Showing 240001 words to 243000 words out of 273152 words
Chapter 81 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
daki daya ya ware mata a matsayin nata sannan ya kawo mata uku wadanda zasu rika yi mata hidima. Wannan furucin da Wasim yai ya saka ba su hana Zainab yin sallah ko saka kalar tufafin da take so ba, hakan kuma da take sai ya burge mutanen garin musamman ganin tufafinta na zamani ne gashi idan ta saka za su rufe mata jiki har kasa, sai dai su matse ta kasancewar duk tufafinta haka suke mata. Idan ta fito waje tana sallah wani lokacin sai su yi taro suna kallonta, alwalar da take ma kallonta suke suna ganin ta yi wani abu na dabam da ba su saba gani ba, gashi bata jin yaren mutanen garin idan tana son magana da su sai ta sha wahala sosai, abinci ma bata iya cin komai sai yayan itutuwa saboda tana jin launin abinci gurin dadi da kala ba irin nata ba, ganin hakan yasa Wasim yake zuwa yana siyo mata abincin irin an yan birni, and haka zai zo ya zauna yana fira da ita duk da kasancewar shi kansa baya cikin sakewar zuciya sai dai a kokarinsa na ganin ya faranta mata rai sai ya samu kansa cikin faranta nasa ran, idan tana sallah kuma sai yai ta kallonta yana tunawa da Fadime. Yau ma kamar kullum yana zaune bakin kofar dakin yana kallon yadda take sallah a kusa da shi saboda zafin dakin yasa ta fito waje tana sallah. Bayan ta gama ta yi addu'a ya kalli kyakyawar fuskarta mai dauke da karamin baki da kuma fararen idanuwa ya ce.
“Wai ku ba ku gajiya da yin wannan abun kullum?”
Kallonsa tai.
“Ka taba ganin mutum ya gaji da ibadarsa? Wannan sallah da kake ganin duk musulmi kwarai ba ya yarda lokacinta ya fita be yi ta ba, hakan yasa ka ga ina kwatantan lokacin ta sai na yi, yin ta tana sakarwa mutun da natsuwa da kwanciyar hankali kuma yana kara kusantar da bawa ga ubangijinsa, sannan ibada ce da ake bawa mutun lada mai yawa a lokacin da yayi ta”
Yayi murmushi ba dan ya gane wani bangare na bayaninta ba. Shiru ne ya biyo baya kamin ta kalleshi ta ce.
“Tun da na zo garin nan ina kokari na koyawa kaina zama da mutanen cikinta da yin rayuwata irin na mutanen garin nan amman na kasa, ina ta kokari na cire Iya a raina amman na kasa, har so nai na yi ma kaina alkawarin ba zan taba tambayar inda take ba, ashe ba zan iya ba saboda soyayyar uwa ta fi gaban wasa, komai zata bata maka rai wata rana sai ka ji kana bukatarta a kusa da kai”
Wasim ya yi shiru yana kallonta sai hawaye take.
“Be zama lallai ki yi rayuwa tare da mu ba, zan tsaya miki ki samu irin rayuwar da kike so a lokacin da kike so, ko da kuwa kasar nan za ki bari gaba daya”
Kallonsa ta sake yi.
“Bana son wani ya sake aikata wani kuskuren saboda da ni, ka fada min ina Iya take?”
Mikewa yai tsaye yana kokarin kawar da maganarta ta biyu.
“Ba zan yarda na sake aikata wani kuskuren ba, dukan abun da zan aikata a yanzu Zabin Raina ne kuma ya zama dole ni ma a ba ni damar rayuwa kamar kowa”
Yana kawai nan ya fara tafiya ba tare da ya bata amsar tambayart ta biyu ba, binsa tai da kallo zuciyarta na hararo mata abun da take jin kamar ba ta shirya masa a yanzu ba.
FADIME POV.
Duk Yadda Shattima ya so ta sake ranta ta koma rayuwa kamar da, a duk lokacin da tunarabuwarta da Wasim maganar da yai mata cewar ba zai sake dawowa ba, idan ta tuna kalmar sai ta ji kamar zata mutu, gaba daya ko abincin kirki bata iya ci, har sai da Shattima ya kebe da ita a wani karamin falon Ammy ya saka gaba da rarrashi da komai sannan ta ci kadan, ko nama domin kazar da ya saka aka soya mata na musamman bata wani ci ba, a daren ranar ma sai da yai mata karatu kamar jiya, sannan tai bachi shi kuma ya tsareta da idonsa yana ta kallonta sai jin yake kamar ya dauke ta ya bude cikinsa ya saka a ciki ya rufe. Washe gari ta farka da wuri saboda tun a daren da zata kwanta Shattima yayi mata albishir da maganar zuwa gida Katsina. Ba laifi ta dan sake saboda tana marmarin ganin iyayenta, a dinning ma da aka kira a karya ta dan ci abinci da yawa, tana ta daukin cin abinci a dinning kasancewar jiya a dakin Nana aka kai mata komai a yau kuma sai Ammy ta aika aka kirata ta fito aka karya tare da Nana da Mama Fulani, daman Aliyu da Muhseen tun ranar da su kai gaisuwa suka juya a mota suka koma Abuja.
“Fulani a saka mata ido, Shattima ya ce bata cin abinci”
Ammy ta fada tana murmushi domin ya jadadda mata cewar ta kula da abinci Fadime baya son ta tafi gida da yunwa shi kuma ba zai samu shigowa gidan ba sai da suna kusan tafiya. A duk lokacin da Ammy ta kira Mama Fulani sai Fadime ta amsa tana ganin kamar da ita ake domin ita ma ta saba a gidan Inna da Bappa suna kiranta da Fulani. Shattima be kira Bappa ya fada masa halin da ake ciki na Fadime ba, shi ma kuma be kira wayarsa ya tambaye shi ba har yau. Ammy da kanta ta shigar da Fadime bangaren Mai Martaba suka gaisa, sannan yai mata goma ta arziki bayan ya tabbatar mata cewar tare da Baba Waziri zata je kuma idan zun tafi Katsina za su sauka a masarautar Katsina ne a hada tawagar da za su mata rakiya har gida, saboda ta jaddadawa Ammy abun da take tsoron Bappa yai mata wato duka ko ma ya koreta gaba daya, ita kuma Ammy tana ganin ko da ba zai mata komai ba ta cancanci karramawa mai girma daga gurinsu.
Cikin wani irin farinciki marar misaltuwa ta fito bangaren Mai Martaba, ba ta sha wahala gurin gane hanyar dawowa ba ta hanyar kwaliyar da aka kawata corridor da zai sada mutum da bangaren Mai Martaba da akai, ta cikin gidan matansa bayan wacan komar mai gate nata na musamman da baki suke zuwa ta can, ga kuma fadarsa a can gefe daya.
Ko da ta shigo falon sai ta samu Shattima shi kadai zaune rike da cup din ruwan sanyi, sabar murna da farinciki ya saka ta manta da ko shi waye da kuma inda take ta soma aro kadan daga halinta na baya tana yafawa.
“Yaro ya...”
Sai kuma tai saurin rufe baki tana kallonsa, sai ya bude mata ido ya watsa mata ruwan hannunsa.
“Yarinya yarinya... Mai Martaba yayi mata kyau”
Kyalkyalewa tai da dariya kamar ba ita ba, shi kansa be san lokacin da murmushi ya bayyana a kumatunsa, murmushin da ya bayyana fararen hakoransa saboda farincikin da ya gani a fuskarta.
“Ko ba haka ba ne?”
“Haka ne”
Ta fada tana dariya, sai ya mika hannunsa baya ya dauko sabuwar waya cikin kwali ya mika mata.
“Ga waya na siya miki, kin ga ba zan yi kewarki sosai ba, sai na rika kiranki da ita”
Hannu biyu tana ta karba tana kara fito da ido waje tsabar mamaki.
“Ni ni Fadime? Waya? Wanda ake shafe shafe touching ko?”
“Yeah Pretty”
Sai ta zauna gabansa cikin wani irin farinciki marar misaltuwa ta fara kokawar bude kwalin wayar.
“Handsome man, amman Wallahi ka biyani ni ma na shigo gari, amman boye ta zan yi ba zan bari Bappa ya gani ba”
“Ba za ki daina halinki ba ko?”
Sai tai masa gwalo kadan.
“Wasa na ke zan nuna masa, sai na ce amman kar ya karbe min ko? Zaka kira ni kuma?”
“Me zai hana ba dole na ji muryar Fatee na ba”
Ta yi dariya sannan ta mika masa.
“Kunna min ka nuna min yadda zan yi tabe tabe”
Yayi murmushi.
“Tabe tabe dai”
“To shafe shafe”
Ya sake yin murmushi.
“To touching touching”
Ta fada da dariya, karba yai ya kunna wayar ya ciro line mtn ya saka mata a wayar sannan ya soma nuna mata inda zata taba, be ko gama ba ta ce.
“Na ma gane komai har wanda baka nuna min ba, ba ni wayar”
A garin karba wayar ta fashi ta tsaga daga kasa, wani irin turo baki gaba Fadime tai.
“Ka gani ko? Daman ba da zuciya daya ka ba ni ba”
Wannan karon dariya yai, daman ana bada abu fiye da zuciya daya.
“Da zuciya nawa na baki?”
“Biyu mana, dayar tana cewa a bawa ni dayar na hanawa”
Camera ta shiga daman ta fi kwarewa can a lokacin da yake nuna mata, daukarsa ta rika yi hoto, shi dai be ce mata komai ba har tai mai isarta ta gama ta shiga daukar falon da hotunan Ammy da suke lake falo, duk abun da take idonsa na kanta wani irin abu yake ji kamar ya kamata ya rumgume.
“Ki je ki shirya karfe daya za ku tafi”
“Ba da kai ba?”
Ya daga mata kai alamar eh. Sai ta bata fuska
“Miyasa?”
Kafadunsa ya daga mata alamar shi ma be sani ba, domin ya so ya rakata sai dai yana jin kamar indan suka tafi tare ya baro ta zai fi shiga damuwa fiye da yai mata sallama a nan, duk da yana da tabbacin bayan tafiyarsa zata sake dawowa rayuwarsa. Dawowa tai kusa da shi ta zauna tana ta kallonsa, sai kuma ta ji kewarsa ta kama ta.
“Ni daman ba ni da sa'a sai na sabu da mutum sai ya tafi ya bar ni”
“Amman ai ke zaki tafi ki bar ni, ni da kuka ba ke ba”
Ya fada da fuskar zolaya.
“Dan Allah ka rika kirana kullum ka ji”
“Dolena ai Pretty”
Bata yarda ba da shi za a je ba har sai da lokacin tafiyar yai, ta ga Shattima ya kirata daman ya bata agogon da ya taba bata lokacin da za su yi wacan lafiyar da su Bappa, a nan ta saka masa kuka tana jin kewarsa.
“No no ki daina damuwa zan kawo miki ziyara ai?”
“Da gaske?”
“I promise”
Da kasa ya kama saka hannunsa ya share mata hawayena.
“Dan Allah ka zo ka ji?”
“Kin fara missing dina kenan”
“Kuma kullun ka kira ni karka gaji”
Ya daga mata kai tana jin kamar ya hana ta zuwa, da farko be yi niyar rakata airport ba sai dai ganin yadda take kuka yasa ya rakata airport din, da katuwar jakar kayan da ya saka ka siya mata masu tsada. Motarsa dabam ya shiga ita kuma ta shiga motar su Baba Waziri da mutanen biyu da suke tare da shi, suna isa airport ko minti talatin ba su ba jirginsu ya daga zuwa Katsina. Kusan duk wanda be saba shiga Jirgi ba zaka tarar yana jin tsoro a shigarsa ta farko da ta biyu har zuwa lokacin da zai saba, amman ban da Fadime ko wa can zuwan da su kai da Mama Fulani bata wani tsorata ba, kawai saboda tana cikin damuwa ne yasa bata maida hankali sosai a kai tafiyar ba, yanzu kan har dadi take ji a zaunar da ita kusa da window jirgin tana hangen waje, ta soma daukar hoto da wayarta har mutanen da ke cikin jirgin dauka take. Suna sauka Katsina zuciyarta ta fara kewar Shattima ta dayan bangaren kuma tana mata zillon na son ganin Bappa da Innarta. Ko da suka sauka airport din Motocin Mai Martaba na harabar da ake aje mota suna jiransu, a Front seat ta zauna mutumen da ke tare da Baba Waziri ya shiga gidan baya, cikin motar ma tana ta daukar reban da kanta. Masarautar Katsina suka sauka akai musu tarba ta ta musamman, sai da suka ci suka sha wannan aka hada su da wata tawagar da zata yi musu rakiya har garin Bandalo. Kamin a isa garin Fadime har ta ayyana yadda zata rika kallon kowa, domin tana jin kamar ta fi kowa dace saboda ta je Masarautar Garuk, da ta Yola haka ma Katsina. Tun daga shigowar manyan motocin guda hudu mutanen garin suka fara kallo suna mamaki wane babban mutum ne ya shigo garin, ita tai ta kwantance hanyar da za abi a isa gidansu a lokacin da ta suka shigo garin Bandalo. Kamar taron kasuwa haka kaiwa kofar gidan Bappa da fifi ana kallon manyan mutane da mamakin su waye a ciki, wasu dai sai fadin suke Fadime ta janyo musu da mata rigimar wasu kuma na fadi daga Katsina aka aiko a tafi da Bappa kowa dai da abunda yake fada, dogaran dake tare da Baba Waziri ne suka fita suka isa bakin kofar gidan Bappa suna masa sallama irin wanda dogarai suke yi a kofar gidan talaka. Inna ce ta fito jiki na rawa tana amsawa domin Bappa yana gurin sana'arsa a lokacin, daman abu ne mai wahala ka tararda shi a gida irin wannan lokacin. Fadime na ganin Inna ta yi saurin bude motar ta fito, Inna ma tsaye tai tana kallonta sai hankalinta ya bar gurin dogarawan da take musu bayanin cewar Bappa ba ya gida.
“Inna”
Fadime ta fada tana fashewa da kuka, sai Inna ta rufe baki jikinta na rawa kamar zata fadi a gurin, da gudu Fadime ta je ta rumgume ta, jamar'ar gari suka hau leke kowa na mamaki, kuka sosai Inna da Fadime suka yi, sannan ta rika hannu Fadime suka shiga gida, makota da yan uwa kusa ne suka fara shigowa suna mata barka, wani makocinsu ne ya hau babur dinsa ya isa har inda Bappa yake ya sanar masa dawowar Fadime da kuma motacin da aka shigo garin da su tare da ita, take Bappa ya rufe shagonsa ya hau Babur din mutanen suka kamo hanyar dawowa gida da tunani kala kala a ransa, shi dai tsoro ya fi kama shi sama a lokacin da yai arba da manyan motocin, fargabarsa daya kar ace wata jamgwal din ce Fadime ta sake janyo musu. Sai a lokacin ne Baba Waziri ya fito daga motar bayan an gabatar masa da Bappa a matsayin mahaifin Fadime, Bappa faduwa yai kasa yana kwasar gaisuwa jikinsa sai rawa yake, ko mutumen birni ya yaji a gaban sarki balle na kauye, da sauri fadawan da suke tare da Waziri suka zo suna gyara masa rigarsa suna masa kirari, gaisawa yai da Bappa sannan ya gabatar masa da kansa sannan ya isar masa da sakon Mai Martaba na kudi da kuma gaisuwa, daga bisani kuma ya gabatar masa da albishir din Shattima na gidanda ya siya masa a Kt, daya daga cikin mutanen da suke tare da Wazari ne suka kira Shattima yai magana da Bappa a waya sannan ya kara tabbatarsa masa da abun da Baba Waziri ya fada, kuma ya fada masa cewar idan ya kimtsa yai masa magana a waya zai turo Ra'ees ya dauke shi ya kai shi har inda gidan ya ke kuma ya hannanta masa komai, Bappa sai ya rasa bakin magana ko godiya sai kuka, yana ganin komai kamar a mafarki.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Khadeeja Candy*
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Kusan duk wanda yake shakiki a masarautar kuma yake da alaka da Hajiya Babba ko Ammy da Mai Martaba ya jin abun da Hajiya Babba ta aikata, an fi jin nata sama da na Iya, domin ita take labarwa mutane abun da ta aikata da kanta, ga bakinta a juye gefe daya abun har ya fara tana kafarta da hannunta domin bata iya amfani da bangarenta na dama hagun ma sai ta dade tana tunani kamin ta iya mika hannu ta karbi abu ko ta rike, and when ever tana cin wani abu a bakinta ko da abinci ne sai ya zuba ta gafen bakinta ta zama kamar wata musaka, duk kalar juyin duniyar nan da akai mata bata gane Kausar ba, yar autarta ta manta da shafin rayuwar Kausar a cikin tata rayuwar, sai dai tai ta kallonta amman bata san wacece ita ba, gashi idan yanzu za ka fada mata abu anjima kadan ta manta sai an sake fada mata, amman bata mantawa da fadawa kowa labarin abun da ta aikata. Kusan asibiti uku Sirleem na canja mata yana ganin kamar za ta samu lafiya amman shiru. Hakan yasa danginta suka dauke ta aka maida cikin familynsu da niyar za a rika yi mata na hausa, hakan kuma be saka Sirleem ya saduda ba sai ya fara planing din fitar da ita waje. Hakan ya saka aka daga ranar da za a bikin mika masa ragamar kamfaninsa da kuma kananan kamfanonan da suke karkashinsa har zuwa karshen sabon watan saboda halin da yake ciki na tashin hankalin mahaifiyarsa da kuma kanwarsa Jurry, ciwon kai ya sakata gaba duk ta bi ta rame ko abu ta tauna a bakinta sai ta ji kan kamar zai rabe biyu, ruwa ne kawai zata sha ta samu salama amman bayansu duk abun da ta ci sai ta ji kamar zata mutu tsabar