Showing 183001 words to 186000 words out of 273152 words

Chapter 62 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72754

ta kwanta tana ta hawayen da bata san ta ina suke zo mata ba, miyasa ranar yau zata zame mata haka? Why rayuwa ta zabi jefata a irin wannan halin? Me ta aikata duniya ta mata juyin masa? Hannayenta ta saka ta rumgume kirjinta tana jin wani irin ciwon kirji da ba zata iya misaltawa ba.
Ana saukowa daga sallah jumma'a aka daura aurenta, yan daurin aure na dawowa gida ya cika da guda sai ta rufe ido ta dukule cikin hijabi tana amsa sallamar da hawaye ke mata, Daman abun da take tsoron jin kenan gudar aurenta gudar da take jin sautin mutuwa zai fi sosuwa a kunnenta fiye da ita. A dolen dole aka cilas mata yin wanka ta saka sabon tufafinta, da mayafi aka kira wata local mai makeup tai mata makeup aka bata 500.
Misalim 5 na yamma tana zaune a dakin ta saka abinci a gaba ta kasa ci, kawarta Khadija ta shigo, tun daga bakin kofar Khadija ta fashe da kuka, Falmata ta fara nata kukan tun tana yi a hankali har ya ci karfinta, Khadija ta zo ta rumgume ta, tana jin kamar ace akwai abun da zata iya yi ta hana auren domin Falmata ta labarta mata komai, gashi bata son rabuwa da kawarta.


“Ki yi hakuri kin ji wata rana sai labari”


Khadija ta fada tana rike da hannayen Falmata, suna ta kuka aka rasa mai rarrashin wani, sosai Falmata ta ji sanyi har ta samu sha zobon da aka aje mata, sai ta kwanta jikin Khadija tana jin kamar ace mahaifiyarta na raye.
Abun da Falmata bata sani ba, shi ne kuka be shirya raga mata ba a wannan ranar da ya kamata ace ta zame mata ta farinciki amman ta zo mata a haka, cikin kuka da bakinciki.
A lokacin da motoci su kai layi bakin titin unguwar ne mutane suka fara tambayar diyar waye za a dauka, Falmata kam tana cikin dakin Baba da Tumba sai nasiha suke mata tana kuka, tun tana kukan na hankali har ta fara bawa mutane tausayi, ana kokarin fitar da ita daga gidan tana riko mutane tana kuka, har sai da Tumba ta saka hijabinta ta kama hannunta suka fita tare, dayan hannunta na rike da kawarta Khadija. Tafiya kawai take tana jefa kafarta a duk inda ta samu tana kukan da babu sauti har suka isa bakin titin yaran unguwar suna biye da su da sauran yan biki suna ta guda, abun ka da Amarya mai farin jini.
A lokacin da suka isa bakin titi sai kallo ya koma sama, Tumba ta saki ido tana kallon mayan motocin da aka jera na alfarma har kusan guda goma sha biyu.


“Jama'a ina motar mu?”


Ta tambaya gabanta na faduwa, Sai yan bikon su ka ce


“Su ne nan ai, amman ga motar da Amarya zata shiga can”


Sun nuna wata kafirar mota mai kyau fara sol kana ganinta ka ga sabuwar mota, a take kallo ya koma sama, daga Tumba har yan biki suka koma mamaki, ba ma kamar ita ta take ganin kamar mafarki take. Fitilar hannunta ta haska fuskar matar da ita dan kara tabbatarwa.


“To”


Ta fada cikin kunya, da tsoro, wata zuciyar na raya mata cewar wata kila arosu yai ko kuma abokansa ne manyan mutane suka yi masa kara. Kamar hawainiya haka ta nufi motar da aka bude musu ta shiga sannan aka shigar da Falmata da kawarta Khadija wanda ita ma mamaki ya kusa kashe ta.


“Shiyasa Tumba ta dage sai an yi, ashe saboda ta san mai kudi ne ta ci duniya”


Khadija ta raya a ranta, haka aka cika motocin har wadanda ba da su ba a bikin sun samu gurin shiga, unguwa ta dauka cewar Falmata ta auri wani hamshakin mai kudi, wasu na fadar wai ai hakurin da tai ne wasu kuma su ce Allah ya sa na kwarai ne. Tumba kam ciki ya duri ruwa ta rasa wane tunani zata fara yi. Ita dai tana ciki motar ana tafiya har suka shiga wata sabuwar unguwa ta manyan mutane, a zatonta wucewa za ayi, ba ta ankaro ba ta ga an kunna kai cikin wani katon gida. Mai bala'in kyau da daukar hankali, fentin gidan fari sol ga haske kamar rana, idan sama ne mai hawa daya an kawata ko'ina da fulawoyi.


“Kai malam gidan Malam Mu'azu za ku kai mu fa? Ya muka ga nan kuma?”


Tumba ta sauko daga motar tana fadar haka, gabanta sai faduwa yake.


“Nan ne gidan ai Inna”


Daga daga cikin matan da suka zo biko ta amsa ta.


“Ke Ta dela wannan ne gidan da kuka he kuka gani?”


Wacce aka kira da Dela ta girgiza kai.


“Aa ba wannan ba ne”


“Inna an canja wacan ne shiyasa, daman saboda ga a yi ma wannan fenti ba ne yasa aka ce a akaita can, sai gashi kuma an gama kamin lokacin”


Numfashim Tumba ne ya fara rawa ta ja kafa kamar wata marar lakka suka doshi cikin gidan dake ta kamshin turare. Bata raina kamta ba sai da suka nas kafarsu cikin falon da za a iya kira da aljannar duniya. Sanyi ac da katon tv ga manyan kujeru farare masu kawata ido da rudarda makiya suna musu marhabun...
03/12/2021, 18:56 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*




Jirginsu na sauka direban Shattima na isowa, duk inda suka bi sai an kalli Shattima dake cikin shiga ta manyan kaya ga kuma Bappa da Kawu dan iroro dake biye da shi cikin shigarsu ta fulanin kauye, kana ganinsu ka ga fulanin ruga. Kawu dan iroro sai washe baki yake ganin a jirgi suka sauko abun da be taba tunanin zai faru, tun kam su karaso gurin motar Baba Adamu ya fito ya bude ma Shattima gidan baya a tunaninsa baya zai zauna kamar yadda ya saba. Sai ya ga sabanin haka ta hanyar nuna ma su Bappa mazaunin baya.


“Bismillah Bappa ku shiga mota”


Shi kuma ya bude front seat ya shiga ya zauna, Baba Adamu ya fisge motar kamar yadda ya san Shattima na son tuki. Bappa be tabbatar da Shattima babban mutum be ne kuma dan Babba mutum har sai da suka shiga masarauta, a nan suka rika kallon kallo shi da Kawu. Shattima da kansa ya sa a kira masa sarkin gida, sai ga shi ya zo da gudu ya zube gaban Shattima yana kwasar gaisuwa.


“Allah ya taimake ka, Allah ya kara maka lafiya”


“Sarkin gida ba bakina nan a basu masauki mai kyau”


“An gama dan sarkin da yafi wani sarki, an gama babbar giwa, Allah ya kara maka lafiya rai ya dade yai karko”


Uffan Shattima be sake ce musu ba, ya wuce abunsa bangaren Ammy, Bappa da Kawu kuma suka bi bayan sarkin gida kowa ne fuskarsa dauke da mamaki.
Kamar wani bako haka Shattima ya shigo cikin falon Ammy ya zauna yana dagawa Jekadiya hannu alamar amsa gaisuwarta da tai masa. Sai da ya fara kallon tv kamin ya kalli dakin yaransa, a idan ya shigo sai ya fara zuwa ya duba su wani lokacin ma sakawa yake a dauko masa su a gidansa dake wajen masarauta. Ba karamin sosuwa zuciyarsa tai ba tunawa da babu yaran a yanzu. Mikewa yai tsaye ya saka hannunsa daya a aljihu ya nufi dakin Nana, kamar yadda ya zata haka ya tarar Fadime na dakin zaune kasa hannunta a plate tana cin tuwon alkama da miyar ganye, kana ganin yadda ta bata fuska kasan bata son cin abincin.


“Waye a nan?”


Ta tambaya kamar an mata dole tana turo baki gaba. Samun kansa yai da murmushi sai farinciki da annashuwa suka baibaye masa zuciya. Sakin kofar yai ya fara takawa zuwa inda take.


“Shattima”


Ta fada tana washe hakora, sai ya tsaya cak yana kallonta a tunaninsa ta ji saitin tafiyarsa ne.


“Ga kamshin turarenka nan Wallahi kai ne”


Ta fada da dariya. Hakan yasa shi dariya shi ma ya karasa kusa da ita ya zauna a kasa kamar ita.


“Me kike ci?”


“Yeeee na gane kai ne, ina Bappa?”


“Na saka a kai shi masauki ya huta a bashi abinci tukuna sai na sadaku”


“Aa dan Allah ka kai ni yanzu, dan ina son na ga Bappana”


“Gani?”


“No ji ina son na taba shi na ji”


“Yanzu muka shigo ki bari na huta su ma su huta”


“Aa dan Allah”


Ta fada tana kokarin saka masa kuka. Sai ya kura mata ido, daman ya san za a rina, wai an saci zanen mahaukaciya. Kamin yace komai har ta mike tsaye tana mika masa hannunta.


“Wanke min hannuna”


Ya daga kansa yana kallonta da dan mamaki irin mamakin yadda take masa abubuwa, wata kila soboda idonta na rufe ne ko kuma saboda halinta ne oho.


“Wa yake wanke miki hannu idan kin ci abinci?”


“Ni nake wankewa”


“Then why yanzu kika ce na wanke miki?”


“Saboda ka zo mana, kasan ai ina jindadinka”


“Really?”


“Yes”


“To je ki wanke sai na saka a kaiki”


Ta fara takawa tana lalebe, ganin hakan yasa shi mikewa tsaye ya kama hannun nata suka nufi toilet din Nana. Da kansa ya kunna fanfo ya tara hannunsa ya saka nashi hannun yana murza mata a hankali.


“Wannan gidan na ku mai kyau ne sosai ko? Fanfo har a bandaki mu a kauyenmu ba mu da fanfo ma sai rijiya”


Be ce mata uffan ba, har ya gama wanke mata hannun, sai ta mika masa dayan.


“Wannan ma ya taba tuwon”


Ya rika hannun ya wanke mata yana mamakin kansa, ko kadan baya son yi mata musu, baya son tai requesting abu ya hanata, sannan baya son ya ga ranta ya bace.


“Sarautar nan gidan Babba ce ko? Ko karama?”


Be dai ce mata komai ba, surutun da take ne yasa Nana ta bude kofar bandakin ta leko sai ta hango Yayanta rike da hannun Fadime yana goge mata da tawul. Tsaye tai tana kallonsa da mugun mamaki shi ma kallonta yake kamin ya kamo hannun Fadime su fito daga bandakin.


“Yaya...”


Nana ta fada tana masa kallon mamaki. Sai ya kalleta.


“Nana me kika gani?”


“No ban ga komai ba”


Ta amsa masa tana zaro ido, sai ya juya sai kuma ta sake kiransa.


“Ya na ga kana wankewa Fateema hannun”


Juyowa yai yana kallonta fuska ba yabo ba fallasa.


“Zan iya sirri da ke?”


“Ba zan fadawa kowa ba, i mean ban ga komai ba”


“Good”


Ya juya ya nufi kofa sai ta bishi da kallon mamaki har ya fice hannun Fadime na cikin nasa. Sai da suka fito sannan ya saki hannunta.


“Bi yo ni”


Saurarawa tai ta fara bin inda take jin takunsa har suka iso cikin falon.


“Jekadiya ki kai yarinyar gurin mahaifinta, sarkin gida zai fada miki inda yake”


Yana fadar hakan ya mike zuwa dakin Ammy. Jekadiya ta mike tsaye da sauri bayan ta amsa ta kama hannun Fadime suka fice zuwa neman Sarkin gidan, sauko suka downstairs tana rike da hannun Fadime har suka fita gate din zuwa inda ta san Sarkin gidan yana zama. Jurry na tsaye jikin motarta tana waya idonta sanye da bakin gilashi ta hango Jekafiya da Fadime sun wuce, da sauri ta sauke wayar ta cire gilashin idonta ta kwalawa Jekafiyar kira.


“Jekadiya”


Jekadiya ta juyo da sauri tana amsawa, juyowar da tai sai ta juyo tare da Fadime da take rike da hannunta, tun kam su karaso inda Jurry take hankalinta yai mugun tashin, ganin Fadime. Tana ganin fuskarta ta gane ta kuma ta tuna inda ta taba ganinta duk da kasancewar wacan mai gani ce wannan kuma makauniya.


“Ina Ina zaki je?”


Ta tambaya numfashinta na rawa.


“Ranki ya dade aike zan isar”


Fadime na jin ance ranki ya dade sai ta saka duka hannayenta ta kama hannun Jekadiya ta rike.


“Okay wacece wannan?”


“To nima dai bana ce ba, domin ko sunanta ban rike ba”


“Ke ya sunanki?”


“Fateema”


Fadime ya fada, sai jurry ta gyada kai.


“Owk Fateema kawai”


“Eh”


“Okay ku tafi kawai”


“Godiya muke”


Jekafiya ta fada sannan ta ja hannun Fadime suka wuce, Jurry ta juya da sauri ta koma cikin gidan tana gudu kamar zata fadi, kamin ta isa dakin Hajiya har hakki take idonta ya cika da hawaye saboda tashin hankali, da karfi ta tura kofar dakin ta shiga wanda ya saka Hajiya yi mata wani kallo na mamaki ganin ta yi abun da bata saba ba.


“Juwairiyya?”


“Hajiya na shiga uku na lalace, asirina da naki ya tonu, Hajiya na ga yarinyar nan da Kausar take fada, Hajiya ashe ita ce a gurin bokan nan, yarinyar da muka gani gurin bokan nan tana tare da wani saurayi da ba shi da riga a lokacin da muka je, Hajiya ita ce Fadime da ake fada, yanzu na ganta tare da Jekadiya na tambaye ta tace sunanta Fateema, na shiga uku Hajiya na shiga uku...”


Ta fadi kasa tana buga hannayenta kamar wata mai aljannu.


“Shiyasa take cewa a boyeta karki ganta Hajiya ta fada musu komai, ni ban ma gane kan wannan abun ba wayyo Allah na, na shiga uku idan Mai Martaba ya ji wannan abun tsine min zai yi, kuma masarautar ta karya da ni, garin Yola zai gagareni zama wayyon Allah na, ko mijin aure sai ya min tsaye Hajiya”


Hajiya ta kankance ido tana kallon Jurry, sai kokarin taro maganar take tana fassarawa da halshen da zata iya ganewa, domin yaren ya mata nauyi.


“Ban gane manufar wannan bokon ba, shiyasa be fada mana wacece Fadimen ba? Yarsa ce ko kuma me? And taya ta zo gidan nan? Ko kuma bokan Hajiya ne muka je gurinsa ba mu sani ba?”


Jurry ta kara fashewa da kuka.


“Hajiya ba lokacin yin wannan tambayar ba ne, dan Allah ki tashi muje wani gurin tun abun be gama girma ba”


Hajiya ta mika hannu ta dauki wayarta ta kira Hajiya Talatu, Hajiya Talatu na yin picking Hajiya Babba tace.


“Kina ina Hajiya Talatu?”


“Ina gida, lafiya dai?”


“Ba lafiya ba, asirinmu ya tonu, ki aika yanzu yanzu nan a dauko matar nan, gani nan zuwa”


“Innalillahi miya faru?”


“Ba maganar waya ba ce, sai na zo”


Hajiya ta katse kiran sannan ta sauka kan doguwar kujerar da take ta nufi inda mayafanta suke ta dauka wanda yai kala da tufafinta ta yafa.


“Tashi share hawayenki, ki shiga mota zan yi magana da Mai Martaba yanzu sai mu tafi gidan Hajiya Talatu”


Jurry ta zabura ta shiga bandakin Hajiya da gudunta ta wanke fuska ta fito tana gogewa da mayafinta ta fito falo a firgice, kana ganinta kasan bata cikin natsuwa jikinta sai rawa yake irin na barawo da mai kaya, tana isa gurin motarta tai ta bude motar ta shiga tai ribas, kamin Hajiya ta nemi izinin Mai Martaba ta fito har Jurry ta fara jikewa da gumi duk da kasancewar ac motar a kunne yake.
Gidan baya Hajiya ta shiga fuska a daure tamau kamar wanda akai wa bushara da shiga wuta, Jurry kam ido sai cika yake da kwalla, gaba daya ta bi ta rude, domin ta san wannan abun har ita zai taba. Kamar ta sato mutum haka ta rika gudu da motar tana sharar kwalla.


“Ki shiga natsuwarki mana, zaki tonawa kanki asiri”


“Asirina ya gama tonuwa Hajiya, indai har ta fadawa kowa to ba abun da ya rage min, kowa zai rika kallona a matsayin yar da take son ta kashe mahaifinta, kuma ace ina budurwa yar sarauta har na san bin bokaye? Wallahi babu wanda zai aure ni Hajiya kuma Mai Martaba tsine min zai yi”


Ta fashe da kuka tana duka sitiyarin motar da karfi, bata taba shiga tashin hankali irin na yau ba, duk wani abu da take tunani a da sai ya tarar na yanzu ya ci uban bata shiri ya zama har da tsonon asiri da bata suna da kuma lalata mata rayuwa gaba daya. Ta yi horn ya kai sau biyar kamin mai gadin gidan Baba Waziri ya bude mata gate ta shiga, part din Hajiya Talatu ta faka motarta ta bude ta fita, ta bar Hajiya a ciki, iyakar kokarin da tai na boye fuskarta ne ta wuce dakin Hajiya Talatu ba tare da ta yi magana da yaran Hajiya Talatu da suke falon ba, cikin har da Haroon wanda dawowarsa kenan daga Abuja, kallo daya yai mata ya dauke kai ya maida gurin Hajiya Babba wanda ta shigo rike da waya tana dannawa.


“Hajiya barka da wuni”


“Ah Ah Haroon sukar yaushe?”


“Ban dade ba, ya gida ya Mai Martaba da jiki”


“Jiki Alhamdulillahi”


Ta nufi dakin Hajiya talatu cikin taku na alfarma da kokarin danne damuwarta. Da waya makale a kunne ta shiga tana fadawa Kausar ta rufe mata dakinta ta manta ta fito bata rufe dakin ba. Tun kamin ta zauna Hajiya Talatu ta saka salati tana dora hannu a kai saboda abun da Jurry ta fada mata


“Mun shiga ukun mu, Allah ni kaina idan Waziri ya ji wannan maganar aurena ya kare kenan, ba zai dubi yaya ko shekarun da akai a tare ba, akan Mai Martaba da Ammy baya jin asss bale kuma ya ji zance har da neman kisa? Gashi na je nemawa Mai jidda maganin hana auren? Wallahi kenan nan tawa ta karewa”


Hajiya ta tabe baki.


“Ta mu ta kare zaki ce, ni kina tunanin idan Mai Martaba ya sani zama zai yi da ni? Korani zai yi ya barwa Ammy gida ita kadai, daman abun da take nema kenan, sannan na shiga a bakin duniya...”


Kamin Hajiya ta karasa Jurry ta jarba tana kuka.


“Ni kuma ba zan samu mijin aure ba, kuma Mai Martaba tsine min zai yi, na zama zakka a gidan nan”


Hajiya Babba ta kalli Hajiya Talatu zuciyata da mugun nauyi.


“Na fada miki ki aika a dauko matar nna yau yau ba sai gobe ba, ta zo nan ta yi mana duk abun da ya kamata, haka mu kai wasa a baya har Falmata da Sardauna suna mana tsaye a wuya, domin su na su duk mai sauki ne ba kamar wannan ba”


Hajiya ta ce.


“Ai kina kirana na kira matar da ta san gurin na ce ta bar abun da take ta dauki shatar motar kasuwa taje ta dauko ta, domin idan na aika tare da direba wani karin tonon asirin ne, amman gaskiya wannan bokan ya iya munafurci, ta ya zai mana haka? Daga neman taimako?”


Jurry dai sai kuka take Hajiya Babba kuma ta nutsa a duniyar tunani tana ganin abun kamar ba gaske ba.




FADIME POV.


Sai da suka wuce take tambayar Jekafiya.


“Wacece wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login