Showing 195001 words to 198000 words out of 273152 words

Chapter 66 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72770

ta gani be mata dadi sam. Idan har akwai wanda ta cancanci wannan uban dukiyar to yarta ne, miyasa ya boye cewar yana da arziki shi ne abun da yafi tsaya mata a rai. Wanene shi ma ai ya kamata a sani tun farko.
Kusan bachinta rabi ne, rabin duk tunani ne da nazari, washe ta kasa karyawa da komai, sai samun Baba tai a can gefe tana tsegunta masa.


“Maganar gaskiya Malam a kara bincike a kan yarinyar nan, kar ya zama mun aurar da ita ga mutumen banza, tsakani da Allah ni dai zuciyata bata kwanta da shi ba, ka ga irin dukiyar da na gani a gidan nan? Da Wahala idan ba yankan kai mutumen yake ba, idan ba haka ba miyasa tun farko be kai mu gidansa na gaskiya ba ya ka mu wani shegen gida, kuma jiya ina jin su Ramatu na fadin wai har 200k ya abokansa suka ba su na siyen baki duba ka gani har fa dubu dari biyu Malam”


Baba yayi shiru yana nazarin maganar ta, tana da gaskiya in dan gaskiya domin mai gaskiya baya boyo, be kamata ya boye komai.


“Ni kaina na yi wannan tunani, amman wai gidan babba ne sosai”


“Malam kasan gidan tsohon ciyaman? To wane shi wannan ya ci ubansa, ga haske ko'ina kuma kare da karau wannan ma fa gidan sama ne, ga wasu manyan kujeru, anya mutumen kwarai mai tarin dukiya kamar wannan sai yarda ya auri yar talakawa irin Falmata? Ai sai dai yar manyan mutane”


A take hankalin Baba ya tashi, tsoro ya kama shi kar dai ace siyar da yarsa yai, duk da kasancewar ba wani barin kudi Malam Mu'azu yai musu ba.


“Dole ne a sake bincike, ba mu san halinsa ba”


“Ni ma shi ma gani, kamata yai ace ta dawo gida ya zauna har sai komai ya daidaita tukuna”


Baba yayi mata wani wawan kallo da bata taba tsammani daga gare shi ba.


“Tumba? Ta dawo gida kuma? Yarinyar da aka akai jiya jiya sai ace ta dawo gida a yau saboda kawai muna zargi akan mijinta? Ina ce ke kika shige masa gaba wajen neman auren nan?”


“Malam ni Tumba kake fadawa haka?”


Ta nuna kanta da mugun mamaki.


“Am fada miki! Uwata ce ke? Kullum cikin tsagwamar yarinyar nan kike, bata tana jindadinki, yanzu kuma ta daga ta samu inda zata raba ta ji sanyi sai ki fara jefanta da mugayen kalamai da mummunan zato? Babu abun da ba ayi ma Fulani a cikin gidan nan ke ki mata kuma ki saka na mata, a haka take ta hakuri har abinci sai da na hana mata, haba haba haba abun nan ya isa haka ya isa haka...”


Ya fada idonta na cika tab da hawaye yana jin kamar ya fashe da kuka tunawa da abubuwan da yake yi ma yarsa ta cikinsa. Tumba kam mamaki ya hanata kara cewa komai, a yau Baba ya bata abun be taba ba, musa mata akan abun da ta fada har yana gada nata da watsa bayan a da ko kallonta yai sai ya ji tsoronta ya kama shi kamar uwarsa.


“Toooo haka yau abun ya zo min?”


Ta fada a ranta, kana ta dora.


“Ban ga ta zama ba”


Ta juya da sauri ta bar turken awakin ta nufi dakinta, sai da ta wuce sannan Baba ya saka hannun rigarsa ya share hawayensa. Tana shiga ta bude kwanon samirarta ta dauko kudinta ta saka a karamar jaka ta dauki hijabinta ta saka ta dauko talkaminta na fita ta saka ta fito tana kiran Naja.


“Na'am Umma ga ni”


“Naja karki kuskura bar min daki a bude, ki zauna a ciki ga bakin nan har na dawo, kuma kowa ya tambaya ki ce na tafi kai kudin na karbo gara”


Tumba ta fada tana jadadda mata, Naja ta amsa da to, sannan Tumba ta shiga cikin dangin mahaifiyar Falmata da dangin Baba ta fada musu cewar zata je ta kai kudin gara.


“Ba ance yace baya son komai ba?”


Inna Laure ta tambaya tana kallonta sai Umma tai dariyar yake.


“Allah yasa ga Laure, dan yace baya so sai a ki yi masa? Ai ba a haka, duk wannan Hidima da yai ai sai mu kuma mu bashi yar gara saboda rabawa baki, ba wai gara ta abincin ba, yar dibilar nan da cincin ai zai samu na ba abokai da yan'uwa, ita sai ta samu na ba kawayenta”


“Eh gaskiya haka ya kamata, kina da gaskiya kowa yana son kyautata wa”


Tumba ta ji dadin da Indo ta taya ta.


“Shine ai ko mutunci da girma ai sai mu fi yi a gurinsa”


Kowa ya goya mata baya, ban da Inna laure, ita ganin take idan ma ta yi ba dan Allah tai ba dan kunya ne da neman gindin zama. Da haka ta sa mu damar barin gidan cikin aminci ba tare da kowa yayi tunanin gurin wani mugun abun za ta je ba. Tana fitowa ta fara uban sauri kamar zata tashi sama, mamakin abun da Baba yai mata ta ci uban abun da ta gani a gidan Falmata, ance mai kidan kare ya ji kidan kura. Kamin ta iso titi duk ta matsu, ganin neman Napep zai bata mata lokaci yasa ta nemi achana ta hau, bayan ta fada masa inda zai sauke ta. Tsakanin unguwar da zata je da kuma unguwar da take tafiya ce mai nisan gaske, domin unguwa ce da take bayan gari, su kuma suna cikin gari ne.
Mai achaba na aikinsa hankalij Tumba yana can gurin abun da Baba yai mata, ko a mafarki ba tai tunanin Baba zai musa mata ba balle har ya furta mata haka ba, sai a yau ta yarda magani dan kwana arba'in ne domin a yau kam ta ga zahiri, kamar a mafarki ta ji an yi sama da ita an buga jikin wata motar, sai kuma ta ji wani abu ya fado mata kamar karfe.


“Wayyoooooooooooooooo”


Ta furta iyakar karfinta tana jinta a wata duniyar mai zugi da radadi tare da gusar da hankali.






SARDAUNA POV.


Washe garin ranar da Ammy ta masa magana ya fara hada takardunsa cikin murna da jindadi, ba shi kadai ba Anti Rabi ma ji tai kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, tsabar jindadi domin ta san abun da kanenta ya dade yana nema kenan cigaba da karatu, gashi a yanzu ya samu ba ma a Nigeria ba a waje.


“Anti ban fada miki ba, haduwata da yarinyar nan alheri ne gashi kin fara gani”


“Amman da farko ai wuya ka sha”


Yayi dariya yana kade takardunsa.


“To ai dadi baya zuwa cikin sauki, kuma wani lokacin sai anjarrabeka kamin a baka abun da kake bukata”


“Haka ne, kuma in da hakuri sai ka ga komai ya zo ya wuce kamar ba yi ba, na jidadi sosai da ta saka maka da wannan, amman tafiyarka ba zata min dadi ba domin zaka yi nisa da ni”


Ya karasa da muryar da ke nuna har a ranta abun ya taba ta, dan murmushi yai irin murmushin nan na rashin jidadi.


“Ni kaina ba zan jidadin tafiya na barki ba, amman Anti wannan ce kadai damar da ke da ita, idan nai karatu na samu result mai kyau, sai na samu aiki da zan iya daukar nauyin kaina da kuma na ki ”


“Allah ya baka iko kuma a taimake ka, ita kuma Allah ya saka mata da alheri ya nisanta da dukan shari”


“Amin ya rabb, bari na tafi na kai mata takardun, wata kila ma idan ta gan ni ta tuna da zancen gidan da tace zata baki”


“Allah ya sa mu samu, aiko da mun gode, wannan sai a saka shi haya ana ajewa yara kudin saboda gaba”


“Zamu ma samu Anti tun da Nana ce tai maganar kuma ita da kanta Ammy sai da tace zata fadawa Mai Martaba, kin ga ko ta manta Nana zata iya tuna mata, ni Wallahi jin nake kamar yar'uwar mu ce, matar nan akwai kirki sosai, ni Wallahi har kunyar ta nake ji”


Anti Rabi ta yi dariya tana cigaba da tankaden garin dan wakenta, sai ya rufe jakar takardun ya maida daki ya dauki na sannunsa ya saka a wata jakar sannan ya kara fesa turare ya fito.


“Ban ce ka labartawa kowa ba, ka bar abun sai ya tabbata sai kawai mutane su ji zaka je”


“Anti ban da abun ki wa zan fadawa, ni kaina ai sai komai ya tabbata sannan jindadi zai kara tabbatuwa a gareni, Allah yai ya bude mana kofafin alheri”


Anti ta amsa da Ameen. Yana ma ta sallama ya fice cikin jindadi da zumudi.


_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*




Juyowa tai ta fito daga dakin tana share hawayenta, da sauri ta nufi kofar fita daga falon ta bude sai ta gashi tsaye jinkin kofar yana kallonta. Wani irin faduwa gabanta yai a lokacin da idonta ya sauka cikin na shi.


“Ina Fadime?”


Ya tambaya yana cire hular kansa wanda hakan ya bawa gashin kansa fitowa ya sarara.


“Bana son jin sunan yarinyar, ita ce silar wagaza farincikina, zuwanta ta zo min da bakaken abubuwa i hate her”


Ta fashe da kuka tana sakin kofar da zimmar faduwa kasa sai ta ji saukar hannayen Wasim a kafadarta. Mikar da ita yai tsaye ya ya girgiza mata kai, sannan ya matsa da shoulder sa ta dora kanta.


“Ba laifinta ba ne, laifinki ne ke da kika nemi kulla alaka da ita tun farko, da baki je garin ba da duk haka be faru ba, har halin da take kokarin shiga a yanzu da bata shiga ba”


Ta dago kanta hawaye na mata zuba.


“Kasan iya abubuwan da ta sanadiyarta na ji?”


“Na sani...”


Ya amsa mata calmy.


“Ba ni da komai a yanzu, ta bata min komai na rasa farincikina, ba ni da kowa sai uwar da bata da tausayi”


“Kina da ni...mu yan uwa ne kin tuna?”


Ta fada yana kallon cikin idonta holding her hand tight, fashewa tai da wani irin kuka wanda hakan ya bashi damar yi mata masauki a kirjinsa. Ya dora kansa saman nata nasa idon na cika da kwalla.


“Na san yadda kike ji, ina jin makamancin abun da kike ji, Baba ya fada min ba zai bar Fadime ta samu idonta ba har sai na yanke alakar da ke tsakamina da ita alaka ta har abada”


Dagowa tai ta kalleshi sai ta ga hawaye a idonsa.


“Hakan na nufin sai ka rabu da ita sannan zata samu lafiya”


Ya daga mata kai.


“Miyasa ba zaka iya rabuwa da ita ba then?”


Ya lumshe ido, can kuma ya bude ya kalleta.


“Miyasa kika bari aka kaita inda zata kara cutuwa?”


“Ban gane ba”


“Waya dauke ta? An kaita inda za a cutar da ita, miyasa kika bari aka tafi da ita? Miyasa kika musguna mata? Bayan duk kyautatawar da tai miki? Ko kin manta saboda ke take cikin wannan hali? Zan miki uzuri ne kawai saboda kina cikin wani kunci...!”


“Ina da tabbacin ba za ta cutu a can ba, ina jin ba za a mata koma a inda ta tafi ba, kuma ba da izini na ta tafi ba, ta bi shi ne saboda ta yi tabargaza”


“Zata cutu, kakana ya fada min akwai wanda zata cutar da ita a gidan, na yi iya kokarin na ganin ya hana faruwar hakan, shi ma ya ki amince min har sai na bi umarnin mahaifina”


“Ba zaka iya rabuwa da ita ba na sani, rabuwa da abun da kake so akwai ciwo sosai”


Zainab ta fada tunawa da yadda ta rasa Auwal, kamin ta zare hannunsa daga nata ta juyo ta shigo cikin falon, binta yai da kallo kamin shi ma ya taka kafarsa zuwa cikin falon. Bayan duk wannan bakincikin hango mata yake wanda zata shiga a gaba.


“Sako na zo na baki...”


Ta juyo har lokacin tana kuka.


“Duk abun da zai sake ta, ki fada musu kar a mata maganin asibiti, musamman idonta kar a taba su, kuma ki bata wannan”


Ya ciro sarewar da yake busawa ya mika mata, sai da ta kalli sarewar ta kalleshi sannan ta tako zuwa inda yake ta mika hannu ta karba.


“Indai har kana sonta da gske, wata rana kai da kanka zaka bukaci rabuwa da ita saboda samun lafiyarta da kuma farincikinta, wani lokacin dole ne mu sadaukar da farincikinmu saboda wanda muke so ya samu farinciki, ba dan haka ba da yanzu na nisanta kaina da Iya, da ni da kaina zan kasheta saboda ta kashe masoyina”


Ta fadi durkushe a gurin tana kuka, gaba daya sai Wasim ya manta da tashi damuwar, tausayin Zainab ya nemi guri a zuciyarsa ya shiga yai lamo. Zuwa yai gabanta ya tsaya yana kallonta.


“Wani lokacin ba ma iya zabe daga kaddarar mu, sai dai kaddara ta zaba daga garemu, da ace zabin kaina ne da Fadime bata kasance a halin da take ba a yanzu, da ace ina da iko da karfin yin wani abu da na canja mahaifiyarki, na dawo da masoyinki kuma na siya miki wani abun, hakan kadai ya ishe ki ishara, ina da tabbaci wata rana zaki samu wanda ya fi saurayin da kika rasa, wata rana zaki nemi labarin Iya ki rasa, wata rana komai zai wuce, yaushe zai wuce? Yaushe komai zai zama tarihi shi ne ba mu sani ba”


Dagowa tai ta kalleshi da hawaye shabe shabe a fuskarta, kamar ta yi magana sai kuma ta gagara ce masa komai, har ya mike tsaye.


“Iya na san kina jina, na san kudirinki akan Fadime, kina da damar ki yi mata yadda kike so, amman tabbas ba zan kyale kowa ba, ina nufin kowa, zan tafi ban sani ba dawowata kusa ne ko nesa, amman tabbas ba zan dawo ba sai idon Fadime sun bude...!”


Ya juya rike da hularsa a hannu ya fice daga falon. Zainab ta mike tsaye da sauri ta isa bakin kofar falon ta tsaya tana kallonsa har ya fice daga gate din Mai Gadi na rike da gate din yana mamakin fitarsa bayan be ga shigowarsa ba.
Lumshe ido tai wasu hawayen suka sauko mata, tausayin rayuwarta take, samun wanda zata so ko ya so ta a yanzu abu ne mai wahala, ba dan komai ba sai dan saboda asalinta. Ta dade a tsaye bakin kofar falon sannan ta juya ta koma dakinta cikin rashin kuzari da walwala.


Iya na cikin dakinta dafe da zuciya, bata samu natsuwa ba har sai da Wasim ya bar gidan, wani irin tsoron Wasim take ba dan komai sai dan tsoron aiken da Babanta yace zai mata, sannan ta san yadda tsafin gidansu yake ba ya haduwa da maye ko kadan. Duk da kasancewar ya fita bata fito cikin dakin ba sai hudu, shi ma saboda Mai gadin ya turo kofar dakin ne yana sallama, sai ta fito ta tsaya daga bakin kofa.


“Waye ne?”


“Hajiya, wai wasu ne suka zo, dogarawa a mota, wai sun ce na sallamo ki”


“Ni”


Ta nuna kanta gabanta na mugun faduwa, ko ba a fada mata ba ta san daga inda suke, sai dai ba kiran ba ne abun tsoro, dalilin kiran ne abun firgitarwa, what if Fadime ta fada musu wani abu ne suka nemi a kirata? Ko dai minene bata isa ta hana kanta zuwa ba, hakan yasa ta share gumin daya karyo mata ta koma ta dauko mayafinta ta fito tana tafiyar kamar bata son fita yadda gabanta yake faduwa sai ka rantse da Allah zuciyarta zata fasa kirjinta ne ta fito, sai da ta kai bakin kofar fita sai kuma ta ji kamar fitsari ya cika mata mara ta juyo ta dawo dakinta da sauri ta shiga bandakin tai fitsari, sannan ta fito cike da tunani kala kala ta fita. Bata raina kanta ba sai da tai arba da dogaran tsaye jikin wata 406 su biyu suna jiranta, abun ka da an saba sai ta sakar musu murmushin karfin hali tana sama gaisuwar da suke mata.


“Lafiya dai?”


“Inshallahu lafiya kalau ne, Jekadiya ta ce mu dauko ki Ammy na son ganinki”


“Ikon Allah Ammy da kanta? Ya akai kuka gane gidan?”


“Jekadiya tai mana kwatanci, duk da haka ma sai da mu ka yi tambaya sannan muka gane”


Dayan ya bude mata kofa sai ta nufi motar ta shiga kamar ba komai, sai dai zuciyarta na ta zillo gumi sai karyo mata yake, babu abun da take hararowa sai Fadime, gashi gidan Sarauta ne asirinta na tonuwa kowa zai ji. Take ta nemi natsuwarta da dakiyar zuciya ta rasa, suna isa cikin masarauta ta sake jin mararta ta cika da fitsari, sai dai bata iya cewa komai ba ta nufi bangaren Ammy tana tafiya kafafuwanta na mata nauyi ga wani uban naso ta da saka fuskarta a gaba. Ta dade a tsaye bakin kofar kamin tai jihadin kai hannunta ta kwankwasa kuma, kamin a bude mata ta share gumi ya kai sau hudu, da ace tana da hawan jinin da tun a lokacin yayi azalinta. Jekadiya da kanta ta bude mata kofar falon, tana ganin Iya ta washe mata hakora tana dariya kamar ba komai.


“Aa Iya har an iso, shigo Ammy ke son magana da ke”


Ta wangale mata kofar dakin, Iya ta yi mata murmushin yake tana cira kafarta ta nasa cikin falon, babu kowa a falon sai tv taku daya biyu Iya ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login