Showing 198001 words to 201000 words out of 273152 words

Chapter 67 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72767

ji wanin abun da ke hana mayu da macizar da aljanu zama lafiya, wato hantiti da tsakin kuka da kuma ƙashi, a rikice ta juya da wani irin sauri ta fice daga falon tana toshe hanci.


“Kai kai yau dakin Ammy ne yake wannan warin haka?”


“Me kika ji?”


Jekadiya ta tambaya tana mata kallon mamaki domin Ammy ta fada mata komai. Tambayar da Jekadiya tai mata yasa ta dawo hayyacinta har ta tuna abun da ta furta, gaba daya sai ta ratsa natsuwarta, ta rika jin warin yana biyota har waje, daman maye baya zama idan irin wannan hayakin yake.


“Jekadiya ki fada Ammy zan je na dawo”


Kamin Jekadiya tace komai Iya ta juya da sauri ta fara sauko kasa sai wani abu take kamar mahaukaciya gaba daya notin kanta ya kwance, duk yadda Jekadiya ta so tsayar da ita sai ta ki saurarenta, gaba daya jin tai bata bukatar zama a cikin gidan ma, sai da ta fita waje ta tari napep ta hau sannan hankalinta ya so ma kwanciya jin ta fara shakar iskar unguwarsu, sai a lokacin ne wani tunani ya zo mata, wata kila Ammy ta yi haka ne saboda ta gasgata zancen Fadime, saboda ta gano idan da gaske ita din mayyace ko kuma a a, kuma yanzu ta san dole ne zata yarda tun da har ta kasa shiga cikin falon balle har ta isa dakin Ammy.
Wani irin bakinciki da bacin rai ne ya kusanceta, bakincikin da ko mutuwa bata kai shi ɗaci ba a gurinta.


“Ammy ta yi haka ne saboda ta gane ko?”


Ta furta a fili tana jin wani tukikin bakinciki na ta so mata. Mai Napep din ya juyo ya kalleta a zatonsa ko magana take masa ne, sai kuma ya ga wani gurin take kallo rai a bace. Kunya ta zame mata biyu, ga ta abubuwan da ta aikata wanda ta san izuwa yanzu Fadime ta fada musu komai ga kuma wata karin kunyar kasa shiga falon Ammy da tai.


“Ba ki tabbatar ba, yanzu zan tabbatae miki, kin yi wauta na kokarin kama ni ta wannan hanyar, dole ne na yi abun da zai dauke mu ku hankali kuma kamin a kara wani abun ya kamata wannan kam na zanja salo”


Wannan karon a cikin fai furucinta tana sauke kafarta kasa daga kam Napep din.


“Hajiya kudinki 500 ne”


“To jira ni ina zuwa”


Ta juya ta shiga cikin gidan domin bata fita da komai ba, kana ganin tafiyarta kasan ba lafiya ba kamar an korota haka ta shiga cikin falon ta, ko ta can Zainab dake kwance kan doguwar kujera tana waya bata bi ba, ta wuce dakinta ta dauko jakar kudinta ta ciro 1k ta fita sai sauri take kamar zata tashi sama.
Bata ma isa gate din ba ta kira mai gadi ta mika masa kudin.


“Ka bawa mai Napep yana nan waje, ka karbo min canjina”


Yana karbar kudin ta juyo da sauri ta dawo cikin gidan. Fuuuu ta wuce dakinta Zainab dai sai binta take da kallo, da ada ne zata iya tambayarta mi yake faruwa amman a yanzu iyakarta da ita ido, duk da tana ganinta cikin rashin natsuwa.


Iya na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe, ta zauna bakin gadonta tana mamakin abun da Ammy ta shirya mata.


“Tun farko ita ya kamata ace na fara kamawa, da yanzu bata samu damar yin wannan abun ba, na yanzu tana can kwance tana jinya kamar mijinta, amman saboda na kyale ta har ta samu damar yi min haka? Ta tona min asiri a cikin Masarautar nan?”


Ta mike tsaye tana jin kamar ana sukanta a zaunen da take.


“Ko da yake ba laifin Ammy ne kadai ba, har da laifin yarinyar nan Fadime? Amman na san maganin abun”


Ta fada zuciyarta na raya mata ta yanke kurwar Maijidda tun a yanzu ba sai biki ya matso ba ko kuma an yi aure kamar yadda take yi ma sauran, domin idan tai tun a yanzu babu wanda zai zargeta kuma hankalin Ammy zai koma a can, sannan bata san abun da aka shirya mata ba a nan gaba.








FADIME POV.


Wata hadimar ce ta shigo falon da su Bappa suke tana sinne kai kasa ta ce.


“Shattima ya turo na tafi da Fadime idan kun kallama”


“Ki tafi da ita ina zaki kaita?”


Bappa ya tambaya, kamin hadimar ta amsa Fadime ta mike tsaye tana fadin.


“Cikin gida can gurin matar sarkin, ai a can nake zaune”


“To yayi kyau, kuma idan kin je ki yi musu shirme da kika saba, Wallahi ki kwantar da hankali ki san irin abubuwan da zaki fada ko ki yi, kina yin wasa Wallahi za su daure ki, kuma Wallahi kin dauro har abada, dan sarki babu ruwansa da makantarki”


“Bappa wai sarki ne babba?”


Fadime ta tambaya jin yadda Bappa yake tsoratata.


“Sarki ne babba, garin Yola fa gaba daya, kamar ace sarkin Katsina”


Ta zaro ido tana jin wani irin kimar Shattima da kwarjininsa suna kankwaro mata, sai a yanzu ta gane ya sarautarsu ta ci uban ta su Wasim da take gani da girma, sai a yanzu ta gane dalilin da ya saka baya son yawan magana kuma yake dadewa kamin ya bata amsa wani lokaci.
Ta mika hannunta ta inda take zaton hadimar na gefen.


“Mu tafi”


Hadimar ta kama hannunta suka fice daga falon Bappa sai nanata mata yake ta bi a hankali da yaren fulatanci. Suna tafiya Fadime na tuna abubuwan da suka faru tsakaninta da Shattima, ita ma ai ya kamata ta gane babbar Sarauta ce tun daga jin gidan sama da suke da kuma yadda suke da yawan hadimai, kuma ga sanyi ac da kayan dadi a ko'ina.
Har cikin fadar Ammy Hadimar ta shiga ta ita sannan ta saki hannunta.


“Ina za ki je?”


Bata samu damar amsa mata ba sakamakon hannun da Shattima ya daga mata sai tai saurin ficewa ta tare da tace da Fadime komai ba.


“Ke ina kika kawo ni”


“Wani guri”


Ta ji muryar Shattima daf da ita, shiru tai kamar ba ita ba tana jin girmasan da kwarjininsa na kamata, sai ta ji ta kamar yar wata kudan zuma a wata duniyar babbar duniya, gabanta ya shiga bugawa da karfi abun da bata saba ba.


“Kin ga Babanki?”


“Eh Ranka ya dade”


Ya wara yana murmushi.


“Ni ne ranka ya dade a yau kuma?”


“Dan Allah ka yi hakuri da duk abubuwan da na yi maka”


Ya juyo da ita tana fuskantarsa duk da kasancewar bata ganinsa.


“Me kika min?”


“Abubuwa da yawa ba za su kirgu ba”


“Baki min komai ba, na san ai ba ki san komai ba, kuma ko kin sani rayuwarki ki simple ba lallai ne komai ya burge ki ba”


Shiru tai ta natsu sosai tana saurarensa kamar ba ita ba.


“Ina son nai miki sallama ne, na siya muku ticket jirginku zai tashi 7am ba lallai ne na shigo gida kamin lokacin ba, so i wanted to say goodbye”


Ta yi shiru tana wani abu na rashin jindadi yana ziyartarta duk da kasancewar tana son gida kuma tana son kasancewa tare da Bappa da Inna da kauyenta, sai dai a yanzu da Shattima yai mata wannan maganar sai ta ji kewarsa da dan sabon da tai tare da Nana ga dadin da take ci kullum.


“Ranka ya dade, yanzu shikenan ba zan sake ganinka ba?”


Ya lakace hancinta yana murmushi.


“Daman kin gan ni ne?”


“Ina nufi ba zan sake jin muryarka ba?”


“Yes ni ma ba zan sake ganinki ba, zai je ki cigaba da rayuwarki kamar yadda kika saba, kuma i hope idonki zai bude soon i mean very soon”


Ta kasa cewa komai sai saurarensa take tana jin kamar ta fashe da kuka. Ya cire agogon hannunsa ya kama hannunta ya saka mata.


“Ga wannan ki rika tunawa da ni, ban taba haduwar da macen da na ji bana son rabuwa da ita ba irinki, tun a ganin farko da na yi miki a Katsina kika kwanta min a rai, to be frank komai na ki yana burgeni i like you”


Ya fada yana kallon cikin idonta dake cike da kwalla. Ya dade yana kallonta kamin ya kai bakinsa saitin kunnenta ya rada mata.


“Bye Allah ya tsare hanya”


Lumshe ido tai hawayen idonta suka sauko, kashe kunne tai tana sauraren sawun kafarsa har ya fice daga falon, sai ta rage tsawonta ta zauna a gurin ta share hawayen da bata san dalilin zubarsu ba. After like 5 min ta ji sallamar Jekadiya ta shigo gurin sannan ta kama hannunta.


“Ta so mu je yace za ki yi ma Ammy sallama, sai na maida ke daki”


Fadime ta mike tsaye tana jin kamar a barta tai ta zama a gidan duk bata iya shaidar fuskar kowa a gidan saboda bata gani. Babu abunda take sai saurare har suka isa dakin Ammy, tana Jekadiya ta rage tsawo ita ma ta rage ta zauna kasa.


“Ammy Shattima ne ya ce na kawo ta ta yi muku sallama”


Ammy dake kishimgide ta dago tana dubanta tare da cire gilashin idonta tana murmushi.


“Yarinyar mai abun al'ajabi, ki zo mana da abubuwa zuwanki ya zama mana alheri, yaushe za ku tafi?”


“Gobe ya ce, da karfe bakwai za mu hau jirgin sama”


“Yayi kyau Allah ya tsare hanya, kamin ku tafi Jekadiya zata ba ki tsabarki”


“Na gode ranki ya dade Allah ya saka da alheri”


“Godiya take, godiya take Ammy Allah kara miki lafiya”


Jekadiya ta fada da dariya sannan ta sake rikon hannun Fadime suka fito daga dakin. Dakin Nana ta sake maida ita, dakin da take komai a ciki wanka abinci canja tufafi duk a dakin take, Nana ta bata kusan kala biyar duka sabon kaya da zata rika canjawa idan ta yi wanka.
A dakin ta wuni, abincin ta na dare ma a dakin aka kawo mata, sai dai bata wani ci da yawa ba, kadan ta ci ta bar sauran, ta tashi da kanta ta shiga bandaki ba tare da ta yi addu'a ba, daman can addu'a bata dame ta ba, tana tura kofar bandakin ta shiga sai ta ji wani irin iska da yanayi kamar ba a bandaki ba, juyowa tai ta zimmar fitowa sai ta ji ta taka abu kamar titi juyowa ta sake yi ta taka gaba sai ta sake jin abun, ta kara yin baya sai ta sake jin abun. Can kuma ta ji wani irin kara ya cika mata kunne gashi bata ganin komai sai duhu, tsaye tai a gurin kamar an dasata. tana ta sauraren karar da bata san ko na minene ba, sai dai tana jin sautin kamar ya mata yawa a kunne, can ta soma jin sautin bugun wani abu kamin ta fara jin sautin muryar mace.


“Lalalala...lafiya ...kika tsaya a tsakiyar titi?”


“Titi”


Fadime ta maimaita tana juyo ta inda take jin sautin muryar matar, kamin matar ta sake magana mijinta ya karaso ya jata ya maida bayansa da dayan hannunsa yayinda dayan yake rike da jariri.


“A ina nake?”


Ta tambaya tana jin kamar ta taba jin abun da ake kira da titi. Matar ta kalli mijinta mijin ma ya kalleta.


“Bana ganin komai sai duhu dan Allah a ina nake?”


Fadime ta sake tambaya, sai matar ta waiga tana karewa unguwar dake cike da haske a ko'ina kamar ba dare ba.


“Daga ina kika zo nan? Waya kawo ki nan?”


“Ni ma ban sani ba, ban sani ba”


Ta fada hawaye na sauko mata.


“Ya sunanki?”


“Ban sani ba, ya sunana to?”


Ta dafe kai.


“Miyasa na ake jin kaina kamar ba komai ciki? Miyasa bana ganin komai sai duhu a ina nake?”


Ta fashe da kuka ta durshe a gurin. Matar ta kalli mijinta cike da tausayi.


“We need to help her”


Wani kallo yai mata na mamaki, kana ganinsa kasan irin miskilan mazan nan ne da magana ke musu wahala.


“Aliyu bana son na ga mutum a cikin damuwa ban taimaka masa ba, na san yadda ake ji, ni ma babu irin wahalar da ban sha ba kamin rayuwa ta kawo ni a nan, har bara na yi, ko ka manta? Babu irin wahalar da ban yi ba babu irin wulakancin da ban gani ba, bana son na ga wani a cikin damuwa na kasa taimaka masa”


Dauke kai Aliyu yai ko kadan baya son tunawa da halin da matarsa ta shiga a baya, domin har yanzu yana ganin shi ne silar komai saboda dashen kodar mahaifiyarta da akai ma matarsa uwargidansa, his late wife Rahma.


“Fine idan kuma ba mutum ba ce ba? Ataa think please”


Ya fada kamar ana matso maganar daga bakinsa.


“Daga gani mutum ce, aljana ta yi wuri ta fito mana haka, ko isha'i fa ba a gama ba wani gurin, idan mu ka tafi muka bar ta nan zata sha wahala kamin ta samu taimako, ka san unguwar nan fa kowa na cikin gidansa, kamin ka ga wulgawar mota ma aiki ne, ko ma dai wacece mu da zuciya daya zamu yi mata taimako, Allah ba zai bata ikon cutar da mu ba”


Kallonta kawai yake yana gyara takwaransa dake kafadarsa. Sai ta saka hannayenta biyu ta rike kunnenta.


“Please Hamma na....”


Uffan be ce mata ba, daman can kowa ya san Aliyu ya san magana ma wahala take masa, juyawa yai ya koma gurin motar ya bude mata back seat alamar ya aminta kenan.


“Yauwa dan wajen Mama Fulani i love you”


Cewar Ataa tana dariya, shi kuma sai yai murmushi ya zagaya side dinsa. Ataa ta leki fuskar Fadime.


“Ta so mu je”


Fadime ta dago tana kallon Ataa kamar tana ganinta.


“Su waye ku?”


“Ni sunana Aisha amman ana kirana Ataa, mijina kuma sunansa Aliyu, cutar ki zamu yi ba taimakonki zamu yi”


Yunkurawa tai ta mike tsaye sai Ataa ta kama hannunta suka nufi gurin motar, sai da tai addu'a sannan ta saka ta a motar ta rufe, ta bude front seat ta shiga ta zauna.


“Ka wo Haidar din”


“Kyale shi bachi yake”


Ya fara tuki da hannu daya yana fadin.


“Za mu fara zuwa police station”


“Why? Ni fa ka san na tsani police, saboda Doc Asim mutanen nan suka rufe ni a cell kwana na biyu a ciki, bayan kuma ni ke da gaskiya, sanadin haka na rasa Lukman the one and only brother da nake da shi”


“Miyasa kike ta kokarin sai kin tuna min da abubuwan da suka faru a baya ne Ataa? Kin san zafin da nake ji? Yanzu ai komai ya wuce ya kamata ki manta”


Ta furta cikin muryar da ke nuna ransa ya bace, kallonta ta kwantar da kanta jikinsa.


“Im sorry”


He kiss her front head sannan ya cigaba da tukin. Lokaci zuwa lokaci take juyawa ta kalli Fadime da ke bayan motar duk da bata ganinta sosai saboda duhun motar sai dai ta gane kuka take saboda yadda take ja majina.
Fadime dai sai hawaye take tana ta sauraren tafiyar motar da take jin kamar ta taba jin irinsa amman ta kasa tunawa idan tai kokarin zurfafa tunaninta sai ta ji kamar an mata yaki a cikin kai.






___________


Ba mu da nepa jiya shiyasa ban samu na yi typing ba. Sai yau da safe aka kawo I'm sorry.




_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*








Ta yi shirin bachi cikin kayan bachinta ba dan tana da tabbacin bachin zai dauke ta ba, sai dan ya zame mata al'ada saka kayan bachi a kowa ne dare. Kwance take a dakinta hannunta rike da waya tana ta kallon sakwannin dake shigowa ta kasa amsa ko daya kuma ta kasa kashe datar gaba daya duniyar wani irin take mata, tun daga lokacin da abubuwan da suka faru suka faru ta saka komawa daidai kamar da. Har kusan 10:30pm bachi be dauke ta ba, sai da ta gaji da rikon wayar ta kashe data ta aje tana kokarin sauka ta leka bandakinta ta ji karar bude gate, hakan yasa ta nufar windows dakinta ta bude lalulen ta leka waje, sai ta hango mota ta shigo cikin gidan, kamin tai tunanin komai Jekadiya ta bude ta fito tare da dogarai. Barin jikin window tai ta bude kofar dakin ta fito falo kamin ta karasa gurin kofar ta bude har gabanta ya soma faduwa, domin ta san ba lafiya ba, ganin Jekadiya a irin wannan lokacin cikin gidanta. Jekafiya na kai hannu ta kwankwasa Zainab ta bude kofar.


“Lafiya?”


“Ba lafiya ba, Shattima ne ya turo mu bincika wata yarinyar Fateema makauniya”


“A nan?


Ta tambaya da mamaki, Jekadiya bata sake ce mata komai ba ta kunno kai cikin falon, mutanen da take tare da su ma suka shigo kowa ya hau aikinsa, har karkashin kujerun falon sai da Jekadiya ta leka duk da tana da tabbacin ba za ta iya boya a gurin ba. Zainan dai na tsaye tana kallonta da mamaki da kuma tunanin inda Fadime ta tafi, wata kila ta sake bin wani ko kuma ta fito gurin karanbaninta wani yayi gaba da ita. Iya ma fitowa tai bakin kofar dakinta ta tsaya tana kallon ikon Allah ba dan ta ji Fadime ake nema ba da tace bincike aka zo mata, ita kanta mamakin yadda akai Fadime ta bata take. Sai da suka bincike dan madaidacin gidan kaf har da harabar ba su ga wani alama na an boye mutum ba. Sai da za su tafi sannan Zainab ta biyo bayan Jekadiya tana fadin.


“Jekadiya ki fadawa Shattima idan an ga yarinyar, Wasim ya ce kar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login