Showing 111001 words to 114000 words out of 146065 words
Chapter 38 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt
wani murmushi yace " ko kana tunanin bansan ni kukaso a ma illa ba?"
Gaban Hisham ya yanke ya fadi.
Turab yace " kaje gidanka yanzu, ka jirani zuwa gobe."
Hisham samun kansa yai da cewa to, ya juya yai gaba jikinsa a sanyaye, yanayi yana waiwayen kofar.
Kallan Abdulmajid Turab yai, ya dade yana kallansa, tsananin tausayinsa ne ke ratsashi gashi duk jikinsa ciwuka banda karaya, kamar ba shiba sam.
Turab ya kalli Sabi'u yace " zo muje gun likitan."
Sabi'u yace " karkuma abarshi shi kadai."
Kallan Mairo Turab yai da take rakube a gefe yace " akwai wanda ahi kansa mara lafiyar yafisan ya gani."
Bai fahimta ba sai dai ya gane akwai wanda zai zauna har suje su dawo.
Sai da sukazo inda taks Turab yace "ki shiga ki duba shi."
Sukai gaba.
Mairo a hankali ta tura kofar d'akin ta shiga.
Jikin gadon ta karasa sannan ta kalli fuskarsa, gaba d'aya an mata faci.
Fuskar ta kurama ido tana tuno abubuwan da suka dinga shiga tsakaninsu.
Sam bata san sanda hawaye suka ciciko a idanunta ba, a hankali wasu siraren hawaye suka gangaro kan fuskarsa.
Jin ruwa a fuskarsa ne yasa ya dan motsa idanunsa kadan, a hankali ya bud'e idanunsa da suka kumbura idanunta a rufe suke, yana kallanta ya maida idanunsa ya rufe.
Ina ya isa ya kalleta a cikin wannan halin? Ba ma wannan halin ba, ina ya isa yi mata magana bayan bai gama sanin wanene shi ba? Menene matsayinsa?
Idanunta ta bud'e a hankali sannan ta juya baya, tare da zama akan kujera, itadai so take ta karyata zuciyarta akan kukan nan tayine saboda tausayin d'an Adam ba wai saboda wani Abdulmajid ba.
Shikam ji yake inama ba wani babban sirri agabsa yaga Mairo tana nuna damuwa haka a gabansa? Meke shirin faruwa dashi?
Wasu zafafan hawayene suka gangaro ta gefe idanunsa.
********
A can kuwa Magajiya takaici ya isheta, har yanzu busa takeji da wasanni a gidan sarauta bata fara jin koke koke ba.
_TURAB_
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*72*
Turab ne ya kalli likitan sannan yace " kana nufin kafarsa bazata dawo dai dai ba?"
Kansa ya girgiza alamar a'a yace " ba wai bazata dawo daidai gaba d'aya ba, sai dai dawowarta daidai din abu ne mai wahala, a yanzu inya warke zamu had'ashi da sanduna dan taimaka masa gun tafiya, idan har Allah yayi sai kaga a hankali kafar ta warke in yana samun kulawa."
Turab yai godiya suka mike, kallan Sabi'u yai bayan sun fito yace " Sabi'u muje ka kaini gida, sai ka d'auko Khadija ka kawo asibitin ta zauna jinyarsa, ni akwai abinda zanyi."
Sabi'u yace " wacce muka kaifa?"
Turab yai murmushi yace " kana tunanin zai sake a gun yarinyar da yake so?"
Gaba yai daga fadar haka, mota suka shiga ya kaishi gida, akan inya d'auko Khadija sai ya maida Mairo.
Magajiya kam ana zaune a waje dan an fito waje wajen wani had'aden kwalliya ta sarauta da aka zagayen gun dashi, matane manya ke ta kid'an kwarya na ruwa, sai gaishe gaishe akeyi.
Turab yana shiga ya wuce bangarensa wanda yanzu komai nashi an kwashe daga bangaren, wanka yai sannan ya bud'e drawer da ya ajiye wata shadda a ciki dan dama ya ajiye ne saboda zuwa bangaren Amarya da ita, jawota yai tare da kallan d'ankwalin daya biyo bayan shaddar.
D'ankwalin Khadija ne, sawa yai a aljihunsa dan yau zai maida mata d'ankwalinta, inhar ya maida mata kuwa to yana nufin komai na alakar dake tsakaninsu ta tsaya kenan.
Fitowa yai daga bangaren, rawani yasa akamai, sannan yasa a d'aukomai dokin da Sarki ya bashi.
Had'aden dokin da mai martaba ya bashi ya hau, yasha ado na ban mamaki, Turab ya hau kai sannan ya nufi inda ake ta mai hawan dawakai.
Yana Isa masu busa suka canza salan busarsu aka saki wani kiraki.
Magajiya tana zaune labari ya iso mata na hawan da Ango yake yi.
Kallan yan aiken tai tace " Turab ne?"
Sukace sosai ma, duk da dai rawanun dayai bazai bari mu tabbatar shi bane amma ai kowa yasan Ango ne.
Tsaki tai a ranta tace " zancen banza kenan, Ango? Ai Abdulmajid ne angon."
Yana gama hawa dan ba dadewa yai ba ya nufi inda Magajiya take.
Aiko mata akai akan d'anta yazo kwasar gaisuwa.
Murmushi ta saki tace " ace ya shiga ciki ina shigowa."
Nan aka sanar ma Turab.
Ciki ya shiga ya samu guri ya zauna.
Magajiya ta mike cikin yauki ta nufi ciki.
Murd'a kofar tai ba tare da ta kula ba saboda bayansa ya juya tace " Ango kasha kamshi, dafatan yanzu ka hakura da aura........."
Juyowar da Turab yai tare da cuge rawanin ne yasa ta tsaya cak da maganar, jitai wani abu tundaga tsakiyar kanta har kafarta.
Turab ya tako cikin isa ya karaso inda take, hannu yasa ya tura kofar d'akin data rike da karfi bai cire hannunsa daga kai ba yace " Kina mamakin ganin wanda ya kamata ya mutu ne a tsaye a gabanki?"
Magajiya ta kakaro murmushi tace " me kake nufi? Kaine Angon mana, ko akwai wani aure da akai da ban sani ba?"
Turab ya girgiza kai yace " ina fa? Ai ni kadai ne a gidan nan aka d'aurama aure yau sannan aka Wani asibiti."
Magajiya tace "asibiti kuma? Me kake nufi?"
Turab idanunsa ne suka canza kala ya juyo ya kalleta yace " sa mayafi mu fita."
Tace " mene?"
Yace " abinda kikaji shi zakiyi."
Wata muguwar dariya ta saki tace " mene?kai harka isa ka sani nayi abinda banyi ra'ayi ba?"
Murmushi ya mata yace " daya wannan lokacin kuwa duk wani abu danai ra'ayi shi xakiyi."
Ranta ne ya baci matuka ta d'aga hannu zata wanka mai mari.
Jitai yace " Ya Abdulmajid zai ji in yasan kece kika sa aka kusa kashe shi?"
Hannunta ta tsayar kusa da fuskarsa, tace " Abdulmajid? Me ya sameshi?"
Turab yace " me ya sameshi? Yana kan gadon asibiti numfashi ma banaji yanayi, ko kin manta ke kika sa a kasheni? "
A rikice tace " to meya kawo Abdulmajid ciki?"
Turab yace " wannan kuma ke zan tambaya, ya zakiyi? D'an da kike gwagwarmaya a kansa gashican nufashinsa na neman d'aukewa."
Wani irin ihu ta saka ta kama kwalar rigar Turab tace " kana nufin d'an nawa ba ma tabbas ko yana da rai?"
Turab yace " ke nake jira muje ki ganshi kafin mu mikashi gidansa."
Wani irin ihu ta kara sakawa tace " kai har ka isa? Waye ya baka damar cewa d'ana numfashinsa na neman yankewa? Amma ban taba ganin mutum mara imani irinka ba, d'an nawa ka tura a ka kusa kashewa?"
Turab yai dariya yace " mara imani? Na tura? Magajiya na kasa fahimtar wa kikema inkiya a wannan maganar, ko kinaso kicemin Waziri shi kadai yai abin ba tare da kin sani ba?"
Magajiya ta kalleshi tace " Hisham? Eh shine yasa akai komai, ni meye nawa na neman ganin bayan rayuwarka?"
Turab yai wata dariya yace " dama ta ina zaki yadda kece sila bayan ni nasan wacce ke? Duk abinda Hisham ya miki kenan kanki kawai kika sani?"
Fuska ta had'e tace " bugar cikina kazoyi kenan?"
Turab ya bi kwayar idanunta da kallo, tace " me? Akwai wasu daka b'oye a d'akin nan? So kake kaji me zan fada?"
Turab yace " me kike san kice?"
Tafin hannunfa ta d'aga tace " ka san me yasa muke da zane kala kala a hannun mu?"
Yace " kwarai, kissa ta biyo akan mata ne lokacin Annabi Yusuf......"
Ta matso kusa dashi sosai yanda shikadai zai iya jin ke take cewa tace " mata ko? Amma tunda kasan wannan kissar kasan me matar da ta sasu tai ko?"
Kallanta kawai Turab yake, tace " mace aka ce, ni kuma a matan ma dabamce. Sharri na da sanin duniya da nai ko rabinta bakai ba, kai baka isa ka shiryamin ramin da zan afka ba."
Hannu tasa ta ture hannunsa ta bud'e kofa tai waje.
Turab ya ciji lab'anbansa.
Mahaifinsa dake jikin d'ayan d'akin ne ya fito.
Bazaka taba cewa sarki bane dan Shadda ya saka ba rawani a kansa sai hula, shida Sabi'u ne.
Abdussamad ya matso ya dan daku kafadar Turab yace " ya kafadar jarumin d'ana zata yi kasa?kana tunanin daga bugun farko zakasa magajya tai kasa? Da daddare naje naga jikin nasa, sannan mayi maganar abinda ke faruwa a hankali, yanzu in aka kula na dade bama fada za'ai zargin wani abu."
Turab yace " Tuba nake."
Sarki yai murmushi yace sannan yai waje.
Turab ya tuno plan dinsa.
Sanda Sabi'u zai tafi d'auko Khadija ya sanar dashi akan in har yanasan ganin d'ansa to yaje ya sanar da Sarki akan Magajiya na san ganinsa ganin gaggawa dan da matsala, saboda shi a ka'ida bai isa yaje fada yasa mahaifinsa tasowa.
Idan mahaifinsa yaji haka ya tabbatar ransa zai baci, sai dai bai isa nunawa ba saboda girmama matarsa kuma uwar gida.
To in ya fito sai Jakadiya ta sanar dashi shigar burtu.
To yasan mahaifinsa inyaji haka yasan Turab ne ya shirya wani abu.
Ita Jakadiya zatazo bangaren magajiya ta tabbatar ta sa mutane sun fita gun kida da wayau, shikuma Sabi'u yana dawowa sai ya taho raka sarki yanda ganinsu tare bazai sa mutane susan sarki bane.
Turab ya kalli Sabi'u yace " da alama nayi gaggawa akan yin plan dina, bazata taba yarda ta a sake fooling dinta twice ba."
Sabi'u ya girgiza kai yace " wacce kake yi da ita ne tafi karfin plan din bawai kayu gaggawa ba."
Turab ya shafi kansa yace " ka kai khadijan?"
Yace " eh, na kuma maida Mairo gun Umma."
Turab yace " nagode."
Sabi'u yace " gobe fa Amarya zatazo haka zaka tarbeta jiki a sanyaye?"
Turab yai murmushi yai waje.
*********
Magajiya na fita tai bangaren Abdulmajid tasa a kira mata Hisham.
Gabanta sai faduwa yake ba kakkautawa, inka kula da hannunta ma rawa suke yi.
Yana shigowa ta taso a rikice tace " Me ya samu Abdulmajid?"
Hisham yace " tun yaushe nake aikawa kizo?"
Tace " meya sameshi?"
Hisham yace " yana asibiti gun Turab."
A rikice tace "wani irin hauka nakeji haka?"
Ganin baiyi magana ba cikin tsawa tace " uban waye ya dakarmib d'a? A kuma wani dalili ne zai kasance gun Turab??"
*Turab*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*73*
Ta gabansa ta wuce a zuciye tai waje.
B'angaren Turab ta nufa, ba kowa a bangaren sai mai kula da kofa, gaisheta yai ya sanar da ita ai ba kowa a nan.
Juyawa tai hankalinta a tashe, ina ya kaimata d'anta? Itakam mai makon wannan ranar ta zama ranar farin ciki yau kam wannan ranar ta gama zame mata ranar bakin ciki.
Ga magrib ta kawo kai.....
***********
Duk yanda Khadija taso da ya bud'e ido amma inaaa, ya kasa,yana kwance idanunsa a rufe, itakam gani take kamar baya haccinsa, sai dai shikam bayaji zai iya bud'e idanunsa yaga maike faruwa a wannan duniyar, bayasan ya bud'e idanunsa yaji abinda kwakwalwarsa bazata iya d'auka ba.
Khadija zama tai a gabansa duk ta rame a 'yan kwanakin nan dan itakam sam yanzu rayuwar bata mata dadi, tace " Yaya ka taimaka ka farka."
A can gidan Barde kuwa kwance take a kan gado banda juyi ba abinda takeyi, ta rasa menene ya hanata bacci, ta dade tanata juyi ta gaji ta mike zaune tare dayin dogon tsaki tace " Allah ya isa? Wannan wace irin muguntace? Haka kawai ku samu mutum ku hau dukansa ba gaira ba dalili?"
Ahh ashe fa akwai dalili tunda Ya Turab akaje daka shi kuma ya shiga motar?
Hannu tasa akan kirjinta tare da turo baki gaba tace " Allah sarki, ashe mutumin nan nada tausayi, sannan zuciyarsa ba wai mara kyau bace duka, me yasa muka kasa gani?"
Ajiyar zuciya tai ta tuno sanda take mai rashin mutunci shi kuma yake nuna ba komai, batasan sanda ta sa murmushi ba, tunowa datai yanda ta ganshi a kan gado yasa jikinta yai sanyi.
Idanunta ne taji ya ciciko, da sauri ta kwanta taja bargo ta rufe duka har kanta.
***********
Mai Martaba ne ya kalli Turab yace " ya akai Abdulmajid ya kasance cikin wannan halin?"
Turab ya kalli Abdulmajid da ke kwance yana bacci, karfe shida da rabi ne na safe dan ana sallar asuba suka taho shida Mai Martaba.
Khadija na kwance akan sallaya rike da karamin kur'ani izu biyu da alama tana karatu bacci yai gaba da ita.
Yace " Tuba nake ranka ya dade amma ni akaso halakawa."
Sarki ya kalleshi yace "Shi kuma yaji kenan?"
Turab ya d'aga mai kyai.
Idansa ya runtse kadan sannan ya juya.
Turab yace " Abba bazaka shiga ba?"
Kai ya girgiza yace " kana tunanin zaiso gani na? Ko kana tunanin zai so ganin kowa? Bayan yaji da kunnensa mahaifiyarsa na neman yin kisan kai? Me kake tunanin yana ayyana wa a kwancen nan da yake?"
Turab ya kalli Andulmajid cikin tausayawa.
Sarki ya kamo hannun Turab yace " Abu Turab!"
Turab ya kalleshi sai dai bai amsa ba.
Sarki cikin wata irin murya yace " na girma, sannan ko ban girma ba haka na taso a rayuwar auranmu da barin Magajiya taci galaba akan dukkan lamuranta, saboda bata taba barin evidence dazai nuna tabbas itace ta aikata abu, sannan inba wanda ya san halinta ba ba wanda zai yanda akan abin da zata iya aikatawa, ina rokonka daka taimakama wannan mahaifin naka ya aiwatar da babban harkar shari'a ta gaskiya na karshe akan gadon mulkinsa, ka kawomin hujjojin da zasusa Magajiya ta fuskanci hukunci akan mayyan laifukan da ta aikata, wannan shine babban burina da ya ragemin a duniya in hakan ta faru inaso inyi murabus in baka mulkin nan, in d'auki mahaifiyata da matata mu ziyarci ka'aba dan ziyarar d'akin ma'aiki sannan mu jira sanda in karasa rayuwata cikin al'umma ina kallan yanda kake tafiyar da naka mulkin wanda shine abinda nafisan gani."
Turab yai shiru yanajin kalaman mahaifinsa,can ya d'ago yace " Abba insha Allah wannan d'an naka bazai baka kunya ba, sai dai maganar murabus mayi daga baya in komai ya kamalla."
Sarki yai murmushi sannan ya kara kallan Abdulmajid cikin tausayawa sannan yai waje.
Turab ne ya murd'a d'akin jinshi a kulle ya kai hannu zai kwankwasa.
Yanda yaga khadija tana bacci ne yasa ya sauke hannu tare da fasawa, ya tabbatar tana bukatar hutu.
Maida kayan mota yai ya zauna a cikin motar tare da kwantar da kansa jikin kujera.
Garzali ya saukemai glass, a hankali shima bacci ya zareshi.
*********
Magajiya kam wannan rana a zaune digirgir ta mata, babban tashib hankalinta duk inda ta aika a nemomata Turab sai ace baya nan, a wani hali Abdulmajid yake ciki? Dan itakam batasan wani abu ya sameshi, yanzu in matsala ta sameshi ta tabbatar shikenan ba shi ba hawa mulki, in hakan ta faru kuwa to wallahi sai dai kowa ya mutu dan Abu Turab bai isa hawa mulki ba sai dai su mutu tare.
Karfe bakwai tai wanka tai kwalliya tsaf kai kace ba matsalar dake damunta ta kintsa ta fito.
Masu kula da ita mutum biyu tace " su biyota."
Wajen karfe takwas tasa driver dinta akan ya wuce da ita ABU, manta wa ma tai ta tsaya tunanin ina aka kaishi.
Suna isa asibitin cikin sa'a ta hango motar Turab a waje.
Driver dinta ta kalla tace " je ka kiramin Garzali."
Nan yai waje, bai dade ba sai gasunan tare, Magajiya ta kalli Garzali tace " me kuke a waje haka?"
Yace " Yallabai ne ya samu bacci."
Tace " ayya, gashi shi yace inzo asibitin mu shiga tare gun Abdulmajid, kuma ba dadi yana bacci a tasheshi, ga ba wanda yasan gun, da alama sai dai ka taso shi din ko?"
Garzali yace "gun Yarima zaku?"
Tace " eh, kasan jiya ina cikin taro ban samu nazo ba sai yanzu."
Sunkuyawa yai yace " nasan d'akin in ba damuwa sai na kaiku kafin ya tashi."
Tace " shikenan."
Ta fada tare da fitowa.
Sun isa har d'akin, ta sa aka kwankwasa kofar.
Khadija dake kwance ta mike tare da zuwa bakin kofar tace waye?"
Magajiya tace " Bud'e."
Kallan masu kula da ita tai a Garzali tace "su juya."
Gaban Khadija ne ya fadi dan Turab ko Ummansu bai bari tazo ba, a hankali ta bud'e kofar
Suna juyawa ta d'aga hannu ta wankama Khadija wani gigitacen mari.
Kuncinta ta rike saboda azabar da taji, shikanshi Abdulmajid sai daya farka daga baccin, dukda dai bai bud'e ido ba amma yana jinsu.
Magajiya tace " Wato ke kin zama rikakiya ko? D'ana bashida lafiya dan tsabar rashin mutinci baki aikomin ba, bare insa ran zaki sanar dani inda yake."
A yanzu ji take zata iya yin komai dan kare d'anta, duk kuwa da yanda takesan Khadija.
Wucewa tai ta kusa da ita ta nufi gadon da Abdulmajid ke kwance.
Kallansa ta shiga yi sannan ta sa hannu kan kafarsa tace " wa ya saka? Wayace ka shiga motar da ba taka ba? Da kai nake magana, ka bud'e ido ka bani amsa ko sai ranka ya b'aci?"
Gaban Abdulmajid ne ke ta faduwa.
Muryar Khadija taji tace " Haka Uwar kirki ya kamata ta fada ma d'anta dake kwance ba lafiya?"
Magajiya ta juyo ta kalleta tace "mene?"
Khadija tace " girma ana bawa wanda yasan darajarsa ne sai dai wanda baisan darajar ba banaji ya cancanceshi, bansan me kike nufi ba da cewa Wayace ya shiga mota ba amma banaji haka ya kamata uwar da danta ke kwance ta fadama d'anta."
Magajiya cikin gadara ta fara takowa inda Khadija take, ba shakka yarinyar nan Turab ya gama lalatata.
Kusa da ita tazo ta d'aga hannu zata kara wanka mata mari.
Har Khadija ta runtse ido jin bataji saukar mari ba yasa ta bud'e idanunta a hankali.
Magajiya ce ta kalleshi tace " me kakeyi hakan?"
Turab ya kalli Khadija yace " bamu guri ko?"
Khadija tai waje.
Turab ya sauke mata hannunta yace " me kike anan?"
Tace " kaine kasa d'ana a cikin motar daya kamata ka tafi ko?"
Turab yace " mene?"
D'anki?
Hannu yasa akasan hancinsa yace " a