Showing 9001 words to 12000 words out of 273152 words

Chapter 4 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72775

Aisha n suke nan ai wahala za su sha sosai tun da su kanana ne, kara dai ni da nake da girma yanzu ni dai muje ki rakani”


“Ga ruwa can a jarka je ki deba ki yi uku da bokitin ki”


Kamar ta dauki kawar tata ta goya haka ta ji dan dadi, da sauri taje ta bulbula ruwan ta cika bokinta ta kai gida ta sake dawowa ta kara wasu har sai da tai bokiti uku sannan ta hankalinta ya kwanta. Bayan ta aje bokitin a mazauninsa ta nufo kofar dakin Tumba kamar mai labe ta tsaya daga bakin kofa murya can kasa tace.


“Ga ruwan nan na debo”


“To Allah yai miki albarka Fulani ya baki miji na gari”


Tumba ta fada da far'arta, Falmata dai bata ce komai ba dan tasan ba da zuciya daya tai mata addu'ar ba sai dan ganin mahaifinta yana nan, daman can haka take mata a gaban idon jama'a ko kuma a gaban mahaifinta. Dukawa tai ta dauki takardar tsiren ta nufi hanyar dakinsu tana lasar yajin dake jiki, hakan be gamsar da ita ba sai da ta cire wani sashe a takardar dake da mai da yaji ta saka a baki ta tauna ta tsotse ruwan tass sannan ta jefar ta shige dakinsu.
Wani tsohon zanen gado ta dauka ta shinfida saman gadon karar da take bachi sannan ta kashe kyandir din ta kwanta tana karanto addu'o'i kamar yadda ta saba, Naja kam tuni tai nisa da bachin.
Asubar fari Falmata ta fito daga dakin ta dora alwala ta shiga ta fara nafila kamin ta gabatar da sallah Asuba, ta saba da wannan dabi'ar ta yin nafila kamin asuba da kuma addu'o'in safe da maraice da na bachi tun tana karama, duk da kasancewar tana da kananan shekaru hakan be saka ta watsar da koyarwar mahaifiyarta ba, ko kadan Falmata bata wasa da addu'a da kuma sallah akan lokacin komai take zata aje taje tai sallah, idan kuma lokacin addu'ar yamma yayi ko aiki take haka zata rika karanta addu'inta, abun har ya zame mata jiki idan ba tai ba sai ta ji bata cikin natsuwa.


Sai da rana ta fito sannan ta fito daga dakin ta fito harabar gidan ta tattara kayan wanke wanke ta wanke komai tas ta share gidan sannan ta cika karamin bokiti da ruwa ta nufi bandaki, sai ta ta tube tufafin jikinta sannan ta daga wani karamin dutse ta dauko ragowar amon da tai wanka jiya ta saka a soson ta soma wankanta.
Bayan ta gama ta fito tana ta tsanda domin ban dakin a kasa kasa ce ba suminti ba idan kana wanka ruwan dake sauka yana tartsatsin yana sa kafar bandakin ta watso maka a kafafuwa.
Gindin biyar ta nufa ta zauna ta saka dutsen gugar kafafuwa ta goge kafafuwanta tas ta sake wanke su sannan ta shiga dakinsu, bata ɓata lokaci ba gurin shiryawa sanin inda zata je gashi rana ya soma takewa.
Duk da irin saurin da take hakan be hana ta kwaliya ba sannan ta saka atamfa tare da Hijab ta fito cikin sauri tana saka talkaminta na roba.


“Fulani zo ga abincin ki”


Cewar Umma daga gindin murhu da take zaune tana kallon Falmata, abun ka da mai neman sai ga Falmata ta karaso cikin sauri ta cire hijab dinta ta rataya a igiya sannan ta tsuguna taja kwanon da Umma ke nuna mata mai dauke da dumamen tuwo masara.


“Fara shan wannan tukuna”


Umma ta mika mata wani ruwan rubutu dake karamin kofi, jiki a sanyaye Falmata ta mika hannu ta karba tai Bismillah da muryar da tasan Umma ba ta ji ba ta shanye, inda sabo da saba da shan magani daga hannun Umma wani lokacin ma a cikin kunu ko madara take kada mata ta mika mata kuma ta karba ta sha, sai dai bata taba mantawa da Bismillah idan zata ci abunda yafi komai batawa Umma rai kenan wani lokacin har hana ta take idan ta ji.


MASARAUTA....


Kowa a dinning din fuskarsa a sake take ana fira ban da Nana wace ta tsuke fuska kamar wata tsohuwa sai wasa take da abincin da ke gabanta.


“Hakan dai be hana ki zuwa makaranta, da ki ci abinci da karki ci duk uwar su daya ubansu daya a gurina, kullum cikin latti kike shiyasa suka aiko suka ce baki zuwa makaranta”


Mama Fulani dake kokarin daukar cup din tea ta kalleta.


“Nana ba ki son makaranta why?”


“Ba makaranta ne bana so ba Mama Fulani auren Sirleem ne bana so”


Murmushi Mama Fulani tai.


“To miya hada aurenki da Sirleem da kuma zancen karatu?”


Ta bata fuska kamar zata fasa kuka bata dai ce komai ba. Shattima ya kalleta kadan ya dauke kai yana kai plantain baki ya ce.


“Gaskiya ne yarinya Wallahi ba ki cancanci auren mawaki ba, yar Sarki Abdallah Umar Jari ace ta auri mawaka ki, abun ai be yi ba”


“Miye matsalar mawaki ne Shattima? Waka ba a sana'a ba ce? Bayan waka kuma ai yana aiki da Unicef ko duk shi din ba aiki bane? He is graduated kasan gaba ina Allah zai kai shi ne? After that yana da restaurant yana da katon Boutique, yana da shagon siyarsa phones and what else kake son ya mallaka kamin a aura masa Nana?”


Ammy na kai aya, Mama Fulani ta wara ido.


“Aa ba laifi gaskiya kuma kin ga yadda yai popular din nan kudi suke samu sosai indai yana da rufin asiri ai ba laifi ta auri abunta”


Nana ta kara bata fuska tana kallon Mama Fulani.


“Mama ni dai bana son shi yanzu”


Sai kuma ta kalli Shattima


“No ki daina kallona kar ace ni nake kitsa miki komai”


Ammy ta tabe baki tana fadin.


“Ko dai minene kyaji da shi ba abunda za a fasa idan ka ga an fasa auren nan sai idan shi ne da kansa yace ya janye ba zai aureta ba”


“Haba Ammy sai kace na yi alo ace sai idan shi ne ya fasa Fisabilillahi”


Ta fada tana kara bata fuska. Zainab dake aikin chakuda wainar kwan da ke ba gabanta da fork ta yamutsa fuska tana fadin.


“Matsalar ba wai ta aikinsa ko kudinsa ba ne, matsalar wakar da yake ne be dace ace zuri'ar gidan nan ta auri mawaki ba”


“Daga ke har Shattima wayayyen mutane ne, kin san miye waka ai kina tare da masu yinta, ba photographer ba ce ke miyasa mazan da suke zuwa neman aurenki ba su ce ai ba zasu aureki ba saboda yanayin sana'arki, kuma yarinyar a gaban kowa Mai Martaba ya tsayar da ita ya tambaye ta tana son shi ko irin kunyar da yan mata ke yi ita ba tai ba, tace tana son shi kuma aurenshi za tai, to sai yanzu dan Mai Martaba bashi da lafiya sai ku kitsa mata magana ku ss ta tsane shi ace ni na hana aure? Daman ance ni da yaya mu ke mulki Masarauta, ku dai kawai saboda ba kya son M2 shiyasa kuke wannan abu ita kuma yarinya ce karama duk inda kuka a zata dauka hawa za tai”


“No No Ammy i'm out of this”


Shattima ya fada yana mikewa tsaye tare da ware hannayensa alamar babu ruwansa a ciki ya fita daga dinning are din, Hajiya Karama ma mikewa tai tsaye daman can bata saka komai a bakinta ba tun zamanta gurin.


“Ina da inda zanje ne, ayi breakfast Lafiya”


Daga haka ta bar wajen, sai ya rage daga Nana Sai Ammy da Mama Fulani ne kadai a dinning din.


“Zaki tashi ki wuce makaranta ko sai na bata miki rai? 9:14 ace baki shiga school ba, anya wai makaranta ma kike zuwa Nana”


Ta mike tsaye tana kuka har da tara hannu a fuska ta fice rike da jakar makarantarta, kofar falon ta bude ta fara sauka saman stairs din kadan kadan har ta sauka gaba daya, sannan ta bude kofar corridor ta fice, ta sani sarai Ammy bata son ana bi ta fadarta idan za a fita amman ita da dan'uwanta abun ya zame musu al'ada ala dole sai ta nan za su fita ko su shiga bangaren Ammy.
Kwankwasa kofar tai fadawam dake can ta gaba suka bude mata da sauri suna gaisheta, ban da turo baki gaba babu abunda take har ta isa gurin direbanta wanda aja tanadar dan kaita school kadai ya faka motarsa, tun kan ta karaso ya fito ya bude mata mazaunin baya ta shiga ya rufe sannan ya shiga ya tashi motar suka fice.


“Hajiya har da yau ma can zamu je?”


“Eh kullum ma”


Ta fada tana ta kara turo baki gaba.


“Amman Hajiya idan aka gane ina cikin matsala”


“To wa zai gane? Kai zaka fada?”


“A a ni na isa ki sa amin daurin rai da rai, Wallahi ba zan taba fada ba”


Ta yi yar dariya tare ta bude school bag din ta dauko 3k ta bashi, haka take masa kullum na rufe baki dan kar ya fada cewar ba makaranta take zuwa ba, a kullum X&Z Restaurant take zuwa tai zamanta sai idan direban ya auna lokacin komawarta gida yai sannan ya zo ya dauke ta.



UNCLE AA POV.


“Sai sardaunan samarin Yola”


“Yes amman na marasa galihu, komai kuke so za ayi da yardar Allah”


Ya fada yana dagawa Wanda yai masa kirarin hannu, bayan ya gama ajewa na kusa da teburin Nana abinci ya kalleta, bachi take hankalinta kwance ta dunkule kanta yadda ba za a gane ko wacece ba. Ba yau ce ranar farko yana fara ganin yarinyar nan ba, yau kusan sati biyu kenan tana zuwa nan, kulluk kuma idan ta zo ruwa kawai rake order ta yi zaman awanin sannan ta tafi kuma kullum da uniform take zuwa, tunani kawai yake anya ba wani rashin gaskiya take tana gudo nan ba?


“Ke Ke”


Ya daki teburin, sai ta farka a firgice.


“Na'am Na'am Na'am”


Suna hada ta watsa masa harara ta turo baki gaba.


“Miye bashi ko tara?”


Ya dan wara ido sannan ya risino yadda babu wanda zai ji ya hade rai.


“Me kike zuwa yi nan?”


“Ina ruwanka ai na biya kudin ruwa”


“Ruwa kawai suke kawo ki a nan? Daga gani wani laifin kika yi shiyasa kike zuwa ki boya or maybe kina gudun makaranta ne ko?”


Ta yi saurin rufe baki tana zaro ido.


“Karya kake ni bana aikata komai kuma bana gudun makaranta, yayana ne yace na rika zuwa nan ina jiranshi kullum”


“Kullum yau kusan two weeks kenan!”


“To wai ina ruwanka wai? Ba na biya kudin ruwa ba”


“Ba kudin ruwa kawai ake biya ba sai kin biya kudin zaman da kika nai awoyi, dan mu nan karanci mutum yai zaman 2 hour ya tafi amman ke har bachi kike, ki biya kudin bachi da na zaman awoyi da kika yi”


Ta bata fuska.


“Wallahi ni ba zan biya ba haka kawai”


“To ko zan saka security can ya fitar da ke waje kin ga dai akwai mutane ko za ki sha kunya”


Yana fadar hakan ya mike tsaye ya juya, sai ta ka karewa kowa kallo tana ayyana yadda zata sha kunya idan yai mata korar wulakanci a gurin wata kila ma akwai wadanda suka santa ita bata san shi ba.


“Baka ji ba”


Ya juyo ya dawo daman Kadan-kadan yake tafiyar yana jiran ta kira shi.


“Nawa ne kudin bachin da kudin zaman?”


Yayi wani shegen murmushi yana shafa kansa.


“5k”


Ya bude school bag dinta ta ciro kudin da zai kai 50k ta kirga 5k ta mika masa.


“Gashi nan”


Karba yai a ransa yana.


‘Shegiyar yarinyar ta gani diyar yar masara tausayin kasar ne bata san zafin kudi ba’


Aljihunsa ya saka kudin daman aljihunsa babu ko sisi, sannan ya juya ya bar gurin mutane da ke vip din suna ta kallonsa shi kam a jikinsa.


FALMATA POV.


Daga unguwarsu zuwa unguwar da take aiki akwai yar tafiya mai nisa sai dai ba sosai ba, wata kila kuma ita din ce bata ganin nisan unguwar sosai kasancewar ta saba da tafiyar kasa daga wata unguwar zuwa wata a cikin garin Yola tun mahaifiyarta na a raye balle yanzu da Umma bata tausaya mata bata isa ko wani garin tace zata aikata da kafa ta ki ba.
Bata sha wahala gurin masu gadin masarautar da kuma polisawan da suke gurin ba kamar kwana biyu da suka wuce yanzu kam sun wayance ta ganin wannan shine zuwanta na uku bayan gabatar musu da ita da akai, sai dai a duk lokacin da zata shiga Masarautar ko ta fita sai ta rika jin tsoron dogarawan da kuma police din da suke gurin, domin Allah ya dora mata tsoron yan sanda sosai da sosai.
Ko'ina na masarautar mutane ne wasu da uniform wasu kuma babu kasancewar safiyata ko wa sai aikin gabansa yake.
Ta kofar data saba ni ta bi ta dauki doguwar hanyar da ke sada mutum da bangaren Uwargidan Mai Martaba, tafiya ta wata karamar unguwar tsakanin Gate din karamar kofar gate din Ammy.
Ta kofofin da ta saba shiga ta fi tana tafiya sai kara karewa gidan kallo take tana ganin kamar ba a duniya take ba, saboda yadda aka tsara gidan da kuma kwalliyar da aka masa, ta bangare daya kuma tana mamakin irin girman gidan wai ace duk ba mutum daya ne, bayan bangaren Ammy ga wani bangare can ta hango wanda aka ce na Amaryar sarki ce can nesa da shi wasu gine ginen na da ta mutane na fitowa ko na miye oho ita dai kallo kawai take, ga wasu manya manyan motoci na alfarma an faka a harabar space din Ammy, wata kila can bangaren Amaryar ma akwai motocin ko ina ma bangaren sarkin yake oho.


Ta fada a zuciyarta tana cigaba da tafiya tare da daga kanta sama tana kallon yadda aka jera windows din dakunan gwanin burgewa.
Sai ta isa bakin karamin gate din mai gadin gurin dake rike da bulalarsa ya dakatar da ita.


“Ke ina zuwa?”


“Ni ce Falmata wacce take gyara dakin yan uku”


Ya mata wani kallo daga sama har kasa ya santa tun da wannan shine zuwanta na uku amman kullum ta zo sai ya mata tambaya, da gangan ya bata mata lokaci sannan ya bata hanya ta wuce. Da sauri ta raba ta wuce daman tsayar da ita da yai a gurin cikinta ya duri ruwa abun ka da mai tsoro, kamin ta karasa kofar shiga tsakar gidan dan ita ba ta falo take bi ba sai dai ta zagaya ta can baya kamar yadda aka nuna mata ta shiga ta inda mutane suke shiga haka ma idan zata fito.


“Ke.....”


Iya dake tsaye lullube da zane ta kwala mata fira fuska a murtuke kamar bata taba dariya ba daman kuma fuskar ba ta dariya ba ce. Suna hada ido Falmata ta fara karanto addu'o'i ta nufe ta sam hankalinta ba kwanta da matar da duk kuwa da bata san aikinta ko matsayinta ko alakarta da yan gidan ba, sai dai ta lura kamar batsa shan inuwa daya domin ko ranar da aka kawota sai da tace ba a dauke ta ba dan kawai Ammy na gurin ne tace a dauke ta, kusan kullum idan ta zo aiki gidan sukai arba sai ta ji gabanta ya fadi ga wani kallo tsana da iya take mata, sannan ta hana ta ganin yaran kullum idan zata fara aikin sai tace a dauke yaran kuma sai ta saka dogari ya tsare ta har tai ta gama.


“Tafi tafi tafi tafi karki karaso nan”


Iya ta fada yana runtse ido, ba karamin dadi Falmata ta ji ba, sai ta juya ta nufi hanyar shiga cikin gidan, sai da ta gaisa da mutane da yawa kamin ta samu isa bakin kofar farko ta falon Ammy. Haka ta ratsa falo kusan uku sannan ta isa gaban wata haraba tana kallon Hajiya karama dake tsaye a backyard tana kallon wani gurin dabam, Falmata ta kasa dauke mata ido, domin ta hadu iya haduwa tana da kyau sosai irin kyaun nan mai daukar hankali ga mayan ido sai dai ba manya can sosai ba, bayan tufafin jikinta mai kamada na turawa da ta saka wato English wears ta saki gashin kanta ya sauko sai tai kamar wata baturiya abun ka da Fulani.
Ba karamin burge Falmata Hajiya Karama tai ba, domin fari na daga cikin abunda Falmata ta rasa kuma yake burgeta iya burgewa idan ta ga wani da fari sai ta ji kamar ta cire ta sakawa kanta, ba dan tana da siffar Fulani ba da kuma yaren da take ji ba zaka ka taba kallonta kace ita Fulani ce saboda bakinta.


“Ko wacece? wata kila yar sarkin ce?”


Ta tambayi kanta tambayar da bata da amsa a gurinta. Wani abun mamaki tana kwankwasa kofar corridor Iya ta bude mata tana watsa mata wani kallo mai kama da harara. Falmata ta bata yarda ta yi ido hudu da ita ba ta sanda kai kasa ta shiga. Kato falo ne mai cike da kayan alatu ga sanyin ac da katon plasma, an jera wasu ɗakunan daga gafe, kai tsaye stairs din ta nufa ta fara takawa a hankali saboda tana gudun kar tsantsin gurin yaja ta ta zame kasa, sai da ta waiga taga babu kowa bayanta sannan ta risina kasa ta shafa tile din, sai a lokacin ta tabbatar ba ruwa ba ne kuma ba mai ba, a iya tunaninta yadda take jin tsantsin gurin da yadda take ganin yana shining a zatonta ruwa ne ko mai duk kuwa da kasancewar bata jin ta taka abu makamancin haka.
Dan abun da aka nuna mata na jikin kofar ta danna wato door bell sannan ta ja ta tsaya sai rabon ido take, sai da ta danna shi sau kusan uku sannan aka bude mata kofar. Har kasa ta risina tana gaishe da Muhseen.


“Ina kwana?”


“Lafiya kalau”


Bayan ya amsa ya juya yana kallon Momy wacce ke tambayar waye a kofar.


“Wata ce ban santa ba dai shigo”


Ya matsa daga kofar wanda hakan ya bawa Falmata damar shigo cikin falon mai kama da aljannar duniya. Da sauri ta fadi ta kasa tana gaisar da Ammy, Ammy ta amsa mata ba yabo ba fallasa sannan ta cigaba da danna wayar da take.


“Ranki ya dade


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login