Showing 15001 words to 18000 words out of 146065 words
Chapter 6 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
Hisham ta rasa inda zata sa kanta, ya zama dole ta fitoda wata sabuwar hanya ta yanda zatai in har d'an ya dawo, ita ta kasa yarda da komai ma.
Mamaki ne ya kamata jin sallamar Jakadiya, ta dade sosai kafin ta bata izini, Jakadiya ta shigo tare da washe baki, ta matso kusa da Magajiya ta zauna a kasa sannan ta kalleta ta mata jinjina tace " Sai ke Sarauniyar da babu irinta, ba aiba kuma baza'ai irinki ba, kinci dubu sai ceto takawarki lafiya matar sarki, takawarki lafiya mamar sarki, takawarki lafiya Haj......."
Wani banzan kallo Magajiya ta mata tace " me kike aikatawa yanzun?"
Jakadiya ta washe baki tace " wato Ranki ya dade matsala aka samu ai yayatace bataji dadi ba shi......"
Wani mugun murmushi Magajiya ta sakar mata tace "Babu ruwan kwai da aski, abinda nakeso naki shine ke din wacece?"
Yawo ta had'iya sannan tace "taki ce sai dai......"
Magajiya tacigaba " waye ya baki wannan matsayin wanda kike takama dashi?"
Jakadiya tai zuruzuru da ido, da kyar tace " kece."
Magajiya tai wata 'yar bazawarar dariya tace " kinsan da haka ke har kin kai matsayin da zakiyi tunanin yimin karya?ke d'in wacece da har...."
Da sauri Jakadiya ta sa gwiwowinta a kasa tace " Magajita tuba nake, sai dai kafin ki yanke hukunci yakamata ki duba yanda nake miki biyayya, nasani sarai Yarima ba......."
Gaban Magajiya ne ya fad'i ta kalli Jakadiya a tsorace, dama Jakadiya tasan wannan ce kadai hanyar dazaisa ta tsira inhar ta nuna mata ta san sirrinta.
Jakadiya tai saurin rufe bakinta tana waige waige tace "tuba nake ranki ya dade, wannan sirri ne da zan rikeshi har kabari na, tuba nake da subutar baki."
Magajiya ta danyi kifikifi da ido sannan ta daure tace " me kike san cewa?"
Jakadiya tace " tuba nake Ranki ya dade ai sirri ki nawa ne, baza'aji wannan zance daga gareni ba."
Ganin tabbas Jakadiya tasan wani abu sai dai da alama batasan duka ba yasa ta daure tace " tashi kije ni ina bukar hutu."
Nan Jakadiya tai waje da sauri.
Tana fita tai dariyar mugunta tace " ni da gidan nan da matsayina mutu ka raba."
*********
Sarki ya kasa zaune ya kasa tsaye, yau ya kamata su Hisham su dawo sai dai yajisu shiru hakan yasa da kansa yai tattaki zuwa b'angaren Magajiya.
Zagi(wanda yake ma sarki iso sannan yake zama a gaba duk inda zaije ya sanar da isowar Sarki.)
Mikewa Magajiya tai cikin mamaki, masu kula da ita ne suka shigo suka kara sanar da ita, nan ta fito dan tarbarsa.
Sai daya shiga ya zauna, sannan ya kalleta yace " Hisham fa? Bayau zai dawo bane?"
Kallan mamaki tamai wato abinda ya kawoahi b'angarenta kenan?so yake yaji zancen matarsa da d'ansa kenan."
Murmushi ta saki duk da bakincikin da take ciki tace " mai zaisa hankalin Mai Martaba ya tashi bayan na tabbata yanzu suna hanya?na tabbata ka matsu kamar yanda nima na matsu inga d'ana."
Sarki ya d'an kalleta yace " niba saboda haka nake tambaya ba, akwai abinda nakeso najine daga bakin Waziri."
Murmushi tai tace "Angon Karni ai ba sai kayi kara ba, nima d'a na ne."
Kallanta yai yana mamaki, sai dai yana jin dadi sosai na yanda takesan d'ansa.
Yace " Ina AbdulMajid?"
Tace " d'azu Uwar Soro( Mahaifiyar sarki, ko yayarsa ko gwaggonsa. ko uwargidansa, wadda ta wanke shi. wadda ke iya gaya masa duk abin da ake jin nauyin gaya masa, ita ake kira uwar soro.)
Amma ita Mahaifiyarsa take nufi dan a lokacin nasu ita ake kira da Uwar Soro.
Murmushi yai sannan yace " ni zan koma."
Kallansa tai a ranta tace ka gama abinda ya kawoka kenan?
Amma a fili tace " ina godiya da wannan ziyarar Ranka ya Dade."
Yana fita ta d'anyi kwafa cikin takaici tace " ni zaka wulakanta?"
************
Basira kam tana gaba Lantana na baya ta kasa mata magana ganin kawai tafiya takeyi da alama batama san inda takesa kafarta ba.
Abu Turab na bayanta, ko da Lantana tai yunkurin ansarsa Basira taki.
Sunyi tafiya mai uban nisa dan Lantana harta gaji, itakam tafiya kawai take dan hankalinta baya jikinta, tunanin yayanta da matarsa sun mata yawa, sai da taji Abu Turab ya sa kuka sannan hankalinta ya dawo jikinta.
Kallan inda suke tai daji ne sosai juyowa tai ta kalli Lantana sannan ta nemi guri ta zauna ta kunto shi daga bayanta, Lantana ta zo kusa da ita ta tsuguna sannan tasa hannu ta fara danna mata kafarta dataga ta kumbura.
Basira kam shayar dashi kawai take ko magana batayi, idanunta ya kafe kaf ta kasa ko hawaye bare taji sanyi a ranta.
Sai da Lantana ta danna mata kafa sosai sannan ta kalleta tace " bakici abinci ba ranki ya dade."
Basira kai kawai ta girgiza mata, ganin ya koma barci yasa ya fara neman goyashi, Lantana tai saurin amsarsa ta sashi a bayanta suka cigaba da tafiya.
"**********
Shikam Hisham da yamma yai tunanin zuwa gaisuwa sannan ya sanar da ita tafiyarsu gobe, dan ya tabbata in bai je ba sai gulmar abin ta bazu a garin killa ma dogarawan da suka zo su kai gulmar har masarautarsu.
Bayan sunzo gidan ne, ya nemi a kira masa Basira ya mata gaisuwa, sai a lokacin aka farga da rashin su a gidan.
Tashin hankali nan fa aka bazama naimansu, ganin Basira bamai yawo bace sannan ba Lantana ba kuma d'anta, wannan ya kara tadama mutane hankali, tun azahar ake nemansu amma ba labari....
Hisham kam hankalinsa ya kara tashi har ya fara zargin kila ko ta samu mota ne ta tafi Zazzau, wannan al'amari ya kara tada mai hankali sosai da sosai......
*********
Basira kam sai da ta fara hakki sosai sannan ta samu ta zauna, dan tafiya kawai suke sai dai in Abu Turab yayi kuka su tsaya yasha sannan su ci gaba da tafiya.
Lantana ta matso tace "Ranki ya dade dan Allah ki samu ki huta?" ita kanta Lantana hakki take sosai ga magrib ta kawo kai dan rana saura kiris ta fad'i.
Kallan inda suke tai, wani kauyeni da ba mutane sosai, nan suka karasa kauyen.
Wani tsoho suka gani a zaune yana wanke alo da alama rubutu yai, lantana ta gaisheshi tace " Baba dan Allah ka taimaka mana da gun kwana zuwa gobe."
Kallansu yai ya kalli Basira wacce ke tsaye kamar zata fadi, yace " ku shiga ciki kafin wannan ta samu ta kwanta.
Lantana ta shiga mai godiya, Basira kam jiri ne yake d'ebanta, tsohon yace "kuyi sauri ku shiga."
Da kayar Basira ta daure tace "Mun gode."
Sannan suka nufi ciki.
*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼*
*11*
Sun shiga ciki sukaga ba kowa a tsakar gidan, nan suka tsaya suna sallama, Basira kam jingina tai da bango.
Wata matace ta fito daga bayan gida rike da buta a hannunta ta amsa sallamar tana kallansu, nan Lantana ta gaisheta ta amsa, Lantana zatai magana sai taji muryar tsohon nan ta bayanta yana cewa " 'yata basu guri su huta sai suyi alwala ki basu abinci."
Ba tare da musu ba ta amsa da to, sannan tace " ku shigo."
Sun shiga wani d'aki wanda da alama nata ne d'aki ne an sa gadu guda biyu d'aya nai rumfa kato sannan sai d'an karami a gefe, sannan ancika d'akin taf da jere na samiru da 'yan china.
Akan tabirma data shimfid'a musu suka zauna, sannan ta zauna itama suka gaisa(wannan shine halin mutanen mu na da basa yarda ayi gaisuwa a tsaye ko me suke yi sunfiso suna daga zaune a gaisa)
Nan ta mike tai waje, Abu turab ya d'an fara abin kuka, hakan yasa Lantana ta kuntoshi daga bayanta ta fara jijigashi ganin ita kanta Basira yunwa takeji ina zai sami ruwan nonon da zaisha? Itakam tana tausayin Basira ganin tana tafe da d'anyen jego.
Matar ce ta sake shigowa rike da fitilar kwai ta ajiye musu sannan ta mike zata fita, kallan Abu Turab tai cike da sha'awa tace " Tabarkalla masha Allah sai dai da alama ba'a dade da haifarsa ba."
Lantana tai murmushi tace " yau fa kwanansu biyu."
Cikin tsananin mamaki ta kallesu tace "da jego haka d'anye kukai tafiya?"
Lantana tai shiru batace komai ba, kallan Basira tai wanda ganin yanda ta galabaita yasa ta fahimci itace Uwar, waje tai da sauri ta karasa murhu ta kada miyar kuka wanda dama ta saka komai kadawa kawai zatai.
Tana gamawa ta kawo musu tuwon dawa miyar kuka tasha manshanu.
Nan fa suka fara cin abinci, sosai Basira taci abinci.
Sai da suka gama sannan Lantana ta tashi tai sallah tunda Basira tana fashin sallah na jinin haihuwa.
Sunyi shiru a d'aki shikam Abu Turab bacci kawai yakeyi.
Basira tunani duk ya isheta da bakin cikin yanda rayuwa ta risketa.
Daga waje sukaji kamar ana dan fada, Lantana ta kalli Basira, jisukai ancigaba da fada " wlh yau bazan bar gidan nan ba sai Shehu ya biyani kud'ina kaf dan kuwa na gaji da wannan rainin wayan."
Hakuri sukaji ana badawa amma kamar zuga matar ake sai kara masifa takeyi da k'ak'aji.
Basira ta daure ta mike ta fita wajen, Matar da ta kula dasu ta gani zaune a gefe tana kuka, sai kuma wani mutumi a tsaye kusa da ita, ga matar nan da take ta masifa a tsaye a kansu.
Wata matace ta fito daga wani d'aki daga gefensu ta saki wani gud'a cikin farin ciki tace "Allah kasheni saboda farinciki, lalai yau take sallah a gurina, anje anci bashi anyi aure gashi an kasa biyan kudin da aka ranta, yo dama ina za'a iya biya tunda an auro mai farar kafa?"
Basira ta kalli matar yanzu ta gane inda abin ya dosa, da alama waccan din uwar gida ce, mijin yaci bashi ya auri wannan gashi kuma ba damar biyan kudin?"
Mai kudin ta kara zak'ewa tana ta zabga masifa, Basira ta fito ta zo kusa da matar sannan ta zare sarkar dake d'aure a wuyanta, sarka ce ta azurfa wanda a waccan lokacin kudi ce sosai, cikin mamaki matar ta kalleta sannan ta amsa ta shiga dubawa, tabbas azurface mai kyau da tsada wacce kana gani kasan sai mai hali sosai shine zai sa ta.
Shehu ya kalleta cikin mamaki sannan ya kalli matarsa yace " wacece?"
Hawayene ya zubo mata, zatai magana matar tace " kina nufin kin bani duka?"
Basira tace " ki saidata kid'au kud'inki ki ba matar nan ragowar."
Wannan d'ayar matar mai guda ta matso da sauri tace " baiwar Allah ked'in wacece?"
Basira ta juya ba tare da ta amsata ba ta koma ciki, Dattijon nan wanda ya kawo kai daidai lokacin da Basira ta mika azurfa ya share kwalla da ta taru masa, ba shakka dama yaji ajikinsa alhere ne su yana kallansu ya kalli yaron.
Matar ta kalli Shehu tace " Shehu ina ka samo wannan?wlh ka bincike ta in har ba matar wani hamshakin d'an kasuwan bane to tana da dangantaka da sarauta, inba haka ba a wannan zamanin waye zai baka wannan shamfad'ed'iyar azurfar?"
Shehu ya fizge azurfar daga hannunta yace "uwar san banza kud'inki dana ranta ko rabin wannan baikai ba, inyaso gobe kizo muje mu sai data inbaki kud'inki."
Haushi ya kamata, haka tanaji tana gani tai waje.
Uwargidansa ta matso da sauri tace "Shehu kawo na ajiye ma,kasan na iya ajiya."
Harara ya maka mata yace "kingama gud'ar?"
Kallansa tai cikin zolaya tace "kai bakasan wasa ba?"
Tsaki ya ja sannan ya mikama Amaryarsa azurfar yace " ajiye tukunna sai na nemi shawar Baffa."
Yana fad'a yai hanyar waje, a tsaye yaga Mahaifinsa, tsayawa yai kusa dashi kansa a kasa.
Mahaifinsa yace "biyoni ciki."
Nan yai gaba shima ya biyoshi.
A tsakar gida ya tsaya, nan Amaryar tai saurin shimfid'amai tabirma, ya kalleta yace "sannu 'yata, d'an shiga ki kiramin bakin nan."
Nan tai ciki da sauri, sun fito sun zauna a kan wata tabirmar, nan ya kalli Shehu yace " Zauna kaima."
Nan ya zauna matansa ma duka suka zauna.
Shiru ne ya biyo bayan kafin yace " Bismillahi Rahmani Rahim, ita bismillah ana san a fara ta akan duk abinda mutum zai aikata, dan haka yana da amfani mutum ya dinga yinta akai akai."
Kai suka jinjina sannan yacigaba " Baiwar Allah ya sunanki?"
Basira! Abinda ta fada kawai kenan kanta na kasa, yacigaba " daga ina kuke?"
Tace " katsina."
Yace " bazan tambayeki rayuwarki ba da yanda kikayi ta da abinda ya fito dake ba sai dai inaso inji abu biyu, na farko wannan yaron ta wani hanya kika sameshi?"
Lantana zatai magana Basira ta rike mata hannu sannan tace " Allah shine shaidata aure nai na sameshi."
"Alhamdulila!" Abinda ya fada kenan sannan yace " tambayar karshe, Yanzu da kuka fito ina zaku?"
Basira tace " ni kaina bansani ba, na rasa yayana wanda shi kadai ya ragemin sannan dole ne in taimaki d'a na."
Shiru yai kafin yace "Shehu."
Da sauri yace "Naam Baffa."
"a guara musu bangaren mahaifiyarka su zauna."
Ya amsa da to, sannan yacigaba " ku zauna anan har iya lokacin da kukaji zaku koma, ni limami ne a nan garin kar kusa komai a ranku ku zauna anan kamar kuna gidanku."
Godiya suka shiga yi, Shehu ya mika mata azurfarta, yace " karki damu zan...."
Kai ta jijiga sannan tace " karka damu nayi ne dan Allah da kuma darajar taimakon da aka mana, nima bani akai dan na bada kuma ba wani abin bane."
Da wannan aka tashi.
Amarya wato ( Kubra) ta mike tai b'angaren mahaifiyar shehu wacce ta rasu wata 5 da suka wuce, b'angarenta daban ne dan sai ka d'anyi tafiya kadan ka shiga kofa sannan zata sadaka da b'angarensu.
************
Tashin hankalin da Hisham ya shiga baya misaltuwa haka suka isa Zariya duk ya gama rikicewa, suna isa yai fada da sauri, Mai Martaba kam ana cewa Hisham ya iso hankalinsa ya kasa kwanciya saboda tsananin farin ciki, kofa kawai ya kurama ido yana jiran shigowar Hisham.
Ganin Hisham ya shigo yasa yai ajiyar zuciya, nan Hisham ya matso duk ya birkice ya gaidashi ya d'auka zai haushi da fada akan yabar matarsa ta taho ita kadai, sai jiyai Sarki yace "Hisham ka dawo lafiya? Sannu da kokari ba shakka ka sha tafiya."
Hisham ya share zufa cikin tsoron abinda zai faru, Sarki yace " ka je gida ka huta kasha tafiya."
Nan Hisham yai godiya yai waje.
Mai martaba yai murmushi, yau zaiga Basira da d'ansa, burinsa na sa wannan suna yayi.
Bazai taba mantawa ba tun sanda mahaifinsa ya bashi labarin sunan a lokacin da ya ganshi ya kwanta a kasa, ya sa aransa sai ya sa sunan nan.
(_Sunan Abu Turab sunane wanda Manzon Allah ya sawa Sayaddina Ali a yayin da ya ganshi ya kwanta a kasa, yai murmushi yace Abu Turab wato Father of Soil."
Murmushi ya sake yi.
Shikam Hisham na fita yai gun Magajiya da hanzari.
Tana tsaye ya sameta dan itama hankalinta ya tashi jin ance Hisham ya dawo amma shi kadai ne ba tare da Basira ya dawo ba.
Yana shigowa ta tareshi da cewa " Yaya meke faruwa?"
Hisham ya rikice yace " Magajiya muna cikin matsala."
Matsala?tame kenan?"
Nan ya kwashe komai ya sanar da ita, kanta ta dafe cikin tashin hankali tace " yanzu kenan bamusan a wani hali take ba daga ita har d'anta?"
Yace " tuba nake."
Wani tulu dake gefenta ta buga da karfi hakan yasa ya fashe, cikin tsoro Hisham ya kalleta, idanunta sunyi ja cikin fada tace " meyasa baka aiki da hankali? Me kake tunani zamu cema Sarki? Bamusan ta mutu ba ko tana raye, in mukace mai ta mutu ta dawo fa? Muce me? In kuma mukace tana raye to tana ina? Me yasa Hisham sam wani sa'in kanka baya aiki? Ni kaji daga bakina nace ka kona musu gida? Waye ya baka damar aiwatar da abinda ban umarce ka ba?"
Hisham takaici ya kamashi, me wannan yarinyar take nufi?
Cikin fad'a tace " jeka banasan ganinka sannan kar ka shigo gidan sai nan da kwana biyu ni zan san yanda zanyi."
Jiki a sanyaye yai waje, wani dogon tsaki taja ta d'aura hannu akai cikin takaici yanzu ya zatai?
Shiru tai ta shiga dogob nazari........
_Hmmmmm_
*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
.. 🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*Na Ayusher Muhd🤸🏼*
*12*
Ana Magrib Magajiya ta kintsa tsaf sannan ta aikama da Sarki zuwanta, alokacin hankalin Mai Martaba ya gama tashi dan yana tasowa daga fada ya aika wani bafaden sa akan ya dubo masa lafiyar matarsa da d'ansa kafin yazo sai dai abin mamaki dawowa akai aka sanar dashi rashin isowarsu gidan.
Magajiya ta iso a lokacin shi kansa ya matso ya ganta dan yana san jin abinda ke faruwa.
Bayan ta shigo ne ta zauna a inda ta saba zama wato d'an nesa dashi kadan, sannan ta numfasa cikin isa da kuma nuna alamar damuwa tace " Ranka ya dade muna cikin matsala fa?"
Kallanta yai cikin mamaki sai dai bai amsa ba, itama ta