Showing 147001 words to 150000 words out of 273152 words
Chapter 50 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
karasa tana mere baki, Momy ta kalleta da mamaki domin ta manta da ta taba mata maganar.
“Dashe kuma? Uhm Hajiya Umaima kenan, ni ai na watsar da wannan alamarin tuni”
“Aa fa Zaliha, ni ba abokiyar da za a boyewa sirri ba ce, kin san mun saba kashewa mu binne babu wanda yata taba ji, kuma na san kin taba min wannan maganar”
“Eh kuma daga baya na zafafa bincike sai nake ganin kamar be dace ba, malamai ma suna fadar yin hakan yana da illa gaskiya”
“Ke ba wata ila, idan kika biye malamai ai ko azumi sai wani yace be dece ki yi ba, ke a yadda kika cikin halin nan kuma kina bukatar haihuwa har dama ta same ki haka ki yi wasa? Haba dai Zaliha, kowa fa yana son haihuwa musamman ke da shekaru suka fara ja, sannan ga gorin yan'uwan miji, sai ki mutu shikenan ba ki da copy nunawa? Mijinki dai na san ba zan hana ba tun da shi ma yana son ki samu haihuwar, kuma ke fa likita ce kin san yadda zaki yi abun nan”
Momy ta nisa duniyar tunani tana sauraren kalaman da Hajiya Umaima take mata.
“Amman irin wannan abun yana da matsala Umaima, saboda yana bukatar sirri kuma yawan idan akai wasu za su yi amfani da damar ne su rika tasar kudi a hannunka ko su maka barazanar tona asiri”
Hajiya Umaima ta tabe baki.
“Ita wannan karamar yarinyar kike tunanin zata iya miki wannan? Kuma ai be zama lallai ki yi da saninta ba, dan ba kowa yake yarda ba, idan har kika da sanin mace shine zata yi amfani da damar tana cin duduniyarki, amman wacce akai wa cikin hikima zata nemi rabuwa da abun ne kawai, haba dai Zaliha, sai kace ba ke ba, duniya fa ta cigaba yanzu, ke fa kika fada a kullum baki cire rai da samun haihuwa ba, kuma duk wannan be saka kin yi tunanin mafita ce Allah ya kawo miki ba?”
Momy ta kalli agogon falon a kokarinta na kawar da zancen Umaima.
“Bari naje na hada abun karyawa yau da wuri zan shiga office”
Hajiya Umaima ta mike tsaye tana yar dariyar mamaki.
“To yayi Allah ya bada sa'a mu dai mun gode da ejection, sai kuma idan asman ta sake tashi, mu na gaida Yaya idan ya dawo”
“Zai ji inshallah”
Momy ta amsa tana kallonta har ta juya sai kuma ta juyo tana fadin.
“Wai Ameer ya koma ne?”
“Eh ya wuce jiya”
“Ah lallai kuwa, shi ne ko sallama? Ko da yake ba laifinshi ba ne laifinki ne ai”
“To ma zauna kullum ana ta dora muku dawainiya, abun kuma ai sai yayi yawa”
Cewar Momy tana murmushin da be kai zuci ba.
“Hmmm To Allah ya dawo da shi lafiya”
“Ameen”
Momy ta amsa tana binta da kallo har ta fice sannan Momy ta soma cire safar hannunta tana ta tunanin maganarta. Upstairs ta nufa tana sauke ajiyar zuciya, sai da ta shiga dakin ta jingina da kofar dakin ta rufe ido can kuma ta bude tana karewa dakin kallo kamar wani bakonta. Bed dinta ta nufa ta zauna still thinking, kamin ta shiga bandakin ta wanke hannunta ta fito daga bandaki kamar wanda bata son tafiya.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:53 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Lalabe take tana nufar inda take zaton kofar bukkar take sai kiran sunan Inna take tana kuka. Kamin ta karasa Inna ta shigo da sauri sai tai tsaye cak ganin tana lalabe ga idonta a bude.
“Fulani?”
“Inna akwai rana?”
“Akwai rana mana, baki gani ne ke?”
“Bana iya ganin komai sai duhu Inna, Inna kina ina?”
Inna ta karasa kusa da ita ta taba hawaye na sauko mata.
“Inna bana ganin komai sai duhu kawai”
Cewar Fadime tana fashewa da kuka, a lokacin ne wani irin tashin hankali ya samu Inna, sai ta rasa inda zata saka kanta, kukan data fashe da shi ne yasa Bappa shigowa bukkar yana tambayar ba'asi, da farko be yarda Fadime bata gani ba domin abun ya zo masa kamar almara, ya kuma san halinta da rashin jin zata iya yin hakan dan ta razana mutane, hakan yasa shi daka mata tsawa.
“Hiyy yo in baki bar wasan nan ba ina dauko sanda in buge miki kai”
Duk da irin tsoron Bappa da take ji be hana ta magana ba, sai ta kamkame Inna hawayena na mata zuba gwanin tausayi.
“Wallahi bana ganin komai Bappa dan Allah ku kai ni asibiti, dan Allah ku kai ni kar na makance gaba daya, wayyo Allah na”
Ta sake fashewa da kuka, Inna na rike da ita itama tana nata kukan, Bappa ya tsaya mata kallon mamaki kamin ya kai hannunsa a fuskarta yana yawo da shi, sai dai har yai ya gama bata san yana yi saboda bata ganin da gaske.
“Inna...Inna dan Allah ki kai ni asibiti kin ji”
Inna ta kasa cewa komai sai sakin Fadime tai ta fito waje, Bappa ya sake kai hannunta a fuskarta.
“Nawa ne nan?”
“Bana ganin komai Bappa dan Allah ku kai ni asibiti”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”
Bappa ya furta ganin da gaske take, a take labari ya canja, unguwar ta dauki wani sabon zance, Fadime ta dawo amman ta makanci, mutane sai shigowa ganinta ake, wasu na Allah ya sawwake wasu na fadin a kaita babbar asibitin Katsina ganin abun ya shafi idanu, hankalin Bappa da Inna duk yabi ya tashi, gashi ita kadai Allah ya bar musu idan suka rasa ta ko kuma makantar ta bita har karshen rayuwa sune a matsala da kuma wahala da ita. A take Bappa ya saka Naggensa daya a kasuwa ya tallata a unguwar wani bafulani dan'uwansa ya siya a wulakanci, shanuwar dubu dari da hantsin ya siyeta a dubu 80k.
Yana shigowa da kudi Inna ta shiga ta dauko hijabinta ta dauko na Fadime ta saka mata, aka kira musu wani mai achaba ya dauke su biyu, Bappa kuma ya nufi bakin tashar garin ya samu wani, kan babur suka isa garin Kaita, sannan suka shiga motar Katsina. Duk abun da ake Fadime bata ganin komai sai da ji murya ko sautin mota.
Direban be sauke passengers dinsa ko ina ba sai cikin tashar Katsina, Inna ta fito motar rike da hannun Fadime, Bappa na gaba suna baya har suka isa bakin gate din tashar suka samu Napep suka shiga, be sauke su ko'ina ba sai General Hospital Katsina, dake Muhammad Dikko Road, sai da suka fita sannan Bappa tambaye shi nawa za a biya shi, ganin kamar baki ne yasa ya tsaga abun da ransa yake so ya fada musu. Bappa ya dauko 1k ya bashi ya karbi canjinsa sannan suka nufi cikin asibitin, duk tafiyar da ake Fadime na lake da littafinta a cikin Hijab da dayan hannunta dayan kuma yana rike da Inna.
Da tambaya suka isa gurin da ake karbar kati suka biya suka karba sannan suka koma bin line mika katin, matar na kallonsu tace.
“Kun yi latti, abun da ake zuwa tun safe? Sai dai ku jira likitan yamma idan ya zo, ko kuma ki bari gobe da safe ku sake dawowa”
“Dan Allah ki taimaka min”
Fadime ta fada tana jin kamar ta fashe da kuka, domin jin take kamar da sun ga likita ya bata magani ido mata zai bude.
“Babu wani taimakon da zan iya muku, ko dai ku dawo gobe ko kuma ku jira likitam yamma ya shigo, domin lokacin tashin likitan safe yayi”
“Inna ki saka baki dan Allah”
Cewar Fadime tana riko hannun Inna da kuka, Inna zata yi magana Bappa ya tari numfashinta.
“Shikenan zamu jira har yamma, ai dai za su zo dai ko?”
Ta watsa masa wani kallo.
“Idan ba za su zo ba karya zan maka ne?”
“Aa Hajiya dan tabbatarwa ne kawai”
Bappa ya fada yana ja da baya, daman can ma'aikan asibiti idan sun ga alamar kai wani bagidaje ne sai su fara neman wulakantata, kalilan ne masu kirki da mutuncin a cikinsu. Komawa su kai can gafe kasa suka zauna kamar wasu mabarata.
“Ba a zama a nan ku koma daga waje”
“To”
Suka sake mikewa tsaye suka fita wajen gurin suka zauna a kujerun dake gefen gurin, Bappa na gafe Inna na hagu an saka Fadime a tsakiya bata komai sai hawaye, ashe gani ma wani abu ne, duk abun da ake yau bata ganin komai, idonta a bude yake amman duhu take gani. Lallai bayan ni'imar musulunci da imani babu abun da ya fi ji da gani. Idan Allah ya hada maka duka to ya maka babbar kyautar.
Suna zaune a gurin Shattima ya shiga gurin ba tare da ya kalli inda suke na balle ya san da su, a natse ya wuce yana wani irin takun kasaita kamar asibitin Mai Martaba, kana ganin tafiyarsa da yanayinsa da siffarsa da yadda yake zuba kamshi kai kasan babban mutum ne dan babban gida.
Sai da ya gama abun da zai yi ya fito yana tafiya kamar dazun, black T-shirt ce jikinsa sai red blazer suit ya rike lab coat din a hannu yana tafiya kamar baya son taka kasa, da sauri Inna ta mike tsaye ta tare shi.
“Malam dan Allah ko kai ne likitan ka taimaka mana?”
Kallonta yai na yan dakiko kamin ya kalli Bappa da shi ma ya mike tsaye, daga kam Bappa idonsa ya sauka akan fuskar Fadime da fuskarta ta jike shakaf da hawaye. Be ji kamar ya san ta ba, ko ya taba ganinta ba kai tsaye zuciyarsa ta raya masa ita ce yarinyar da Ra'ees yaje nema masa, kuma ita ce yarinyar da ya kade a mota.
“Me ya faru?”
Ya tambaya yana kallon Fadime, yadda take kallon direction dinsa sai ka rantse da Allah tana ganinsa, shi kanshi abun da ya zata kenan sai dai ya san kukan da take ba zai saka tai saurin ganeshi ba.
“Wannan yarinyar muka kawo asibiti, a duba idanuwanta”
Cewar Bappa yana matsowa da Fadime, haka yake kiranta yarinya ko kuma yace Fulani be taba nuna yarsa ba ce, kara ma Inna ta kan nuna wani lokacin, sai a lokacin Shattima ya gane cewar bata gani, domin kallon da take mishi ba irin na normal mutane ba.
“Miya samu idon?”
“Wallahi ba mu sani ba, dazu da safe abun ya same ta”
Bappa ya fada yana kokarin tare Inna dake son dauko dogon labari. Hannunsa ya kai yana yawo da shi a fuskarta sai ya g bata motsa idon ba alamar bata gani kenan.
“Ku biyo ni”
Da sauri suka bi bayansa Fadime na rike da hannun Inna, yana gaba suna biye har y shiga office dinsa dake cike da sanyin ac da kuma kamshin tsadaden turarensa, sai da ya zauna sannan yai musu izinin zama, Bappa ya zauna daga can gurin kofa Inna da Fadime kuma suka zauna a kujerun dake gaban teburin.
“Miya samu idon na ki?”
Inna zata yi magana ya daga mata hannu yana kallon Fadime.
“Komai be samu idona ba, haka kawai idona ya rufe ina cikin rubutu sai na ga duhu”
“Kin shafa wani a idon ne?”
“Aa”
“Wani abu ya fada miki a idon ne?”
“Aa”
“Daman can idon yana miki ciwo ne?”
“Aa”
“Kina jin ciwo ko kaikayi a idon ne?”
“Aa bana jin komai”
“Me kike lokacin da abun ya same ki?”
“Rubutu”
“Wane irin rubutu?”
Ta ciro littafin daga cikin hijabinta ta mika masa, sai ya kai hannu ya karba still yana kallonta.
“Ya kai awa nawa yanzu da abun ya same ki?”
“Yau da safe ne, ni ban san ko awa nawa ba ne”
Ya ya buda littafin ya fara dubawa rubutun hausa ne, sai dai tana good handwriting, kana ganin kasan tarihim rayuwarta ne take rubutawa domin be yi kama da gata ba ko novels. Farkon ya karanta sai kuma ya tsakalla tsakiya ya kuma duba inda ta tsaya sannan ya sake kallonta.
“Me kike ji yanzu a ido”
“Duhu kawai”
Ya dauko wata yar karamar fitila ya zagaya gefenta ya matsa kusa da ita ya saka hannunsa ya bude idon ya haska, dayar ma haka yai mata sannan ya koma ya zauna yana kallon Inna.
“Am ina ganin likitan ido ya kamata ya ganta”
“To a ina zamu gan shi?”
“Ina zuwa”
Ya dauko wayarsa ya shiga contact dinsa, ya nemo number Habib. Cikin natsuwa ya aika masa kira ba bata lokaci yai picking.
“Hello Shattima”
“Doc Habib ka shigo yau?”
“No ina aikin yamma ne sai 4 zan shigo”
“Ina da patient da nake son ka duba min mai matsalar ido”
“Ba matsala a buda mata file kamin na zo”
“Okay”
Shattima ya aje wayar b tare da ya kashe ba, har sai da shi Doc Habib din ya kashe wayar. A natse ya kalli Bappa dake can baya yana fadin.
“Da yamma zai shigo, amman kamin y shigo za a bude mata file, so that yan zuwa dubata kawai zai yi”
“Tau nawa ake bude file din?”
Bappa ya taba yana saka hannu a aljihu.
“No ba a nan ake budewa ba, bari na kira wata ta kai ku”
Telephone din dake gabansa ya danna ya kara a kunne.
“Zo”
Ya fada sannan ya maida telephone din a muhallinta, ba bata lokaci sai ga wata kyakyawar budurwa ta shigo tana sanye da kayan nurse.
“A kira min Sule”
Ta juya ta fita, babu bata lokaci wani dattijo ya shigo sanye da uniform da alama shi ma ma'aikacin asibitin ne.
“File za a bude musu guide them pls ka yi musu komai”
“Tau ranka ya dade, ku ta zo muje”
Mutumen ya fada sannan ya nufi kofar fita, a tare Inna da Bappa suka mike tsaye Inna na kokarin kama hannun Fadime Shattima ya dakatar da ita.
“No Mama ki bar a nan, kuje ku dawo, zai zama mata wahala ne tun da ba gani take ba”
“To mun gode Allah ya rufa asiri”
Inna ta fada sannan ta bi bayansu Bappa da Sulen da suka rigata fita. Sai da suka fice sannan Shattima ya kalli Fadime dake zaune gabansa.
“Fada min gaskiya, miya samu idonki”
“Wallahi gaskiya na fada”
“Na fa san halinki ba ki jin magana”
“Ka san ni ne?”
“Eh”
“A ina? Wanene kai?”
Ta tambaya tana ta kyabce kyabce da ido, mikewa yai tsaye ya zagaya inda take ya kai hannunsa ya kama hannunta da nufin kaiwa a fuskarsa ta lalaba sai tai wani irin jan numfashi kamar ta ga abun tsoro, sakamakon sanyin da ta ji a hannunsa ya gauraya da nata hannun, wanda hakan yai daidai da shigowa kira a wayarsa.
Saurin sakin hannunta yai yana kallon kyakkyawar fuskarta da makantar bata rage ta da komai ba a kyau da haske, what if bata saba rika hannun maza ba? What if tsoron mutane take ji a yanzu tun da bata gani? Ya ma kamata ya rikata ne? Shi ne abun da yake tambayar kansa kamin ya nufi gurin wayarsa dake ringing ya dauka ya fice daga office din gaba daya.
Hawayene ya sauko a blind eyes dinta, zuciyarta ta hau bugawa da mugun karfi, jikinta ya hau bari, sai ta jimke hannun sosai kamar wanda aka cewa idan ta bude hannun zai fadi.
“Wanene wannan? Wanene kai?”
Ta mike tsaye ta fara lalaben teburin kamin ta juyo ta ta fara tafiya da lalabe tana nufar inda take zaton kofa take, tafiya kadan ta ji ta ji ta taka mutum, sai ta dauke kafarta ta yi baya, ya mika hannunta sai ta ji mutum, matsawa tai tana lalabe riga ce a jikinsa mai kamar ta sanyi, sai da ta lalabe kirjinsa tsab sannan ta kai hannunta gurin fuskarsa, hancinsa ta taba ta sauko gurin bakinsa sai kuma tai sama gurin idanuwansa, can kuma ta saka hannu biyu tana lalabar fuskar gaba daya, dage tai ta lalabo kansa sai ta ji hulla a kan facing cap, dawowa tai gurin fuskarsa tana lalaben sai ta ji hawaye ya sauko a idon mamallakin fuskar, numfashinsa kuma na kara kusantota.
“Zo muje na kai ki gurin su Inna”
Ya rada mata a kunne har lips dinsa na laba hijabinta lumshe ido tai hawaye ya sauko mata.
“Wasim...”
Ta furta domin ta gane muryarsa, wuyan hannunta ya kama ya fita da ita daga cikin office din.
FALMATA POV.
Tana cikin gyara dankalin ta ji kara door bell, sai dai bata tai wani yunkuri ba har sai da ta ji an sake danna kuma an kwankwasa irin yadda tai, sai ta aje wukar da sauri ta fito falon, ganin babu kowa yasa ta nufi kofar ta bude cike da zumudi, domin ko ba a fada mata ba ta san Sirleem ne.
“Wow”
Ya furta yana fito da idonsa waje. Sai ta sakar masa murmushinta mai kama da dariya.
“Ina kwana?”
“Lafiya Kalau, ya kike har kin iso?”
“Eh”
Ya kara fito da idon waje, ganin be daga murya sosai gurin magana ba amman ta ji.
“Kin ji abun da na fada?”
“Eh”
“Taya aka yi kika ji?”
“Na ji dai”
Ta furta cike da far'a, sai ya sako kafarsa cikin falon yana kallonta mamaki.
“Jinki ya dawo kenan?”
“Eh amman ba kamar da ba, ina jin maganar kamar daga wani daki ne?”
“Wow..... ”
Ya furta yana jin kamar ya dagata sama ya juya.
“Soon zaki dawo normal inda kina amfani da maganin daman mai karfi ne sosai, I'm happy”
Ita ma ta yi dariyar jindadi, sai ya sakar mata ido hakan nan kawai take burgeshi, if you ask him miya