Showing 165001 words to 168000 words out of 273152 words

Chapter 56 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72755

ace za a aura mata tsoho? Wata kila shi ma mutumen banza ne, da zai zo yana azabbatar da ita.


“Ke baki da wanda kike so ne Fulani? Karki yarda a aura miki tsoho, karki yarda a aura miki wanda baki so, ki fada min idan akwai wanda kike so”


Falmata ta yi kasa da kanta kamar a zata ce komai ba, Momy da Sirleem suka zuba mata ido.


“Wanda nake so, ba so na yake d aure ba”


“Taya aka yi kika sani? Ya taba fada miki ne? Kuma idan ba son aure yake miki ba me zai saka ya zo yace yana sonki?”


Momy ta tambaya.


“Ai kin san akwai masu son mace da son banza, bana aure ba, musamman irinta da ake ganin kamar idan an tabata ba za ayi komai ba”


Sirleem ya bata amsa.


“Ke yanzu duk a cikin samarinki babu mai yi da gaske?”


Ya girgiza kai, alamar aa Momy ta sauke ajiyar zuciya, can kuma ta sake kallonta.


“Fulani zaki iya auren Ameer, yaron da kika gani ranar da kuka zo gidan nan wani baki haka?”


Falmata ta dago ta kalleta, Sirleem ma ya kalleta da sauri.


“Momy?”


Ta kalleshi.


“Na san me nake yi Sirleem i want to help?”


“Amman Ameer?”


“Yes”


“Ina da iko da Ameer duk da kasancewar ba ni na haife shi ba, kuma mahaifinsa ba zai musa min ba”


“Makaranta fa yake yi yanzu kuma baya ma kasar?”


“Na sani, na san abun da nake yi Sirleem, idan ba Ameer ba muna da wata mafitar ne akan yarinyar nan?”


“No Momy gaskiya a canja wata shawarar ba Ameer ba, Ameer yaro ne ba zai iya kula da ita yadda ya dace ba”


“Waye zai kula da ita yadda ya dace Tsoho?”


“Amman Momy ba ki yi tunanin kowa ba sai Ameer what if shi baya sonta?”


“Kai kana sonta? Zaka iya aurenta?”


Yayi shiru ya saka cewa komai domin tambayar ta zo masa kamar saukar aradu. Falmata ta kalleshi zuciyarta na bugawa da karfi tana jin kamar ya amsa da eh, duk da tasan bata da kwarji da haifar da zai so a jikintaz gashi ita ba yar kowa bace balle tace ko dan arzirkin gidansu ko sarauta wane ita.


“Ba ni da iko da kai Sirleem saboda Hajiya Balki tana nunawa kowa isa akan yayanta, ban isa na cilasta a ba saboda ita ko da kuwa ace ni din daga bangarenta na fito, balle kuma ina kanwar mahaifinka, kuma na san yadd Hajiya ta tsani talaka, ba zata saurara maka ba idan ka auri Falmata bayan ta zaba maka Nana a matsayin mata, ko da ace zan iya cilastaka Falmata ba zata samu jindadi a gefenka ba saboda Hajiya, zata ma iya cilastaka sai ka sake ta, yarinyar nn tana bukatar kula, mutumen da zai bata ilmi ya kula da ita, idan ta auri Ameer zata dawo karkashina ne”


A take Sirleem ya datse maganar yana duban agogon hannunsa.


“Momy daman na biyo da ita ne ta fada miki abunda ya faru saboda kar ki ga bata zo ba, bari na wuce akwai abubuwan da zan yi”


Wani kallon mamaki da rashin fahimta Momy tai masa, har za ta yi magana sai kuma wata zuciyar ta hana ta, ba tare da ta ce komai ba ta mike tsaye ta haye sama. Da kallo Sirleem ya bita sai da ta haye sama sannan ya kalli Falmata.


“Tashi muje”


Falmata ta mike tsaye ta ni bayansa har suka isa gurin kofar ya bude mata ta fara fita sannan shi ma ya fita. Sai da ya fara shiga motar sannan ta zagaya ita ma ta shiga yai ma motar key tare da danna horn tun kamin ya yi ribas. A wata kemis ka kaita suka duba kafar suka bata magani tare da yi mata allura sannan suka fito. Be shigar motar ba ya tsaya yana kallonta.


“Zai fi ki hau Napep da ace na sauke ki a gidanku, wata kila za a iya kara miki doka ko?”


Ta daga masa kai alamar eh. Sai yaja wani dogon numfashi ya sauke.


“Teema, ki yi hakuri da abun da zaki ji ko ki gani, kuma ki min afuwa ina son nai magana da mahaifinki gaskiya”


“Dan Allah karka yi maganar ka bashi da wani amfani a gurinsa sai ma kara jamin duka da zai yi, zan hakuri da duk yanayin da zan samu kaina, na yarda wannan rayuwar a haka ita ce kaddararta, kuma na san Allah be manta da ni ba, zai min mafita inshallah, na gode da duk wani abu da kai min, cikin har da saurarena da bani lokacinka, bayan taimako na kudi da gudumawa da ka bani Allah saka maka da alheri, ina son na bi zabin mahaifina, wata kila auren tsohon shi ne kwanciyar hankalina, na gane yadda rayuwata take tafiya, ba zan taba samun abunda nake so ba, kuma na hakura da komai zan rumgume kaddara”


Sirleem ya kasa ce mata komai sai kallonta yake yana jin wani yanayi marar dadi. Ta share hawayenta.


“Ba zan taba mantawa da kai ba, babban mutumen sananne yayi hidima da ni, ya taimaka min yayi mini gata kamar uba, Allah ya saka maka d alheri Sirleem kuma ina maka fatan alheri sai wata rana”


Ta sauke kanta kasa hawaye na zuba.


“Ba zaki sake fitowa ba ne?”


“Bana jin za a sake barina na fito, sai dai na san ba za a hanani kallonka a waya ba ko a tv, ba zan manta da kai ba, na gode kuma dan Allah kai min godiya gurin Momy ita ma ta rike kamar ya, babu kyama babu nuna tsangwama”


Sai da ta share hawayenta sannan ta juya ta fara tafiya wasu hawayen na sauko mata tana jin kamar ta fasa ihu domin ta san ba zata sake ganin Sirleem ba sai a hoto. Da kallo ya bita ya rasa tunanin da zai fara? Maganar Momy ko kuma ya kyale ta tabi zabin mahaifinta kamar yadda ta ayyana? Kalamanta sun ratsashi, sun shiga zuciyarsa sun dada masa tausayinta. Sai da tai nisa sosai da inda yake sannan ta tari Napep ta shiga tana fada masa inda zai kaita. Tun da ta shiga cikin napep din sai ta ji kamar ta samu gurin da zata fasa kurjin damuwarta ta ji sanyi, damuwarta ta soma mata aiken hawaye babu kakkautawa.


“Allah ka kwanar min da hankalina, ka saka min natsuwa a cikin zuciya da ruhina, na tuba ka yafe ni ya Allah”


Shine kawai abun da take ta maimaitawa tana kuka sosai har Mai Napep din sai da ya juya ya kalleta, daidai inda aka saba aje ta ta bukaci ya sauke ta, ta fita ta zaro dubu daya cikin kudin da Shattima ya bata ta mikawa mai napep din ya cire kudinsa ya bata canjinta, ta karba ta kama hanyar gida, tana tafe tana dingishi dayan hannunta rike da ledar maganin da Sirleem ya siya mata, hawaye kuma be fasa mata zuba ba, kirjinta sai zafi yake tana jin zuciyarta kamar zata rabe gida biyu.






_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:54 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*




Bakin gate din gidansa ya tsaya yai horn sau biyu, mai gadin ya fito da gudunsa ya bude masa gate, a hankali ya shiga da motar ya faka a yalwantaccen parking space din dake gidan. Sannan ya bude motar zai fita.


“Ina zaka?”


Ta tambaya tana kokarin kai hannu ta taba shi, be kula ta ba ya fita ya rufe ya zagaya side din da take ya bude mata.


“Fito mun kawo gida”


Ta mika masa hannunta alamar ya rikata ta fito, samun kansa yai da kallon hannun ya yan dakiku sannan ya mika mata nasa hannun ya riko nata, tafin hannunsa na shiga cikin nata sai ta tsaya cak ta fasa fitowar tana sauraren sanyi da take jin yana ratsa hannunta, a hankali ta zame hannunta tai wani sukuku kamar ba ita ba, can kuma ta fara lalabe ta ta yunkura zata fito sai kanta ya bugu da motar.


“Careful...”


Yana kokarin taimaka mata ta fito, tsaye tai ta saka dayan hannunta tana taba goshin.


“Be yi jini ba...”


Ya fada yana kallonta, bata ce komai ba, gaba daya yanayinta ya canja.


“Waye kai?”


Be ce mata komai ba ya janye ta jikin motar ya rufe motar.


“A asibiti na ji irin wannan sanyin da wani ya taba ni”


“Sanyin me?”


“Sanyi a hannuna, Wasim ya fada idan na taba hannun namiji na ji sanyi to shi ne mijina...”


Wani kasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskar Shattima, ya kalleta yana jin tana kara kwanta masa a rai, saboda kiriniyarta da yadda take abubuwa babu kintsi, sai dai ya lura iya gaskiyar take fada domin yanayinta ba bayyana.


“Ni ne na taba hannunki a asibiti, saboda batanki mahaifinki zai iya kaini kotu, saboda nemanki yake gobe gobe zan kaiki gida”


Ta yi shiru bata ce komai ba, sai murzar hannun take da dayan hannunta idonta ya cika da kwalla. Ganin hakan yasa Shattima fadada murmushinsa.


“Kin ga shikenan na kawo matata har gida”


“Aa ni bana son ka, Wasim nake so, shi nake son na aura”


Ya sake yin murmushi ya kai hannunsa a karo na uku ya riko hannunta har lokacin bata fasa jin sanyin ba.


“Dan Allah akwai wani namiji a nan ka kira shi na taba hannunsa? Ina son na tabbatar”


“Idan kuma wasa yake miki fa?”


“Sai na tabbatar, ina son Wasim ina son shi, bana son ka bana son wani mutum”


To ni nace ina sonki ne? Ya tambaya a ransa, a fili kuma sai ya ce


“Gashi kuma idan na aure mace mutuwa take, duk matan da na aura sai sun mutu”


Ya karasa yana janyo hannunta su nufi entrance har din.


“Taka a hankali”


Ya fada yana kokarin taimaka mata ta haura gurin.


“Kai baka jin komai?”


Yayi shiru be ce mata uffan ba, har su ka hau gurin ya kai keys din dake hannunsa ya saka ya bude kofar. Sai ya fara shiga sannan ya janyo hannunta ta shigo, yana kokarin tura kofar ya rufe ta fashe da kuka mai karfi.


“Miya faru?”


“Dan Allah ka kaini gida gobe, zan fadawa Bappa gaskiya zan fada masa komai”


Ya kura mata ido, hawaye take wasu na bin wasu babu tsayawa.


“Na fada miki zan kaiki gida ai, and dole ne zan fadawa iyayenki gaskiya saboda su binciki waye Wasim din”


“Mutumen kirki ne, ba mugu ba ne, yana so na yana min duk abunda nake so, zan fadawa Bappa wannan, zan fada musu gaskiya”


“Then share hawayenki, indai akan aurene, ba zan aureki ba domin ina da wanda zan aura a yanzu, ko da ma bana da ita, ba zan so kusa miki a rayuwa na datse miki jindadi da walwala ba”


Ya fada yana kallon fuskarta, maganar yake har a zuciyarsa, idan ace za a aura masa Fadime tabbas ba zai ki ba, domin har ga Allah yarinyarta ta masa kuma zai so zama da ita, sai dai ba zai so ya aureta ta rasa rayuwarta kamar sauran matansa ba.


“Wannan Wasim din ya dace, sai sha dariyarsa ya more, zai nishadantu da rayuwarki you cute”


Ya fada yana lakatar hancinta da murmushi a fuskarsa. Kalaman da yai mata ne yasa ta ji sanyi a zuciyarta har ta share hawayenta.


“Zo ki zauna”


Ya zaunar da ita a kujera.


“Kin ce kina jin yunwako?”


Ta daga mishi kai da sauri tana kara share hawayen.


“Okay zan mana order abinci yanzu me kike so?”


“Yogurt da kaza”


Ta fada har tana hade yawu. Murmushi yai yana tuna wacan lokacin daya kadeta tace ya siya mata kaza da yogurt. Ya juya ya nufi upstairs yana lasa wayar hannunta.


“Ina zaka je?”


“Sama”


Jin abun da ya fada yasa ta dan tsorata.


“Sama kuma? Nan inda nake a ina ne?”


Murmushi yai har yana daga kansa ya sauke.


“Seriously rabon da na samu kaina cikin nishadi irin wannan har na manta, ina da damuwa sosai a raina, amman haduwar da nai da ke a yanzu yasa kin mantar da ni komai, ina jin kamar babu abun da ya faru”


“Saboda me mi nai?”


“Baki yi komai ba, saboda ba intentionally kike yi ba, rayuwarki ce a haka, and i like it”


Ya fada yana kallonta daga inda yake tsaye zuciyarsa cike da shauki. Fadime ta gyara zamanta tana saurarensa domin ta jidadi da yace he like it. juyawa yai ya cigaba tafiya har ya haye sama ya shige dakinsa, Shaddar jikinsa ya cire ya saka kananan kaya sannan ya dauko wayarsa ya sauko kasa, ko da ya fito ya sameta tsaye a tsakiyar falon tana lalebe a hankali.


“Ina zaki je?”


“Ban jika ba ne shiyasa nake lalabawa”


Yayi murmushi ya karasa saukowa.


“Ya kamata a samo miki sanda ko? Ki huta da lalaben hannu”


“Aa bana son sanda ni warkewa zance, abun da mutum yake kira shi ke binsa, ni bana son muguwar sara, zan warke inshallah”


“Ni ma ai fatan warkewa nake miki ai, amman sandar zata taimaka miki ne wajen gane abubuwa da kuma tafiya kamin ki samu lafiya, na san likitan da zai dubaki ma sai ya bada wannan shawarar kamin idonki ya bude”


“Aa Wasim yace kar a taba min ido, idan aka taba min ido zai lalace ba aikin likita ba”


Shattima ya riko cinyar hannunta ya zaunar da ita.


“Shi wannan Watsin din aljani ne ko mutum?”


“Ba Watsin ba, Wasim ba aljani ba ne mutum ne, ba na baka labarinsa ba?”


Ya daga mata kai kamar tana ganinsa, ba dan ya tuna ba ko ma bata taba bashi labarin ba oho.


“Ina ka tafi dazun?”


“Sama”


Ya fada ba tare daya kalleta ba.


“Sama? Sama?”


Ta sake maimaitawa wanda hakan tasa shi dagowa daga kan wayarsa ya kalleta.


“Yeah gidana gidan sama ne, so na hau sama ne upstairs”


Ta wara ido har da jan numfashi.


“Irin gidan masu kudi ne ko?”


Ya daga kansa yana karewa katon falon dake ciki da kyalikyali duniya irin na masu naira kallo.


“Ba laifi”


Ya fada yana tabe baki, sai ta daga kai tana ji kamar ace zata iya ganin komai a gidan, abunda bata taba mafarki ta shiga gidan sama irin a masu kudi.


“To ina matan gidan?”


“Ni kadai ne!”


Ta bude baki sai dai bata ce komai ba, har sai da ta ji motsin mikewarsa tsaye.


“Ina zaka je kuma?”


“Kicin”


“Ruwa zan dauko”


“Daga ina kicin din yake?”


Be ce mata komai ba ya nufi kicin.


“Baka ji ba?”


Ya juyo kamar an amsa dole domin har ga Allah tambayoyinta sun isheshi.


“Ba zan maimata ba ai ka ji, shiyasa na ke son Wasim, da shi ne ba zai kyale ni ba, kuma ba zai tafi kicin ya bar ni ba”


Yayi murmushi.


“Wacan ai Wasim ne, ni kuma Shattima ne, Wasim yana Katsina right? Ni kuma ina yola kin ga da banbanci”


“Shattima?..”


Ta maimaita tana tunanin inda ta taba jin sunan. Be sake ce mata komai ba ya nufi cikin kicin din dan yi abun da ya kawo shi. Sai da ya dauko ya fito rike da cup guda biyu sannan ta sake aika masa da wata tambayar.


“A nan ina ne?”


“Yola?”


“Yanzu, Wasim har yola ya kawo ni? Ina ne yola ma?”


“Ba ki jin bachi? Idan kin ci abinci ki yi bachi idan an yi magariba zan tashe ki”


Ta ji gabanta ya fadi, bata sake cewa komai ba har aka danna door bell din kofar, sai ta mike tsaye da sauri jikinta na rawa.


“Na ji wata yar kara minene?”


Sai da Shattima yai kamar ba zai ce mata komai ba, sai kuma ta bashi tausayi saboda ya san bata gani dole ne idan ta ji bakon yanayi ko wani abun ta tsorata.


“Kofa ce aka bugawa, ba kin ce zaki ci kaza ba, da yogurt? Maybe shi ne aka kawo, zauna bari naje na duba”


“Ta”


Ta zauna ba dan ta natsu ba. Tana ta sauraren takunsa tana auna tafiyarsa da inda ya dosa da zuciyarta har ya isa gurin kofar ya bude. Leda biyu ce a hannun mutumen dake sanye da uniform din restaurant dinsu ya mikawa Shattima cikin girmamawa yana gaishe shi, Shattima ya karbi ledodin sannan ya rufe kofar ya juyo ya dawo gaban Fadime ya aje. Tana jin kamshin kaza da motsin leda ta hade yawu, tana jin wani irin dadi. Kicin ya shiga ya dauko mata plate ya zo gabanta ya aje ya bude ledar dake dauke da kaza biyu ya ciro dayar kazar da aka rufeta da paper ya zuba mata a katon plate din, sannan ya dauko cup din da ya aje dazun ya bude yogurt din daya ya zuba mata.


“Sauko ki ci”


Ta sauko da sauri sai ya matsar mata da su gabanta ya kama hannunta ya saka a kan kazar.


“Kai har da zafinta, Allah ya saka da alheri Allah ya biyaka”


Take ta fara aikin kazar tana tsude hannu idan ta kamo kabeji sai ta cinye ta kara da nama. Shi dai yana hakimce saman kujera yana kallonta yana murmushi, yadda take lalaben kazar ta dauka ta ci idan ta cinye ta aje kashin a kasa, duk sai ya ji ta bashi tausayi, makanta babu dadi ci kawai take ba dan tana ganin kazar ba.


“Har na tuna wata mata, lokacin da ina garin su Wasim ta zo tace tana son a mata magani, wai a kashe mijinta da dan mijinta, sunansa ma irin naka ne har da mai irin sunana”


Ta fada tana tauna kashin, daman tun da ya fada mata sunansa take ta tunanin inda ta taba jin irin sunan bata tono ba sai yanzu da ta ji naman kaza a bakinta dadinsa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login