Showing 186001 words to 189000 words out of 273152 words
Chapter 63 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
ta tambaye ni?”
“Ba ki santa ba”
Jekakadiya ta amsa mata a takaice haka take mata a duk lokacin da ta tambaye ta, ba ma ita kadai ba har wasu da ba Ammy ko Shattima ba idan suka tambaye wani abun gudun laifi ko ace ka yi sai ta ba shi takaitacciyar amsa, hakan da Jekadiya tai ba karamin kufula Fadime yai ba, daman ta lura a duk lokacin da ta tambaye ta wani abun sai ta amsa mata kamar bata son amsarwa ko kuma ta takaita, cikin bacin rai Fadime ta bi ta har suka isa inda Sarkin gida yake ta gabatar masa da sakon Shattima, sai ya zabura da sauri ya ya shiga gaba suna binsa a baya har suka isa gurin da ya sauke su Bappa, shi da kansa ya shiga karamin falon da sallama suka amsa masa, suna bata cikin hakkinsa. Fadime na jin muryar Bappa ta fara kokarin sakin Jekadiya tana kiransa.
“Bappa...”
Kamin ya fito har Jekadiya ta kama hannunta ta shiga da ita cikin falon, ganin Fadime yasa idon Bappa cika da kwalla ita kam tu ni nata hawayen suka fara zuba sai hannu take mikawa ta taba shi.
“Bappa... Kai ne”
Ta fada cikin kuka da shauki, sai ya amsa mata da yaren fulantanci yana kama hannunta.
“Fulani...! Har nan kika kawo mu? Fulani baki jin magana dubi yadda kika koma?”
Sai ta fashe da kuka tana taba fuskarsa.
“Dan Allah Bappa ka yafe min, na yi dana sani kuma ba zan sake ba, Bappa idona na ya rufe bana ganin komai tun ranar idon be bude ba har yanzu, Bappa ba dadi bana ganin kowa, sai dubu kullum komai zan yi sai dai na yi lalabe”
Ta kara fashewa da kuka sosai, sai lalaben fuskar Bappa take, Jekadiya na ganin haka ta juya ta fice tare da Sarkin gida.
“Ai rashin jinki ne ya ja miki, daman wanda be ji bari ba zai ji hoho... Ko ina ke ce Fadime ke ko tsoro baki ji”
Cewar Kawu dan iroro cikin fada yana tsude hannu, Fadime na jin haka ta kama Bappa ta rike tana kokarin rumgume shi.
“Bappa dan Allah karka min fada, ka ga bana gani yanzu, dan Allah kar ka ga laifina, zan fada maka gaskiyar komai da komai Wallahi na rantse”
A gurin da take tsaye ta zauna ta fara labarta musu abubuwan da suka faru na gaskiyar inda ta san ta yi karya sai ta fashe da kuka tace Bappa ya yafe mata ita ma ba da son ranta tai ba, duk abun da ta fada kwatankwacin abun da Wasim ya fada musu ne, sai karin wasu abubuwan da Wasim be fada ba domin ita zai ta fede daga biri har wutsiya, sai da ta kai karshe sannan ta tsaya tambayar Bappa tambaya mai nauyi.
“Bappa zaka bar ni na auri Wasim?”
Kamin Bappa yace komai Kawu ya kwatseta ta hanyar daka mata tsawa yana zaginta da hannu kamar tana ganinsa.
“Ke arrrr Fadime, kina abu kamar ba ki sha nonon Fulani ba, duk wannan abun da ya faru da ke be isa ya saka ki natsu ba, ki yi hankali? Ke wace irin yace? Rashin kunya kiri kiri har kina tambayar aure? To shi Wasim din musulmi ne aka ce miki? Kuma mutumen da danginsa suka miki haka kina tunanin za su yarda ki aureshi ne? Tsafe ki za su yi ko ma su kashe ki gaba daya”
Ta dafa zuciyarta da karfi tana zare ido.
“Na shiga uku... Bappa ai zai iya musulunta kuma dan sarauta ne baka ga yadda ke masa ba”
Ta fada da iyakar gaskiyarta, domin ta gani da idonta irin yadda ake bawa Wasim girma a garinsu saboda yana dan sarki abun da ya kara mata son sa kenan a ranta, tana jin ita idan ta aure shi haka za ayi mata. Bappa ya sauke ajiyar zuciya yana kallon yarsa, gaba daya ya rasa a wane muhalli zai saka Fadime, tunaninta har yanzu be bata ta fara jin tsoron ta nisanta kanta da Wasim ba sai neman aurensa take, kuma kai tsaye take fada masa haka abun da ya tabawa al'adarsu ta fulani.
“Fulani natsu ki saurareni, kin girma ya kamata ace kina da hankali da tunani kamar sa'o'inki, ke yanzu mutumen da zuwa garinsu kadai ya maida ke haka har zuciyarki take miki shaa'war aurensa? Ki fara bari ki ga idon idan ya bude tukuna kika sani ko a haka zaki zauna har abada? Sanadinayar abun da kika aikata Allah kadai ya san halin da kika jefamu, Shatu har da ciwo tai ke kuma kin zama a haka ni da Kawu da ba mu taba mafarkin zuwa yola ba gamu a gidan babba sarki a yola saboda ke, to ya isa haka nan idan kina yin hankali da tunani ki fara tun yanzu idan kuma ba zaki yi ba, ni na san maganinki?”
“Menene maganina Bappa? Ai shi Wasim din ba zama zai yi a garinsu ba, zan fada masa ya dawo garin mu ya zauna tare da mu, Bappa dan Allah”
Bappa ta ji kamar ya dauke ta da mari sai kuma wata zuciyar ta hana shi ganin halin makantar da take ciki.
SHATTIMA POV.
Yana tura kofar dakin Ammy suka yi ido biyu da Baba Waziri, wani irin abu Shattima ya ji kamar ya fasa ihu ko kuma ya juya ya koma amman ba hali, yanayin yadda ya ga Ammy na murmushi ya san ba zai wuce zancen aurensu da Maijidda ba.
“Waziri samun dan'uwa irinka abu ne mai wahala a wannan zamani, kwata kwata kai ta kanka kake ji ba ta dan'uwanka”
Cewar Ammy tana kallonsa da murmushin irin yadda yake nunawa mai martaba da yayansa kulawa abun har mamaki yake bawa Ammy. Baba Waziri yayi murmushi.
“Ammy kenan, irin mu suna nan da yawa, ai ko'ina akwai mutanen kwarai, kuma rayuwar duniyar nan idan ba ka yi dan Allah da zumunta ba dan me zaka yi? Mu na yi saboda yaranmu su ma su gani su koya daga garemu, a can ba mu san kanmu ko yayan mu sai yayan yan'uwa su ne namu na mu kuma su ne na su”
“Allah ya saka da alheri ya kara hada kanku kuma ya hada kan zuri'ar gaba daya”
Sai da Baba Waziri ya gama magana da Ammy sannan Shattima ya mika masa gaisuwa yana kallon Ammy domin ta hanyarta yake gane labari mai dadi ko akasin haka, tsoronsa daya kar ace zancen aurensa ne Baba Waziri ke yi, tun da ya sanar masa tun a waya cewar ya fara shiri, Baba Waziri ya duba Shattima duba bana wasa ba, irin duban nan na babba da yaro ya soma magana cikin dattijantaka.
“Shattima ka yi hakuri, ban nemi shawararka ko izininka ba na tsayarda rana karshen watan nan, na san idan na tsaya neman shawararka zaka fara kawo wasu kabli da ba'adi ne, kuma ina jin na isa da kai shiyasa nai haka”
Shattima yayi shiru be ce komai ba, sai dai har ga Allah be son wannan hadin da Baba Waziri yai tsakaninsa da Maijidda, ya san tana tsoron ta aureshi ta mutu kamar sauran matan, kuma ko da babu mutuwa ba lallai ne a samu kwanaciyar hankali a tsakaninsu ba, domin shi be taba kawo ta a ransa ba, ita ma kuma bata taba kawo shi a ranta ba, ko da ma ace sun taba irin yadda Hajiya Talatu taka kin Ammy abu ne mai wahala ta bar su su yi zaman lafiya balle kuma ga wannan jarabawar da take tare da shi.
“Ba ka ce komai ba”
Baba Waziri ya fada jin yayi shiru ya kasa furta komai, ga fuskarsa bata nuna jindadi ko akasin haka ba. Shattima ya dago ya kalli Ammy sannan ya kalli Baba Waziri ya ce.
“Baba ita Maijidda ta amince? Idan har bata amince ba dan Allah kar ayi mata dole, ni akwai wanda zan iya nema a hadamu...”
Ammy ta watsa masa wani kallo mai kama da harara, Baba Waziri ma kallonsa yake.
ZAINAB POV.
Cikin abun da be fi kwana biyu ba, ta rame ta koma kamar marar lafiya, ko da yake za a iya kiranta da marar lafiyar amman ta zuci ba na jiki ba, damuwar da take ciki ya mata yawa, idan ta fara tunani sai ta rasa ta ina zata tonke. Ta ya zata tuna cewar mahaifiyarta ce ta kashe mijin da zata aura ta ji sanyi? Ta ya tunaninta zai tsaya akan abun da mahaifiyarta ta aikata na kashe mutanen da basu mata komai ba face kyautawa hankalinta ya kwanta? Ta ya zata tuna yadda rayuwa ta zo mata a birkice a haife ta bata hanyar sunna ba kuma ta jidadi? Anya farinciki zai sake kusantarta? Sai a yanzu ta gane darin dukiya da kyau ko isa ba shine farinciki ba, kuma a yanzu ta yarda ba komai kudi suke iya siya ba, domin da ace kudi suna siyen komai da ta siye wata uwar ta canja iya, da ta siye wani uban ta canja wacan da yai cikinta a tasha wanda ko sunansa ba ta sani ba.
Barin jikin window tai ta saka hannunta ta share hawayen da suka zubo mata, sannan ta nufi kofar dakinta ta bude ta fita, a falo ta samu Iya tsaye tana gyaran zane da alama fita zata yi domin har ta sanya hijabi.
“Ina zaki je?”
Zainab ta tambaya daga jikin kofar dakinta da take tsaye, sai Iya ta dago ta kalleta.
“Unguwa”
“Unguwa gurin me? Shekaranjiya kin fita jiya ma kin fita kullum sai kin fita, amman wannan fitar da alama mai muhimmanci ce shiyasa kika saka sabon kaya”
Iya ta daura zanenta tana kallon Zainab da mamaki.
“A da can baki min irin wannan sa'idon, ke da na haifa kike da damar fita ki yi yadda kike so balle kuma na haife ki? Ni ce uwarki fa karki manta”
“Na san ke ce uwata ai, na san ke kika haife ni haihuwar da bata min rana ba, enough is enough Iya! Ki bar Ammy da iyalanta su huta, ki bar Shattima yayi rayuwa kamar kowa, mutanen nan ba su miki komai ba sai karamci da kyautatawa, idan ma tsoron kike asirinki ya tonu miyasa kika aikata tun farko? Wallahi idan baki kyale su ba Iya sai na aikata abun da baki taba tunani ba”
Ta karasa cikin kuka mai karfi hawaye na sauko kamar dan ta kadai akai yi su, juyawa tai da sauri ta koma dakinta tana kukan da ita kanta ba zata iya fadar na wanene a cikin danuwarta ba, kamin ta karaso gurin gadonta ta hango Wasim tafe sanye da kananan kaya kamar wacan karon, banbancin wacan dress din da wannan wacan black ne wannan kuma red T-shirt da blue jean sai hular sanyi da ya rufe fuskarsa da ita ma red ce.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:56 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Tumba ta ja da baya da sauri tana rike da hannun Falmata.
“Aa indai Malam Mu'azu ne da aka daurawa aure dazun tare da Falmata ba wannan ne gidan ba”
“Inna nan ne gidan fa”
“Aa”
Tumba ta jata ta tsaya a waje ita ala dole ba gidan ba ne, domin a iya ganinta tsohon da aka aurawa Falmata be da tarin wannan arzikin, mutumen da yake kamar maroki ma taya ya samu wannan uban arzikin kato gida haka komai a tsare falon ma a kawatashi kamar na yar minister, sai da ta gama kallon ko'ina harabar gidan. Sannan ta ciro wayarta ta kira line Baba, wayar bata dade tana ringing ba ya dauka yana sallama. Ko amsawa ba taba tsaya yi ba ta ce.
“Malam ka kira mutumen ka tambaye shi ina za a kai Falmata, motocin da ya aiko sun dauko mu sun kawo mu wani katon gida da ni na san ba na shi ba ne”
“Wani gida kuma?”
“Eh ba gidan da muka je muka gani ba, wani gidan ne na dabam, ka kira shi ka tambaye shi inda za a kai yarinyar”
“To shikenan”
Ya kashe wayar, Tumba ta saka wayar a cikin zanenta tana kallon yan'uwan Baba da sukai cirko cirko.
“Ni sam ban yarda gidansa ba ne, domin be da irin wannan arzikin da zai samu wannna katon gida, idan ma yana shi to boye mana yai kuma ba na halal ba ne, wannan irin abu haka”
Ana nan dai wasu suka saka na su baki, suka taya ta wasu kuma su ka kama bakinsu su kai shiru, Inna laure dai na tsaye da tunani biyu a ranta, domin a yanzu ta gane dalilin kukan da Falmata take yi, bata son auren ne, ita kuma Tumba ta tsaya mata akan auren ne saboda ta sha wahala sai gashi ta ga abun da ba tai zato ba hakan yasa ta rudewa tana fadin wani ba gidan ba ne. Suna nan tsaye Baba ya kira Tumba jiki na rawa tai picking.
“Tumba yace nan ne za a kaita indai Unguwar 300 House's ne”
“Unguwar ne Wallahi, amman Malam ba wacan gidan da muka je muka gani ba ne”
“Babu komai tun da har yace nan ai sai ku kaita kawai”
“To Amman Malam baka ga gidan ba, abun tsoro ne kar sai mun bada baya ya yanke mata kai”
Inna laure na jin haka ta kada baki ta ce.
“Wane irin magana ne wannan Tumba? A maimakon ki jidadi ki yi mata fatan alheri sai ki fara wani magana marar dadi”
Ta fisge hannun Falmata ta jata zuwa ciki.
“Zo mu je, mu da zuciya daya muka aurar da ke, kuma muna miki fatan alheri fatan na gari, yi bismillah ki shiga da kafar dama”
Falmata ta yi bismillah sannan ta shiga da kafarta ta dama kamar yadda Inna Laure ta umarta, Inna Laure ta shiga da sallama mata biyun da ke ciki suka amsa mata.
“Mashallahu”
Ta fada sannan ta kai Falmata saman doguwar kujera ta zauna. Sauran yan'uwa da yan unguwa suka shiga sauran dakunan da kitchen suna dubawa, dakuna uku ne a upstairs din na farko ya bi na biyun kyau na biyun kuma ya fi na ukun kyau, sai dai kowane daki fararen kaya ne, kicin din ma an cika shi da kaya ga abinci kala kala a store din. Khadija ce ta zo ta zauna kusa da Falmata ta kama hannunta ta rike, tana ta murmushi kamar ba ita ce ta gama kuka ba a dazun, ganin gidan da irin kayan dakin da aka zuba a gidan ga gidan ya hadu iya haduwa. Nasiha sosai Inna Laure tai mata ciki har da ta addu'a.
“Karki kuskura wasa da addu'a kuma kar wani ya kawo miki wani abu yace ki baw mijinki ko ki amfani da shi da sunan kayan mata ki karba, kin ga Tumba nan ki yi hankali da ita, ki san abun da zaki fada ko ta baki ki karba, sannan ki yi ta hakuri zaman aure sai da hakuri, idan kin samu ki taimaki babanki mamanki kuma ki bita da addu'a da sadaka Allah ya ba ku zama lafiya”
Khadija ce ta amsa da Ameen, sannan Inna Laure ta saki hannunta ta hau sama ta duba dakunan ta sauko tana ta sanya albarka. Tumba dai na tsaye bakin kofar dakin ta kasa shigowa, gaba daya kanra ya dau zafi ga zuciyarta kamar zata fashe take sai tukiki take mata, gaba daya ta rasa ma kalar tunanin da za ta yi, cikinta har murdawa yake.
Tana a bakin kofar har su Inna Laure da matan da suka musu rakiya suka fito sannan ta juya ta bi bayansu ta kasa cewa komai har suka shiga motar aka juya da su, sai gidan ya rage daga Falmata sai Khadija sai kuma sauran kawayenta da yan'uwa da suke sa'aninta. Khadija ta bude mata mayafi.
“Bude fuska ki ga gidanki, duba ki ga inda Allah ya kawo ki Falmata”
Falmata ta dago kadan tana kallon falon, sai ta ji kamar ba gaske ba daman ranar yau ta zame mata kamar a mafarki. Jan mayafinta tai ta rufe kanta, a yanzu bata sna me zata yi ba kuka ko murna? Idan murna ne anya ya dace tai murna da auren tsoho ko da ace ya tara mata wannan uban dukiyar. Sai da aka maida su Inna Laure da Tumba sannan motocin suka je dauko ango.
Kawayen Falmata na jin tsayawar motoci suka fara gyare gyaren jiki, Falmata kuma ta kara maida kanta kasa.
Abun da ya bawa mutane mamaki ganin abokan ango yara amman angon tsoho da har da hurhura, yana sanye da mayan kaya har da babbar riga shaddaraa sai shinning take. Kusa da Falmata ya zauna yana ta kamshin turare kan ganinsa ka ga sabon ango. Duk wani abun da ake fada be ce komai ba iyakarsa murmushi, abokansa ne suka bawa yan matan da suke tare da Falmata kudin siyen baki har 200k, ba karamin mamaki ne ya cika su ba, har tsoron karbar kudin suka yi, sai Khadija ce ta karba har tana fadar wai a karo amaryar mai tsada ce, ita ce ta fara yin addu'a tana bada shawarwarin zaman lafiya, wani abokin ango ma yai nasa sannan suka Fita tare da kawayen amaryar domin aje su gidansu, sai da suka fice sannan ya mike tsaye ya isa bakin kofar falon ya rufe ya