Showing 132001 words to 135000 words out of 146065 words
Chapter 45 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
sama sannan ta kallu Abdulmajid tace " zuwa nai in maida kai gida, a kula dakai acan."
Kallanta yai yace " gida?"
Tace " eh, sannan dama inasan inma wata tambaya agaban kanin nan naka, nikam Abdulmajid tsakanin Waziri da Abu Turab wanene ya nemi halaka maka rayuwa?"
Kallan mamaki ya mata yace " ban gane me kike nufi ba?"
Tace " tsakanin Turab da yayana wanene yasa aka kamaka?"
Yace " ni ai ba........"
Katseshi tai da sauri tace "bakaji tambaya ta bace? Tsakanin Turab da Yayana wanene yasa akama ka?"
Turab ya kalla wanda daidai lokacin shima ya kalleshi.
Turab a hankali yamai wani murmushi.
Magajiya tace " kai nake jira."
Yace " Turab ne."
Wata dariya ta saki tace" kaji ko? Ina fatan kasan yanzu amsar da za'a bada a zaman da za'ai, sannan banasan wanda ya nemi kashe min d'a yazo kuma yana neman shiga jikinsa, dan haka karna kara ganinka da Abdulmajid."
Turab ya kalleta idanunsa na kanta ya taku har inda take yana tafa mata, sai dayazo daf da ita yace " Bravo! Kai gaskiya Umma u are indeed a very dangerous woman."
Da yake lokacinta ba makaranta tai ba, sai dai tsabar basira datake dashi ta tabbatar magana ce ya fada mata, tunda lokacin karatun mata ba'a wani daukeshi da wani abu ba.
Kai ta jinjina mai tace " in fadama wani sirri?"
Kallanta yai, tace " abinda kake dashi akaina ba abinda zasumun, kasan dalili? Ta matso daf dashi saitin kunnenaa tace "Saboda kai jinin mahaifinka ne, bazaka taba sanar dashi d'an dayake tunanin nashi ne ba nashi bane."
Sannan ta kalleshi tace " kasan dalili?saboda kana tsoron halin da zai shiga."
Turab kam jiyake zuciyarsa kamae zata fashe saboda takaici, daurewa yai ya kalleta yace " haka kike tunani?to in har haka kike tunani kin bada ni, domin in har irin wannan d'an karamin abun zai firgitashi to ba shakka bai dace da mulki ba."
Ya juya yai waje.
Dunkule hannunta tai ta matse a jikin zaninta, ji take kamar ta jawo yaran can ta shake shi.
Shikansa yana fita ya saku wata ajiyar zuciya sannan ya dan cije labbansa, yai gaba.
Kallan Abdulmajid tai wanda ganin yanda suke magana yasa ya runtse idanunsa saboda takaici, waje tai a zuciye Ta tambayi inda likitansa yake.
A hankali ya bud'e idanunsa, hawaye ne suka zubo mai dan ba shakka shikam yasan duk abinda ke faruwa duk saboda shi ne.
Tura kofar tai a hankali ta shigo, taba kallan sanda Turab ya fita, Sannan taga yanda Magajiya ta fito rai a bace.
A hankalu ta tako inda yake, hannunsa ya rike yana karza babban d'an yatsansa a kan bayan hannunsa sam bai kula ba gun yar ya d'an fashe.
Har ta karaso gun baimasan tazo ba, hannunta tasaka akan hannun da yake karzawa, idanunsa ya d'ago ya kalleta, kura mata ido yai, daurewa tai tace " me kakeyi hakan?"
Kasa magana yai sai kallanta kawau da yakeyi, tace " ko me ke damunka addu'a zakai bawai karza hannu ba."
Ta zare hannunta tace " zan wuce."
Ganin yanda fuskarta take a had'e yasa yai saurin riko hijab d'inta.
Tsayawa tai ba tare data juyo ba, yace " kiyi hakuri."
Kallansa ta juyo tai cikin zafi tace " me yasa kake cutar da kanka? Me yasa in abu baima ba bazaka fadi abinda ke ranka ba? Mahaifiyarka tafi wanda ya halliceka ne? Akan me bazaka dinga nuna mata abinda take aikatama ba daidai bane? Ko zuciyarka ba irinta Turab bace at least kai namiji ne ya kamata in har tai abinda bai dace ba ka nuna mata."
Ko mai ta tuna, sai kuma tai shiru taja hijab dinta tai waje.
Magajiya na dawowa ta sa aka sashi a keken guragu aka kaishi mota, sykai gida.
***********
Juyi tai ta ganshi akan sallaya, agoggo ta kalla taga karfe d'aya saura minti goma.
Farkawa ta kara yi , Abu Turab ta gani a zaune a kan kujerar dake d'akin, ya had'e hannayensa alamar dogon tunani, dayake ba haske sosai a d'akin, sai wata yar karamar fitila dake gefen gado ta d'aya bangaren ne a kunne.
A hankali ta kalli agoggon d'akin karfe biyu da kwata, mikewa tai ta zauna sannan ta kalleshi.
Kallanta yai dan yaji motsi, ganinta a zaune yasa ya mike ya taso yazo inda take.
Kusa da ita ya zauna sannan yace " farkawa kikai?"
Kallansa tai tace " eh, kai fa? Kasa bacci kai?"
Kai ya girgiza, tace " tunanin gobe kake?"
Juyowa yai saitin da take kallansa yace " Bilkisu."
"Uhmm mm"
Shiru yai sai kallanta da yake, tace " inajinka."
Hannayenta ya kamo duka biyun ya rike yace "bansan ya zata kaya mana ba gobe, shiyasa nake tunanin wani abu."
Kallansa tai tare da tattara hankalinta zuwa kansa.
Yace " idan har Magajiya taci galaba akaina, wani abu ya sameni inaso ki koma gida, ba tare da waiwaye ba, kiyi rayuwarki kamar baki san niba, zan aiko da takardarki......."
Hannunta ta zare daga cikin nasa sannan ta sa kalleshi tace " me kake sam cewa?"
Yace " nama mahaifinki alkawari bazan......."
Katseshi tai tace " kana nufin in had'a kayana kenan kafin gobe ko me?"
Baice komai ba sai kallanta da yake, mikewa tai ta kunna fitilar d'akin sannan ta bud'e wardrobe dinta cikin kunar rai ta shiga zubo da kayanta kasa.
Ganin yanda take zubo da kayan ne yasa ya mike ya karasa inda take, hannu yasa ya riko hannun da take zubo da kayan, yace " Bilkisu!"
Juyowa tai ta kalleshi idanunta sun ciciko da kwala tace " na d'auka kai kace in shirya kaya na?"
Yace " Na fada amma."
Tace " kanaso ka nunamin ni da kau ba d'aya bane? Kanaso ka nunamin matsalarka ba tawa bace?"
Bata taba nuna bacin ranta ba a iya zamansu tun kan suyi aure sai yau, hannunta ta shiga kokarin kwacewa.
Rungume ta yai a jikinsa, sai da yaji tayi sanyi da kokarin kwace kanta sannan yace " ba haka nake nufi ba, banaso insanyaki cikin damuwar da ni kaina bansan sanda zata kare ba."
Idanunta ta lumshe tace " menene tsakanin miji da mata? Na d'auka duk runtsi duk wahala su shanyesu tare, su birne matsalarsu sannan su taimaki junansu? Da wannan buri nai aure, taya zaka cemin inka shiga matsala in tafi gida? Bakasan gwara kace mu rabu saboda baka sona ko saboda akwai wani abu nawa da baka so ba?"
Kara rungumeta yai yace " ko d'aya, in fact a kullum nai sallah ina gode ma Allah daya bani ke a matsayin matata, wacce ban taba zato ba, sannan maganar bamu zama d'aya ba ko kad'an ba haka bane."
D'agowa tai ta kalleshi tace " me yasa kake tunanin fad'uwa? Baka tunanin kaine zaka kada ta?"
Murmushi yai yasa hannunsa d'aya a kan kafadar ta, tace " mai gaskiya baya faduwa, sannan Allah na tare dakai, muma muna ma addu'an samun nassara, inaji a jikina matsalar ka ta kusa warware wa, sannan da yardar Allah ba wanda zai cutar dakai."
Murmushi kawai yakeyi yana binta da kallo, tace " me? Baka yarda dani........."
Batai zato ba taji bakinsa cikin nata, shikansa bai san sanda zuciyarsa ta sashi hakan ba.
Sun dade suna aikama juna sakwan ni, abinka da wanda bai taba yi ba, jinsa ya dinga yi kamar ana angizashi.
Sam ya manta da alkawarin da ya d'aukarma kansa.
Jin kafafunta suna neman kasa d'aukarta ne yasashi sa hannu ya zareta zuwa kan gado, a hankali ya zare bakinsa daga nata, ya kai fuskarsa zuwa wuyanta tare da sa hannu yana kokarin rabata da kayanta.
Cak ya tsaya, tare da saurin mikewa idanunsa sunyi jaa sosai.
Kallansa tai ita kanta duk da tana tsoron wannan rana sai dai abinda takeji a yanzu dadi ne muraran.
Idanunsu ne suka hadu da juna, dawowa yai ya zauna tare da rungumeta tsam yace " what should i do?"
A hankali tace " akan me?"
Yace " the promise......"
Kanta ta sunkuyar tana murmushi, dan ya bata dariya.
A hankali yace " ya zanyi?"
Murmushi kawai takeyi, d'agota yai ya kalleta, idanunta a lumshe a hankali ya maida bakinsa cikin nata...........
Nace su Turab dai to😂
*************
Washegari da sassafe bawan da Magajiya ta aika ya iso, rabansa da gidan sarki yau sati d'aya kenan.
Tanajin shine ta ce ya shigo.
Yana gaisheta yace " Magajiya na samoshi."
Tace "yana ina?"
Yace " yana wajen gidan."
Tace yauwa na gode........
*THE LAST BATTLE 😄*
*TURAB*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*Gaisuwa, jinjina gareku Aminan Arziki 'yan Sauyi, Dizzy, Rabes, Faty Shafi'u, Yar Gaya, Salamah, Kozali, Sharubutu, J.B, Rambi, da sauran Yan Sauyi......
*85*
A hankali ya bud'e idanunsa, sannan ya kalleta, bacci takeyi akan hannunsa na hagu, haka kawai ya samu kansa da yin murmushi, sannan ya tuno abinda ya faru jiya.
Ya akai jiya idanunsa suka rufe? Sam ya kasa controlling din kansa? Har sai da ya maidata mace? Lalai jiya yaci sa'a Bilkisu tayi wankan tsarki, da tabbas yanda yaji jiya in har bata sallah baisan yanda zaiyi ba, abu yaji wanda tunda aka haifeshi bai taba ji ba.
Lalai wannan rana ta zamar mai ranar da bazai mantata ba, murmushi yai sannan ya tuno da, a da ko zaiyi tunanin aure sam zuciyarsa bata raya mai farin ciki.
Khadija zuciyarsa take kauna kuma ya tabbata in ba dai wani ikon Allah ba bayanda za'ai ya aureta, shikuma bayaji zan iya rayuwa da wata ba ita ba, sai dai a yanzu ya tabbatar abin ba haka bane.
In har ka samu mace wacce ta sanka, sani ba wai na suna ba, sannan wacce ta ke sanka, take kokarin farantama rai, zuciyarta da kuma suffarta masu kyau ne, mai addini, to lallai shikam yana gani a hankali zuciyar mutum zata koya ma san wannan yarinyar.
Zuciyarsa haryanzu tana so da kaunar Khadija sai dai baxai taba auranta ba, saboda har abada ya tabbata bazai taba manta abinda jininta suka aikata mai ba, sannan inya hukunta iyayenta me zaice da 'ya'yan da suka haifa nan gaba in har sun tambayeshi kakaninsu na bangarenta? Kuma abu ne na sarauta wanda zai bar tarihi, ko da ya b'oye musu ya tabbatar labari zai isa har kunnensu, mai zai ce dasu a lokacin? Iyayenta sune suka...........
Motsin da Bilkisu tai da kanta shine ya katsemai wannan tunanin, kiran Sallah ake tayi a massalaci, idanunta ta bud'e cikin bacci ta kalleshi.
Ganin idanunsa a bud'e shima ita yake kallo yasa tai saurin maida idanunta ta rufe, sunkuyowa yai ya sumbaci goshinta sannan yace " zanyi alwala."
Kai ta daga mai alamar to, yace " zan dan fita daga nan kina ganin ba matsala? Naga........"
Da sauri tace " zan iya." dan batasan maganar kunya takeji.
Kanta ta zame daga hannunsa a hankali, murmushi yai bayan ya mike.
Bandaki ya shiga yai alwala sannan yai waje.
Idanunta ta bud'e a hankali bayan taji alamar fitarsa, sannan ta mike zaune, yaye bargon tai, sannan ta mike a hankali.
Dama tasa an sanar da ita duk abinda ya dace tai, yanzu zamani yazi ilimin addini ya kara wadata balle a mata tonon silili.
Bedsheet din ta yaye tai toilet, a roba ta sashi ta zuba ruwa sannan tai wankan tsarki bayan ta gasa jikinta da ruwan dumi wanda sai data dafa a heater.
Kallo d'aya zakama yanayin tafiyarta ka fahimci ba daidai take tafiya ba, bayan tayi sallah ta dade tana ma mijinta addu'a kafin ta mike.
Turab kuwa a massalaci, bayan ya gama addu'oinsa ya fito shida Garzali bayan gari yayi haske suka fito wajen gari.
**********
Magajiya kam jin an taho dashi yasa taji wani nishad'i ya kamata, gari yana haske tasa aka kira kata matan sarki.
Bayan sun zauna ne ta kallesu tace " yau munada zama na shari'a da za'ai, hakan ne yasa nakiraku dan inji ta bakinku, da Abdulmajid da Abu Turab wa kuke ganin zai gaji Sarki?"
Kallanta sukai fuskarsu da murmushi sukace "Abdulmajid mana."
Tace " ba sai na tsaya bata lokaci na ba tunda kunsan abinda ya kamata, ina fatan zaku bi bayana anjima."
Kallan juna sukai kafin su amsa da to, suka taso suka fita, suna fita d'aya tace " matar nan tana neman maidamu yaranta, da izinin Allah d'an datake takama dashi bazai zama sarkin ba."
D'ayar tace "Ameen."
************
Gimbiya tayi kwalliya tana zaune a falo wata yarinya ta nemi izinin shigowa.
Bayan ta shigo ne ta mika kata wani dan karamin kwali na agoggo tace " daga fadar mai martaba nake, aikoni yai da agoggo wai aba Yarima Turab, sannan yana mai fatan alkairi."
Kallanta Bilkisu tai sannan ta amshi agoggon, tana shiga d'aki ta d'aurashi akan madubi dan ita kam bata ji hankalinta ya kwanta da agoggon ba
Sai daya gama shiryawa yazo kan madubi yana sa turare yaga kwalin agoggo, yace " wannan fa?"
Ta sanar dashi abinda yarinyar tace data kawo sannan tace " ni amma......."
Kwankwasa kofar da akai ne ya katse maganar, kofar ya nufa tare da zura agoggon yana tambayar waye.
Mai kula da Gimbiya tace itace sannan tace wai lokaci yayi, yce to.
Sannan ya kalli Bilkisu yace " Muje?"
Tace " ina?"
Yace " gun mana."
Cikin mamaki tace " harda ni?"
Murmushi yai sannan yazo inda take ya tsaya yace " bakyasan kije?"
Tace " inaso inje amma......."
Kasa tai da kanta alamar kunya.
Murmushi yai har hakwaransa suka fito yace " kunya kike?"
Ta mike tace " bafa haka bane, tafiya......"
Sai kuma tai shiru.
Yace " menene a ciki? Indai bazaki bane, bazan takura miki ba."
Ya juya, takunsa uku ana hudu tace " zanje."
Murmushi yai kafin ya juyo sannan yace " muje."
Komawa tai ta d'auko babban mayafinta.
********
Karfe 11 na safe an gyara babban d'akin da za'ai shari'a.
Basira itada Lantana sun iso gidan, dan Sarki yace duk a kira na cikin gida tunda shari'ar ta cikin gida ce, sai a kara shaidu.
A d'akin taro kuwa, Hisham na gefe a zaune daga gefe, dogarawa biyu na tsaye kansa.
Galadima da Barde da mai Shari'a su suka fara zuwa.
Sai Matan sarki ne suka fara isowa a mata, sannan Basira.
Magajiya ce ta iso cikin shigarta ta isa da jin kai da sanin akwai kudi da matsayi, gefenta Abdulmajid ne aka turoshi a kekensa.
Kallo d'aya tama Hisham ta d'auke ido sannan taje gaba ta bangaren Mata ta zauna, bangaren maza kuma akasa Abdulmajid wanda ya zamana yana saitin ta.
Ranta ya baci ganib ta riga Abu Turab zuwa.
Sanar da isowansu akai, shigowa sukai shida Gimbiya a tare, tayi iya kokarinta na ganin ta saita kafafunta kar a gane, shikansa Turab saboda ita yake tafiya a hankali.
Suna shigowa aka zubo musu ido, Abdulmajid sai a wannan lokacin shima ya ganta.
Ba shakka ta hadu sosai, Magajiya ce ta dago ta kallesu, takaicinta daya yanda ita kanta sai da kayan jikin Bilkisu suka birgeta, Turab ya samu gu ya zauna kusa da Abdulmajid wanda hakan yasa ta zauna kusa da Magajiya dan Basira ce ta nuna mata gun zama.
Bilkisu sai data gaida Basira ta gaida matan sarki sannan ta kalli Magajiya tace " Umma Barka da warhaka."
Magajiya ta kalleta, bata amsa ba.
Basira tai murmushi tace " Bilkisu da alama bakisan tsarin mu na masarautar zazzauba, a ka'ida sai kin fara gaida Magajiya.
Bilkisu wacce dama tasan da hakan, tai murmushi sannan ta kalli Magajiya tace "Umma nayi laifi kenan?"
Magajiya tace " karki damu ai bakisan tsarin bane."
Bilkisu tace " godiya nake." sannan ta d'auke kanta.
Shigowar Sarki ne yasa aka tsaya da gaishe gaishe, mai martaba ya samu guri ya zauna.
Sannan akai addu'a aka tunatar da abinda akazo yi.
Turab yace "Takawa ina neman izinin shigowar wata bakuwa wacce take da dangantaka akan shari'ar nan."
Sarki yace " to bismillansu."
Shigowar Matar Hisham ne yasa Magajiya ta kalli Turab, murmushi yai sannan ya d'auke kai daga kanta, kallan juya sukai da sauri shida Abdulmajid ganin wacce ke tafe a bayanta, Khadija? Me ya kawo ta.
Khadija kuwa wacce d'an aiken ita ya sanar mawa tace ma Mahaifiyarta ai tare aka ce suzo, ta kalli Turab sannan ta kalli Abdulmajid.
D'auke kai tai har suka zauna.
Mai shari'a ya kalli Magajiya yace " Magajiya ta kawo nata sharhin a game da shari'ar da akai kwanaki, in akai duba da kalamanta tabbas suma suna da nasu ma'anar, hakan ne yasa aka daga shari'ar zuwa yau."
Sarki ya kalli Abdulmajid yace " Abdulmajid sanar dani da bakinka a kuma cikin mutanen nan, wanene yasa a kama ka? Mahaifiyarka tace Turab ne, shi kuka Turab yace Hisham ne ya nemi halakashi kai kuma ka sadaukar da kanka, wanene yake fada mana gaskiya?"
Abdulmajid ya kalli Magajiya wacce itama kallanshi kawai take yi, Khadija ya kalla wacce itama shi take kallo.
Juyowa yai ya kalli Turab, wanda yake kallan Kasa.
Sarki yace " Abdulmajid!"
Abdulmajid yana kallan Magajiya yace " ni kaina bansan wanene ya sa aka kamani ba."
Magajiya ta kalleshi tace " mene?"
Turab kam ko gizau baiyi ba.
Magajiya ta kalli Sarki tace " ta yaya Turab bazai nemi halaka Abdulmajid ba? Bayan yasan in akaji sirrin mahaifiyarsa shida sarauta sai dai a lahira? Amma in ya halaka Abdulmajid ko ma menene shi kadai ne jinin sarki dole ne a yafe mai."
Galadima ya kalleta yace " sirri? Mai kike nufi kenan?"
Kallan Sarki tai wanda idanunsa suka fara canzawa, sannan ta kallu Turab wanda ta tabbatar maganin ta yafara aiki dan