Showing 93001 words to 96000 words out of 273152 words

Chapter 32 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72748

domin idan wutar ta motsa mata ta laso mata zuciya sai tai ta barin zance.


“Ku ce wacan mutumen ya yafe min dan Allah, Wallahi ba zan sake ba, jama'a wuta a cikina, na ci Tanin na ci Murja yar gidan Almajiri, daga na aike ta na tankwashi kanta na kama kurwarta na cinye ta, na ci yar gidan Hajiya Ayawa ta birni na kama mai gadinsu, kurwarsa na cikin dakina”


Kusan duk wanda ta ci ko ta kama sai da ta fada, ta saka hannu biyu ta dafe cikinta sai kuka take, idan tai yunkuri kuma sai aman jinin. Sosai mutanen da take fadar ta ci yayansu suka so afka mata da duka Dattijawan da suke gurin suka hana, Wani makocinsu ne ya hau babur dinsa dan zuwa fadawa Bappa halin da ake ciki. Ba iya mutanen da ta ci ba har mutanen da suke maitar tare sai da Amo ta fada. Hajjo na tsaye ta rasa inda zata saka kanta sai kuka take.


“Kaka ta bawa uwata Maitar nan, uwata ta ba ni, ni kuma na bawa tun da ban haifa ba? Yau na yi leke na ga mugun abu, wuta ce a cikin tana ta ci kun ganta”


Sai nunawa mutane cikinta take tana ta tarin jini, kowa sai matsawa yake nesa da ita.


“Ina zama mage ina zama doki har kadangare ina zama, ina zama jaki ina zama bakin kare, idan dare yayi a filin can nake rawa, jama'a wuta a cikina”


Ta karasa a galabaice. Inna dai na tsaye tana kallon ikon Allah hawaye sai zuba suke mata, bata jin dacin wata magana kamar wacce ta ji daga bakin Amo ba a yau, ta cinye mata ɗa tara, saboda ita bata taba haihuwa ba bata san zafin haihuwa ba, ka dauki ciki wata tara ka haihu, wasu ta yi rainonsu wasu kuma tun suna kanana suke mutuwa, ko da rana daya Amo bata tausaya mata ba Fadime ma dan ta gagareta ci ne.
Juyawa Inna tai ta koma cikin gida tana jin wani irin zafi da bakinciki a ranta, uwa ce kadai kan iya labarta yadda bakinciki rasa da yake, balle ita data rasa yara har tara, zaunawa tai a kujerar dake tsakar gidan ta fashe da wani irin kuka, ta sani ko da zata yanka Amo a yanzu ta gasa namanta, ta soyata ba yaranta ba za su dawo ba, kuma ba zai goge bakincikin dake ranta ba. Tun ba yau Inna ta dade tana zargin Amo da maita tun a wani lokacin da suna fira take fada mata suna da maita gado ga kuma mafarkai da take kala-kala akan amman bata taba tabbatarwa ba sai a yau da idonta ya gani zahiri, hannu ta saka ta dafe zuciyarta tana jin wani irin zafi a kirjinta, ta haifi yara goma sai Fadime ce ta tsaya, kuka sosai Inna take tana ayyana yadda wasu yaran suke mutuwa a hannunta da irin azabar da suke sha kamin su mutu, da kuma ita ma irin wahalar da take da wasu. Shigowar wasu makotan ne yasa ta tsagaita kukan da take tana jin wani irin son Fadime na kara fadada a kirjinta ganin ita kadai ta rage mata a rayuwa.


“Ki yi hakuri Allah ya saka miki Allah ya isar miki”


Shi ne mafi yawan abun da mutanen ke fada, ita kam ta kasa ce musu komai, kukan kawai take hawaye na mata zuba domin ita kadai tasan zafin da take ji a ranta. Da yamma lis, Bappa ya iso, shi ya riko Amo ya shigo da ita cikin gidan, kana ganin fuskarsa kasan babu walwala a tare da shi, domin ko baka son mace baka son ta fita waje daga ita sai dan kanfai balle matarka ta sunna ga kuma tonon asirin da take ta yi ma kanta. A tsakar gidan ta fadi tana ta ihu har lokacin ta kasa dawowa hayyacinta tana ta faman rikon ciki tana fadin wuta, har kamo hannun Hajjo take tana kaiwa a cikin nata.


“Allah ka yafe min na tuba Allah, ba zan kara ba, wayyo wuta wuta a cikina na shiga uku, Fulani ki yafe min ki ce masa na bari”


Babu irin tambayar da Bappa be mata ba ina ta samo ciwon me ke damunta? Amman ta kasa bashi amsa sai fadin take wuta a cikinta domin bata cikin hayyacinta. Can ya koma gurin Fadime ganin tana ta ambatar sunanta.


“Ke kin san wani abu ne?”


Fadime ta yi saurin daga hannunta sama.


“Aa ni ban san komai ba, Allah ya tsare”


Yadda tai da ido sai ka rantse da Allah bata san komai ba, bayan labarin na kasan halshenta, sai dai tana tsoron fada kar ta sha duka gurin Bappa.
Bappa fita yai daga gidan gaba daya ya koma can gefe ya kira wani Kawunta bugu biyu ya dauka.


“Assalamu Alaikum Kawu Manu”


“Wa'alaikassalam, Sama'ila ya gidan ya kowa?”


“To Alhamdulillah, Kawo ina bukatar ganinka yanzu idan kana da dama ka zo dan Allah”


“Lafiya dai?”


“Lafiya amman ba lau ba ka daure ka zo dan Allah”


“Dare ya fara yanzu haka na yi alwala sallah magariba, indai ba wata matsala ce babba ba ka bari har gobe biyo mota na zo”


“Aa ka zo dai yanzu Kawu”


“To shikenan idan mun gama sallah zan kamo hanya yanzu”


“To Allah kawo ku lafiya”


Bappa ya sauke wayar daga kunnensa tare da sauke ajiyar zuciya, sam be ji dadin abunda ya faru ba sai dai be isa ya hana komai ba, ba tun yau Inna ta dade tana masa maganar zargin da take na Amo shi kansa ya dade da sanin abun da take sai dan gudun kar ya budewa Inna da take kishiyarta da kuma sauran mutane damar fada ko aikata wani abu yasa be taba nuna yana zarginta ba idan ma Inna tai sai ya kwatsuleta saboda be taba gani da idonsa ba, sai dai irin tonon asirin da tai wa kanta a yau da kuma fadar irin mutanen da ta ci ya canja masa tunani, an labarta masa komai tun kamin ya iso bayan ya iso kuma ya ga komai a idonsa. Dawowa yai cikin gidan a lokacin Inna na tsugune tana alwala Fadime kuma na zaune gefen bukkar Inna ta rafka uban tagumi tana kallon Amo dake ta dalalar da jini a baki ta rike ciki sai kuka take muryarta ma bata fita. Inna sai da ta gama alwalarta sannan ta zubawa Bapppa ruwa a butar ta kawo gabansa ta aje, fuskarta kawai yake kallo yadda idonta ya kumbura kana ganin kasan ba karamin kuka ta sha ba.


Shi kansa da yake uba abun be masa dadi ba balle kuma ita da take uwa ta san zafin daukar ciki da haihuwa. Bukkarta ta shiga ta dauko tabarma ta shimfida waje ta saka hijabinta ta fara sallah magariba. Fadime na ganin haka ta tashi itama ta dauki wata karamar buta tai alwala ta shiga bukkarta ta dauko hijabinta ta saka ta tsaya kusa da Inna ta kabbarta sallah.


Daga garin Dan-isa zuwa garin Bandalo tafiyar awa daya ce har da yan mintuna a mota, balle kuma su Kawu Manu da suka hau babur din dansa suka kamo hanya saboda babu motar da zata je garin Bandalo a yanzu. Tara saura kwata suka iso garin, ba shi da aka kawo ba har dansa daya goyosa a babur din zullum abun da za su ji ko su tarar yake, sun sani duk abun da zai saka Bappa ya nemi ganinsa ba karamin abu ba ne a matsayinsa na uban daya rage ma Amo a yanzu. Ko da suka iso Bappa na tsaye bakin kofar gidan tare da wasu abokaninsa biyu, sai da ya mika musu hannu suka gaisa sannan yai musu iso.


“Kawo Manu Bismillah”


Bappa ne a gaba Kawu Manu na bayansa tare da dansa suka shiga cikin gidan, tun kan Bappa ya labarta masa komai ya fahimci ba lafiya ba, ganin Amo a tsakar gidan Hajjo na gafenta tana kuka, Inna da Fadime kuma suna kan tabarma zaune fitilar aci balbal na gafensu. Amo na ganin Kawu Manu tai saurin mikewa tsaye ta nufo inda yake tana fadin.


“Kawu ka fada ma Fulani ta fada masa na daina dan Allah ta cire min wutar nan, ba zan sake maitar ba zan daina Wallahi”


A take gumi ya karyo masa, ya juya ya kalli Bappa sai kuma ya saka hannunsa aljihu ya haska Amo, gaba daya ta fita daga kamaninta ta canja kamar ba ita ba ga wata uwar ramar wahala da tai har lokacin kuma idan tai tarin sai jini ya fito ta bakinta, sai wani leko halshe take waje tana zaro ido kamar sabuwar mahaukaciya, tun da take a rayuwarta bata taba shan wahala ko shiga jalala irin wannan ba. A tsanake Bappa ya labarta Kawu Manu komai sannan ya dora da cewar.


“Ban san abun da ya faru ba, Aisha ta fada min cewar daga bandaki ta fito wahale tana ta aman jini tana ihun wuta a cikinta kamin ta fara tonawa kanta asiri, daman kuma ba tun ba na dade da fahimtar abun da Amo take yi, sai dai ba ni da hujjar fadin hakan saboda ban gata ido da ido ba, amman yanzu ita da kanta ta tonawa kanta asiri”


Kawu Manu ya gyara tsayuwarsa yana kallon Amo kamin ya haske Fadime da fitilarsa mai shegen haske.


“To ita wannan da take ambatar sunanta bata san komai ba?”


Inna kamar tana jira ta mike tsaye tana nuna shi da yatsa.


“Kurwar Fulani kur Wallahi sai dai ku ci kanku, kuma duk abun da Amo tai min na bar ta da Allah shi zai saka min”


Inna ta karasa cikin kuka tana jin wani irin zafin a ranta, wani murmushi Kawu Manu yai ya tabe baki har lokacin fitilarsa na haska Fadime.


“Inna ki yi shiru, Allah shi zai saka miki Allah ya isar miki”


Fadime ta fada tana sharewa Inna hawayenta, ita kuma tana wasu hawayen ganin zubar hawayen Inna yasa ta ji wani irin no matter how mother is ɗa ko ƴa baya son ganin kukan uwarsa, ganin yadda yake ta kallon Fadime yasa Inna ta mai ita bayanta.


“Fulani bata ciyuwa Wallahi sai gani sai bari, kurwarta kur mugun abu ya bi dare ku ga abun ku a kanku”


Wani dogon numfashi Kawu Manu ya sauke sannan ya juyo yana kallon Bappa.


“To yanzu ya ake ciki? Kai kana ganin wannan abun da take yin kanta ne?”


“Kawu ga zahiri kana gani, shiyasa na kiraka ka zo ka tafi da ita”


Cewar Bappa, sai Kawu Manu yai wani murmushin takaici.


“Ka kyauta Sama'ila, duk yadda ake ka yi, Allah ya saka maka da alheri, ke kuma ki jira sakamakonki”


Ya karasa yana haska Inna d Fadime, sannan ya kama hannun Amo.


“Ba ni da sakamako sai alheri, sherinka ya bika, ka ga mugun abu kai da yarka can mukan alheri zamu gani da yardar Allah”


Uffan be sake ce mata ba, yana dai rike da hannun Amon har suka fita, sai da dansa ya fara hawan babur din sannan ya dora Amo a baya, hajjo ta hau sannan shi ma ya hau a baya suka kama hanyar garin Dan-Isa.








FALMATA POV.


Sai da suka yi bachi sannan ta fito daga dakinsu, a falo ta samu Ammy da Jekadiya da kuma wata bakuwar suna gaisawa, har inda Ammy Falmata ta karasa ta risina kasa ta kwashi gaisuwa sannan ta mike tsaye ba tare da ta ji amsawarta ba, daman ba amsarwa take jira ba ita dai muradinta ta gaishesu ta tafi gida ganin dare ya soma yi sosai gashi a kafa zata je, sai ta fito waje ta kara tsinkewa ganin hadari ya hada ko'ina a garin iska sai kadawa yake. Cira kafa tai tana kallon sama gabanta ya fadi yadda hadarin ya hadu yana da wahala ta iya isa gida ba a sako ruwa ba. Ta baro gate din gidan sai ta tsinci kanta ita kadai a unguwar sai wata mota dake can gefen titi a fake, arzikinta daya unguwar manyan mutane ce ko'ina a haskake yake kamar wani gurin taro. Daga nesa aka dallo mata fitilar motar dake fake har sai da ta tsaya cak sai kuma aka kashe, aka sake dallo mata aka kashe sosai hakan ya firgitata wanda ya saka har ta juyawa ta waiga bayanta tunanin komawa take a masarautar, ganin hakan yasa Sirleem ya bude motar ya fito ya nufo inda take tsaye, tun kan ya karaso ta gane shi, hakan yasa ta dan ji sanyi har tai kokarin daidaita natsuwarta. Kallon mamaki yake mata tun da ya hango ta ta fito daga masarautar ya gane ta, sai dai mamakinsa me ta zo yi a nan? Ko wani take nema?


“Uhmmm”


Ta furta yana nunata kokarin tuna sunanta yake amman ya kasa.


“Me kika zo yi nan?”


Ganinta tana ta Kallonsa ba amsa yasa ya tuna cewar bata ji sosai, sai ya matsa kusa da kunenta.


“Me kike a nan?”


“Aiki nake yi”


“A ina?”


“A gidan Mai Martaba”


“Aikin me?”


“Raino nake ina kula da wasu yara”


“Oh ke kike kula da yaran Shattima kenan”


Ya fada da sigar da ba zata ji yana dan mamaki. Kamin ya sake kai bakinsa a kunnunta.


“Kike kaiwa dare haka ba ki jin tsoro”


“Ina ji su suka ce ba zan tafi ba sai yaran sun yi bachi”


“Kasa kike tafiya?”


Ta daga mishi kai, sai ya ji tausayinta ya kara kama shi, as her age ace tana bin hanya zuwa gidansu a kafa kuma a irin wannan lokacin.


“Babanki ya san kina aikin nan”


Wannan karon ta sigar da zata ji yai mata tambayar, sai ta daga masa kai ta maida idonta kasa tana ta wasa da hannayenta cikin hijab dinta.


“Kuma ya aminta ki kai irin wannan lokacin a waje?”


Nan ma kan ta daga masa tana kallon hadarin dake haduwa a garin.


“Ina ne unguwarku?”


“Unguwar madinka”


“Muje na sauke ki”


Yana fadar hakan be jira cewarta ba ya juya ya nufi inda motarsa take fake, ita kuma ta bishi a baya tana masa kallon mamaki, a iya yadda ta fahimta ko kadan Sirleem be da rayuwar wulakancin ko kyamar mutane ba kamar sauran celebrities ba.
Tsayawar da yai yana magana da Falmata yasa ran Mansura daya baro a mota ya bace, gashi tana hangensa sai kai bakinsa yake kunnen Falmata zuciyarta sai tafarfasa take kamar zata fasa kirjinta ta fito, tana ganin sun doso motar ta bude ta fito tai tsaye hannunta rike da ganbun motar. Sirleem na iso gurin motar ya budewa Falmata back seat.


“Zo ki shiga nan”


Kamin Falmata ta karasa Mansura ta daka mata wata muguwar tsawa.


“Keeeeeee!”


A zarane Falmata taja ta tsaya tana yi ma Mansura kallon tsoro, ba kasafai take jin komai ba amman ta ji wannan tsawar da Mansura tai mata cikin daga murya.


“Ban gane ta zo ta shiga ba, ashe Sirleem kana tare da yarinyar nan biyoka take har gida... Amman ni yanzu ka gama fada cewar kar na sake biyoka gida, amman ita har cikin gidanku take shiga”


“Ba abun da kike tunani ba ne, I'm just helping her”


Ita ce amsar daya bata cikin natsatsiyar murya yana kallonta da manyan idonsa masu kyau da haske. fashewa Mansura tai da kuka akan Sirleem bata ji zata iya saurara ko wace mace balle kuma Falmata da a sanadinsa ya santa.


“Zo ki shiga”


Sirleem ya fada yana kallon Falmata wacce ta tsaya kallonsu duk kuwa da bata jin abun da suke fada amman ta san fada suke. Kai ta girgiza masa da mugun tsoro.


“Aa zan tafi a kafa...”


Tana rufe baki aka fara saukar da yayafin ruwan sama, barin jikin motar Mansura tai tana kallonta.


“Shiga”


Ta fada a tsawace, ganin hakan yasa Falmata ta nufo motar da zimmar shiga, kamin ta karasa Mansura ta rika kanta ta buga da murfin motar na front seat iya karfinta, wani irin mahaukacin ihun Falmata ta saka tai baya da sauri ta fashe da wani irin mahaukacin kuka.


“Baki da hankali Mansura me yake damunki? Taya za ki cutar da innocent girl, miyasa kike abubuwan hauka wai?”


Cikin wani irin tsawa da fusata yake fadawa Mansura haka jinin zuciyarsa na wani irin zillo, domin ba karamin baci ransa yai ba. Yadda yake jin tausayin Falmata da ace ba Mansura ce ta taba ta da sai ya dake ta ko waye kuwa. Falmata kan firgicewa tai ta fara tafiya tana kuka ga ruwa ya fara sauka da karfinsa, cira kafa yai yai hanzarin cin mata ya riko hannunta.


“Zo nan a duba miki”


Da sauri ta girgiza masa kai tana kuka duk da bata ji abun da ya fada ba.


“Aa aa a kafa zan tafi”


Be bi ta kanta ba ya rike hannunta ya nufo motar da ita, da kansa ya saka ta a motar ya rufe ya zagaya dayan bangaren yana yi ma Mansura wani kallo na bacin rai.


“Wallahi kika sake cutar da wani akaina sai na baki mamaki”


“Ba ni da hankali akanka Sirleem kai min duk abun da zaka min, amman ba zan lamunci ganinka da wata mace ba, kuma Wallahi idan baka rabu da yarinyar nan ba sai na kasheta”


Uffan be sake ce mata ba, ya bude motarsa ya shiga tana ganin haka ita ma ta shiga front seat din ta rufe motar tana ta kuka, kamar Yadd Falmata ma take ta kuka tana jin goshinta na mata wani irin zugi na bala'i ga jini sai zuba yake, gaba daya a firgice take har wani zazzabi take jin yana kokarin rufe. Key yai ma motar ya hau titi har ya isa wata silent unguwa be kalli inda Mansura take ba, gaban wani madaidacin gate ya faka sannan ya juyo ya kalleta.


“For the very last time kar na sake ganinki kofar gidanmu ba tare da izinina ba, and ki shiga hankalinki i won't tolerate nonsense”


“Ka kira abun da nai da nonsense? Fine, idan baka rabu da yarinyar nan ba sai na kasheta Wallahi, Wallahi zaka jama mata bala'i”


Ya karasa cikin kuka sannan ta bude motar ta fita tana haki. Sosai Falmata dake bayan motar ta sha jinin jikinta tsoro ya gama kamata, duk abun da Mansura ta fada ta ji saboda ta fada a fusace ne da kuma muryar da Falmata zata iya ji. Sai ta fashe da sabon kuka jikinta sai kyarma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login