciki, na rashin mutuwarki ne ko na rashin sanin halin da yaron yake ciki."


Zatai Magana Lantana ta zo da sauri tace " Ranki ya dade nima naga Kafilu(wannan bawan na Waziri) a lokacin da muka fito sai dai abinda yaban mamaki daga nesa na ganshi ina kallo ya juya yai gaba ba tare da yazo inda muke ba."




Basira ta kalleta tace "ya akai kika san shine bayan dare ne?"




Tace " akwai hasken farin wata sannan akwai hasken wuta da take ci."


Basira bata sake magana ba ta mike zata fita, jitai yace " ni zan fita gun amsar gaisuwa."


Basira ta mike ta koma ciki, kallan Abu Turab tai sannan tai shiru tana tunani, randa ta zubar da jini sosai har ta d'auka tayi b'ari shine ya fara zuwa mata, ba shakka ranar abu d'aya taitacu wato tuwon da Magajiya ta kawo mata, sannan ansha sanar da ita akan ta kiyayi Magajiya da Yayanta dan hatta Mahaifiyarsa sai datace mata tai a hankali da Magajiya.


Tuno maganar matar Yayanta tai, zumbur ta mike idanunta duk sun kumbura.


Hijab ta zura tai waje, tana gani yanda mutane suka taro a waje amma da yake idanunta sun gama rufewa yasa tai gaba.


Gidan Hakimi ta nufa inda Hisham yake, basu tsaya mata wasu tambayoyi ba suka mata izini ta shiga wani ya mata jagora, sai da suka kusa zuwa d'akin da yake sai wanda ya mata jagorar yace " bari na kirashi."


Nan yai gaba, daga lungun dake bayanta taji ana magana kasa kasa, jitai ance " ina kallansa ya fita da daddare ni kuma da gulma sai dana bishi wlh a idona ya d'au kalanzir da ashana yai gidan."


Nidai tsoro yasa na juyo, ni dama nayi mamaki sosai danaga Waziri kamar bai damu ba da haihuwar nan bayan kuma kowa yasan abokin takara zai zamewa d'an Magajiya nan gaba."




Jikin Basira ne ya fara rawa, da sauri ta juya cikin kid'ima, tana shiga gida ta kalli Lantana dake cikin mutane alama ta mata da hannu akan tazo, d'aki suka shiga, Basira cikin rikicewa tace " Lantana ke Baiwa ta ce ko?"


Kai ta d'aga, tacigaba " kin yarda da duk abinda zanyi?"


Nan ma ta d'aga kai, Basira tace " zan fara fita, zan tsaya a karshen layin nan in nai minti biyar ki biyoni.


Ba tare da tambaya ba Lantana ta amsa da to, Basira ta kalli Abu Turab tace "Dolene in kareka, nayi rashin yayana da matarsa akan shirme da rashin wayau na dan haka bazan yarda inyi rashinka ba a wannan halin, hawaye ne suka shiga zubo mata, lalai bazata taba yafema Hisham ba in har da bakin Magajiya itama bazata taba yafe mata ba, sannan zata kare d'anta har zuwa lokacin da zai girma ya daukar mata fansar abinda aka mata.


Cewa tai Lantana ta fita, Lantana na fita ta had'e kai da gwiwa ta saki wani irin kuka mai tsananin ban tausayi.




********
Da yake yaran da suna dadewa kafin ma su dinga bud'e idansu sannan ko sun bude ma ba alokacin zasu fara gani ba shi yasa sam Basira batai tunanin an ma d'anta wani mugun abu ba.


**********




Yanda suka tsara hakan ce ta faro, ta goya d'anta ta fita, ta dade da fita sannan Lantana tabi bayanta.......





_To fa abin babba ne🙊_








*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)





*HASKE WRITERS ASSOCIATION*


*Wattpad :-AyusherMohd*



*Na Ayusher Muhd🤸🏼*




*10*


( Abu Turab an haifeshi a shekara ta alif dubu d'aya da d'ari tara da saba'in da d'aya, shikuma Abdulmajid an haifeshi a alif dubu d'aya da d'ari yara da saba'in, karku manta farkon labarin a shekara 1970 aka fara wanda ya kasance ranar sunan Abdulmajid, a kuma shekarar ne Sarki ya auri Basira har ta samu ciki.)




_Wannan tuni ne_


********
Hisham ya fito sai dai baiga kowa a waje ba, ciki ya koma cikin halin ko in kula dan shi babbar damuwarsa bai wuce ya d'au mataki a kan Basira da d'anta ba dan tuni aka sanar dashi suna raye, ba shakka inya sake wani yunkuri za'a gano bakin zaren shiyasa yake tunanin in suka tafi a hanya ya zama dole ya san yanda zaiyi kafin su karasa garin.





*********


Magajiya tun bayan tafiyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login