Showing 111001 words to 114000 words out of 273152 words

Chapter 38 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72772

ta shiga motar sai ya rufe ya bude mazaunin direba ya shiga ya zauna, sai ya samu kansa da rashin natsuwa har sai da ya juyo ya kalleta, be taba ganinta da kwaliya ba sai a yau, ashe haka take da kyau? Ya raya a zuciyarsa.


“Kin yi kyau”


Ya furta a fili yana jin wani irin girmanta na kama shi, duk sai yaji ta zame masa kamar ba ita ba ya ji nauyinta na sauko masa.


“Na gode kai ma ai ka yi kyau”


“Thank Youu, ina zamu je?”


“X&L Hotel”


Ya juya yana shakar kamshin turarenta daya cika motar ya bata da na shi karamin turaren. Madubin motar ya saita ya juya ta inda zai rika ganin fuskarta sannan ya kunna wutar motar ya kunna ac. A hankali yake ta tuka motar yana satar kallon Nana ta madubin motar, a duk lokacin da suka hada ido sai ta saka masa murmushi. Daga ita har har shi babu wanda yai wata magana har suka isa.
X&L Hotel babbar Hotel ce a garin Yola, wanda manyan mutane suke zuwa yin taro ko biki ko sauka idan ta kama, ko kuma shakawatawa.
A harabar Hotel din ya faka motarsa sannan ya fito ya bude mata ta fito.


“Zaka shiga ciki?”


“Ana bari a gashi?”


“Yes zan ce kai bodyguard dina ne”


“Okay”


Ya rufe motar yana jindadi, daman can ya dade yana son ya shiga gurin domin ya dade yana jin labarin Hotel din sai dai be taba zuwa. A maimako tai gaba ya bi bayanta sai ta tsaya ta jera tare da shi, yadda ya ci ado ita ma ta ci sai abun ya bada kala kamar saurayi da budurwa, a tare suka doshi wata karamar hanya da aka kawata kamin su karasa wani saurayi ya kira sunan Nana, da sunan da Zainab take kiranta da shi.


“Baby”


Nana ta juyo tana arba da saurayin ta washe hakora ta doshi inda yake, AA kuma ya tsaya a gurin yana kallonsu, side hug tai masa suka gaisa.


“How are you?”


“I'm fine, kai ma ka zo biki”


“Yeah friend din mu ne zai yi aure, amman mu ba ciki zamu shiga ba, waya kawo ki Sirleem?”


Juyawa tai ta kalli AA a ganin be cancanta ta kira direbanta ba a yadda ya ci gayun nan.


“No wani ne”


“Okay sai mun hadu ciki”


Ya fada yana sannan ya nufi hanyar shiga gurin. Ita kuma ta juyo ta dawo gurin AA.


“Mu tafi”


“Ba zamu je din ba”


Ya fada yana watsa mata harara.


“Me akai?”


“Ya zaki rumgume wani kato da ba muharramin ki ba”


“To ai cousin dina ne”


“Ba cousin ba kwarkwata, bari na sake ganin kin rika hannun wani sai na fasa miki kai”


Ya karasa da kwafa ita kuma ta turo baki.


“To Wallahi zan ma koreka daga aikin”


Ya kwaikwayi muryarta yana yatsina fuska.


“To Wallahi zan ma koreka daga aikin”


“Kuma karka bi ni ciki, ba zan shiga ba”


“Wallahi sai na biki, sai na shiga, kuma muna shiga ciki kika ga wani kika masa magana sai na bata miki rai”


Ya fada with serious face, yana kara hade mata rai kamar irin shi ne boss ita take aiki karkashinsa. Tana yin gana ya bi bayanta sai ta juyo tana turo baki.


“Ka daina bina”


“Sai na biki kuma ki kaiwa wani namiji magana sai na bata miki rai”


Wani irin abu taji kamar ta saka kuka, sai kuma ta juya ta cigaba da tafiya yana binta bayanta har suka isa gurin. Bata nuna gate pass din ba sai kawai ta fada masa sunanta.


“Nana Aisha Abdallah Jari”


Da sauri ya bude mata kofar ta wuce AA ya bi bayanta yana fadin shi bodyguard dinta ne. Kato dakin taro ne da aka kawata da ado na zamani ga haske ko'ina kamar rana, mutane ta ko'ina kana ganin bikin kasan na manyan mutane ne. Kusa da kofar AA ya tsaya Nana kuma ta fara raba ido tana kallon mutane, ta nan ta hango Hajiya Babba cikin matan manya sai far'a take ana ta fira, can kuma ta hango kawarta Amal, da sauri ta nufi inda suke Amal din na ganinta ta rumgume ta tana murna kamin ta ja mata kujera ta zauna, duk abun da suke idon AA na kanta ita a tana yi tana satar kallonsa, tana son ta bar kujerar ta koma wata inda take hango wasu friends nata, da zarar ta mike tsaye sai AA ya bata mata fuska na babba da yaro sai ta koma ta zauna tana watsa masa harara tana turo baki. Sai da ya tabbatar ta natsu sannan ya fita daga gurin ya koma cikin motar ya zauna.
Kari aka fara yi ma Amarya wanda hakan yasa su Amal din tashi ita da kawayenta, suka nufi gurin Amaryar aka bar Nana ita kadai, wata kawar Amal din ce mai suna Rukayya ta dawo gurin ta aje handbag dinta ta cire sarkarta ta zinari ta saka a jakar.


“Sis dan Allah zan bar jakata a nan ki kula min, sarkar tana damuna ne”


“Okay”


Nana ta amsa duk da bata san ba sai a lokacin. Yarinyar na barin gurin zuciyar Nana ta fara raya mata ta dauki sarkar, hannunta ya soma wani irin kai kayi, wani abu ta soma ji ba dadi, har ta kai hannunta a jakar sai kuma gai saurin cirewa tana kallon jama'ar gurin da ba su kula da ita ba. Dagawa tai daga zaunen da take ta saka hannunta a kasa ta dannenshi amman bata ji ya daina mata kaikayi ba, ba kaikai irin wanda aka saba ji ba kai kai yi a daukar abu wanda take jin a duk lokacin da so satar wa Ammy ko Mai Martaba kudi. Ciro hannun tai tana yarfarwa sannan ta kai cikin jakar ta dauko sarkar mai tsada ta saka a purse dinta ta mike tsaye da sauri ta fice daga gurin.
Sai da ta fito daga gurin sai kuma tai tsaye idonta ya cika da hawaye, bata taba abun da ba na Ammy ba sai da yau bata taba sata in public place like this ba sai a yau. Ji take kamar ta koma ta maida kuma tana jin tsoro. Takawa ta fara yi ta nufi gurin motarsu, tana isa ta bude motar ta shiga gidan bayan. AA dake zaune ya juyo ya kalleta.


“An gama bikin ne?”


“Aa”


Ta amsa da muryar kuka, jin hakan yasa ya juyo da kyau ya kunna wutar motar yana kallonta, sai hawaye ya gani a fuskarta.


“Ya akai?”


“Wani abu nai”


“Wani abu na mi?”


Ta yi shiru sai kuma ta ce.


“Sata nai na saci sakar wata kawar kawata”


Ba shiri AA ya zaro ido.


“Sata kuma?”


“Eh ai be kamata nai sata ba ko?”


“Then why kika yi?”


“I don't know i just feel like ina son nai, amman be kamata nai ba, kuma na san akwai camera a gurin zata nuna ni, kuma yarinyar ni ta bawa ajiyar jakarta”


“Nana me zai saka ki yi sata? Why, be kamata ace kina sata ba Nana baki bata sunan gidanku da mahaifinki, mi kika rasa ma da zaki yi sata? Why?”


“Ban sani ba, haka nan kawai nake yi”


Ta amsa shi tana kuka, wani tunanin ne ya zo masa kar dai ace kudin da take kashewa sato su take?


“Ina sarkar?”


Ta bude purse din ta dauko ta mika masa.


“Gashi”


Ya mika hannu ya karba.


“Akwai gate pass ne”


“Eh”


Ta ciro ta mika masa, sai ya karba.


“Ki koma ciki ki dauki wayarki sai ki samu gurin da babu mutane sosai ki kara wayar a kunne kamar kina waya, idan tai magana ki ce kin bar jakar ne kin je ki yi waya, zan shigo yanzu”


“Amman bani da waya Baba Waziri ya karbe”


Ya kika mata wayarsa.


“Rike wannan”


Ta Karba sannan ta bude motar ta fita ta nufi gurin tana share hawayenta gabanta sai faduwa yake. Da kallo ya bita har ta shige sannan ya sauke ajiyar zuciya yana jin wani iri a ransa.


“So. That's mean kudin da take bani satarsu take yi? What's wrong with her?”


Ya furta yana ganin rashin dacewar hakan, sannan ya bude motar ya fita ta doshi guri.




FALMATA POV.


Tara da yan mintuna yaran su kai bachi amman tana zaune a dakin domin cika umarnin Shattima da jekadiya ta fada mata sai 10 zata tafi gida, ko kadan bata jidadin hakan ba, sai dai bata isa tai musa ba balle ta tsaba, ta sani suna mata haka ne saboda kawai bata da galihu, saboda tana aiki karkashinsu. Wannan abun kadai ya isa yasa ta kara kaunar Sirleem a ranta, ko ba komai ya tausaya mata, ya nuna mata kulawa kuma ya taimaketa. Sai da goma tai sannan Jekadiya ta shigo dakin.


“Za ki iya tafiya yanzu, direba na waje yana jiranki, daga gobe har kullum zai rika zuwa daukoki misalin 7am”


“Tau na gode”


Ta fada tana risinawa sannan ta mike tsaye ta fice daga dakin. A natse ta shigo falon Ammy, al'adar ta ce indai akwai mutane a falon ba zata fice ba sai ta taje ta gaishesu. Hakan yasa ta karasa gaban Ammy ta kwashi gaisuwa sannan ta risina gaban Yarima ta mika masa gaisuwa. Kara ma Ammy ta amsa shi kam ban da kallonta komai be yi ba, babu alamar amsar a tare da shi. Mikewa tai tsaye ta nufi kofar fita, fitarta da kamar minti daya ya mike tsaye ya nufi backyard din falon Ammy, tsaye a gurin yana kallon yadda ta nufi motar, da kuma Sirleem daya fito daga bangarensu ya doso inda take.


“Ina wuni, Malam dan Allah kai ne aka ce zaka kai ni gida?”


Falmata ta tambaya tana leken Baba Adamu dake gaban motar.


“Eh ni ne”


Ya amsa mata, sai ta matsar da kunnenta kusa da shi.


“Dan Allah sake fada bana ji sosai”


“Eh ni ne”


Ya fada da karfi.


“Tau na gode”


Ta mike tsaye tana jin alamar mutum a bayanta, da sauri ta juyo sai tai arba da Sirleem.


“Gida zaki je?”


Ya rada mata a kunne yana murmushi.


“Eh wannan zai kai ni gida”


“Ina maganinki yake?”


“Gashi”


Ta fada tana kokarin fiddo da hannunta cikin hijabin, bata karasa ba ya kai hannunsa cikin hijabin ya karbi maganin ya dora saman motar yana amsa gaisuwa da Baba Adamu ke masa, sai da ya fitar da maganin na digawa sannan ya rika fuskarta ya ja hijabinta baya ya fito da kunnuwanta ya kwantar da kanta ya diga mata maganin a kunne daya, ya saka mata kada sannan ya sake digawa a dayan kunne ya saka mata kada kana na rufe maganin.


“Karki yi wasa ki rika amfani da shi kullum, ta fada min magani ne mai tsada ta siya miki”


“Inshallah, na gode Allah ya saka da alheri”


“Never mind”


Ya fada yana fadada fuskarsa da murmushi sannan ya bude mata bayan motar, ta shiga ya rufe ya daga mata hannu, ita kuma ta juyo tana kallonsa ta bayan motar har suka fita daga harabar sannan ta juyo ta zauna daidai tana jin wani irin abu a zuciyarta mai wuyar fassara, abun da bata taba ji ba sai a yau, abun da ba zata iya fadar ga kalarsa ba balle yanayinsa, idanuwanta ne suka cika da kwalla sai ta rumgume hannayenta ta lumshe ido.


**


Sai da suka wuce sannan Shattima ya bar backyard din ya dawo cikin falon ya zauna kusa da Ammy.


“Ni kam sai nake ganin kamar Sirleem ba son Nana yake ba”


Ammy ta kalleshi.


“Kamar ya?”


Ya daga kafadunsa, alamar haka nan dai.


“Idan baya son ta ai ba zai nuna ba, tun da ba dole aka masa ba, ya dai rage kula ta ne kamar baya, saboda kun saka masa ido”


Be sake cewa komai ya ciro wayarsa dake aljihu, ganin Number Baba Waziri yasa ya mike tsaye ya fice daga falon. Kasa ya dauko gaba daya sannan ya kara wayar a kunnesa da sallama. Bayan sun gaisa Baba Waziri ya ce.


“Ban jika ba, tun da muka yi magana, idan Maijidda bata maka ka fada min wanda kake so, ba abu ne da zai dauki lokaci ba balle nai ta jiranka”


Shattima yayi shiru kamar ba Waziri ne a wayar ba, can kuma ya sauke ajiyar zuciya silently ya ce.


“Ina sonta Baba, amman dan Allah a tambaye ta idan ita ma tana so na, kar a mata dole”


“Mashallah, Allah ya hada kanku ya fada zaman lafiya sai ka fara shirye-shirye tun yanzu”


“Na gode Baba”


Ya furta sannan ya sauke wayar tare da sauke wani dogon numfashi. Data kunna ya shiga wani side ya siye ticket din jirgin da zai tashi zuwa Katsina a gobe.


**


Shattima na fita falon, Iya ta shigo lullube da zane, tana shigowa ta fadi gaban Ammy tana zuba mata kirari bakin nan cike da goro, sai da ta kalli ko'ina a falon ta ga Jekadiya ce kadai a falon sai Ammy sannan ta kara matsawa kusa da Ammy tana wasar hakora.


“Ranki ya dade, ina da magana”


Da gangan Ammy ta ki kallonta ba dan wulakanci ba sai dan nuna isa, daman can Allah ba hada jinin Ammy da Iya saboda Iya ta fiye shiga hanci da kuddudumi ga salo irin na tsofin mayu, Ammy kuma bata son haka.


“Tau ina jinki”


Ta kalli Jekadiya tana dariya, kamin ta sake kallon Ammy.


“Daman wata yar shawara ce na zo da ita”


Sai kuma tai shiru kamar mai tsoron fada. Ganin hakan yasa jekadiya ta ce.


“Iya ki bude baki ki yi magana, Ammy na saurarenki”


Iya ta juyo gurin Jekadiya tana yar dariya kamar ta kunya.


“Daman na ce wai akan Babban Mutum ne, na ce mi zai sa sai an tafi nesa”


Ammy ta kalleta domin ta fahimci inda zancenta ya dosa tun kamin ta karasa, Jekadiya kuma gabanta ya fadi duk da ta san ba wai ta fada ne ta siffar gulma sai dai ta san Ammy ba zata jidadi ba ta fada mata abu kuma aji shi gurin wani.


“Wannan lauye lauyen da kike ba zai fitar da ke ba, da kin fito kin fadi maganarki a fili da Ammy ta fahimta”


Iya ta shafa zanenta tana murmushi.


“Daman cewa nai me zai hana a hada Babban Mutum da yar'uwarsa? Ai ba sai an je can nesa ba an dauko bare tun da ga abu a ciki gidan”


Jekadiya makis tai a gurin kamar an kama munafuki, ta rasa abun cewa. Ammy ta juyo da kyau tana kallon Iya.


“Eh lallai haka, jindadi yayi muku yawa ke da yarki, har hauka take raya muku wannan, shine dalilin shigewa Shattima da Zainab take? To ai kalar zaren ba kalar yadin ba ne, kuma lalacewar takalmin sarki yafi karfin sakawa kafar bafade, Maijidda ce bare? Yar waziri ce nesa? Gata da sakin fuskar da ake muku a gidan nan ya muku yawa shiyasa har raini ya shiga ciki, har kike iya duban idona ki fada min wannan maganar, Iya wai ko kin manta waye ke?”


“Aa ina ya zan manta... A gafarce ni Hajiya salo na ne... Amin afuwa”


Iya ta fada da dariyar kunya, zuciyarta tab da tsanar Ammy sai kallon kurwarta take.


“To daga yau sai yau, ba ke ba ko Zainab kar na sake ganin kafarta a falon nan, idan kina bukatar wani abu ko yin wani abu ki nemi iso karki sake shigo min falo, idan kika yi wasa ba a masarautar ba a yola gaba daya ma sai na canja miki zama”


“To Ammy ba za a kara ba ayi min afuwa a gafarta min”


Ta farasa tana fashewa da kuka, ta mike tsaye rumgume da kunyarta ta fice daga falon, tana kuka kamar gaske.
Ammy ta kalli Jekadiya da duba na mamaki.


“Kin ba ni mamaki, ban yi zaton haka ba, amincewa da ke kuma farinciki abun da Waziri yai yasa na labarta miki taya zaki dauki sirri ki baza a kunne Iya?”


Jekadiya ta rasa inda zata saka kanta, a take ta hau rantsuwa, tana labartawa Ammy yadda akai ta Iya ta ji.


“Wallahi ranki ya dade ban yi hakan da nufin labarta mata komai ba, a gafarce ni, ni kaina murna ne yasa na fadi haka, ban yi zaton zata kawo wannan tunanin ba, Wallahi ba halina ba ne”


Ammy bata sake ce mata komai ba ta mike tsaye a fuce ta shige dakinta cikin mamakin yadda Iya ta iya karfin halin wannan tunanin, har ma ta iya furtawa.


***
Iya na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe.


“Idan ba yi da lala ba ayi da tsiya, tsaya mu gani ida ita ma Maijidda ta mutu sai wacce kuma? Wata rana da kanki za ki zo kina rokon na taya ki nemawa Shattima auren Zainab, ita kadai ce matarsa kuma da ita kadai zata haifa masa yaya, daga lokacin ne komai zai dawo na mu, ke kanki Ammy sai kin zama abar tausayi...”


Ta fada cikin wani irin zafin rai na jin zafin abun da Ammy tai mata.


“Tana jin kanta matar nan kamar ita ce sarkin, ke kuma bari na gani zaki taya ni yake ko kuma ta gawa za ki yi”


Ta karasa tana janyo wasu sabbin tufafin a cikin wardrobe dinta, atamfa mai kyau da tsada ya janyo ta dora saman gado domin bata son gobe ta tsaya jiran komai.
Haka ta kwana cikin bacin rai da sakesake kalakala a ranta, kamin garin Allah ya waye duk ta matsu, karfe tara ta shirya cikin atamfar data ciro jiya, ta dauki turare ta fesa sannan ta dauki jakar kudinta da makullin dakin ta fito, ta rufe dakin ta nufi kofar fita sai gaisawa take da hadimai kamar ta Allah, kowa sai bata girma yake har ta isa gate din. Sai da ta fita daga unguwar gaba daya sannan ta samu Napep ta shiga tana fadin.


“Malam Unguwar Waziri”


Ta shiga ta zauna har tana kwafa.






_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login