Showing 57001 words to 60000 words out of 273152 words

Chapter 20 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72761

yaja mata koma minene.


‘Ai ban ce yai min a lokacin ba, amman wai yai min mugunta’


Ta fada a ranta, a fili kuma sai tai kwafa har sai da Inna ta juyo da tsoro ta kalleta, domin yanzu tsoronta take ji ganin abunda ya faru jiya. Mikewa tai tsaye ta karasa gurin Inna tana dan murmushi kamar ba ita ba.


“Inna yaushe shi mutumen zai zo?”


“Wane mutume?”


“Shi mana”


Ta rufe ido tana dariya wai ita kunya. Inna ta tabe baki, ta wani bangaren bata ganin laifin Fadime, tun da ba a taba cewa ana son ta ba ba a taba sallama mata ba da sunan fira ba dole kuwa idan ta ji ana sonta ta jidadi.


“Ban sani ba”


“Inna in be zo ba ni a kai ni to, kin san su mutane birni basa zuwa kauye ko saboda irin hanyar nan, kin ga tun da na iya boko shikenan sai mu yi ta magana da turanci zai ji na burge shi”


Ta fada tana ji wani irin dadi a ranta, jiya har mafarkinsa tai, ta ganshi wani mummuna amman bata ji komai ba saboda neman mijin kawai take ita dai burinta ta ga miji. Jin Inna ta mata shiru yasa ta tashi ta koma inda take ta zauna tana kallon yadda Inna ke raba kokon da ta dama.


‘Ni ma idan na yi aure haka zan yi, sai na yi girki nai komai irin na mata, kuma na haihu ni ma’


Ta saka a ranta tana shafa cikinta murmushi ya wanke fuskarta. Mikewa tai tsaye ta nufi gurin ruwa ta dauko wani tulun.


“Ina zaki je?”


“Ruwa zan debo”


“Aa ba yanzu ba, jiya jiya kika je kika kwashe aiki yanzu kuma kice zaki je, a a ban yarda ba, waya sani ko gulbin ne ke da aljanunn”


Amo dake cikin daki ta fito tana amsawa Inna.


“Lallai kam indan ruwa bari Hajjo ta debo sai ta cika mana gidan”


Ba dan ranta ya so ba ta aje tulu ta koma ta zauna ta fara motsa kokon tana ta tunanin abun da zata yi ta fita. Bata sha rabin kokon ba sai ga Ma'u ta shigo gidan bakinta har rawa yake sai dai gani Inna yasa tai shiru bata ce komai ba bayan gaishe da ita da tai sai kuma ya jikin da tai mata. Can dai Ma'u ta tashi tana kyafta ma Fadime ido.


“Na tafi Fulani Allah kara sauke”


Sai Fadime ta mike tsaye tana satar kallon Inna.


“To bari na rakaki”


Har sauri saurin take ta riga Ma'u fita daga gidan. Suna fitowa Ma'u taja ta gafe


“Fulani Wallahi naje na fadawa Inna Bubakar kin ce mijinta zai kara aure nan da kwana biyu”


Fadime ta zaro ido.


“Miyasa kika fada ba nace miki sirri ba ne”


“Dan dan ta tabbatar idan da gaske ne kuma ni na tabbatar, yanzu ta aiko tace a kira ki”


“Wallahi ba zan je ba, dan ta karyata ta ni ko? Ko taja Bappa yai min duka”


“Ba duka zata ja miki ba, kika san ko kudin zata baki tace ki fada mata wani abun”


Duk yadda Ma'u ta so taje kiran da Matar take mata sai Fadime ta ki saboda ta san bata da gaskiya, idan aka ce waya fada mata dole tace aljannun ne kuma tasan Bappa zai iya dukanta ko ya sake mata wani karatun.


“Ki ce mata anjima zan zo”


Ta juya ta koma ba tare da jira abunda Ma'u zata fada ba. Dawowa tai ta zauna, da an yi sallah sai ta ji gabanta ya fadi dan gani take kamar matarce zata so ta fadi maganar a gaban Inna. Can dai ta tashi ta shiga daki ta rubuta abunda ya faru jiya tun daga kan yadda su kai da Wasim har zuwa karatun da akai mata da aljanun karya da tai. Ana gama sallah la'asar Fadime ta kwance shanu wai zata je gurin kiwo.


“Fulani kin san yadda kika yi jiya, ki bar zuwa kiwon nan sai gaba idan kin samu lafiya”


“Ni lafiya ta kalau, idan ina zaune ma sai na ji kamar nai ihu ai kara naje dajin dai”


Duk yadda Inna ta so Han Fadime zuwa kiwo a yau abu ya ci tura, dan Fadime tsayawa tai kai da fata akan sai taje ganin Bappa ya tafi gari, ta sani idan shi ne bata isa ta musa masa ba duk kuwa da irin son da yake mata.
Haka ta kora shanun suna gaba taba biye har suka isa cikin daji, a iya alkawarin da tai a yau ba zata yi magana da Wasim ba, kuma ba zata sake kusantar inda yake ba, duk kuwa da irin burin da take da shi na wani taimako da take son yai mata, kin magana da shi na nuna fushinta ne, ta dayan bangaren kuma tana jin tsoronshi, dan ta san duk mutunen da zai iya dabon maciji a take ba karamin matsafi ba ne.
A inda ta saba zama ta zauna, tana ayyana cewar ko ta ji busarsa ba zata leka ba, zuciyarta na raya mata dole zai zo inda take. Kamar yadda ta saka haka ta faru tana jin takun mutum a gefenta ta ki ta daga kai ta kalli gefen dan ita ala dole tana fushi. Murmushi ne mai kama da dariya a fuskarsa, ya zauna kusa da ita yana kallonta, sai ta ki ta juyo balle ta san da mutum a gurin, dauke kai yai yana cigaba da murmushin mai kama da dariya yana cin guava dake hannunsa, can kuma ya leko fuskarsa wacce ita ce tafi komai daukar masa hankali a cikin hallitarta, bayan kyau da fari da gashi Fadime bata da wani abu da za a kalleta da shi a ce ana sonta, domin kirjinta da shi da babu duk daya, balle ayi maganar mazaunai.
Wata uwar harara ta watsa masa, har ga Allah haushinshi take ji kuma da ace ba shi bane tabbas da mai raba su a yau sai Allah, amman tana tsoron tai masa wata rashin kunyar ko wani sherin yai mata wanda ya ci uban nata.


“Ina ta tunaninki tun jiya”


Ya fada yana kokarin danne dariyarsa, domin babu abun da be sani ba na isa da tai da maciji a kanta. Ta masa banza tana son ta harare shi ba dama tun da tana tsoro. Ya mika mata guava hannunsa.


“Karbi ki ci”


Ta yatsina fuska alamar kyama, daman can bata jin ragin kowa ciki har da Babanta da Inna balle kuma shi. Dan karamin bakinta ta kurawa ido yana ta kallonsa sai ta soma jin halshenta na motsawa, ta kalle shi da sauri.


“Me ka min?”


Ba shiri ta rufe bakin jin muryata kamar ta wani kwaro. Ta mike tsaye da sauri tana zaro ido.


“Wayyo Bapppa”


Kamar wani karamin kwaro na magana haka muryarta ta zama, zata ranta ana kare ya riko ta.


“Zaki min magana?”


Ta gyada kai da sauri hawaye na sauko mata, sai yai murmushi yana kallon fuskarta yana jin kamar ya hade ta, duk wani motsi nata burgeshi yake. Bakinta ya sake kurawa ido sai ya halshenta ya sake motsawa bata bari ya kara ta sa hannu ta rufe baki tana fashewa da kuka, sai ya kara rike ta gam yana dariya domin fisge fisgen take tana son ta subuce daga rikon da yai mata.


“Ki zauna idan ba haka ba, ba zan gyara miki halshen ba, kuma zaki tafi da shi gida a haka, zaki zauna”


Ta gyada kai da sauri, sai ya sake ta har lokacin dariya yake, ta zauna saman karamin dutsen sai ya mika mata guava daya bata dazun ta ki karba, kamin yace komai ta karba ta saka a baki ba ta ma wani tsaya taunawa da kyau ba ta hade.


“Na hade”


Sai ta ji muryar kamar duro, a take ta fashe da wani irin kuka, sai kuma tai saurin yin shiru ta rufe bakinta domin ita ma kanta tsoron muryar take, ji take kamar kukan da muryar ba a bakinta suke fitowa ba. Ta fara masa na kurame alamar roko tana nuna masa bakinta. Sai ta sake jin halshen ya motsa zata saka hannu ta rufe ya rike mata hannun. Wani uban ihu tai shi kanshi sai da ya duke kanshi ya runtse ido saboda kyakyar muryarta har cikin kai take shiga.


Wani mamaki ne ya cika ta jin muryarta ta dawo daidai, sai tai dan murmushin tsoro tana kallonshi.


“Dan Allah da gaske kai ba aljani ba ne?”


Ya zauna kusa da ita yana ta kallonta.


“Ni mutum ne mana, bana fada miki muna tsafi ba”


“Na yarda...”


Ta fada cikin tsananin mamaki tana kallonsa.


“Miyasa kake kallo?”


“Burgeni kike”


Ya ansa mata still yana kallonta, sai ta nuna kanta.


“Kana so na kenan?”


Sai ya dauke kai yana murmushi, ita kuma ta ji kunya ta rufe ta, ai be kamata ta tambaya, idan yana sonta shi ya kamata ya fada, ba ita ba. Ta sinne kai kasa tana yan zanezane.


“Ba ni labari”


Ta dago kai amman sai ta kasa kallonshi saboda kunyar maganar dazun.


“Ba ni da labari... ”


Ta yi shiru, shi dai sai kallonta yake can kuma tace.


“Kishiyar Innata tace ta min miji a birni, amman har yanzu be zo ba”


“Aure za a miki?”


Ta yi shiru ita dai kam tana son aure a rayuwarta, da za a mata auren ma a take da ta huta. Ta kalleshi


“Zaka iya min tsafi na gan shi? Ko ka kira shi ya zo?”


Yayi murmushi yana kallon cikin idonta.


“Kina son ki san mijinki?”


Ta daga kai ta sauri.


“Eh”


Ya mika mata hannunsa.


“Kawo hannunki”


Sai ta miko masa hannun, ya dora saman tafin hannunsa yana kallon idonta.


“Washhhh sanyi hannu sanyi sanyi”


Ta fada tana saurin janyewa.


“To duk namiji da ya taba hannunki kika sake jin irin wannan sanyin shine mijinki”


Da dan bude ido tana kallon hannun nata.


“Da gaske? To mu gaisa”


“Idan kika ji sanyi a hannunki fa?”


“Shikenan kai ne mijin”


“Idan kuma ba kiji ba fa?”


“Shikenan ba kai ba ne”


Ya mike tsaye yana murmushi ya ciro guava a yar karamar jakar da ke kugunsa, sai tai saurin kai hannu ta taba hannunshi, saurin fisgewa yai.


“Tafin hannunsa zaki taba ko ya taba naki, idan tafin hannunki da hannun wani namiji su kai taba juna kika ji sanyi to shine mijinki”


Yana fadar hakan ya fara tafiya yana cin guava.


“Ina zaka je?”


“Garin mu”


Tayi shiru tana kallonshi.


“Miyasa jiya nan kai min tsafin maciji a nan ba a gida ba?”


“Ba ke kike ce a miki ba”


“Amman ai ban ce a nan ba, a gida na ce”


“Ina son ki ba ni nishadi ne shiyasa”


Ya fada yana ta kallonta. Sai tai dariya.


“Har da karyar aljanu nai nace sunan aljanina Sama'ila, kuma sunan Bappa na ne”


Shi ma dariyar yai, ya sake kai guava bakinsa sannan ya mika mara ragowar. Sai ta girgiza kai alamar a'a tana kyankyami, be ce mata komai ba yai murmushi ya juya ya cigaba da tafiyarsa har ya haye saman dutsen ya dago mata hannu ita ma ta daga masa, sannan ta sauke tana kallon hannun na shi.


“Yana zuwa zan taba h.... ”


Bata karasa ba ta ji muryarta ta zama kamar ta shanuwa saboda kara da munin sauti, da sauri ta rufe bakin ta fara hawa saman dutsen tana nemansa amman ko alamar sa bata gani ba, ta sauko a firgice ta nufi gida bata ko bi ta kan shanun ba.
Kamar wacce aka koro haka ta iss gida, Inna na zaune da Rammu Fadime ta shigo gida babu ko talkami.


“Ke lahiya Fulani abun ya tashi kuma?”


Har ta bude baki tai magana sai kuma ta rufe bakin ta fara mata na kurame, tana nuna mata bakin nata. Inna ta taso da sauri tana fadin.


“Bude na gani”


Ta hangame bakin tana hawaye kamar ba ita ba.


“Ke babu komi ciki Fulani ya kai ne wai?”


Bata son ta yi magana Inna ta ji murya, ita kanta tsoron muryar take dan ji take kamar ba a bakinta take fitowa ba. Babu juyin duniya da Inna ba tai ba amman Fadime ta ki magana sai dai tai nuna. Shanun ma Hajjo aka tura ta dawo da su gida, hankali Inna duk yabi ya tashi, a zatonta Fadime ta daina magana ne, gashi ita kadai cikin gidan dan Amo bata nan kuma bata son kiran makota kar Bappa ya dawo ya hau ta da masifa, tun da komai cewa yake sirrinsu ba sai wani ya ji ba.


Sai daf da magarina Bappa ya shigo gidan da yar tsarabarsa, daman a duk lokacin da yaje burni ya dawo sai ya musu tsaraba, Bappa irin mazajen nan ne da basa son shigowa gida hannu sake. Sai dai tashin hankalin da ya tarar a gurin amaryarsa ya kawardar komai, domin kuka ya tarar tana yi kamar yadda Fadime ma take kuka. Bappa ya nufo Fadime cike da mamaki da kuma tsoro a lokaci daya.


“Fulani ba zaki iya magana ba?”


Kasa cewa komai Fadime tai sai hawaye take, tsoro take kar tayi magana ta sake jin murya, ga kuma tsoron Bappa kar yace zai kira mai karatu ko ya daketa.


“Zan iya”


Ta fada da muryarta mai ban tsoro, gaba daya Bappa jin yai kamar muryar ta cika duniyar nan gaba daya, be san lokacin da ya jefar da kayan hannunsa ba ya riko rigar Inna wacce ta kusa wuce da gudu ya dawo ta ita baya ya kara ma kafarsa giya.








FALMATA POV.


Tana zaune ya turo kofar dakin ya shigo hannunsa rike da takeaway da robar ruwa, mikewa tai tsaye da sauri tana kallonsa, kallo daya yai mata ya dauke kai ya aje mata abincin ya fice. Bata bukatar ya fada ci zata yi a yadda take jin yunwa ko da guba aka saka a abincin zata iya cinsa. Naman kazar ta fara cinyewa rabon da ta ci nama har tun na sallah, shimkafar ma sai ta ji kamar ta fi ko wace wane abinci dadi saboda bata cin abinci mai dadi a gida.
Ruwa kan kadan ta sha saboda ta riga ta cika cikinta da ruwan fonfon da ta sha na bandaki. A maimakon ta hau saman gadon ta kwanta sai ta kwanta a kasa, tana ta kallon pop bachin yace mata ba dai shi ba, yadda ta ga rana haka ta ga dare, babu komai a cikin ranta tunanin kudin Tumba data taba idan ya maida ita gida yace guduwa tai ta san Baba zai iya saka wuka ya yanka ta ne, wasa wasa ta ji ana kiran sallah asuba, kamar yadda tai a jiya haka ta shiga bandakin tai alwala ta fito ta sake shimfida dankwalinta tai sallah. Tana cikin addu'a Sirleem ya turo kofar dakin ya shigo. Tea mai kauri ya aje mata da bread sai sake mikewa tsaye kamar dazun tana kallonsa.


“Dan Allah karka maida ni gida”


Uffan be ce mata ba, daman kuma be da niyar ce mata komai yana aje mata tea ya juya ya nufi kofa.


“Wallahi idan ka maiyar da ni Baba ya ji cewar na gudu sai ya yanka ni, kuma Umma sai ta kusa kashe ni saboda na taba mata kudi”


Daf da zai fice ta fadi haka, sai ya tsaya cak ya juyo ya kalleta, tausayinta ya kama shi how old she is da zata zabi guduwa da bar gidansu? Ko bata fada masa ba ya san ana azabtar da ita tun da har ta zabi barin garinsu da gidansu ta zo inda bata san kowa ba, amman rayuwarta yake ji kar ta aikata irin abun da Mansura ta aikata ya zame mata tabo, a kurciyarta zata iya lalata rayuwarta, amman idan tai hakuri da wahala zata ci riba kuma zata wuce kamar ba ayi ba.
Juyawa yai ya fice daga dakin, ita kuma ta zauna ta fara kuka tana tunanin irin mugun dukan da Baba zai mata, bata tunanin zai barta ta rayu ma idan ko har ta rayu to sai dai ta zama musaka.
Misalin 6:30 ya sake turo kofar dakin, ya tsaya daga jikin kofar yana kallonta, ya same ta a yadda ya fita ya barta, tana kuka kuma bata taba tea ba.


“Fito muje”


Mikewa tai tsaye ta nufi kofar hawaye na sauko mata kamar dan irin wannan ranar kawai ta tanade su. Bata ce me zata ce masa ba, tun da har ya kasa sauraranta ta san ba zai fahimce ta ba, a yanzu ba ta da wanda zata karantawa damuwata balle ya nade mata kuncinta. Ta yarda a gidansu bata da gata, a nan din ma bata da gata. Da kanshi ya bude mata gidan gaba ta shiga ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga mazauninsa ya ja motar.


Tun da ya fara tafiya wata kalmar bata shiga tsakaninsu ba, daji take kallo tana share hawayenta lokaci zuwa lokaci, ta sadakar kuma ta yardar da kaddarar da ta rabo da gida, ta yarda wata kaddararce take bibiyarta a yanzu na fadawa wata damuwa. Tun yana tukin tana kallon titi har bachi ya sallama mata ita kuma ta amsa masa cikin sauki, daman tun jiya basu hadu ba. Sai da ya tabbatar da bachin nata ya yi nisa sannan ya faka motarsa gefe ya fita ya zaya gefenta ya bude mata a hankali kwantar mata da kujerar ya rufe, kamin ya dawo motar ya ciro wayarsa ya kira Mansura bugu daya ta dauka.


“Sirleem ina yarinyar nan ta kwana?”


“Tun jiya na saka ta a motar Yola”


“Ina ta kiranka baka dauka ba tun jiya, kuma ka san zan samu”


“Shiyasa na kira ki yanzu”


Ya fada yana kallon Falmata ta cikin farin gilashin motarsa, bachinta take hankali kwance kamar wacce bata da damuwa. Ta saka hannu ta share hawayen idonta.


“Kana ina kai”


Ya daga kansa yana kallon katon dajin.


“Somewhere.... Anjima zan kira ki”


Be jira cewarta ba ya yanke wayar ya maida aljihu ya zagaya ya shiga motar ta cigaba da tukinsa. After every deep breath sai ya kalli Falmata wacce ke ta ranko bachi har ya shiga garin Yola.
Kai tsaye ya nufi GRA, a gaban wani katon gate ya faka motarsa sannan ya fita ya doshi gate din yai knocking, babu bata lokaci mai gadin ya leko.


“Ranka ya dade kai da kanka kake buga gate”


Sirleem ya dan yi murmushi.


“Allah yasa Momy dai tana ciki”


“Yanzu yanzu ko ta dawo”


Mai gadin ya fada yana matsa masa daga kofa. Sai da ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login