Showing 159001 words to 162000 words out of 273152 words
Chapter 54 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
gama zana yadda abun ya faru Shattima be ji komai ba hankalinsa yana kam waya, sai bayan kamar minti uku ya dago ya sake kallonta.
“Ban ji ba”
Haka ta sake karanta masa abun da ya faru kamar dazun. Aje wayar yai yana nazari, mi zai saka Jurry tai haka? Saboda ta batawa Ammy suna cewa mai aikinta tana saka ko kuma saboda wani abun dabam.
“Kin taba shiga bangaren ne kamin nan?”
“Aa”
“Then what happen da Sirleem ya dauke ki ina ya kai ki?”
Tsoro ne ya ziyarce ta, wata kila idan ta fadi gaskiya zai jefa Sirleem din a matsala hakan yasa ta zabi yin karya.
“Gida ya kai ni”
Hannunsa ya kai ya bude gurin da yake ajiyar kudi ya dauko bandir din 500 ya mika mata.
“Gashi hakkin aikin da kika yi, and idan kina ra'ayi cigaba da aiki a nan ki fadawa wani sai a sanar da ni”
Ta saka hannu biyu ta karba.
“Na gode Allah ya saka da alheri, ya baka wasu yayan masu albarka, su kuma Allah yasa masu ceto ne”
“Ameen”
Ya amsa yana kallonta, sai ta mike tsaye ta fara tafiya da dingishi, binta yai da kallo kamin ya maida dubansa gurin Nana data doso inda yake da saurinta tana sanye da Hijabinta na islamiya.
“Har kun ta so?”
“Yeah yau wa'azi ake mana yau laraba ba a dadewa”
“Zagoyo ta nan”
Ya fada yana rufe gilashin motar, sai ta zagaya ta dayan side din ta bude motar ta shiga ta zauna ba tare data rufe ba.
“Ya dan Allah karka yi bushi da ni idan na fada maka gaskiya”
Ya tattara dukan hankalinsa ya maida a gurinta.
“Ina jinki”
Cikin kunya da badama ta labarta masa abun da ya faru, na satar da tai da kuma barazanar da tai ma Hajiya har da abun da ta ji Hajiya Babba ta fada. Ba karamin mamaki ne ya kama Shattima ba, baya son ya munanawa Hajiya zato duk da ya san basa jituwa da mahaifiyarsa sai dai shi yana daukar hakan ne a matsayin kishi kasancewarsu mata, amman be yi tunanin fitowar lafazi irin wannan a bakinta ba.
“Ammy ta ji wannan?”
“Bata saurare ni ba, tana fushi da ni saboda abun da na aikata sai da aka yi rasuwar nan ne ta sauko”
Shattima ya sauke ajiyar zuciya.
“Shikenan, karki fadawa kowa wannan maganar ko da Mai Martaba ne, zaki tada masa hankali ne kawai, kuma dan Allah karki sake aikata abu makamancin wannan”
“To Ya Shattima, daman Sardauna yace na yi masa alkawarin ba zan sake aikata ba, kuma zan rika zuwa makaranta kullum zan zama yarinyar kirki, kuma duk na masa yace ma na daina zuwa bangaren Hajiya kuma ko ta bani abu na daina karba, yace wai ita ba son gaskiya take min ba Ammy ce take so na, tun ranar ban sake zuwa bangarenta ba ma, kuma ina zuwa school both islamiya da boko, ko bana jindadi ina daurewa haka nan saboda na cika alkawarinsa”
Maganar take idonta na cika da kwalla, Shattima kam kallonta kawai yake yana karantar abun da ita kanta bata san tana tare da shi ba.
“Ya dan Allah kai wani abu ya dawo I miss him, kuma yana da kirki sosai”
Shattima yayi murmushi.
“That's good gashi ya sa kin fara natsuwa ai”
Ta yi murmushi domin be fadi karya ba ita kanta ta san ta canja cikin yan kwanakin nan.
“My little girl, ya kamata a saka masa da abun da yai miki daman ai”
“Eh yaya dan Allah kaje gidan kai magana da yayarsa sai ta bar shi ya dawo aikin nan”
“Aa zamu dai saka a nemota ba zamu je ba kam, zamu saka a nemosa dai”
“No Yaya he's important to me kuma yayar shi ba, amman idan ta ga ka tafi zata bari maybe”
“Waye za a cewa Yarima yana nemansa yace ba zai zo duk garin nan? Wa zan yi ma magana yace min ba zai yi ba? Ko ke aka ce kina kiransu dole ta zo, kuma idan kika fada dole ta ji, kira daga masarauta ba kira daga makota ba ne, ke kanki da ace kin natsu kamar sauran yayanki da bata isa ta musa miki ba”
“Amman yaya ba komai ne Zaka ce sai an zo maka ba, sometimes you need to go, musamman idan abun yana da muhimmanci a gareka”
Ya dan yi shiru yana kallonta.
“You're right, zan sam abun yi”
“Yaushe? Anjima?”
Ya busar da iskar bakinsa daman ya san halin Nana akwai zakuwa.
“Tomorrow Morning”
“Okay thank Youu”
Ya daga mata kai yana murmushi sai ta juya ta fita cike da jindadi zuciyarta har wani zillo take tsabar murna da jindadi kamar ance mata Sardaunan ya dawo gidan ma gaba daya.
Sai da Shattima yai ribas sannan juya kan motar zuwa gate, a hankali yake driving din har ya fice daga gate din suna daga mishi hannu. Da hannu daya yake driving dayan hannun kuma yana rike da wayar da yake ta amsa sakonnin gaisuwar da ake masa, domin ko an kirashi a waya sai ya dama yake dagawa, daman can baya son yawan magana, balle kuma yanzu da yake jin komai ya masa nauyi, hakan yasa most of his friends musamman wandanda suka san halinsa da kuma wadanda suke nesa suke aike masa gaisuwar ta chat. Maganar da Nana tai ne yasa shi daukar hanyar da zata kai shi million quarter's, ba kamar yadda yai niyar aika mata da sakon kira ba ta waya, sai dai a yanzu ya zabi ruwa ba dan yayi niyar hakan ba sai dan abun da Nana ta fada cewar sometimes you need to go... Daman kuma hanyar gidansa ne da yake son tafiya a yanzu. Gaban gate din ya tsaya da motarsa ya danna horn, daman ya san gidan tun a lokacin data siya, shi ne mutum na farko data fara fadawa kuma ta dauko masa hoton gidan da komai, kamin ta takurashi yaje ganin gidan a lokacin da aka gama gyara. Mai gadin ya leko ganin mota yasa ya fara zuwa gurin motar ya ga ko waye kamin ya bude, sai dai bakin gilashi ne, kamar yadda motar take baka, isowa yai gurin motar a zatonsa ganinsa zai saka mutumen dake cikin motar ya sauke gilashi, amman sai ya ga tsabanin haka, hannunsa ya kai ya kwankwasa gilashin, domin aikinsa sanin wanda ya shiga da kuma wanda ya fita a gidan a matsayinsa na Mai Gadi. Anan ma Shiru Shattima be sauke gilashin motar ba, ko dagowa be yi ya kalleshi ba, sai amsa sakonninsa yake, hakan yasa Mai gadin ya juya ya koma cikin gidan dan sanarwa masu gida.
FADIME POV.
Gajiya da tai da zaman dakin yasa ta mike tsaye ta fara lalaben hanyar fitowa zuwa falo. Ta fara sabawa da yanayin gidan, domin ta san inda bandaki yake ta san yadda zatai ta fita daga dakin ko kuma ta shiga, ta kuma san ta inda zata bi ta fita kofar falon, sai dai ta saka saboda da mutanen gidan, ta ki ta saki jiki da su, babu ranar da bata kuka. Tun da Wasim yasa kafa ya tafi Zainab bata sake kula Fadime ba duk kuwa da kasancewar ya fada mata ta kular masa da ita, bata mata komai sai kyara, idan ta zauna a kujera zata ce mata ta sauka kasa, bata taba saka hannu ta rikata da sunan kaita bandaki ba ko kuma dakin da take kwana wanda babu komai a ciki sai tile, balle har ta dauko abinci ta bata, kwata kwata Fadime bata kwanta mata ba, jininta be gadu da nata ba. Abinci sai dai Iya ta bata, bandakin ma Iya ce ta nuna mata inda yake haka ma dakin da take kwana duk aikin Iya ne, ita kuma tana yi ne saboda Wasim, kwana ukun da sukai suna zuwa gaisuwar Labib kullum a gidan take wuni ita kadai da yunwa, har sai sun dawo sannan Iya ta dafa wani abu su ci har ita.
Da lalabe ta fito falon har ta karaso inda kujerun suke ta lalaba karamar kujerar ta zauna, Zainab dake kwance a doguwar kujera rike da waya, ta cire Bluetooth din da yake dayan kunnenta tana shan waka tare da dakawa Fadime tsawa.
“Wai ke wace irin marar jin magana ce, bana fada miki ki rika zama a kasa ba? Tun da kika zo gidan nan baki yi wanka ba, kin bi sai lashe kujeru kike”
Fadime ta sauka da sauri ta zauna a kasa, idonta na cika da hawaye, ita dai bata sam Zainab ba bata taba ganinta amman ta fahimci ta tsaneta tun da ta zo gidan, bata mata komai sai kyara.
“Yunwa na ke ji, tun abincin safe ban sake cin komai ba”
“To ba a dora girki ba, ki ci wuta, ke dai kin cika damuwar mutane Wallahi Mtchssssssss”
“Yi hakuri”
Fadime ta bata hakuri a sanyaye, sai ta sake jan tsaki, ba tsanar Fadime ne kawai a ranta ba, har da gaskiyar data gano ta ita, duk da kasancewar har yau ba ta yi ma Iya maganar ba, abun ka da rashin kunya irin ta maye ita ma Iya bata ce mata komai ba, kuma ta wanyance sai harkokinta take, Zainab tana kara jin haushin Fadime ne saboda a ganinta da ace bata zo gidan ba, da yanzu bata ji mummunan labari ba akan mahaifiyarta, domin a yanzu ta rasa ta wace hanyar zata zauna da ita, gashi ta kasa samu natsuwa da iya duk dai ita dai bata san abun da ake nufi da maita ba, sai dai ta san ba abu ne mai kyau ba, kuma ta san tsafi ne. Sai dai abun da ya tsaya mata a rai kuma ta kasa tambayar Iya shine dalilin Iya na daukar maitar, da kuma boye mata asalinta na gaskiya.
Bayan yunwa har da kishin ruwa Fadime tana ji sai dai jin alamar Zainab ce kadai a falon ta san ko ta fada ba zata bata ruwan ba, hakan yasa ta mike tsaye ta fara lalaben hawaye na bin fuskarta ta koma dakin, da lalabe ta shiga bandakin ta duka kasa tana lalaben buta dayar data fara dauka bata da ruwa, dayar ce da ruwa sai ta dauko mai ruwan ta kafa bakinta a kai ta sha mai yawa sannan ta aje, ta juyo ta fito.
Tashin Fadime yai daidai ta kwankwasa kofar falon da Mai gadin yai.
“Shigo”
Zainab ta fada daga kwancen da take, sai ya turo kofar ya shigo cikin girmamawa da taka tsantsan irin na bawan gidan da ubangidansa.
“Hajiya Wani ne ya zo da mota a waje yayi horn sau daya, sai na leka na ga motar da bakin gilashi na leka na ga ko waye be sauke gilashin motar ba, har kwankwasa masa na yi be bude ba”
Ya dago.
“Wace kalar mota ce?”
“Baka ce, Mai bakin gilashi”
Tana jin hakan ta gane Shattima ne domin shi kadai zai zo da mota a gate din gidan kowa yai wannan abun, ta san kuma a cikin motoci black ita ce fav dinsa, domin most of him cars duk black color ne sai dai designs da price ya banbanta.
“Bude masa gate da sauri Shattima ne”
“To ranki ya dade”
Ya juya da sauri ya fita jiki na rawa, ita kuma ta mike tsaye da sauri ta nufo kofar falon. Ko da ta fito Mai gadin ya bude masa gate din shi kuma ya kunno kai cikin gidan, a daidai inda take tsaye ya faka motarsa sai da yai minti biyar a cikin motar doing nothing sannan ya bude ya fito, tana ganinshi ta saki murmushi.
“Sannu da zuwa”
Be amsa ba har sai da ya rufe motar sannan ya nufi entrance din yana wata irin tafiyar kasaita da be san ma yanayi ba, biyo tai a baya har sai da ya shiga cikin falon yai makansa mazauni sannan ta zauna tana facing dinsa. Tana ganin yadda yai ignoring dinta ta san ta masa laifi ne. Yana zaune a gurin rike da wayarsa Fadime ta fito tana lalabe, da gangan yaki dago kansa duk da be san ko waye ba har sai dai tai kokarin zuwa kusa da kujerar da yake zaune.
“Wai ke miyasa baki da hankali ne? Ba zaki zauna a daki ki natsu ki zauna a daki ba sai kin rika saka mutane magana, ko kujerar nan kika taba sai na ci ubanki...”
Fadime ta tsaya cak.
“Yi hakuri dan Allah”
Ta furta tana jin wani irin rashin galihu da tausayin kanta, domin ta kai yau har ta zagi ubanta. Dagowa Shattima yai ya kalli wanda ake zagin sai yai arba da abun da be zata ba, mutuwar zaune yai yana kallon Fadime da tsananin mamaki marar misaltuwa, mamakin da be san yadda zai misaltashi ba, sai dai hakan be saka shi nuna ya santa ba.
“Who's this?”
Ya tambaya yana kallon Fadime data juya ta fara tafiya da zimmar komawa cikin dakin.
“Fadime ta zo zama ne kawai na kwana biyu”
“Zo ki zauna”
Ya fada still yana mamakin da be yarda ya bayyana a fuskarsa ba. Abun ka da mai nema sai ta juyo da sauri daman zaman dakin ya isheta saboda kadaici, sai dai taba zo ta zauna din ba sai ta tsaya.
“Tace na zo?”
Fadime tayi abun da yafi komai batawa Shattima rai, ya baka umarni kace sai ka jira umarnin na kasa da shi.
“Ni nace ki zo ki zauna?”
Ya fada calmly, hakan yasa Fadime ta kara takawa tana lalaben, ko bata umarni ba ta san wanda yai maganar ya isa da ita tun da har ya furta a gabanta. Sai da ta iso kusa da shi har yana jin kamshin turarensa daya cika falon ta lalaba kasa ta zata zauna.
“Zauna kam kujera”
“Tace na zauna hawa kan kujerarta fada take”
Ta zauna kasa tana jin kamar ta taba jin kalar kamshin turaren da muryar amman a ina? Zainab ta mike tsaye ta nufi kicin dan dauko masa lemu duk da ta san ba sha zai yi ba. Tashinta ya bawa Shattima damar tambayar Fadime.
“Yaushe kika zo nan?”
“Wanene kai?”
Ta kai hannu tana lalaben inda take jin muryarsa na fitowa. Sai ya kai bakinsa saitin kunnenta.
“Kin san mutumen daya kadeki da mota kika ce ya siya miki kaza da yogurt?”
Fadime ta zare ido kamar tana ganinsa tare da bude baki.
“Kai ne?”
“Eh”
Ya amsa mata yana murmushi kamar tana ganinsa.
“Kai kadai ne?”
“Eh ta shiga kicin”
Ta yi saurin riko kafarsa.
“Dan Allah ka taimaka ka kai ni wannan tashar sai ka saka ni motar garinmu, bana jin dadin zama nan, dakin ba komai haka nake kwanciya, kuma basu bani abinci sai na ji yunwa sosai yanzu ma yunwa nake ji, kuma kyamata suke yi ita wannan sai ta tai min fada ko ban mata komai ba, kuma tun da na zo ban yi wanka ba, bani da wasu tufafin canjawa kuma...”
Sai ta rage murya ta dogo kasa kasa kamar an fada mata Zainab ta fito daga kicin din da doso inda suke rike da lemu.
“Kuma tsohuwar gidan Mayya ce, wai ta cinye matan wani mutum kuma yanzu yayansa ta cinye wai shi take bibiya, kuma ina ganin ita ma yarta tana yi, dan Allah ka dauke ni kar su cinye min kurwa, bana son na mutu yanzu ka taimaka min ka ji”
Babu abun da Zainab bata ji ba, har wani dauke numfashi tai saboda kunya da rikicewa a lokaci daya, sai ta rasa me zata ce, domin a tunanin Fadime karya tai na fadar ta cinye matam wani mutum kuma yanzu ta cinye yayansa saboda ba a gabanta Iya ta fadawa Wasim hakan ba. Shattima kuma be ce uffan ba ganin Zainab din, hakan kuma sai ya bawa Fadime damar cigaba, domin ba ta yi tunanin Zainab ta dawo falon ba, hankalinta be bata ta saurara ta ji takun tafiyarta ba.
“Ko Wasim daya kawo ni cewa yai gata nan idan kin ga dama ki cinye idan kin ga dama ki aje, kaga kenan mayya ce ko? Dan Allah ka dora mu a hanyar garinmu kaji?”
Still Shattima be ce mata komai ba, sai hannu yai wa Zainab alamar ta zuba lemun data aje, ta mike tsaye tana jin jikinta kamar ba nata ba tsabar kunya kanta yayi mata kato ji take kamar kasa ta bude ta shige ciki. Ta duka ta zuba lemun a zaton Fadime shi ne yake zuba lemun, sai ta zuba ta koma ta zauna sai Shattima ya dauki lemun da kansa ya kama hannun Fadime ya saka mata glass cup din.
“Sha lemu”
Ba karamin mamaki Zainab tai ba, sai dai ta alakanta hakan ta tausayin Fadime, domin bata sa ran ya santa. Sai da Fadime ta sha five alive ta ji sanyi har cikin kai da ruhu ta fara masa addu'a, murya kasa kasa gudun kar Zainab dake kicin ta ji ta
“Na gode Allah ya saka maka da alheri, ya rabaka da iyayenka lafiya, kuma Allah ya tsare ka daga sherin mayu, da zuwa garin su Wasim, duk wata bakar mata ce ta jamin min, ta zo daga can wani gari can nesa wai yola tasa na rakata a can garin, gashi nan ta tafi ta bar ni da bala'i, gashi nn na makance kuma an kawo ni gurin su mayu, Allah ya isa, da wani jikinta kamar yar tsana, wai hoto zata dauka, muguwa banzar Allah ya isa...”
Ta karasa da kuka. Zainab ta hade wani numfashi da karfi tsabar bakinciki yasa shi kin wucewa har sai da ya dawo mata ta fitar da shi, mikewa tai tsaye da zimmar marin Fadime sai Shattima ya watsa mata wani mugun kallo, na me zaki yi? Hakan yasa tai tsaye cak tana hucin da bata san ta ina yake zuwa mata ba.
“That's mean ke ce dalilin makantarta, and you're treated her badly”
“No ba ni ce silar makantarta ba she's lie, bata da hankali wannan yarinyar kuma kanta rawa yake”
Zainab ta fada tana kokarin kare kanta, uffan Shattima be sake ce mata ba, irin yadda yake kallonta kadai ya isa ya sanar da ita irin bacin ran dake cikin idonsa, and the second thing he hate is argue, ta kuma san haka.
“Ka yi hakuri ka gafarce”
Ta furta cikin muryar dake nuna tana daf fa fashewa da kuka, domin numfashinta har wani sama yake yana kasa. Fadime na jin hakan ta aje kofin lemu ta kama kafar Shattima ta rike gam.
“Dan Allah dan Annabi karka bar ni nan, yauna shiga uku na, Wallahi yau farfesuna za