Showing 93001 words to 96000 words out of 146065 words

Chapter 32 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

a bud'e har sanda zan tsayar da wasan, zakiga inda mara karfi yake kaskantar da masu karfi."


Magajiya tama kasa magana kallansa kawai takeyi.
Turab ya juya ya fara tafiya, har yayi nisa ya juyo yace " Ahh ki gaida Khadija banaji zan iya zuwa yau ba, ko da yake bata sani ba."


Kallansa tai cikin takaici tace " Kana tunanin ita Khadijan yarda zatai dakai?"


Wata dariya ya saki yace " Khadijan? Kin tabbatar Khadijan da kika sani kike fad'a? Ahh Umma ya zakiyi? Dan Khadija ba sai na tambayeta ba dan nasan abinda ke ranta."
Ya juya.
Jiyai tace " Lalai na yarda yarinta na damunka kanka kuma na rawa, ya zakayi to? Dan kuwa an kusa sa ranarta da Saifullahi."


Bai san me yasa ba amma sai dayaji wani abu ya taba zuciyarsa.
Sai da ya daure ya juyo fuskarsa d'auke da murmushin da yake iya lab'ansa yace " ai mace sai anyi aurenta an shafa fatiha ake tabbatar da mijinta."
Ya juya ya fita.


Agogon dake manne a bangon gun tasa hannu ta fizgo sannan ta bugashi a kasa, kanta ta dafe sannan ta shiga d'akinta, da karfi ta bugo kofar.
Ji take kamar ta saki kara.





**********


Turab na fita ya dafe kansa, ba shakka matarnan bala'ice, wacce mutum zai dinga neman tsari da ita (irinsu sai a karshe zakaji suna cewa sharrin shaid'an ne)


Khadija ya hango daga nesa, tafe take kamar mara laka a jiki, da alama batajin dadi.
Me ya sameta?
Juyawa yai da sauri dan bama yasan zuciyarsa ta nemi yin rawa saboda ita.


Ganin ya juya zai wuce yasa ta tsaya cak, idanunta ne suka ciciko dan taga da alama goje mata yake sanyi, ita kanta bataso shigowa ba sai dai dolene ta fadama Magajiya akan bazata auri Saif ba, ita dai su barta ta karashi rayuwarta a haka, inta tunan mumunan abunda suka aikata ji take baxata iya kallan wata zuri'ar da sunan mutum na gari ba.


Ko me ya tuna sai kuma ya juyo, kallan kallo sukayi daga nesa.
Juyawa yai a hankali ya fara tafiya.


Bata san tana binsa ta baya ba, ji take ganinsa kamar yanasa taji abinda ke tokare a ranta na raguwa.


Yasan tana binsa sai dai ya rasa dalilinsa na nuna mata bai sani ba, sannan ya rasa dalilinsa nayin tafiya a hankali cikin saibi.
Har ya isa bangaren Hajiya.
Yarinyar nan ya gani tana shara, kallanta yai yace " ajiye tsintsiyar ki kuma biyoni."


Gabanta ne ya fadi ta kalleshi tace "Yarima laifi nai?"


Wani mugun kallo ya mata, da sauri tai kasa da kai tace "Tuba nake Yarima."
Ajiye tsintsiyar tai tabi bayansa.


B'angaren sa ya nufa da ita, suna shiga cikin falo ya d'aga hannu cikin zafin rai zai kai mata mari, idanunta ta runtse dan ta gama sadaukarwa.


Saura kiris ya mareta sai kuma ya tsaya cikin tsananin b'acin rai.


A hankali ta bud'e idanunta ta tsugunna da sauri tace " Tuba nake ranka ya dade."








*TURAB*






🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*61*


Jin bataji saukan mari ba yasa ta bud'e ido a hankali, kallansa tai sannan tai saurin zubewa a kasa ta saki wani irin kuka.


Turab idanunsa ne suka canza, kallo d'aya zakamai ka tabbatar da tsantsar b'acin rai, maganin nan ya cilla mata.
A tsorace ta d'ago jiginta ya hau karkarwa.
Cikin kakkausar murya yace " Waye ya saki?" ba wai dan baisan amsar bane, a'a yanaso yasan ko tana danasanin abinda takeyi.


Kasa ta karayi tana kuka sosai tace " Ranka ya dade ka yafe min wlh in na fad'a kasheni za'ai, sannan mahaifina karshensa yazo."


Magajiya? D'agowa tai da sauri jin abinda yace, yanayin kallan da tai yasan dama abinda yake zargi haka ne, kusa da kafaffunsa ta matso tace " Ranka ya dade wlh nima ba'a san raina nakeyi ba, mahaifina na bukatar aiki na gaggawa a asibiti shine akace in ina sa maganin nan za'a biyamai kud'in aiki, sannan komai ua faru in sanar da ita.


Fuskarsa ya shafa da hannayensa biyu a ransa yace Inalilahi wa ina ilaihi raji'un.
Zama yai a kan kujera sannan yace " me ya faru tsakanin Hajiya da Magajiya?gaskiya nakeso ki fadamin, ni zan taimakeki, zan kuma bayar da kudin aikin."


Tana kuka ta girgiza kai tace " wlh ban sani ba, nadai san a ranar da Umma Rabi tazo a ranar ta aika a kira Magajiya, sannan daga ranar aka fara sani aikin."


Turab ya kalleta yace " naji, zan sa Lantana ta koma dake bangaren Hajiya da kula da ita, zan gani ko kinyi dana sanin abinda kika aikata, sannan ki jira hukuncin da zansa a yanke miki, mahaifinki ni zan taimaka mai sai dai ke dole ki fuskanci hukunci."


Kuka take sosai tace " na sani Ranka ya dade, na gode kwarai da cetoni da kai daga cikin masifa."


Turab yace ta tashi ta tafi.
Fitowa yai, ya nufi can cikin gida bangaren kannen mahaifinsa dan zuwa gun Umma Rabi.


Ko Garzali baya yarda ya biyoshi duk da kuwa ya yarda da shi.
*********


Khadija kuwa ganin Turab ya shiga bangaren Hajiya yasa ta juya.
Har zata wuce bangaren Abdulmajid sai kuma ta karkata ta shiga.


Bayan an sanar da zuwanta, Abdulmajid dake zaune abin duniya ya dameshi yace ta shigo.
Khadija ta shiga, kallan bangarensa tai sannan a ranta tace " yafi na ya Turab kyau sosai, da ban kula da hakan ba amma yanzu na gani, ya zakai in kaji kai ba toshen gidan nan bane?"


Idanu ta kura mai tana wannan tunanin, ji tai tsananin tausayinsa ya kamata.


Batasan ma ya miko yazo kusa da ita ba, sai jitai yasa kafa ya d'an harbota.
Kallansa tai tace " Yaya."
Abdulmajid ya hard'e hannayensa ya shiga zagayeta yana kallanta yace " me ya kawoki? Ba dai zuwa kikai akan rabamu da Mairo ba?"


Hannu tasa ta riko rigarsa tace " Yaya wannan zagayen fa? Ai sai jiri ya kamani."


Murmushi yai sannan ya koma ya zauna.
Kallansa ta karayi a ranta tace " ya ya zanyi? in har kaji abinda suka maka wace rayuwa zaka shiga? Alokacin ba ka da wanda zaka gani kaji dadi, komai da kake tunanin naka ne a lokacin xakaga babu abu ko d'aya daya kasance naka, dama ace Mairo na sanshi ne....."


Khadija meye hakan?
Abinda ya fadane ya dawo da ita daga tunaninta.
Fara'a ta saki sannan tazo ta zauna kusa dashi tace " Yaya."


Ya kalleta yace " menene? Nifa na fara shakkar me kikazo dashi naga sai wani kafeni da ido kikeyi."


Murmushi tai tace " yanzu ace kai ba dan sarki bane wace rayuwa kake tunanin zakai?"


Dariya ya saki sosai yace " ban taba wannan tunanin ba, dan tun ina d'an shekara uku Umma ta fara horar dani akan magajin sarki, kinga kuwa banda wannan lokacin."


Khadija ta jinjina kai tace " Haka ne, amma ka taba tunanin rasa mulki?"


Wani kallo ya mata yace "Khadija meke damunki? Kinsan tun ina dan shekara uku Umma take sanar dani ni kadai ne magajin sarki, shi kanshi Abba a lokacin nunamin yake nine magajinsa, a haka na taso har sai bayan zuwan Turab sannan na fahimci canji daga gun Mahaifina wanda hakan na kona min rai, sam ya daina wasa dani gaisuwa ce kawai ke had'amu, bayan da shi dakanshi yake aikawa a kirani."


Yai wani murmushin takaici yace " Khadija duk wani abu na rayuwata a da ina yinsa ne dan faranta ran mahaifina, burina naga ya dubeni yacemin Abdulmajid kayi daidai, sai dai inaa duk wani abu dazanyi bana birgeshi, ko jarabawa ta na kawomai banaji ma yana bud'ewa...."
Wani abu ya had'iya sannan ya kalleta, hawaye ne yaga ya zubo mata.
Harararta yai yace " tausayi na kike?"
Shiru tai batace komai ba.
Yai murmushi yace " tundaga lokacin na tsani Abu Turab tsana mai yawa sannan akoda yaushe Umma na sanar dani shi din fa makiyinane, kar na kuskura ba barshi."
Yai ajiyar zuciya yace " kinsan me?"
Kai ta girgiza alamar a'a
Ya matso alamar rad'a yace " ko kiran mata da nakeyi bangarena yi nakeyi dan in batama Sarki yai ko naki dadin rashin damuwa dani dayakeyi."


Idanu ta rufe a hankali wasu zafaffan hawaye suka biyo mata, kallanta yai yace " Karki damu Khadija, na saba da rayuwa, kinsan tunda nake a gidan nan ba wanda ya taba tambayata ya nake? Tambaya ta kulawa, ina nufin Umma na ko Abba na, ita burinta shine in zama abinda takeso, shikuma dama bana cikin shafinsa."


Hawayenta ta share tace " Yaya me yasa baka taba fad'amin ba?"


Dariya yai sannan ya mike yace " na fizan na zama bad guy, hakan ne zaisa in rage takaicin abinda ke raina, sai dai Khadija kiyi hakuri amma bazan taba ba Abu Turab Mairo ba, ya kwacemin uba, mutane, na bar masa amma banda wannan."


Jitai tama kasa magana, me yasa itama a koda yaushe takejin zafinsa? Gani take baya kyautawa sannan shidin mutumin banza ne? Ashe bakincikin dake ransa ne yake amfani dashi dan kuntatawa na kusa dashi? Ya zaiyi in yaji sirrin nan?


Daurewa tai tace " Yaya kana tunanin Mairo zata soka? Bayan kai din mutum ne wanda yake had'uwa da Magajiya su aikata abinda bai daceba na zalunci?"


Yace "Ahhh zalunci? Hmmm Khadija kenan bana tunanin kinsan Umma."


Kallansa tai tace " bansan ta ba sannan bana bukatar Saninta, sannan kaima Yaya zuciyarka na neman riked'ewa gaba d'aya ta koma ta Umma, ka gaggauta kaucewa daga sharrinta."


Murmushi yai sai dai baice komai ba, a ransa yace "hakan na nufin in bijiremata ita kuma ta yarda ni, ita kadan da nake sa rai tana sona itama ta juyamin baya."
Khadija ta mike tare da kallansa tace " Yaya zanje gurin Umma Magajiya ne, akan maganar aurena da Saif."


Yace " Ya ya? Maganar auren an kusa ne?"


Kai ta girgiza tace " a'a."
Juyawa tai ta fita, aranta tana mai fatan kub'uta daga sharrin Magajiya da Mahaifinsu."


********


Falon yai tsit kamar ba kowa a ciki, Umma Rabi tai shiru kamar ruwa ya cinyeta sannan ta d'ago ta kalleshi.


Abu Turab yace " Umma ki taimaka ki sanar dani, Hajiya na cikin wani hali."


Tace " Turab sirri ne...."


Yace "wa ke zancen Sirri rayuwar Hajiya na cikin had'ari?"


Umma Rabi tai shiru kafin can ta d'ago ta kalleshi.
Nan ta sanar da shi abinda ta sani.


Shiru yai kafin yace "ita waccan d'in wacece? Wacce ta aiko da wasikar?"
Umma Rabi tace " ban santa ba sai dai kafin Hajiya ta fara rashin lafiya da yamma na koma gunta, a lokacin ne ta sanar dani wani sirri wanda ahi nake tsoron sanar dakai."
Yace " na menene?"


Ta dade batace komai ba, yace Umma dan Allah ki fadamin.
Tace " ka tabbatar zaka iya ja da Magajiya?"
Yace " kwarai kuwa."
Yanda yai maganar ya bata kwarin gwiwa tace " Maganin da ake zubawa sarki na hana d'aukan ciki ne."


Tashin hankali.


Bakinsa ne ya shiga rawa yama rasa mai zaice.
Umma Rabi ta kalleshi sai dai itama batasan me zatace mai ba, a hankalu tace " ni kaina ina zargin ciwon Hajiya da Magajiya, sai dai banida shaida sannan bansan wa zan tara da maganar ba."

Turab mikewa yai kamar wanda bashida laka a jikinsa.


Tafiya kawai ya keyi yana tunanin wannan al'amari.


Jiyai kansa ya d'au wani zafi, tsayawa yai a jikin wata bishiya ya dafata, addu'a kawai yakeyi Dan neman sauki a zuciyarsa.




Ya dade sosai kafin ya nufi bangaren Hajiya.


Hajiya kam babu, dan jikinta ba dadi to abune da anriga an gama halakata, ba shakka bai taba ganin mutum irin Magajiya ba, kenan duk wanda yasan sirrita ajali shine zai biyoshi?


Kallo d'aya zakama Hajiya kasan inaa sai dai wani ikon Allah.




***********


Magajiya na kwance a d'aki dan tun tafiyar Turab takejinta haka, a kwance take taji sallamar Khadija.
Daurewa tai ta mike zaune, Khadija ta shigo.
Bayan ta gaisheta, Magajiya tace " Khadijata ina kika shiga? Kwana biyu sam ban ganki ba."


Khadija fuskarta a had'e tace "Ina gida."
Magajiya ta kalleta cikin kulawa ganin duk ta rame, tace " Khadija mai kike tunani akan dawowa nan da zama kafin lokacin aurenki?"




Khadija ta kalleta duk da gabanta na fad'uwa saboda tsananin kwarjini da Allah yaba Magajiya ta daure tace " Dama zuwa nai in fadamiki akan bazan auri Saifullahi ba."


Magajiya ta zaro ido tace " mene? Wace irin banzar magana ce hakan?"

Khadija tace " dama abinda nazo fadamiki kenan."


Magajiya ranta ya b'aci tace " Akan Abu Turab?"


D'agowa Khadija tai ta kalleta, Magajiya tace " ke kina tunanin zan baki Abu Turab?"


Jitai zuciyarta ta dake tace " ina fa zance Ya Turab zan aura? In ba so nake ku halakashi ba?"


Magajiya ta kalleta cikin tsananin takaici tace " in kin san da haka to kiyi gaggawar cireshi a ranki."


Khadija jitai ranta ya b'aci wato duk abinda sukeyi baya damunsu? Tace zasu halakashi amma ko a jikinta.


Sun biyu suna neman ruguza rayuwar mutane dayawa, na farko sun gama cin amanar sarki, sun jefa Abdulmajid cikin halaka, suna neman jefata sannan sun takurawa wanda yake jinin gidan, suna neman halakashi.


Ita kanta batasan tace " To ko Ya Abdulmajid zan aura."


Jitai gabanta yayi wani fad'uwa, mikewa tai tace " wani irin hauka kike fad'a, bakida hankali ne? Ko kanki me ya zare?"


Khadija tace " in har ba Ya Abdulmajid ko Ya Turab zan auraba inaso ku barni, banaji zan yi aure har karshen rayuwata dan bazan iya auren wani da hali irin na mahaifina ba."


Magajiya tace " Khadija? Me kike cewa?"


Mikewa tai saboda ta fara jin dakewar tata na neman gazawa tace " na barki lafiya."


Magajiya mamaki ma ya hanata magana sam, anya Khadija ce? Ba waccan tsinanen yaran bane ya zigata kuwa? Yace tace a aura mata Abdulmajid?


Jitai idanunta sun daina ganin komai sai duhu, baya tai lyuuu kamat zata fadi sai kuma tai saurin rike gadon tana maida numfashi.


Cikin wata sarkakiyar murha tace " *ABU TURABBBBBBBBB*"








Nima na tayata fada *ABU TURAB😂*
*KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*62*


Khadija tana fita ta samu guri a waje ta xauna, jitai jikinta duk ya kaure da rawa, ba shakka wannan ce rana ta farko da tai tafa kukewa tai ma wanda ya girmeta magana irin haka, balle Magajiya mace mai tsananin kwarjini da mulki.


Mikewa tai a hankali, so take ta samu Abu Turab taji a wani mataki na aure ya d'auka tsakaninsa da Mairo? Dan ba shakka tana san d'an uwanta ya aureta ko dan ranar da wannan sirri ya bayyana ya zama akwai wanda zai gani yaji dadi, ta tabbata in tai magana gani za'ai kamar kishi ne ke damunta sai dai ko d'aya, tasan akwai kishi na wanda take tsananin so shikuma ba ita yake so ba, sai dai a yanzu burinta tai kokarin ganin ta gyara wani abu ko yaya ne na daga cikin laifukan da aka aikata.


Bangarensa ta nufa, har takai hannu zata kwankwasa ta fasa saboda batasan da wace kalmar zata fara masa magana ba, a hankali ta juya cikin damuwa.


Idanu ta zaro, kallanta yai sannan ya kalli kofar, miyau ta had'iya sannan tace " Ya Turab."


Kallanta ya sakeyi sannan yace "Lafiya?" daga bangaren Hajiya yake sam bayasan magana.


Khadija tai shiru tana wasa da hannayenta, tunanin abinda zata cemai takeyi.
Ta gefenta ya wuce zai shiga ciki ganin batada niyyar magana.
Itama ganin haka yasa tai saurin cewa "Magana nakeso muyi."


Juyowa yai ya kalleta sannan ya kauda kai yace "Banaji akwai wata magana da zamuyi."


Kasa tai da kai tare da jinjina kai cikin rashin jin dadin abinda ya fada tace " haka ne, na tabbatar ba wata magana datai saura tsakaninmu, sai dai inaso ka bani ko minti goma ne."


Harshensa ya zaro kadan ya d'an lashi lab'ansa da suka bushe yace muje.
Mai makon yai ciki sai taga ya juya ya fara tafiya.


Bata tambayi inda zasuba itama binsa kawai tai a baya.
A hankali suke tafiya yana gaba daga gefen dama, ita kuma tana bayansa daga gefen hagu, tafiya kawai yakeyi. Yana kara tattaro duk wani tugu da ya sani wanda Magajiya ta aikata ita da yayanta wanda ya kasance mahaifin yarinyar dayafiso a rayuwa.


Ta yaya zai iya zaman aure da ita ko bayan komai ya kamala? In har ya sa akama mahaifinta da Magajiya hukunci ta yaya zai iya kallanta da sunan soyayya? Itama ta yaya zata iya kallan wanda ya ruguza rayuwar gidansu da sunan soyayya? Ai duk san da takemai bai kai na iyayenta ba, shima haka, duk sanda yake mata bazai taba kwatanta shi da wanda yakema mahaifiyarsa ba.


Juyowa yai ya kalleta, ganin irin kallan da yake mata yasa jikinta yai wani irin sanyi.
Baice mata komai ba sai nuna mata inda zasu shiga dayai.
Kallan gurin tai, inda ya ke hutawa ne, sai daya shiga ta bi bayansa.
Can yaje ya zauna akan kujerar dake gun.
Rasa inda zata zauna tai dan kujerar gud'a d'aya ce a gun doguwa.
Kallanta yai sannan ya mata alama da kai akan ta zauna daga gefe.


Nan ta zauna, ta d'an kalli sararin samaniya, kasancewar yamma ce garin yayi luf abin sha'awa, bare lokacin na zafi ne, iska tana kad'awa a hankali.


Jitai yace " ina jinki."
Khadija ta kalleshi kallo na tsananin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login