Showing 21001 words to 24000 words out of 273152 words
Chapter 8 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
ta, ya san zai ba zai sake kaita gidan Anti Rabi ba, bayan dazun da safen nan ma sai da tai masa gargadi, to ina zan kaita? Ko ya kaita gidan Gwaggonshi? Ko gidan Kawu Bala? Kuma idan na kaita suka gano abunda cewar boyeta na yi za su min fada? Sai tambayar kansa yake yana neman mafita, be an karo ba yaji kamar an bugu babur din da suke kai yana kokarin saita babur din suka fadi kasa daga shi har ita, babur din ya haye shi ita kuma ta mulmula ta fada kwalbati.
Kamar ita ta fi kowa ihu a duniya haka ta kwala ihu ta fashe kuka na gaske tana duba hannunta da yaji rauni da kafarta, daman can ko allura aka ce za a mata sai anyi da gaske take tsayawa balle kuma wannan da ta gurje a hannu da kafa da gefen fuska.
“Wayyo Allah Wallahi sai na fadawa kowa, sai an kashe ka yau Wallahi kai ne ka ji min rauni kai ne ka fadar da ni da babur, sai na fadawa kowa yau sai an kashe ka”
Cikin wani irin kuka da tsoro take fadar hakan tana kallon jikinta, AA na jin haka ya manta da nasa ciwon ya taso ya nufo ta ya daga ta, mutane sai sannu suke musu, ganin yana jan kafar wani yace
“Zaka iya jan babur din kuwa”
“Eh zan iya ku taimaka ku dora min ita dan Allah”
Sai da ya hau sannan suka dora masa Nana dake ta ihu tana fadin sai ta fada a gidansu. A hankali ya fara tafiya gabansa na mugun bugawa kamar zai fito, sai da ya samu wani mai chemist sannan ya faka babur dinsa a gurin ya sauko ya rikota ta sauko ya shiga da ita cikin chemist din, zaunar da ita yai sannan ya ce.
“Bari na gyara fakin din babur di na”
Bata ko kula shi ba tana ta kuka da duba kafarta domin har a cinya ta ji ciwo. AA na isa ya haye babur din ya auna a guje be be nufi ko'ina ba sai unguwarsu, kamin ya isa har wani zazzabi ya rufe shi babu muryar da yake ji sai ta Nana tana fadin sai ta fadawa yan gidansu yau ko sai an kashe shi, laifi goma da ashiri, ga boyon da yake mata ga na fadar da ita akan babur dinsa dan ya san yarinyar yar masu abu ce wata kila ma ita kadai iyayenta suka haifa ya san kuma ba za su kyale ba.
Kamar wani mahaukaci haka ya shigo gida hannunsa na ta jini sai dingishi yake. Anti na ganinshi gabanta ya fadi.
“Lafiya AA”
Kasa ce mata komai yai ya zauna bakin kofar dakinta ya dafe kanshi.
“Lafiya hadari kai?”
“Eh yarinyar ce ta roki na kawo ta nan shine na sake aro babur, muna tahowa sai wani mai Napep ya kade ni muka fadi ta ji ciwo ni ma na ji”
Anti Rabi ta daki kirji.
“Me? La'ilaha illallahu Muhammadu Rasulullah Sallalahu Alaihi Wassalam”
AA ya kalleta a tsora ce ya soma magana gumi na karyo masa.
“Kuma Wallahi na ji tana cewa sai ta fadawa duk yan gidansu, wai yau sai an kashe ni tun da na fadar da ita akan babur”
A take cikin Anti Rabi ya murda, ta dora hannu aka ta fashe da kuka.
“Ka gani ko? Sai da na gargade ka amman baka ji ba, Allah kadai ya san waye ubanta mun shiga uku, ina yarinyar take?”
“Na barta a can wani chemist na gudo”
“Kai Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, mun shiga shida”
Ta fada tana nufar butar da ke tsakar gida ta dauka ta nufi bandaki. Mikewa tsaye AA yai ya fice daga gidan, chemist din unguwarsu ya nufa yana isa be ko tsaya gaisawa da abokin nasa ba ya ce.
“Dan Allah Ilya kai min treatment din ciwon nan kuma ka min allurar malaria, ina jin zazzabin malaria na ta so min”
_________________
Waye zai zo ya cece AA 🤣😂
Me iya take kullawa? 🤔
Anya dai Hajiya Karama mace ta tana neman miji da kanta kamar yadda kike?😥
Wai me Falmata ta tarewa Tumba ne?😭🤧
03/12/2021, 08:07 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄*
By Khadeeja Candy
*6*
HAJIYA BABBA POV.
“Jarma har yanzu ban ga komai ba”
Ta fada tana karewa Jarma dake zaune a gabanta sanye da babbar riga, kansa kuma da rawani.
“Kina gaggawa ne kawai Hajiya, ba gashi mun fara ganin haske ba? Komai a sannu ake binsa”
Ya dauke kai tana kallon wani bangare na dakin.
“Ba Mai Martaba nake magana ba, Shattima shine matsalata a yanzu”
“Da Shattiman za mu fara kamin Mai Martaba ya biyo shi, idan mu ka yi gaggawa to kamar muna fallasa sirrinmu ne, ya kamata mu bi komai a sannu”
“A sannu na ke bin komai Jarma, domin burina dole ne ya tabbata, Talba kadai na ke son ya yi mulkin garin nan, so na ke na ga Ammy na zubar da hawayen bakinciki, shekarun da ta saka na yi a damuwa so na ke ta ninka a cikin bakinciki, na san a yanzu tana farinciki da ciwon Mai Martaba saboda tana ganin Shattima ne zai gaje shi ko? Hmmmm”
Ta karasa tana murmushin gefen baki. Jarma ma murmushin yake yana kallonta zuciyarsa na saka masa burinsa.
‘Za mu kawar da Shattima da Mai Martaba, amman dan ki ba zai yi milkim garin nan ba, indai ina raye’
A zahiri kuma sai ya gyara babbar rigarsa ya ce.
“Da sannu komai zai wuce Hajiya, kuma kar Salim ya fasa neman Nana”
Sai a lokacin Hajiya ta dawo da kallonta a gurinsa.
“Ai dole ya neme ta, tun da har Mai Martaba ya sallama masa babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu, dole ne Ammy da zuri'ar ta su dawo karkashin kulawata, duk abun da tai min a shekarun baya sai na maimaita mata shi”
Ta karasa zancen fuskarta na sauyawa alamar bata son tuna bayan.
“Komai zai wuce Hajiya komai zai zama tarihi da yardar Allah”
Ya daga masa kai tana sauke wani dogon numfashi.
“Haka ne, tashi ka je kar a fara yi mana zargi”
“Zargi kuma na nawa? Sai dai kar a koma”
Ya fada yana mikewa tsaye da murmushi a fuskarsa, sannan ya dan risina mata.
“Na bar ki lafiya”
Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta mike tsaye ta nufi gaban drawer ta dauki wayarta ta aikawa Hajiya Talatu kira bugu daya ta daga tana jerowa Hajiya Balki wani irin kirari da ke kasa kan Hajiya fashewa.
“An gaishe da Talatu Uwargidan Waziri”
Talatu ta risina kamar Hajiyar ce a gabanta.
“Allah ya kara miki lafiya da imani, Surukar Ammy kuma Uwar Sarkin gobe, a ganki a bar ki kuma a bi ki a dole”
Hajiya Bilki ta yi wani irin kasaitaccen murmushi.
“Yanzu Jarma ya fita daga nan”
“Tsohon makiri, Allah yasa dai ba ki masa zan ce na ba, domin tsab zai labartawa Waziri komai ya kashe mim aure a asirance”
“Taya za ayi na bar shi ya san shirin mu Talatu? Bayan na san shi akwai kwadayin masarautar nan a ransa? Ubansa daya fa da Mai Martaba kuma babu yadda be yi ba Mai Taba ya bashi Babbar masauta ya ki, yanzu kuma kike tunanin baya sha'awar wannan?”
Hajiya ta dan yi jimm tana murmushi mai sauti
“Mu dai gama da bangaren sauran ne sannan mu dawo kansa, na kira ki na ji yadda ake ciki”
“Zan shigo da kaina ranki ya dade, domin maganar ba ta waya ba ce”
“Ina jiranki”
“To ranki ya dade”
Daga haka ta aje wayar ta juya ta fice daga dakin, kofar dakin bata kara idam an bude ko an rufe gashi akwai yar tazara sosai tsakanin dakunan da inda aka jera kujerun falon, hakan ne yasa Sirleem be ji motsin mahaifiyar tasa take tsaye a bayansa tana kallon Mansura wace ke a fuskar Laptop dinsa yana video chat da ita ba. Har sai da ya ga Mansurar ta kasa karasa maganar da take tana kallon gafensa, sannan ya juya sai yai arba da mahaifiyarsa. Da sauri na rufe laptop din.
“Hajiya Barka da fitowa”
“Ban maka iyaka da yarinyar nan ba?”
Ya sinne kai kasa, ya kasa cewa komai gabansa sai bugawa yake da karfi. Wata irin tsawa ta daka masa rai bace
“Waye miye hadin Bayarabiya da bafullatani ne Sirleem? Me ta baka ka sha da baka iya rabuwa da ita? Ni uwarka ban isa na ce ka fita hanyar Mansura ka fita ba? Me yake damunka ne?”
Dagowa yai ya kalleta cike da ladabi ya ce.
“Hajiya ba fa cewa nai zan auri Mansura ba, Mansura kawata ce kawai, i think Nana kike so na aura ai”
“Yes wannan kuma dole ne, auren Nana ya zame maka wajibi matukar ina raye, yaushe rabon da ka je ka dauki Nana ku fita ko na kira a waya? Amman ka zauna kana video call da wata yar iskar yarinya marar tarbiya, kuma a cikin falona”
Cikin wata kalar murya dake nuna bacin ranta ta karashe maganar tana nuna shi da yatsanta da ke rawa kamar zata doke shi.
“I'm sorry”
Shine abunda ya fada ya mike tsaye ya dauki system dinsa ya fice daga falon. Zaunawa tai saman kujerar tana kokarin daidaita fushinta.
AMMY POV.
Bayan Waziri ya gama zayyana mata komai, sai ta amsa masa da.
“Okay babu wata matsalar zan saka Shattima ko Jarma ya wakilce shi tun da kai ba zaka samu zuwa ba”
“Jarman ma yafi dacewa tun da shine Dattijo kuma kin ga abu ne na manyan mutane”
“To sai a yi ma Jarma magana da wuri ya shirya komai kamin lokacin”
“Zan sanar da shi”
Waziri ya fada yana karantar yanayin matar dan'uwan nasa. Har ya mike tsaye da zimmar yai mata sallama ya fice sai kuma ya koma ya zauna ya kalleta.
“Hajiya ko dai akwai wata matsalar ne?”
Ammy ta sauke ajiyar zuciya, daga inda take zaune ta saka hannunta na dama ta rike kanta, a take idonta ya cika da hawaye abun ka da mai neman kuka an fada masa mutuwa.
“Ina cikin damuwa Waziri, na rasa da wanne zan ji, matsalar Nana ko ta Mai Martaba ko kuma ta maganganun da suke tasowa a masautar nan?”
“Matsalar Mai Martaba tana damun kowa, addu'a yake bukata da kuma kulawa, gulma kuma ta daina damunki daman duk daukaka ta gaji haka, za ka samu akwai hassada da kiyayya da kananan maganganu, sai dai Nana nake son na ji abunda ya same ta?”
“Abubuwan da take min bana jindadinsu, tun jiya take damuna da zancen sai an canja mata driver yau da safe har tsawa ta daka min akan haka, taya yarinyar da ke neman albarka za ta yi ma mahaifiyarta haka? Yanzu kuma na duba drawer dubu dari uku da saba'in na aje a ciki yanzu na duba na ga babu kudin sai dubu talatin da biyu suka rage, abubuwan da Nana take suna tsorata, kuma suna damuna, ba a nan kadai ba Nana ko dakin Mai Martaba ta shiga indai idonta ya ga kudi sai ta saka yadda tai ta dauke su, ina tsoron kar wannan abun ya zame mata hali, ga shi bata da natsuwa duk wani abu na masu hankali Nana ba ta yinsa....”
Ta karasa hawaye na sauko mata, ba dan komai ta tsaya ta fada ma Waziri damuwarta akan Nana ba sai dan sanin shi ne kadai mutumen da zai tsawatarwa Nana ta ji kuma shine mutumen da idan ta fada masa damuwarta ko damuwar Masarautar nan yake fadi tashin ganin ya same mata mafita.
Waziri ya kankance ido irin na su na manya yana mamaki.
“Me take yi da kudin da take dauka?”
“Wallahi ban sani ba, amman kai kanka kasan babu abunda Nana ta nema ta rasa”
“Zan daukar mata mataki kuwa, amman duk da haka ki rika gamawa da addu'a ta tsari da kuma ta shiriya”
Sosai Ammy ta jidadin maganar Waziri domin tana ji a ranta kamar ba zata iya da Nana ita kadai ba. Har ta bude baki ta yi magana sai ta Yusra ta shigo dakin da gudu har tana haki.
“Ammy Nana ta fadi ta ji ciwo gata can an kawo ta....”
Tun kan ta karasa Ammy ta mike tsaye hankalinta a tashe ita da Waziri suka fita daga dakin. A kwance suka samu Nana saman gadonta an saka mata bandeji a kanta da kafarta da hannu, Shattima na tsaye tare da Hajiya Karama, Driver ba kuma yana daga bayansu jikinsa sai rawa yake. Da sauri Ammy ta zauna saman gadon ta taba jikinta.
“Me ya same ki Nana?”
Ta kalli Shattima da Hajiya Karama, sannan ta kalli Ammy, ko da wasa bata kalli Waziri ba domin yadda take tsoronsa ko mutuwarta albarka.
“Mai Babur ya kade ni, na fito daga school ina jiran Driver ya zo ya dauke ni be zo ba har babur ya kade ni, sai wani ya kai ni asibiti aka saka min wannan shi ne ya kawo ni nan ma da motarsa”
Nana na fadar hakan driver ya risina kasa yana rokon Ammy.
“Hajiya dan Allah dan Annabi amin afuwa, uzuri ne ya rike ni shiyasa ban samu isa da wuri ba”
Ammy bata ce komai ba sai duba jikin yarta take cike da damuwa.
“You fired, saboda ita aka dauke ka aiki, then why all this? Har mai babur ya kade ta ta ji ciwo wani dabam ya kawo ta gida”
Zainab ta fadawa driver, a take ya fara magiya yana kallon Ammy.
“An kore ka aka ce fita ka bar dakin nan”
Ganin Ammy za ta yi magana yasa Shattima ya nanata masa abunda Zainab ta fada domin abunda yake da niyar yi kenan, cikin rashin dadin rai driver ya fice daga dakin fuskarsa kamar zai fashe da kuka.
“Me kike son ki ci? I will cook for you”
Ammy ta tambaye ta cike da kulawa, sai Nana ta kawardar fuska ita aka dole har yanzu fushi take da Ammy.
“Bana son komai”
Ammy ta hade abu da karfi sannan ta mike tsaye ta nufi kofar fita sai kuma ta juyo ta kalleta fuskarta da mamaki.
“Amman ya akao kika fito ba lokacin tashi daga school ba? Ya akai suka bar ki kika fito? Yanzu fa karfe 11:40am how?”
Shattima ya kalleta.
“Ammy za mu yi wannan maganar daga baya yanzu dai ta samu lafiya”
Ammy bata sake cewa komai ba ta juya ta fice. Sai a lokacin ne Waziri yai magana.
“An kori direban ko? To kin samu abunda kike so idan ma ke kika tsara haka saboda a kore shi burinki ya cika, amman bari na fada miki daga yau school bus ce zata rika kai ki makaranta tana dauko ki, ba ki wayar ki”
Ya mika mata hannunsa sai tai saurin kallon Shattima tana son saka kuka, kai ya gyada mata alamar ta ba shi din, sannan ta kai hannu ta bude school bag dinta ta dauko wayar ta mika masa tana hawaye. Shattima ya zauna kusa da ita kenan Waziri ya ce.
“Daga yau kar wanda ya sake daukar kudi ya bata ko ya siya mata waya, daga kai har Zainab shi ma Sirleem zan masa magana”
Da mamaki Zainab ta kalleshi sai dai babu damar tambayarsa dalilin hakan dan ta fi kowa sanin waye Waziri.
“Zainab je ki kira Baaba ta zo ta bincike dakin nan duk inda kudi suke ta fito min da su, kuma ta kwashe kayan kallon nan da system din nan bana son ganinsu a nan”
Ta amsa masa ta to, sai da ta kalli Shattima sannan ta fice zuciyarta cike da tambayoyi. Waziri ya kalli Nana.
“Da kin ji sauki ke za ki fara gyara dakinki da kanki, ba za a sake miki ba, ko tufafin da ke saka miki a wardrobe daga yau ke zaki saka idan sun yi datti ki wanke da kanki”
Ta kankame Shattima tana fashewa da kuka.
“Wayyo Yaya mutuwa zan yi”
“Kin dade baki mutu ba”
Waziri ya daka mata tsawa yana matsowa kamar zai doke ta, da sauri Shattima ya mike tsaye ya tare ta.
“Ayi hakuri Baba zan mata magana”
Shi kan shi Shattima sai da Waziri ya watsa masa harara sannan ya fice daga dakin, wanda hakan yayi daidai da shigowar Baaba, a take ta hau aikinta sai da ta bincike dakin tsab ta fiddo kudi ba kanana ba har da dollars din da Nana take daukowa dakin Mai Martaba ta fito falo ta kawowa Waziri sannan ta kira Sarkin Dogarai ya cire tv da decoder da system din dake dakin. Nana na ji na gani aka kwashe kayan aka bar mata daki wayan daga gadonta sai wardrobe da dan karamin dinning dinta na karatu domin har hotunan artists da saka sai da Waziri ya saka aka cire su a lokacin da ya sake dawowa dakin dan ganin idan an yi yadda ya ce.
“Yaya Wallahi Baba Waziri da Ammy basa so na”
“Shiiiiiiiiii kar na sake jin wannan kwanta ki yi bachi idan kin tashi zan kira Doc Deen ya duba ki Okay”
Ya daga masa kai sannan ya mike tsaye ya fice daga dakin. Tai saman gadon ta fara kuka na gasken gaske tana jin kewar mhaifinta domin ta tabbatar da yana raye babu wanda ya isa ya mata haka har shi Baba Wazirin da kansa. Can kuma ta fara murmushi mai sauti tunawa da yadda AA ya rude a lokacin da suka fadi din, sai a lokacin ta soma dariyar abunda ya faru tsakaninsu tun haduwar farko har zuwa yau.
FALMATA POV.
Cikin rashin jindadin ta isa gida tana jin ina ma ace tana da wata dama da zata hana kanta aiki a gidan da ta huta, domin abunda Zainab tai mata a yau be mata dadi ba ga Iya data saka ta gaba ga wahalar tafiya kasa kullum kuma ta dawo.
Sai dai babu yadda ta iya idan tace zata bar aikin ta san sakamakonta a gurin Umma wacce tai ruwa da tsaki ta sama mata aikin saboda ta rika bata albashin. Kamin ta isa gidan sai da ta biya ta gidansu kawarta Khadija ta su kai yar fira har ma ta kunan wakar Sirleem M2 a wayar Khadija ta kalli video wakar sannan ta wuce gida. Tana isa bata ko tsaya hutawa ba, ta dauki bokitin diban ruwa ta nufi bohol daman diban ruwa ne abu na farko da take idan ta dawo daga aikin, sannan tai surfe.
Haka ta cika komai na gidan sannan ta zuba