Showing 219001 words to 222000 words out of 273152 words
Chapter 74 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
Alhamdulillah”
“Kuma idona ya bude ina ganin komai har wannan mutumen da ke tsaye gabana ina ganinsa”
“Da gaske?”
“Wallahi kuwa amman a asibiti muke, ban sani ba ko ya taba min idon ne, kuma Wasim yace idan aka taba min ido a zai bude ba”
“Hey... Karki sake maganar wani Wasim ko Hajiya Karama ko Iya, mutanen nan ina tunanin suna da hannu a abun da yake samunki, and now babanki yayi fushi ya tafi, sai kuma aka tsince ki Abuja? Wannan wane irin abu ne?”
“Bappa ya tafi?”
Ta tambaya tana shirin fashewa da kuka.
“Zan kira anjima”
Ya katse kiran wanda hakan yayi daidai da saukowa hawaye a idon Fadime. Muhseen ya karbi wayarsa yana kara yarda cewar ta san Shattiman da kuma labarin da ta ba shi na Iya da Zainab.
Fashewa tai da kuka marar sauti tana ta sharar hawaye, shi dai be ce mata komai ba ya fita ya barta a office din.
Sai da ya gama abun da zai yi sannan ya dawo ya dauki abun da zai dauka ya ce mata ta ta so su tafi.
Sai da ya ga tana bin hanya daidai sannan ya mara tabbatar da tana gani, ko a gurin motarsa ma ita da kanta ta bude ta shiga ta zauna, sai dai bata daina hawayen ba har ya fara tuki.
“Ki daina kuka idan aka maida ke gurin Shattima sai ya saka a kaiki gurin mahaifinki ai”
“To”
Ta share hawayenta, tana bin titin da kallo.
“A ina kuka tsince ni a kasa?”
Sama sama ya labarta mata abun da Aliyu ya fada masa, suna isa gidan Mama Fulani ta fara bude ido tana kallon katon gidan.
“Nan ne gidan ka?”
“Gidan Mamata”
Ya amsa mata yana bude motar ya fita, sai ita ma ta bude ta fito tana mamaki kato gida kamar wannan ga tsari da kyau kamar gidan minister. Yana gaba tana binsa sai kalle kalle take gaba daya ta zama bakauya har da kai hannu ta shafa fentin da take ganin yana ta wani haske. Bata kara raina kanta ba sai da suka shiga cikin falon, kamar yar gida haka ta zama domin ta riga Muhseen isa gurin kujeru sai dai bata zauna a kai ba ta zauna a kasa ganin manyan kujeru ne na alfarma, Muhseen kuma ya zauna a daya daha cikin kujeru kamin yai mata magana yace ta taso ta zauna akan cushion dina, har ta mike tsaye ita ta zauna akai tana kallon fuskarsa ta ga ko hanata zai yi ko kuma yace ta sauka, haka ta daga kai tana ta kallon falon mamakin duniya ya cika ta, irin gidan da bata taba gani ba yau ga ta a ciki.
“Ku nawa ne a nan gidan nan?”
Ta tambaya tana mamakin katon gida kamar wannan ace na mamansa ne, Muhseen ya nuna mata Mama Fulani da ke saukowa rike da tissue da alama hawayen mutuwar yar kanenta be tsaya mata ba har yanzu. Fadime na ganin Mama Fulani ta san ba irin iyayen nan ba ne masu daukar nonsense ga ta da jikin dake nuna arzikinta a fili tufafin jikinta ma kadai sun isa shaida. Saurin sauka tai ta zauna a kasa tana gaishe ta tun kan ta karasa saukowa.
“Sannu da zuwa Ina wuni”
“Lfy Kalau Yasmin”
Mama Fulani ta amsa sannan ta nufo kusa da Muhseen ta zauna, har lokacin bata kura Fadime na gani ba, domin hankalinta be kai kanta sosai ba.
“An dubata ta?”
“Ba zancen dubawa yarinya ta tashi”
“Kamar?”
Ya nuna mata ita, tana kallon Fadime sai Fadime ta sakar mata murmushi, Mama Fulani ta kalli Muhseen ta sake kallon Fadime.
“Tana gani kenan?”
“Ba gani kadai ba har komai ta tuna”
“Magani kuka bata?”
“Aa...”
Ba karamin mamaki ne ya kama Mama Fulani ba, da Muhseen ya labarta mata abun da ya faru, can kuma ya tsakuro daga labarin da Fadime ta bashi ya samman Mama Fulani inda be yi daidai ba Fadime ta gyara masa, daga nan ya sakar mata linzamin ta labartawa Mama Fulani komai. Kamar almara haka Mama Fulani ta ji abun mamaki da al'ajab suka rufeta lokaci daya.
“Ashe ita take cinye mana zuri'a? Ba sididi ba sadada daga gamon tsintsiya da zagga? Ban zumuntar uwa ba ta uba take mana wannan sherin ba duk abun alherin da aka mata?”
“Ita da yarta mayyu ne, har yar mayya ce”
Fadime ta fada tana tsina fuska domin ita har ga Allah ta dauka Zainab mayyace.
“Lallai kuwa ai biri yayi kama da mutum, tana zaune a gida tana cinye mana zuri'a ko wannan ma waya sani ko ita ta cinye ta tun da Waziri ya fada min ya bawa Shattima ita? Tabbas ita ce ita Ammy ma take ne Fisabilillahi? Wace iri mata ce wai? Ta san da wannan ta zuba bata yi komai ba? To Wallahi ba zata sabu ba bindiga a ruwa, Allah ya kai ni Yola gobe lafiya Na rantse da Allah sai Iya ta bar garin nan, ta koma can inda ta fito, ba dan ma guduna alhaki ba ba zan barta da rai ba”
“Ashe ma ba ma yar garin ba ce amman yarta har wulakanci take wa mutane tana cewa kar a hau mata a kujeru ta barin mutun ya kwanta ba ko abun lullubi”
Fadime ta fada tana tuna abun da Zainab tai mata. Sai Mama Fulani ta biye ta kamar mai fira da sa'anta.
“Ba yar nan ba ce, waya san ma inda ta fito wata kila maitar tasa aka rokota ta zo nan ta lake har suke mata gata, amman shi Mai Martaba ya san da wannan zancen?”
“Wai daman shi Sarkin yana da rai? Ai na dauka ya mutu saboda wannan matar Hajiya Babba ta tafi tace a kashe shi kashe Shattima...”
Fadime ta fada tana kallon Mama Fulani da ta mike tsaye tana nuna ta, Muhseen ma gyara zama yai yana mata wani kallo.
“Keeee idan kika min karya sai na saka an yankaki an daddatsa namanki an zubar ni nan Fulani ba uban da isa yai komai”
Fadime ta sako mata ido hantar cikinta na kadawa, Mama Fulani dai ba tai mata kama da mayu ba, duk da kasancewar gidan yana mata kama da na masu yankan kai, to amman me ya kawo maganar yanka da daddatsewa daga bada labari, ta fara kuka.
“Na shiga ukuna”
“Ba wani kin shiga uku fada min gaskiya, ta ya akai kika sani...?”
“Zan dafa miki qur'ane kuma na yarda ki kira Shattima ki tambaye shi Wallahi ba karya zan fada miki ba”
Maman Fulani ta koma ta zauna tana kallon Muhseen da ke kallon Fadime. Tun daga salsalar zuwa garinsu Wasim har zuwan su Hajiya Babba da duk abubuwan da suka yi har kawowa zuwanta gidan da yadda ta labartawa Ammy komai sai da ta fadawa Mama Fulani. Mama Fulani bata san lokacin da ta daki kirjinta ba ta sake daka har sau uku.
“Dan'uwan nawa za a kashe? Ita Hajiya Balki rashin imaninta har ya kai haka? Akashe shi a kashe Shattima? Yanzu ita Ammy ta ji duk wannan abun amman ta share take zaune ta saka musu ido? Ko kuma ita ma asirin suka mata da bata iya komai? Ba zan dauka ba, na san dai na yi rashin mutunci a baya ammn ban yi rashin imani kamar na wannan matar ba, mijinta na sunna? Saboda Sarauta? No wonder ciwo yai ma Mai Martaba yawa, Mata ta yi yan'uwa su yi jamar'ar gari su yi, ba ma wanda zai fi kamar n matarsa tun da dole ne ta bashi ya ci, ai dole ne gobe Mai Martaba ya ji wannan maganar kuma dole, za ki iya maimaita wannan maganar a gaban kowa ko?”
“Eh Wallahi zan iya”
Fadime ta fada with full confidence. Mama Fulani ta mike tsaye ta nufi upstairs sai bala'i take.
“Kuma Wallahi Nana ba zata auri danta ba, muguwar mata kawai mai bakar zuciya...”
Sai da ta wuce Muhseen ya baro inda yake zaune ya motsa kusa da Fadime ya kai hannunsa ya kama lebenta yana ja.
“Kin gani wannan bakin na ki, zai kai ki ya baro, daga ganin ki na san zaki yi surutu, i wonder how Shattima ya zauna da ke shi da baya son hayaniya, kin ga yanzu kin takalo wata fitinar Mama Fulani ba zata kyale wannan maganar ba, kuma at end idan karya kike kin jefa kanki a matsala ko ma da gaske ne, za su iya wanke kansu ke ki kwana a ciki, kin san waye Hajiya Babba kuwa? Wannan bakin na ki wata rana sai ya yanka ki, wata kila shiyasa akai miki wani asirin aka kawo ki Abuja aka mantar da ke komai”
Wani tsoro ne ya kama Fadime jikinta ya fara rawa.
“Kenan yanzu ni za a jefa a matsala?”
“Ban ce kuma, amman ki san irin maganar da kike fada, kin ga Mama nan bata saurarawa kowa kan nata, ina tunanin ma yanzu waya ta je ta kira, kin ga kin ta da rigima a gidan Sarauta, sai an zo gurin magana ganki yar ficika ba wani auki”
Fadime ta taba jikinta tana jin wata zababbbiyar yunwa na taso mata.
“Ni yunwa ma na ke ji”
“Wato har yunwa kike ji? Duk baki ga abun da kika yi ba hankalinki kwance ko?”
“To ni wai ina ruwana ba su suka je suka yi ba, dan na fada kuma sai ya zama laifi, ma na Taimakawa Mai Martaba ban ai sai a karramani”
Ta fada tana turo baki gaba, tsoro dai kam ta ji shi, amman sam bata ga laifi a abun da tai yi ba. Muhseen yayi murmushi yana kallonta kamar yadda take kallonsa da fararen idanuwanta.
SHATTIMA POV.
Shattima ya kalli Ammy bayan sauke wayar da yai a kunnesa.
“Fateema ce wai an ganta a Abuja hannun Muhseen”
Ammy ta kalleshi duba irin na mamaki duk da kasancewar bata cikin yanayin dadi, bata damu da hawayen da ke fuskarta ba ta ce.
“Wane Muhseen din?”
“Na Mama Fulani”
“A Abuja kenan?”
“Eh ina tunanin abun da nai ma Hajiya Karama ne yasa ta janye kudirinta a kan Fateema, ita kuma mahaifiyarta ta kashe Maijidda”
“Ba ka da tabbacin yarinyar ta bata ne saboda Zainab, sai na ke jin kamar babu sa hannunta a ciki, kuma be zama lallai dan Maijidda ta mutu ba ace Iya, domin Waziri ya fada min asibiti sun ce tafoit ce, amman na san mahaifiyarta da kowa kai zai zarga, idan har Iya ce ai ita sai ka aura suke mutuwa wannan kuma tun kamin ayi auren ta rasu”
“Mai son abun ka ya fika dabara Ammy, bana iya gane komai a yanzu, ba zan iya cire Iya daga zargi ba, kamar yadda zuciyata ta kasa aminta da Zainab”
“Ka tafi gurin jana'izar kar ayi ba kai”
A hankali ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya fice daga dakin, Ammy ta share hawayenta ta mike tsaye ta nufi dan karamin dakinta dake gefen wardrobe inda take canja tufafi, wani yadi marar nauyi ta saka ta saka Hijabinta sannan ta fito, sai kuma ta zauna bakin gadonta ta dafe kanta, babu wanda take tunani sai Hajiya Talatu, da Waziri duk da kasancewar ta san Baba Waziri mutum ne mai tawakkali sai dai be zama lallai Hajiya Talatu ma tai ba daman can ba son ta take ba balle kuma yanzu da zata ga kamar saboda za a hada auren yarta da Shattima ne ta mutu. Ammy ta kusan awa daya a dakin kamar mai kunyar fita, tana tunanin mikewa tsaye ta fita sai wayarta dake gafen gadon tai ringing, Hannu ta kai ta dauka ganin number Mama Fulani be bata mamaki a tunaninta ko zata sake wata maganar ko kuma ta fada mata cewar tana tafe.
“Ammy...! Yarinyar ta fada miki abun da ta fada min?”
“Kamar na me?”
Mama Fulani ta labarta mata kadan, sai Ammy ta sauke ajiyar zuciya.
“Ta fada min”
“Amman kike zaune a nan? Har kina kallon Hajiya Balki? Kai ba ma Hajiya ba Balki zance, ta ashe miji da ta kashe miki miji ta tarwatsa rayuwarku?”
“Ba komai ya kamata na yarda da shi ba, domin babu hujja kwarara a kan haka, idan nai tunani sai na ga ita ma ai tana da yaya fiye da yadda na ake da su da Mai Martaba, to mai zai saka ta aikata haka? Ko da ma ace akwai Hujja, idan nai unkurin yi mata wani abun za a zargi ko dan tana kishiyata ce ina son na kashe mata aure ne, kuma idan yarinyar kadai bata isa shaida ba”
“To zauna nan kina jiran hujja, ai komai bincike yake so, kuma idan aka titseta dole wata rana a gano gaskiya, ke ma dai ina ganin sun dan taba ki kin zama wata Salahu zaune kawai kike a gida?”
“To Fulani ya zan yi? Mijina ba lafiya, duk wata dawainiyarsa da kula da shi akaina yake, ga yayana ma ba su cikin natsuwa Nana ma daga baya baya nan ne na samu ta natsu, ga jama'ar gari da yan'uwa, ga Hajiya Balki ita kanta, abubuwa sun min yawa kwakwalta a cushe take”
Ammy ta fashe da kuka tana jin kamar ta mutu ta huta.
“To ni tawa bata cushe ba, na kira wayar Waziri bana same shi ba, ki aika a fada masa na ce kar a kai Maijidda a kabari a kira Iya ta tsallakata”
“Tafiya kam Maijidda ta tafi Fulani, sai dai fatan samun rahama”
Haushi ne yasa Mama Fulani ta kashe wayar, Ammy ta mike tsaye ta saka wayar a jakarta sannan ta fito ta rufe dakinta. Ko da ta fito direbanta har ya faka mota yana jiranta, daman tun da ta saka Jekadiya ta fada masa yake jiran fitowarta, fitowa yai da sauri ya bude mata ta shiga, sai dogaran da suke dayar motar suka matso da motarsu gaba.
“Ka fada musu kai kadai zaka kai ni, gaisuwa ce bana bukatar rakiya”
“An gama ranki ya dade”
Ya fita motar da sauri ya isa gurinsu ya sanar musu sakon Ammy, sai suka ja motar zuwa inda aka saba ajeta, shi kuma ya dawo cikin motarsa ya shiga.
“Allah ya ja zamaninki ya kara miki lafiya”
Ammy dai bata ko kalli inda yake ba har suka isa gidan Waziri, a nan Ammy ta dauko mask dinta ta saka, daker suka samu gurin fakin a cikin gidan saboda motocin da suka cika gidan, haka Ammy ta fito ta ratsa cikin mutane tana sanye da hijabinta da kuma face mask ta wuce cikin gidan domin wajen gidan maza ne a ko'ina.
Hankalinta be kara tashi ba sai da ta shiga bangaren Hajiya Talatu, baka jin komai sai dariyarta dariya bata wasa ba, irin dariyar da ake kyalkyaltawa wanda ake cewa bata da kyau ko a musulunci, mutanen da suke falonta kuma suna ta aikin kuka, kanen Maijidda da yayenta babu mai iya ba wa wani hakuri, Ammy bata san lokacin da hawaye suka fara saukowa mata ba, sai jikinta yai sanyi sosai.
HAJIYA BABBA POV.
Haka ta wuni ta kwana ba eh ba aa, bata cewa komai kuma duk abun da aka bata bata ci, sai dai tai ta kallon mutane, idan aka ce ci sai ta bude baki ta saka ta tauna amman ta kasa hadewa, haka take a ruwa ko tea ko ruwa duk abun da ta saka a baki ko yayanta suka saka mata sai ta kasa hadewa sai dai ya dawo mata. At first sun dauka ko damuwar abun da Sirleem ya aikata ne, sai dai ganin har an kwana an wuni bata canja ba gashi tsawon dare bata runtsa ba ya fara bawa Karima da Jurry tsoro. Sirleem kan tun da ya bar gidan be dawo ba sai washe gari misalin takwas a tunaninsa zuwa lokacin abun ya sauka a ranta ta dan huce. Ko da ya shigo dakin Kausar na zaune kusa da ita ta kama hannayenta ta rike sai kuka take.
“Hajiya ina kwana”
Ya fada da tunanin zata amsa masa ko da a cikin fushin ne, ko kuma ta kalli inda yake amman ba tai ko daya ba.
“Ba ta yi magana ba tun jiya, kuma komai aka saka mata dawowa take da shi, bata cewa komai kuma ba ta runtsa ba har garin Allah ya waye”
Sirleem ya mike tsaye da sauri ya karasa kusa da ita ya kama kafafuwanta ya rike.
“Hajiya dan Allah ki yafe min? Dan Allah ki yi magana, ki yafe min Hajiya”
Tana bude bakin da zimmar magana sai bakin nata ya juye ya bar muhallinsa koma gefe daya, wato gefen kuncinta na hadu.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Hajiya”
Ta kalleshi yawu na zazzago mata kamar wata musaka. Take Sirleem ya fashe da kuka.
“Dan Allah ki yafe min Hajiya, ba zan sake tsaba umarninki ba, kuma zan saki Falmata yanzu, zan auri Nana, Wallahi ba zan sake saba umarninki ba”
Ya juya ta sauri ya fice daga dakin, Kausar ma ficewa tai da gudu tana kuka. Sai ga Jurry da Rima sun shigo hankali tashe, su suka rikata ta mike tsaye da taimakonsu suka saka ta mota zuwa asibiti, suna isa abun ka da babbar asibiti kuma ga ta matar babban mutum sai su karbe ta da sauri suka shiga yi mata gwaje gwaje. Bata motsa ba sai da aka soka mata allura za a debi jininta.
“Washhhhhhhh”
Ta fada yawu na biyowa ta bakinta da yaki rufuwa. Duk iya gwanje gwajen da sukai ba su gano ciwom komai ba, domin da farko likita ya dauka ko hawan jini ne domin shi ya fi yiwa mutum haka, sai dai ya auna ba awo daya ba be ga hawan jinin ba.
SIRLEEM POV.
Driving yake hawaye na sauko masa kamar ba gobe, ko a lokacin da ya rasa mahaifinsa be yi zubar hawaye masu zafi kamar yanzu ba, domin a yanzu yana ganin idan Hajiya ta mutu shi ne sila, domin be taba ganinta a hali makamancin wannan ba, be taba tunanin abun zai taba ta har haka ba.
“Hajiya dan Allah ki yafe min”
Ya fadi haka yana tukin ya fi a kirga, jikinsa sai rawa yake, kukan da yake ya saka zuciyarsa sai zafi take, kuka yake bana wasa ba, kuka irin na mace hawaye sun sama sa'ar lalata masa fuska, sai da ya iso gidan Momy sannan ya ciri tissue ya goge fuskarsa, rabonsa da gidan tun jiya da ya shiga ya ga Falmata sai dai be yi maganar komai da ita ba