Showing 258001 words to 261000 words out of 273152 words

Chapter 87 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72753

kina fadin ayi miki da hausa, arrrr Fulani da abun kunya”


“Eh na ji, fada min wacece Shattima zai aura?”


“Ke ce mana, ba shiyasa za a tafi dake jibi ba”


“Ya za'ayi na yarda?”


“Na taba miki karyar?”


“Aa”


Ta girgiza kai. Inna ta soma bata labarin tun a lokacin da Mai Martaba ya nada wasu mutanen ciki har da Waziri suka zo neman aurenta cikin sirri ba tare da duniya ta sani ba, kuma Bappa ya sallama musu ba tare da ya nemi izininta ba, akai komai a sirrance domin su a can basa son a bayyana Bappa ma a nan baya son a bayyana hakan yasa babu wanda ya sani sai yan'uwansa. Inna ta yi zaton Fadime zata tashi ta fara rawa ne tana murna saboda jindadi, amman sai ta ga akasin haka a gurin yarta, wai yau Fadime ce ta saka hannu ta rufe fuskarta da sunan kunya.


“Wallahi Inna kunya na ke ji”


Ta fada wani kalar dadi na rufeta, Inna dai ta yi dariya tana girgiza kai


“Ashe kina da kunya”


Fadime ta tashi ta bar gurin da gudunta, ba Inna kadai ba har Bappa sai Fadime ta koma tana jin kunyarsa, fadar irin murna da dadin da take ji za'a mata aure kan har ba ya misaltuwa, tun ranar ta fara ayyana irin yadda za a rika bata girma idan ta auri Shattima, ta dayan bangaren kuma tana misalta yadda za ta yi girki.


“Da safe in ce masa ina kwana”


Ta yi dariya tare da rufe ido duk kuwa da kasancewar ita kadaice a sabon dakin na Inna.


“Da rana na dafa masa taliya ko shimkafa da miya ko wani abun na kawo masa lemu da ruwa, na ce sannu da zuwa”


Ta yi wani murmushin jindadi, sai kuma ta mike tsaye tana gyara sabon gadon Inna na masu karamin karfi.


“Kullum na gyara gadona na yi shara na goge komai, idan ya dawo na ce sannu da zuwa, da dare na hau gadona na kwanta shi kuma na shimfida masa bargo,.... Aa be dace ya kwanta kasa ba, sai dai ya kwanta a gado ni sai na shimfida bargo na kwanta a kasa”


Ta rumgume hannayenta tana jin kamar ga nan ma dakin mijin, ko dan damuwar da mata suke idan za su tafi su bar iyeyensu Fadime bata yi.


“Ita kuma Ammy kullum zan gaishe ta na duka mata har kasa, ko Nana da take kanwarsa duka mata zan yi ai ance ayi ladabi da biyayya...”


Haka tai ta surutunta tana misaltar yadda za ta yi idan anyi auren, tun daga ranar bata sake gaishe da Inna a tsaye ba sai dai ta duka har kasa haka ma Bappa, kuma bata yarda ta hada ido da su domin indai kunya ce tana jin kunyarsu a yanzu kam. Ana gobe za ayi tafi Inna tace ta je tai ma kawayenta bankwana amman kar ta fada musu komai, haka Fadime taje tai musu bankwana da sunan zata tafi Yola bikin Shattima, a kasan ranta sai fadar take wai sai dai kawai su ji ta auri dan sarki. Inna Uwani da Inna Dije a gidan suka kwana domin Ra'ees ya fadawa Bappa cewar da sassafe zai zo ya dauke su.
Cikin daren Inna ta ja Fadime gafe tana mata nasihar da ta saba mata tun a lokacin da aka saka mata rana, cewar ta natsu ta daina abubuwan da take, kuma ta rike addu'a ban da raina mutane surutun nan da take kamar an bude redio.


“Kina gani dai Allah ne ya kai ki wannan matsayin ba dan kin isa ba, kuma duk wanda yake cikin gidan sarauta zaki ganshia natse, ba kamar ke ba, kina musu hauka za su koroki ki dawo ruga”


“Aa duk watsar da komai zan yi, ba zan yi komai ba na natsu zan yi biyayya”


Fada sosai Inna tai mata irin na ya da uwa, sannan ta motsa mata fura ta bata ta sha, Fadime ta je ta kwanta babu komai a ranta zai zumudi kamar wanda aka cewa ana zuwa za a daura mata auren, mafarki babu kalar wanda ba tai ba. Washe gari sun da asubar fari Inna ta shirya musu abun karyawa tana ta tunanin Fadime a ranta irin kewar da zata yi amman Fadime hankalin baya kan Inna, Bappa ma sai da yai mata nasa fadan ya ja mata kunne sosai sannan yai mata albishir da gafararsa na abubuwan da tai ta masa na bacin rai. Misalin 8am Ra'ees ya iso ya daukesu zuwa Katsina sannan su wuce airport, Inna da Bappa suka tsaya suna ta kallon motar har sai da suka daina hangota sannan Inna ta share hawayen idonta ta koma cikin gida tana jin kamar ta fashe da kuka, zuciyarta ta cika.


SHATTIMA POV.


“Amaryarka ta iso”


Ammy ta fada da murmushi a fuskarta, Shattima ya aje cup din hannunsa yana murmushin jin kunya


“Ammy har da ke?”


“Ramawa na yi, ni ma dazun Mai Martaba yake zolaya ta wai ana masa kuri za'ayi sabuwar in-law, na ce masa lallai kam wannan Amaryar ta fi saura domin ina son yarinyar sosai da sosai Wallahi ta kwanta min rai kuma ta mana komaia rayuwa”


Shattima ya fadada murmushi yana shafa kansa.


“Mai Martaba dai lafiya ta samu”


“Wallahi yanzu kam Alhamdulillah sai dan abu ba a rasa ba, gashi har yana fita abu kamar wasa”


“Daman ai komai yai farko yana da karshe, sai a cigaba da addu'a”


“Haka ne kam, addu'a kuma ai ta zama dole, daman can Mai Martaba baya wasa da addu'a ni ma kuma ina masa, ai da baya addu'a da abun be zo a haka ba, kasan wani lokacin ko da addu'a abubuwan su kan samu bawa saboda an rubuto masa hakan sun kafi na haife shi”


“Haka ne Allah yasa mu dace, amman ita ba nan zata sauka ba?”


Ammy ta yi murmushi domin ko fito kai tsaye ya mata magana ba ta san wa yake nufi.


“Kai da ganinta yanzu ai sai an kai maka ita”


“Tooo”


Ya mike tsaye yana cigaba da murmushi.


“Nana ta min maganar graduation dinsu, wai a Abuja za su yi”


“Eh ta fada min ni ma nace ban yarda ba, yayi nisa duk abun da za a ce sai an bar Yola anje wani guri ayi sa ban zan bari ba”


“Ni ma ban bata shawara ba gaskiya, mace kiwonta ake, na ce mata dai zan yi magana da ke, zan fada mata kin ce ba ki aminta ba”


“Haka ya kamata Allah ya muku albarka”


Ya amsa da Ameen sannan ya fice daga dakin sai zuba kamshin turare yake.










_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Khadeeja Candy*


*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*




Bayan kowa ya fice masu nasiha sun yi daga bangaren Amarya kuma Nana da wata cousin dinta sukai kasancewar Fadime bata da kawaye a gurin.
Shattima ya kai hannunsa ya daga mayafin amayarsa dake ta kuka, domin ta gane da gaske rabuwa za tai da kowa ta koma sabuwar rayuwa, hakan yasa duk wata murna da farinciki da take na aure sai ya kau. Ido ya kura mata yana ta kallon kyakkyawar fuskarsa da ta sha makeup hawaye sai sauko mata yake. A yau ta fi masa kyau fiye da kullum domin har wani annuri da haiba take tsabar kyau da tai.


“Subhanallahi ahsanal halikin”


Ya furta yana kallon yadda Allah ya jera mata kyau gwanin kyau da burgewa, kuka take amman dan karamin bakinta motsi yake kana gani kasan magana take da kanta can cikin rai. Matsawa ya kara yi daf da ita ta yaye mayafin gaba daya ya rumgumeta.


“Na san zaki ji babu dadi, amman ba a kuka a irin wannan ranar ta farinciki ranar da mutane da dama suke ta fatan gani ba su samu haka ba, ranar yau rana ce mai muhimmanci a rayuwarmu”


Lamooo tai kamar wata mage tana saurarensa, fanfan kirjinsa ya wadatar da kukanta a take ta ji kukan ya yanke mata, sai dai bata jin wani abu mai kama da farinciki a yanzu kuma bata tare da kishiyarsa. Hannunsa ya kai ya kama hannunsa da ya sha jan lalle ya rike yan siraran yatsunta yake kallo yana wasa da su a hankali, dayan hannunsa kuma na shafa bayanta.


“Yau kin zama yar gata, matsayinki ya karu, za a fara rubanya miki ladarki daga yau, kina so ai ko?”


Ta daga masa kai a hankali.


“To ki gode Allah”


“Alhamdulillah”


Ta furta a shagwabe.


“Iyeee ashe kin iya? Fada min ina kika tsaya a karatunki?”


“Na sauke ai”


“Really?”


“Yes”


“Bayan nan fa”


“Shikenan”


“Ba ki yi wasu littafan ba?”


“Ban yi ba”


“Amman ai a makaranta an koya miki yadda ake wankan haila ko?”


Ta dan yi shiru kamar ba zata ce komai ba.


“Eh Inna ce ta koya min”


“Janaba fa?”


“Minene kuma Janaba?”


Ya wara ido tare da saka hannunsa ya dago kanta ta fuskance shi.


“Da gaske ba ki sani ba?”


“Wallahi ban sani ba, abinci ne?”


Murmushi yai mai kyau murmushin da ya bayyana hakoransa, sai ya kai bakinsa saitin nata, a tunanin wani abun zai fada mata sai ta ji bakinsa cikin nata ya kama lips dinta ta tsosa tana ta kokarin kwace kanta ta kasa, har sai da ya daga fuskarsa daga nata, sai ta sa hannu ta goge bakin ta fara tara yawu tana jin wani kyankyami a zuciyarta. Ba dan tana kunyarsa a yau ba da sai ta fada masa bata son kazanta, amman ta masa uzuri saboda ita amarya ce a yau, kuma ance tai biyaya an fada mata kar ta daukaka halshenta sama da na shi, kuma idan yana mata fada tai shiru ta saurara sai ya gama sannan ta fada masa manufarta cikin kyakkyawan lafazi. Kokarin mikewa tai tsaye.


“Zan shiga ban daki”


Yana jin haka sai ya rigata mikewa tsaye ta saka hannayensa ya dauke ta cak sama, abun da da marar jiki sai gai sama sosai kamar ya dauko filo, dariya tai ta saka hannayenta ta zagaye wuyansa.


“Ashe zaka iya daukata”


Murmushi yai ya nufi upstairs da ita, ya tura kofar dakin ya shiga har cikin bandaki ya sauketa.


“Fitsari zaki yi?”


“Aa bakina zan wanke”


Sarai ya gane saboda ya yi kissing dinta ne zata wanke bakinta.


“Ashe ina da aiki”


Ya furta yana murmushi.


“Aa baka da aiki ai ni zan wanke da kaina”


Kamin yace komai ta kunna fanfon ta fara kurba ruwan tana kuskurewa, sai da tai hakan sau kusan bakwai yana tsaye yana kallonta sannan ta juyo.


“Ya wanku?”


Ya tambaya yana matsawa kusa da ita, sai ta daga masa kai.


“Eh”


“Mu gani”


Ta wangale masa bakin sai ya kai hancinsa kamar zai shinshina sai ya sake kama lips dinta ya fara tsotsa ya saka hannunsa ya rike kwankwasonta ta yadda ba zata iya matsawa ba, abun ka da an dade ba a hadu ba sai ya samu damar shanye 15% na kishirwar kiss din a tsaye cikin bandaki, tun tana iya tsaye ta kafafuwanta har ta kai ta ta fara yin kasa sai saka hannayensa ya dauke ta yai sama da ita, duk yadda zata yi ta ya saki bakinta ta yi yaki saki domin daukar da yai mata sai ta bashi damar matse hannayenta inda karfinta a nan yake, sai ya zura mata halshensa sannan ta sama damar cije sa ba shiri ya zare bakinsa yana runtse ido.


“Wai Wai Wai Wai haba Baby”


Ya rufa tana sauke ta, sai ta tuna ance karka kuskura ta bata masa rai kuma idan ta bata masa rai ta duka ta bashi hakuri tace ya yafe mata. Saurin dukawa tai kasa.


“Dan Allah kai hakuri ka yafe min”


Kallonta yai da murmushi, sai ya ji ta kara burgeshi, hannunsa ya mika mata sai ta rika ta mike tsaye tana tara yawu a bakin..


“Miyasa kika cigeni?”


“Bana son kazamta ne shiyasa kai kuma...”


Ta yi shiru bata karasa ba sai tai kasa da kanta, hannunsa ya saka ya dago kanta.


“Ba kazanta bace hakan yana nufi soyayya ne da rashin kyamar juna, idan na sha yawunki na yarda da tsaftarki kuma ina kaunarki ne matuka, idan kin sha nawa hakan na nufin kin yarda da ni kuma kina kaunata, dan haka ki daina kyama”


Ta daga kai tana kallonsa fuska a yamutse, sai wani abu take ta ji tsabar kayan matan yar gidan mai fata da aka dura mata.


“Yanzu zubar da yawun”


Ta zubar da sauri daman abun da take nema kenan, tana juyowa sai ya kai bakinsa saitin nata.


“Kama ki yi kissing”


Ba dan ance kar ta masa musu ba, da babu yadda za ayi ya ce tai wannan kazantar ta yarda tai. Ta kama kadan ta dan yi kissing tana runtse ido kamar mai shan magani, sai tai saurin cirewa ta kalleshi.


“Zan iya yin amai gobe?”


“Yeah Allah ya kai mu, oya cigaba”


Ba dan ranta ya so ba ta kusan kwashe rabin awa tana kissing dinsa sun tana kin hade yawun har ta fara hadewa tana jin kamar zata yi amai.


“Good”


Ya juyar da ita ta yadda ita da shi za su fuskanci madubin da yake bandakin.


“Kalli kyakkyawar fuskanci da dan karamin bakin nan”


Ta kalli kanta sai ya saka hannu ya cire sarkar wuyanta yai kissing din bayan wuyanta, sai kuma gefen wuyanta na dama zuwa hagu. Ita kuma tai shiruuuuuu tana ta kallonshi ta madubi da tunani kala kala a ranta, ba yau ya fara kissing dinta ba Wasim ma ta taba kissing goshinta hannunta, amman ban da wuyanta amman shi har da wuyanta yake kissing kuma ya saka ta sha yawunsa, tsoro ya fara kamata Allah dai yasa na jininta ya shanye ba ta cikin yawun, kuma wannan abun da yake mata abu kamar dan iska sai wani jarrrrr take ji. Hannunsa ya saka yana zirya da yatsansa a wuyanta yana kallonta ta cikin madubin.


“Yanzu alwala za ki yi sai mu yi sallah”


“Ina da alwala, sai da na yi alwala sannan akai min kwaliya”


“Okay ni bari na yi alwala”


Ya fada sannan ya sake kissing din wuyanta, wannan karon juyowa tai tana kallon fuskarsa, sai ya doko mata da fuskar hakan yasa tai saurin rufe idonta kamar ta san idon zai sumbanta, sai ya dora bakinsa kan fatar idonta ya sumbance both eyes dinta da suke rufe sannan ya saka bakinsa a hancinta ya tsotse hancinta tasss, sannan ya sumbance shi ya dauke bakinsa.


“Jirana zaki yi?”


‘Kazami babban kazami hancin da ake cire majina ake kwakwata antoni shi yake tsotsawa, ina masa kallon mai tsafta ashe babban kazami ne’


Ta fada a ranta sannan ta bude idon ta kalleshi.


“Zan zauna a falo”


“Okay”


Ya furta idonsa kamar wanda ke jin bachi, sai ya murza yatsun hannunta sannan ya sake ta ta fice. Tana fitowa taja masa kofar bandakin ta rufe, arba da tai da furnitures din dakin sai yasa ta manta da komai, ta shafa fuskarsa tana zaro ido.


“Yanzu nan dakina ne?aahahahaaaaaa”


Ta furta kadan kadan ta zauna bakin gadon tana ta mamaki yadda aka cika dakin da katon farin gado dan turkish da wardrobe kamar wata yar govno, hawa tai saman gado ta kwanta ta sauko ta nufi wardrobe ta shafa, tana jin motsinta sai tai saurin ta dawo bakin gado ta zauna ta kama jikinta ta marairace fuska kamar da gaske babu ruwanta. Bude kofar bandakin yai ya fito rike da babbar rigarsa ya dorata saman gadon sannan ya nufi wardrobe ya bude ya dauko mata hijab. Sai ta karba ta saka gaba ya tsaya ta tsaya daga bayansa kadan kamar yadda ya nuna mata sannan suka soma gabatar da sallah akan katon center carpet din da yake dakin, bayansu sallama yai musu addu'a sannan ya juyo ya kama kanta ta rike ya karanta mata addu'ar da annabi ya koyar da mu.


“Alhamdulillah wannan Allah da mu ka yi godiya ce ga Allah akan irin ni'imar da yai mana, ya hada mu ta sigar da ba mu yi zato ba, kuma ya daidaita mu ya shirya tsakaninku har muka kawo yau da aka daura aurenmu”


Ta gyada masa kai alamar gamsuwa.


“Na yi mana addu'a kuma ina fatar ke ma kin yi mana”


“Eh na yi”


Yayi murmushi.


“Me kika ce?”


“Na ce Allah ya tsare mu daga dukan shari kuma ya ba mu yan biyu, kuma ya mana albarka”


“Yan biyu kike so kenan?”


Ta yi kasa da kai tana jin kunya, to mi ya rage tun da ta yi aure a yanzu ai ba ta da burin da ya wuce haihuwa, ita ma ta zama uwa kamar kowa.


“Samun yan biyu ba sauki fa”


Ya fada yana kallon fuskarta.


“Ni dai ina so haka nan suna burgeni”


“Yanzu fada min yadda ake wankan haila”


Sai ta ji wata kunya ta rufe ta, wai ta fada masa ai da kunya kam ta ina zata fara.


“Fada min mana”


“Gaskiya ni dai ina jin kunya”


Ya kai hannunsa ya kama hannunta.


“Fatee na”


Ta kalleshi.


“Babu kunya tsakanin mata da miji, kuma babu boyewa juna sirri, sannan babu yi ma juna karya, ni mijinki ne sirrinki komai nawa a yanzu na ki ne, haka ke ma sirrina ce, ko da wasa karki kuskura ki fadawa wani cewar mijinki yayi miki kaza ko taba miki kaza ko yace miki kaza kinji ko?”


“To fada min”


Ta fada masa kamar yadda take kuma kamar yadda Inna ta koya mata, ta fada daidai sai dai abun da bata sani ba shi ne yadda ake wankan haila haka ake wankan janaba.


“To


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login